Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 12

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 12

.....I only want you, as long as she is sure that I don't have a problem knowing who you are or what your job is until the end of my breath". A heavy weight.....haisam felt very heavy on his heart. Oh God.....what kind of trust and loyalty is this?, what kind of love is this?. Oh lord, don't give him the power to hurt the sultan or contradict his opinion. He couldn't say anything to him. "D'ana ahmad?" He looked at him with some emotions. "He's alive, he's not dead." "Where is Muhammad?" He asked, "Ahmad is alive".

Standalone post1,962 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 12*

Wani irin shuru da ya wanzu saboda idanu kawai da sultane ya zubawa haisam. Yana zaton zaiji tsoro ko wata fargaba amma game da maganar haisam da tazo ba zato ba tsammani......yana zaton zaiji wani tashin hankali ya sauko masa amma ba wani sauyi da yaji.

"Na sani......na sani muhammad,koa hankalce bakayi kama da malamin nan ba.....malamin da baida aikin yi,malamin dake komai kara zube ba,na karanceka kafin jawoka jikina.....na karanceka sosai kafin na sanyaka tsakiyar ahalina.....amma ban sani ba,na karanceka gaba daya ne ko bai karanci komai daga kai din waye ba". Yayi maganan da wani iri laushi da hope sosai a muryarsa ba.

"Baka karantani duka ba.....saidai ina me baka albishir ba zakayi nadaman sakani amana cikin ahalinka ba......ba wannan ne abu mafi muhimmanci ba sultane......aikina ya ratsa ta wani bigire.....aikina ya biyo takan wani muhimmin abu cikin rayuwarka".

"Ban damu ba muhammad.......ban damu ba,nagartarka kawai nakeso,muddin ta tabbata bani da matsalar sanin waye kai ko meye aikinka har qarshen numfashi na". Wani nauyi.....nauyi haisam yaji sosai saman zuciyarsa. Ya Allah.....wanne irin yarda da aminci ne wannan?,wacce irin qauna ce wannan?. Ya rabb,kada ya bashi ikon cutar da sultane ko sabawa zatonsa.

"Wanne abune haisam?.....sanar dani" Sultane ya fada yana gyara zamansa.

"D'anka.....d'an ahmad" Idanu sultane ya zuba masa ya kasa cewa komai.

"D'ana ahmad?,d'a kuma jinin farko na safeena da muhammad hammud?" Kai haisam ya jinjina masa yana kallon yadda wasu emotions ke tasiri a tattare dashi.

"Shi......yana raye,bai mutu ba". Wani irin abu sultane yaji ya doka tsakiyar kansa,sai ya dinga jin maganar haisam tana amsa kuwwa a kunnensa.

"Yana nan a raye,lafiya qalau" Ya sake fadi don ya bawa sultane qwarin gwiwar tambayarsa ko sau daya ne.

"Yana ina muhammad?,ahmad fa?,ba irin neman da bamu masa ba,ahmad hatta da safeena duk da zurfin haqurinta ta saddaqar ta rasashi....ahmad dai?" Ya tambaya cike da shakku.

"Ahmad yana raye.....ubangiji yaga dama ya raya abinsa". Yayi furucin a tausashe.

Zumbur yaga sultane ya miqe,ya kama hannuwan haisam sosai cikin nasa yana duban idanun haisam din da nasa idanun,idanuwan da suka cika sosai da ruwan hawayen da jarumta irin nasa ya hana musu kowanne tasiri.

"Ya girma ko?,yayi hankali haisam?,kaini na ganshi,kaini naga ahmad,inama ace safeena tana raye?"

Wani irin tausayinsa me narkar da zuciya ne ya saukarwa haisam,sai ya kama hannuwansa shima,yayi taku uku ya matsa dab da sultane din don bashi kafadar da zai jingina ya samu sassauci.

Kamar yasan me manufar haisam kuwa,sai ya rungume kafadar haisam yana sauke wani irin numfashi,wani numfashi me tsananin nauyin dake bayyana girman tsananin da zuciyarsa ke cikin tsahon shekarun.

Ya tabbatar inda gama garin namiji ne sultane din kuka zai fashe dashi. Ashe duka shekarun nan yana rayuwar kawai,yana maida komai ba komai ba?,amma akwai ciwon rashin ahmad din tattare dashi.

Yadda yaji jikinsa ya fara kyarma sai ya kamashi a nutse ya zaunar dashi,don yasan zuwa yanzu abinda ya bawa me wada ya dinga shayar dashi ya ratsa jikinsa sosai.

"Akwai shaidu ga gwajin qwayoyin halitta.....bari na gabatar maka dasu" Caraf yaji sultane din dake ajiye wani irin numfashi ya riqe hannunsa

"Ba buqata haisam.....na tabbatar yadda akhnan ba zatamin qarya ba,ba zata cutar dani ba hakazalika kaima". Maganan ya sanyashi dakatawa daga warware takardun yana duban sultane da girman yadda da amincewar da yayi masa.

