
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 4
...., tears filled my eyes. I have cried in private this week. One day when I came home from school, I found her in the living room. I approached her carefully and said, "Mommy, my perfume has run out, my body has also started to smell... She just turned around and said, "Are you taking yourself off your feet right now?" You look like a cow, but you feel like a perfect girl. As if cold water had been poured on me, I stopped. I couldn't move. I was shocked. However, I said, "Forgive me if I make a mistake." I went back to my room in pain. The next day, dinner was eaten, but I was not called. I was silent, until I went and told her that Momy didn't call me... She looked at me with a kind of look and said, You don't know the kitchen. Do you know if I will install it for you? I bowed down and apologized. I said that even if I have sinned against her, she has forgiven me. But then she went too far, she turned around and said, Get yourself in this house! It is my husband's house, not yours. And if you said that you would speak to me in front of Abba, then I will ask you on purpose. We are currently in the middle of exams at school. God is the witness, I am just writing, not because I re
SHAFI NA HUDU
Idan zan gaya muku irin wahalar da nasha cikin yan kwanakin nan, wallahi sai kun tausaya min. Aiki ne kawai nake yi babu hutu.
Gashi kuma momy ta sanar da yaya Abbas cewa kada ya kawo yar aiki. Ta ce wai ta bayar da cigiyar mai aiki.. Na sani, ba da gaske take ba.
Abin mamaki kuwa, duk sanda na dawo daga makaranta sai in tarar da gidan a hargitse. Da fari na dauka ko ba?i ke zuwa, amma daga baya na gane da gangan ake ?ata gidan domin in gyara.
Momy ta canza. A da kulawa da ?auna take nuna min. Amma yanzu sai ta taga Abba kafin ta nunamun kaunar. Hakan yana cutar da ni sosai, amma bana cewa komai. Sai zuciyata ke kuka.
Duk rana da na dawo daga boko, zan fara gyaran gida. Bayan haka in dafa girki, in fita islamiya. Da daddare bayan magariba nake dawowa gida. Duk da gajiya, sai na hau wanke-wanke da sauran ayyukan da ba za a rasa ba.
Ina tuna lokacin da momy ke cike da ?auna a kaina. Tana sona kamar ni ka?ai nake da ita a duniya. Amma yanzu? Idan na ga yadda take wulakantani, sai hawaye ya cika min ido. Na sha kuka a sirrance cikin makon nan.
Wata rana na dawo daga makaranta, na same ta a falo. Na tunkare ta a hankali nace, Momy turarena ya kare, jikina ma ya soma wari...
Sai kawai ta juya ta ce, Ai ke yanzu kina ?aukar kanki sa ar kowa ko? Ga ki kwaila ce amma kina jin kanki kamar cikakkiyar budurwa.
Kamar an zuba min ruwan sanyi haka na tsaya. Na kasa motsi. Na shiga shock. Duk da haka, na saki baki nace, Ki yafe min idan nayi kuskure. Na koma dakina cikin ?aci.
Washegari kuwa abincin dare aka ci, amma ba a kirani ba. Na yi shiru, har na je na ce mata Momy ba a kirani ba...
Ta kalle ni da wani irin kallo tace, Ke ai kin san kitchen din. Koni zan girka miki?
Na dur?usa na bata hakuri. Na ce ko laifi nayi mata, ta yafe min. Amma sai ta wuce gona da iri, ta juyo tace
Ki kama kanki a nan gidan! Gidan mijina ne, ba naki ba. Kuma idan kika ce zaki yi min magana gaban Abba, sai na sa?a miki da gangan.
Yanzu haka muna tsakiyar jarrabawa a makaranta. Allah ne shaida, kawai rubutu nake yi, ba don nayi karantu sosai ba. Yaushe zan samu lokacin karatu ne, jikina gaba ?aya gajiya ne gajiya da bautar Momee.