*M A M M I N A*

Ji da ganin komai take kamar a mafarki,an aurar da falaak ana shagulgula dukka cikin gidan ita bata sani ba?

Wai yaushe?,yaushe haka ta faru?,yaushe tayi wannan baccin?,yaushe tayi sake haka..yaushe al'amura suka fara mata sako sako?.

"Bai kamata kici gaba da zama ba komai yana zamewa daga hannunki......bai kamata ki zauna har sai an gane akwai wata babbar barazana data tunkaroki ba". Ta fadawa kanta da kanta,abinda ya bata qwarin gwiwar miqewa,saidai kuma tana miqewar ta koma ta zauna saboda wata bahaguwar faduwar gaba daya ziyarceta.

Tunawa tayi a yanzu kamar bata da kowa......ba wani da zatace ya rage mata idan ka dauke tamim qarami.....ba tamim babba,ba babban tamim dukka,salihi.......naziru....bashir.....lawan.....ashiru.....dahiru......rabi'u.....labaran......kanzu.....dan tala.......habu dukkaninsu bata da masaniyar ina suke?. Qasqantattun bayinta da ba wanda yasan girman kusancin dake tsakaninsu sai ita. Yan shige da ficenta masu mata kowanne aiki hankali kwance.

Abinda yafi bata mamaki bataga kowa yayi noticing bacewarsu ba,ba wanda taji yayi cigiyarsu,wannan ya dasa mata tsoro tayi magana akai. Tayi magana a kansu tace me?,tace sun b'ata?,me yasa ba wanda ya gani sai ita?.

Motsawa tayi tafisu tana fado mata a rai,ta sake juyawa tana qwalawa hadimarta kira.

"Ki shaidawa tafisu ina buqatar ganinta a yanzu yanzu".

" An gama" Ta fada tana miqewa cikin qasan ranta tana gulmar mammina din.

Sumammakin data dinga yi a jiya tamkar me cutar farfadiya.......kamar wadda bugun jinnu suka kama,sai gashi daga tsakanin jiya zuwa yau din ta wani fede tayi fayau da wata irin ajiyayyar rama.

Ta zurfafa tunani tana lissafin jimawar tafisu kafin taji sallamar tafisun. Kai ta daga tana dubanta yadda take takowa da wani rashin kuzari,kafin ta qaraso gabanta ta zube kaman yadda ta saba tana gaidata.

Batabi takan gaisuwarta ba......sai magana data fara cikin izzar nan tata.

"Wanne sabon salon tsari ne kika ajiyewa kanki?,yin nesa dani a sanda yafi cancanta ace kina kusa dani?". Kai kawai tafisu ke mirginawa.

" Allah ya huci zuciyarki ranki ya dade,na shiga wata dimuwa ne kan abinda ya sameki a jiya,abinda har yakai ga rikicewar cikina na barke da zawo,dole.na kasance a shiyyata kusa da bayan gida". Shuru tayi tana kallonta,kafin taja numfashi.

"Ko meye ya faru dake.....bana buqatar wannan nisan.....inason a shirya komai,kyaututtuka na alfarma da bajinta,inason na shiga hidimar bikin gidan nan ayi komai dani,a waremin suturar alfarmar da zanyi amfani da ita" Shuru kadan tafisu tayi kafin ta amsa da "To ranki ya dade" Sannan ta yunqura tana miqewa kamar wadda bata da cikakkiyar laka a jikinta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Inda giwa zataji......inda giwa zata aminta da ta yarda taci gaba da zamanta kawai a shiyyarta. Iya yadda tayi muzu muzu kawai zata zama wata ayar tambaya ta daban a kanta a idanuwan al'umma,wanda duk yadda takai ga yin ado da kwalliya don ta boye ta sani ba abu bane da zai iya boyuwa ba.

*A K H N A N*

Juyi kawai takeyi cikin bargon tun da ta bude idanuwanta daga bacci har kawo yanzu da azahar ta gota ake kuma shirin gudanar da yininsu na al'ada wanda aka yishi akan wani tsari me kama da zamani zamani.

Babbar makeken filin dake qarshen gidanne,morsa safiyya ta sanya aka qawatashi da dukkan wani ado me daukan hankali nutsuwa da kuma dacewa.

Tana daga dakin a kwance,amma tana ji a jikinta taron yau yafi na jiya,saboda yawan hayaniya da takeji daga can sasanni daban daban na gidan.

Idanunta ta sake maidawa ta lumshesu,bata kuma budesu ba,batasani ba ba kuma zatace ga taqamaime ko ainihin abinda yake damunta ba.

Abu daya zata iya dorarwa.....tana jin wani d'an baci bacin rai a tattare da ita,musamman idan ta lumshe idanunta ta hangi sanda ya zubawa wayarsa idanu ba tare daya damu da kallonta ba. Ita din dai da ya kwashe kwanaki hudu zuwa biyar bai ganta ba.....bai nemeta ba,ya dawo kuma baice gashi ya dawo ba....... Abu na biyu wani irin fayau take jin zuciyarta,tamkar dai akwai wani abu me girma da aka cire da yabar mata fili har haka. Qamshin nan na jiya,shine har yau yake mata yawo a hanci,duk kuwa da cewa tayi nesa da dukkan rigunan nasa guda biyun gaba daya.

Hairaan ce tayi sallama gami da turo qofar dakin gaba daya tana shigowa,idanunta akan akhnan,bayanta kuma shehnaz ce rungume da wasu kaya da akhnan batasan na meye ba. Waya take amsawa,amma itama akhnan din take kalla.

"Biftu.....lafiya dai ko?" Ta tambayeta cikin nuna kulawa. Sai data aza idanunta akan shehnaz sannan ta soma ture duvet din tana qoqarin zama. Batason ta nuna duk wani weakness dinta,saboda tasan muddin shehnaz zata gani ta banu ta lalace.

Jiya da qyar ta barta ta runtsa,tunda ta shigo dakin wanda a nan ranar shehnaz taga daman kwana ta hanata sakat. Motsi kadan sai tace.

"Wallahi qamshin turaren sheikh Muhammad nakeji" Ta sanyata dukka ta tsargi kanta,yayin da taji ta fara kaiwa bango da yadda take maimaita qamshin turaren haisam din. Wanne irin sani ta yiwa qamshinsa?,a ina tayi masa wannan kyakkyawan sanin data dameta da maganar qamshin turarensa?.

Sanda ta fito daga sauya jiqaqqun kayan jikinta tana ware gashinta yasha iska shehnaz ta sake maimaitawa a karo na babu adadi.

"Wannan turaren na shiekh.....basan daga wacce aljannar aka sauko masa dashi ba.....ko yaya yake sai ya nun......"

"Shehi!" Ta fada da siririyar muryarta wadda ke tsike da maganganun shehnaz din.

"Ni ko ke wani zai iya fita ya barwa daya dakin nan ya kwana shi kadai?".

"Daga ni har ke ba wanda zai barwa wani dakin nan......wai kwana nawa nema ya rage tsakani biftu?.....saura kwana kadan kwananki ya qare a agadez fa". Maganan ya doketa sosai,don sai a sannan ma abubuwa da yawa suka dawo mata. Ta watsawa shehnaz harara.

"Waye yace miki zan tabbata ne a can?,inbar sultane in bar sahel couture?" Dariya sosai shehnaz ta dinga yi.

"Kinga idan zaki shirya gwara ki shirya fa.....sai yadda kawai ta yiwu,sai abinda mijinki yace".

" Mijinki" Kalmar ta dinga maimaituwa cikin kanta. Wannan maganan da sukayi da shehnaz,da kuma wannan mayen qamshin da wanka ma bai hanata jinsa a hancinta ba su suka hadu suka nuqurqusa karsashinta.

"Idan ya dawo.....me yasa bai nemeni ba?" Ta tambayi kanta da kanta yafi sau shurin masaki.

"Birra tace baki fadi me dame kike buqatar a shirya miki ba.....me yasa?" Hairaan ta tambayi akhnan din tana dubanta.

Duban hairaan kawai tayi,don ita ta manta ma da batun wani hada kaya,tafiyan ce wai da gaske?.

"Komai ma.....kawai komai ma da zata iya" Ta amsawa hairaan tana sauke qafafunta qasa.

"Shehnaz ki taimakawa birra ku hada abinda ya dace" Hairaan ta fada tana jawo jakar da tasa aka shigo da ita dazu tana nufar qofar fita.

"Ta zama ta zama.....aure ibada" Shehnaz ta fara rera waqar da akhnan ta tabbatar idan ta biye mata rigima zasuyi,kawai sai taji kewar AISA ta kamata.

Tunda AISA din ta tafi basuyi waya ba.....sannan duk wannan hidimar da ake ko daya bata kirata ba bare ta samu daman zuwa taron. Shin meye ya tsare AISA din?.

_oho......muma bamu sani ba......amma dai.....muje zuwa_

Cikin abinda ya rage mata tasaki kuka ganin yadda qamshinsa da tunaninsa ke maqale a zuciyarta lokaci bayan lokaci kadanne. Ta lumshe idanunta ta kira sunan Allah har batasan adadi ba.

Guri ne da aka masa wani irin tsari,taro ne na manya,manyan mutane dama matan masu hannu da shuni da kuma fada a ji daga agadez da wajenta.

Kai kana kallon gurin basai an gaya maka ba zakasan cewa taro ne masu hankali aji da kuma taqama da mulki da tarin dukiya.

Ba kide kide.....ba maza ko daya,daga masu daukan hoto har masu serving abinci ga mutanen dake zazzaune saman carpet carpet na alfarma dake gurin duka mata ne.

Duk da yawan al'ummar amma ba cikowa ba hargowa,wadatacciyar iska ke kadawa a gurin wadda hadarin daya hado ya baje zuwa sanyi ya bada gudunmawa me kyau wajen daidaitar yanayin gurin.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