Da ace tana da sau?in kai , da ba za ta bar ni ba har na zama mai wanke mata pant da bra dinta da kaina. Amma yanzu kuma sai naji wai tana gaya wa Abba cewa ciwon hannu ne ke hana ta wankewa. Ashe dai ni ce zan ci gaba da wanke mata komai.
A wannan satin, sai gashi naji Mumy na waya da Yaya Billy. Har kusan makonni biyu kenan ba ta dawo gida ba. Da farko ban san dalili ba, sai dai da safe sai naji Mumy tana cewa a waya
"Ai Dady As ad ne ya ?aga tafiyar, sai gobe zasuzo tare.
Mumy tana ?arfafa ya Billy
"Ki dai ci kwalliya sosai. Ki cakare, kin ji?"
Araina nace, ai ba sai an fa?a wa Yaya Billy tayi kwalliya ba. Ko yaushe haka take kamar aljana wadda bata taba gajiya ba. Shafe-shafen fuska da hoda,jambaki.
Amma fa, bana fahimtar dalilin da ya sa Mumy take hura mata wuta haka sai na kauda kai, na cigaba da sabgogina. Allah ne ka?ai yasan bana jin da?in jin zata dawo. Wallahi har cikin raina bana sha awar ganin ta koma cikin gidan nan.
Na san idan ta dawo, azaba ce zata karu gareni. Na yi shekaru ina mata aiki kamar yar aikinta daga ?ebo mata ruwa, share daki, gyara kayanta, hatta jakar kwalliyarta idan ta fita, ni ke ?auka. A gabanta, bani da wani daraja, kuma ba abinda nake yi ya gamsar da ita. Amma fa duk da wannan halin nata komai auta komai auta.
Yau Juma a. Saboda haka, da wuri muka tashi daga makaranta, kuma bamu da islamiyya. Tun safe na tashi na gyara gidan, na shirya cikin kayan makaranta. Na je na gaida Abba, ya amsa da murmushi yana addu a kamar yadda kullum yake yi. Bayan ya kare nasiha, na ?auki jakata muka huce makaranta.
Kasancewar jarabawa muke yi, da zaran mun shiga ajin ake farawa. Bayan mun gama, muka fita waje. Kawayena suka fara hira kala-kala. A yawanci zancen samari suke yi ni dai shiru nake.
Sai Fatima, kawata, ta matsa kusa dani tana dariya. Tana ri?e da wani kwali. Tana cewa, Kalli wannan. Na kalle shi an rubuta a jikin kwalin Dwell Weight Gain Capsule. Na ?ago mata kai da tambaya a idona.
Sai tace, Jiya nasiya. Magani ne na ?ara kiba. Ramlah, kema ki kar?a ki fara sha. Bakiga yanmatan ajin nan ba? Kowacce da nonowa da hips. Suna yi mana wani irin gayu. Amma mu kamar muciya...
Na yi dariya, amma zuciyata cike da tunani. Gaskiya ne, ramar nan ta dameni sosai. Ina son in ga jiki na ya ?an cika. Ko dan in daina zama abin dariya a idon wasu.
Na kar?a daga hannunta, ina tambayarta yadda ake sha. Ta bani bayani da fara a. Na ji da?i sosai. Na saka a jakata, muka tashi muka kama hanyar gida.
Kwana uku kenan da na fara shan maganin ?ara kiba. Babu wanda ya sani a gida. Ko Fatima da ta bani maganin, bata tambaye ni ko na fara ba. Na yanke shawarar sai na fara ganin canji a jikina tukunna zan sanar da'ita.
A cikin wa?annan kwanaki uku, abinda na fi lura da shi shi ne yadda yunwa ta ?i barina. Kullum cikin ci nake. Da safe, da rana, da dare sai na ci abinci kamar jaka. Har ita kanta momy ta fara zargina.
Ranar Laraba da rana, bayan na ci shinkafa da miya da gasasshen kifi, na ?auki garin kunu da aka rage jiya, na zuba a kofi, na zuba sugar sosai, na sha gaba ?aya. Sai na tashi na ?auko biskit guda biyu na ci.
Momy tana zaune a falo tana kallon labarai. Ta kalleni da mamaki, tace Ramlah lafiya kuwa? Kwana uku kenan kina ta cin abinci kamar wadda ake tura. Ko mai sabon ciki ?
Na ?an yi dariya da ?yar nace A a momy, kawai yunwa ce fa. Nima ban san me yake damuna ba, amma ina jin ci kawai.
Ta zuba min ido kamar tana nazarina. Amma ta kame. Sai tace Kar ki je kina janyo ciwon ciki da kanki fa.
Na girgiza kai kawai, na bar falon. A zuciyata nace:Da sun san me ke faruwa da ni... ai da za su tsaya mamaki.
Kuma duk da yunwar da nake ji da abincin da nake ci, har yanzu bana jin canji sosai. Amma zuciyata cike take da fatan Ko da zai ?auki sati biyu, in dai zan cika kamar sauran yan mata, ni wallahi zan dage.
Na lula sosai gurin shan maganin. Kullum da safe, da dare, sai na ?auka in sha, kamar maganin ciwon zuciya. Ranar Juma ar nan, da na farka, na je gaban madubi sai naga fuskata ta kumbura. Kamar ba fuskata ba ce. Hankalina ya ?an tashi, amma saboda yarinta da son ganin canji, sai kawai naji dadi.
Na matsa na kalli kirjina... ko su suma sun soma cika? Na dan bubbuga saman rigata da jin da?i. A zuciyata nace, Yanzu dai na fara zama mace.
Sai na ?auki maganin, na sha, na kuma sha afa ban daukeshi daga ?an gadona ba.
Da safe na shirya cikin rigar makaranta, na je na gaida Abba. Ya dube ni sosai sannan yace Ramlah, lafiya fuskarki ta kumbura haka?
Momy ma ta ?aga kai da sauri tace, Wai me ke damunki ne? Idan kin dawo daga makaranta zamu je asibiti.
Na ce musu, Ba komai, kawai yunwa ne jiya ban ci abinci da kyau ba. Sai na yi sallama na tafi.
Ban san cewa yau ce ranar da komai zai fallasu ba.
Momy na shiga dakina don duba wani abu, sai idonta ya sauka a jikin kwalin maganin. Tayi saurin ?agowa ta karanta. Da farko ta fara karantawa da siririyar murya, amma tana kai ?arshe sai hawayenta suka zubo. Ta fito da maganin hannunta tana fadin
Abba... ka duba wannan. Ka karanta ka gani da idanunka.
Abba ya kar?a, ya karanta shiru. Bayan yan dakiku sai ya kalli momy da murya mai nauyi yace
Na wanene wannan? Waye ke shan wannan maganin?
Momy ta share hawayenta tace, Daga dakinta na samo. Ashe ita ce take shan shi. Ita ce take kumbura. Tana shirin janyo mana bala i!
Abba ya sauke ajiyar zuciya, yana girgiza kai.
Abba na zaune, kwalin maganin a hannunsa. Ya na kallon rubutun da ke jikinsa, fuskar sa cike da alamar damuwa. Momy kuwa bata bari ya gama karantawa ba, ta fara zuba kalamai:
Abba, wallahi ban gane Ramlah yanzu ba. Kwana biyu kenan tana canzawa a idona, har na soma tsoro. Fuskar ta ta kumbura, jikinta yana sauyawa, ita kuma kamar ba ta lura da kanta ba.
Abba ya ?an ?ago kai da mamaki, bai ce komai ba.
Sai abin ya ta?a lafiyarta kenan tukunna za a dau mataki?
Ta matso kusa da shi, ta zauna da girmamawa, amma tana kuka. Tana cewa Wannan maganin da na gani a dakinta fa? Idan wani abu ya faru da ita fa? Ashe ni za a ce na cutar da ita.
Ta sake girgiza kai tana cewa, Wannan capsule ?in fa? Magunguna masu kara kiba ne da ke jawo cancer da cututtuka masu ha?ari. Yanzu ace ita yarinya karama tana sha... kuma a gidana?
Sai ta lumshe ido, hawaye na bin kuncinta Abba... da gaske nake... wallahi ni fa na rasa abin cewa. Da ace wani abu ya same ta, me za a ce? Ashe idan tayi rashin lafiya gobe, ba zan zama abin zargi ba? Kai kanka zaka iya cewa ina kallonta amma ban hanata ba Alhali bansan halin datake ciki ba.
Abba ya shiru, ya sauke ajiyar zuciya. Sai ya ce a hankali, Allah ya kyauta
Ba karamin zafi Abba ya ji ba, amma ba ya nuna komai a fili. Sai dai yana kallon Momy da kwalin maganin a hannunsa, kamar yana jiran jin karin zuga daga gare ta. Ita kuma, kamar ta jima da jiran wannan dama.
Ranar, kuwa Momy ta kama girki da kanta. Ta gyara falo, ta canza labule, ta zuba turaren wuta. Komai ta shirya kamar ba ita bace ta tayar da bala i da safe. Abba kuma da zarar ya gama Abunda yakeyi ya fice kasuwa shiru kamar ba komai ya faru ba.
Ni kuwa a makaranta, sai wani jin da?i nake ji a jikina. Ganin fuskata ta cika, jikina ya ?an cika, sai naji kamar nayi nasara. Nida Fatima muna ta dariya, tana cewa
Wallahi Ramlah, ki gani fa yanzu. In muka gama wannan kwalin, zamu sayi wani daban sai mu zama kamar yan Instagram.
Na kyaleta da dariya. A zuciyata nace Kowa yasan me yake nema, ai da kyau ake bi ana shiga gaban mutane.
Yayin da muka tashi daga makaranta, muka fito, muka same Malam Idi direban mota. Ya zuba min ido yace
Auta wannan kumburin naki... anya ba sanyi baniba?
Na fashe da dariya nace, Ko ?aya Malam Idi, kiba ce fa, ina jin dadin jikina yanzu. Shi ma ya kyalkyale da dariya yace, Allah ya kara lafiya.
Na dawo daga makaranta da yamma cikin gajiya, amma zuciyata cike da farinciki. Sai kallo nake yi wa jikina a madubi, ina murmushi. Na ji kamar wata sabuwar ni ima ce ta sauka a kaina.
Na ci abinci fiye da yadda nake ci na ha?a da kek da kunun tsamiya. Bayan isha i, na kwanta jikina cike da nauyi, amma zuciyata na motsi da da?in canji.
Ban san lokacin da na lumshe ido na fada bacci ba. Sai kawai na ji azaba kamar wuta ta fa?o min a baya!
Wata irin zafi ce ta farka da ni daga barci!
ZAAFFF!!!
Na yi ?ara, na bu?e ido cikin firgici. Idanuwana suka sauka a kan Abba. Tsaye yake da bulala a hannu, fuskarsa ta cika da fushi.
Ke Ramlah! Ashe guba kike sha kina boye mana?! Ashe kina neman mutuwa da kanki, a cikin gidana?
Na ce da murya mai rawa Abba dan Allah wallahi ban .
ZAAFFF!!! ZAAFF!!! ZAAFFF!!!
Ya sake zane ni ba tare da sauraro ba. Wata bulalar ta doki gefen ?irjina, wata ta shige min a bayana. Na zube a ?asa ina kukan da ban taba yi ba a rayuwata.
Sai kace ba ya ba! Sai kace na samo ki daga titi! Wato kina neman kiba har da shan magungunan banza da za su kashe ki kafin ki kai shekara ashirin?!
Na dur?usa da gwiwoyina, jikina na rawa, zuciyata kamar zata bar jikina. Na rarrafa zuwa gefe, amma kafin na isa gado sai na sake jin
ZAAFF!!!
"Abba don Allah!" Na ?walla. "Wallahi ban san me nake yi ba!"
Amma fushinsa bai daina ba. "Kin girma da wauta! Kin raina ilimi da tarbiyya! Sai kin illata kanki dan uwanki?!"
Na fara haki da gumi, numfashina yana rikicewa. Har na soma jin kamar zuciyata zata tsaya.
Wallahi yau sai kin sani, ya ce yana rarrafe a kaina da bulala.
Na yi ta jijjiga kaina, ina kuka, ina kokarin kare jikina da hannaye. Amma bulala sai karfi take kar?a.
A can sama, a ?akin Momy, tana jin komai. Amma shiru tayi. Maimakon ta sauko ko ta ce ya yi hakuri, sai dadi ya rufe zuciyarta. Ta ma juya gefen gado, tana cewa a ranta
Ai sai an koya mata hankali. Tana ganin zata yi min fintinkau? Tasaka dariya.
Ta rufe kunnen ta da bargo, ta lumshe ido da jin da?in azabar da Ramlah ke sha.
Ni kuwa, na dawo can ?asa cikin ?aki, hawaye sun goge fuskar da na ji kwana uku tana cika. Jikina duk yana rawa. Zuciyata na dukan da ban taba ji ba.
Abba ya zube bulalar ?asa a ?arshe, yana haki kamar mai gudu. Ya dubeni da idon da bai da?e da zafin bulala ba, amma har yanzu cike da takaici.
Abba ya tsaya bakin ?ofa, ya juyo ya kalle ni. Idonsa ya dan lafa daga fushi, amma yana dauke da alamar zafi a zuciyarsa. Ya numfasa da ?arfi, kamar yana kokarin danne fushin da bai ?are ba.
Ramlah, ya kira sunana da murya mai nauyi, zauna ki saurare ni da kunnuwan ki biyu.
Na gyara zama a ?asa, jikina yana rawa, hawaye kamar ruwan sama. Amma zuciyata tana bu?atar jin kalmarsa fiye da bulala.
Abba ya tako zuwa gabana. Ya zauna a gefen gadon, yana kallona kai tsaye. Kiba? Kina shan guba domin ki cika jiki? Ashe hakan ya fi miki muhimmanci fiye da lafiya?
Na dur?usa na ce da kuka Abba dan Allah... kayi hakuri. Wallahi na yi kuskure.
Ya ?an dafe kansa, ya girgiza shi, sannan yace
Maganin da kika sha kin san yana illata hanta? Kin san yana iya lalata ?oda? Kin san yana iya jawo ciwon da ba zaki warke ba? Kin san akwai mata da suka mutu sabodashi?
Na sa hannuna a baki, kukan ya ?ara tashi. Abba ya dafa kafa?ata, yace
Rayuwa ba ado ba ce kawai, Ramlah. Kyau yana da rana, amma lafiyar ki... ita ce ke da daraja fiye da komai.
Ya cigaba cikin natsuwa Akwai masu kiba da basu da hankali. Akwai masu kyau da babu tarbiyya. Amma idan mace tana da ilimi, tausayi da kima ko tana da ?iba ko a'a kowa zai girmamata.
Na kalle shi cikin hawaye. Na ce da murya mai rauni Na gane Abba. Ka yafe min. Wallahi zan daina. Zan tuba.
Ya dafa gashina yace Na yafe miki, amma ki yafewa kanki. Ki zama sabuwa daga yau. Ki bar kowane abu da zai cutar da rayuwarki.
Na rungume ?afarsa da kuka, nace Na tuba Abba. Na gode. Na gode da ka tsawatar min. Allah ya saka da alheri.
Abba ya mi?e, ya ?auki kwalin maganin daga inda ya jefar. Yana kallonsa da ha?uri yace
Yanzu zan zubar da wannan. Sannan gobe da safe, za mu je asibiti. A duba ki. A tabbatar komai lafiya.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH