Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 11

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 11

.......some kind of closeness that is in every mouth that can air to her nose, pass through her nose and shoot the message to her skull. She was just feeling that she was melting again.......now what she was feeling was not just fear, it was some kind of strong influence. He was saying the words in a low voice...... he was talking with her ears and she felt as if the world was slowly spinning around her, or something heavy was taken and placed between her palms and her heart muscle. He bit his lips gently, the warmth of her body was passing through every part of his body... a kind of change was very close to him, he pulled her a little from his body, and he crouched down and took her cloth that was left on the ground and separated it very much. He raised his long hands above her head and began to cover her without looking at her face. "This is intentional...it's not a special place like that" He finished saying, taking two steps back and leaving a distance between them. Slowly, with a kind of feeling and weight, she put her hand and gathered the cloth to hold it between her palms, then she raised her eyes slowly and put it on his face. Today, she only sees the man of the hippodrome

Standalone post1,845 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 11*

Wani irin shuru ne ya ratsa a tsakaninsu,wani irin tsoro yake gani tattare da ita. Basu gushe ba tana cikin jikinsa suna musayar bugun zukatan junansu da kuma qamshin turarensu daya cakude guri guda ya bada wani sassanyan qamshi me narka zuciya. Yana jin yadda zuciyarta ke dokawa sosai,sai ya lumshe idanunsa a hankali yana mamakin tsananin tsoratar da tayi.

Hannunsa ya sake miqawa ya riqo qugunta da kyau saboda yadda yaji kaman tana neman sulalewa qasa. Ya fahimci har yanzu bata gama nutsuwa ba,ya daidaita tsahonta sosai a jikinsa,sai ya aza hannunsa a hankali saman gashinta yana shafawa daga gaban kanta har zuwa gadon bayanta da yabi ya kwanta lambas kamar ba nata ba.

"Relax......calm down.....nine......haisam ne" Ya fada da wata irin rarraunar murya da tayi wani irin sanyi kaman wanda magana takewa wahala. Yadda maganan ta sauka a kunnenta.......yadda qamshinsa a karon farko ya zama kusa da ita fiye da ko yaushe......wani irin kusa da ya zamana cikin kowacce shaqa da zata iya iska zuwa hancinta ta ratsa ta hunhunta ta kuma harba saqo zuwa kwanyarta. Ji takeyi kawai tana sake narkewa.......a yanzun abinda takeji ba tsoro bane zalla,wani irin tasiri ne me qarfin gaske. A sanda yake furta kalaman a jejjere......sanda yake maganar dan da kunnuwanta sai taji kaman duniyar tana juya mata a hankali,ko kuma an dauko wani abu me nauyi an azashi tsakanin tafi hannuwanta da tsokar zuciyarta.

Lips dinsa ya cije a hankali,dumin jikinta ke ratsa kowacce gaba ta jikinsa......wani irin sauyi yakeji sosai tattare dashi,sai ya janyeta kadan daga jikin nasa,ya kuma tsugunna yasa hannunsa ya dauki mayafinta dake yashe a qasa ya wareshi sosai. Dogayen hannayensa ya daga saman kanta ya soma rufawa ba tare daya kalli fuskarta ba.

"Ganganci ne wannan......ba guri bane kebantacce har haka ba" Ya qarasa fada yana yin taku biyu baya gami da bada tazara a tsakaninsu.

A hankali da wani irin yanayi da kuma nauyi ta sanya hannunta tana tattaro mayafin ya riqe gam tsakanin tafukan hannayenta,sai kuma ta daga idonta a hankali tana ajeshi saman fuskarsa.

A yauma mutumin hippodrome kawai take gani.....wannan me zagayayyun idanuwan masu nauyin gaske......idanuwan nan da suke da wani madaukakin tasiri a tattare da ita.....idanuwan da koda sau daya shape dinsu.....kyansu da yadda suke da wani irin zurfi basu taba bacewa dubanta ba.

Kamar wasa....kamar almara saita gaza jurewa ci gaba da dubansa,ta zare idanunta gefe tana jin yadda zuciyarta keta birkicewa cikin qirjinta.

Wani abu takeji can qasan zuciyarta.

"Ya dawo kenan?,tun yaushe?,me yasa bai nemeni ba?......bai kirani ko sau daya ba tunda ya tafi me yasa?" Ta samu kanta da jerowa kanta da kanta dukkanin tambayoyin da a tashin farko wani sashen na zuciyarta ke tuhumarta.

"Me yasa?......me yasa kika damu da dukka wannan?" Juya tuhumar kawai takeyi......juya tambayar takeyi cikin ranta tanason gano eh meye damuwanta?me yasa taji ba dadi.

"Muje?" Ya fada da wani yanayi me kama da tambaya wani sashen kuma cike maganar yake da umarnin da taji yakai mata har cikin kwanyarta.

Samun kanta tayi da daga qafafunta,a hankali ta juya tana saukesu da wani irin yanayi da har yanzu ya gaza barin jikinta. Batasan zai bita bane......sai jin takunsa tayi a hankali a bayanta.

A qasa yake sauke idanunsa......yana qoqarin kammale ganinsa guri guda,saidai bai bada wata tazara me yawa tsakaninsa shi da ita ba. A hankali yayyafi ya fara sauka,wani irin yayyafi daya taho da qarfinsa,abinda ya sanyashi daga kansa kenan yana zubeshi akan bayanta da take takawa da wani irin sanyi da nutsuwa. Ida har idanunsa sun gane masa daidai,idan har yana iya.ganin zahiri to kamar ta tattare jikinta ne ta cure guri daya.

Gabansu ya duba,akwai sauran taku kafin sukai ainihin qofar sashenta ta baya. Ya sani ya kuma gama fahimtarta,kamar batason ruwan sama ya tabata da alami,wannan yayyafin kuwa muddin yaci gaba da sauka da qarfi kamar haka ba abinda zai hana ta jiqe kafin su isa ko tayi damshi sosai.

A hankali ya saki cloak thobe dinsa ya kuma zareta daga hannunsa,sannan ya taka ba tare da saninta ba ya budata sosai yana aza mata ita saman kafadunta.

Har cikin qasusuwanta taji tsaiwarsa a bayanta. Har cikin b'argonta taji saukar cloak thobe din saman gangar jikinta,bata gama da wannan ba taji lallausan tafin hannunsa cikin nata yana qoqarin cusa mata gede da gefan rigar cikin hannuwanta gudun kada iska ya debeta ta fadi.

Tana jin sanda ya zame hannun nasa bayan yaji alamun ta riqe,wani irin lallausan tafin hannu da ko cikin 'yan uwanta mata bata tabajin irinsa ba.

Yana biye da ita tamkar wanda ke gadin wata tsadaddar kadara,dukkan dagawa da saukar fararen tas din qafafunta masu shige da nasa akan idanunsa ne,tanason waiwayawa ne......tanason juyawa ta kalli cikin idanunsa amma tana jin wani abu me nauyi kamar ba zata iya hakan ba.

Dab da bayanta ya zura hannu sanda suka isa personal qofanta ta baya.......bata sani ba,ba kuma zatace ba taga ya fidda keya ya zura ya murza ya kuma bude sannan ya turata ta bude. Bata sake jin motsinsa ba saidai tasan yana tsaye a gurin,zuciyarta na sake zugata.

"Kidan waiwaya ko sau daya ki kalleshi.....ki juya ki gani ko shurunsa ke yake bi da kallo". A wani irin sace ta saci kallonsa ta gefan idanunta,sai taga wayarsa ya fidda a aljihu yana latsawa,alamu kuna sun nuna gajeran saqo yake turawa.

Haka kawai taji wani iri.....haka kawai taji ba dadi. Bata taba satar kallon d'a namiji ba a rayuwarta,saidai ita a saci kallonta harma ta hukunta mutum,amma a yau wai itace ke satar kallon wani?. Waninma da ba ita yake kalla ba?,kallon wayarsa yafi kallonta muhimmanci?.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Sai data shige duka sannan ta juyo a hankali,ta kuma sake wayancewa da dora hannunta saman handle tanayi kamar zata rufe qofar. Wannan karon kuma kai tsaye ta zuba masa dukka blue eyes dinta,tanason tabbatarwa da gaske wayar tasa yake kalla har yanzu?.

Tabbacin kuwa ta samu,don yadda yake typing da sauri da sauri ya gaya mata wani saqon gaggawa ne zai aike. Sosai a yanzun taji ranta ya sosu fiye da dazun,sai kawai ta zabi rufe qofar wanda tana dab da hade gap don da yayi saura qofar ta qarasa kullewa ya daga kansa daga wayar,saidai bai samu daman ganin komai ba sai gefan fuskarta da blue eyes dinta guda daya.

Murza muqullin jiki tayi tana jin zuciyarta tana mata zafi,sannan ta juya a hankali tana sake riqe cloak thobe don cikin hannuwanta tana damqeta da kyau kamar wani zai qwace mata.

"Bai kula ba....bai damu ba?" Ta tambayi kanta tana jin ranta yana sake baci,saidai qamshin nan nasa da ya sanya takejin kamar yana dab da ita ya hana bacin ran nata yaci gaba.

A parlor din da yafi kama da harabar da zaka zauna jiran neman izinin ganinta direct daga bedroom dinta ta iske birra. Ta sani koda kowa zai tafi birra zata zauna.

Ta miqe tana nufota da zummar karbar cloake thobe din saman jikinta ta kuma taimaka mata ta sauya kayan jikinta,amma daga idanun da akhnan tayi tana duban birran da gane rigar waye a jikinta ya sanya birra janyewa da baya. Ganin birran ta fahimci abinda takeson fada kafin ta fadi,saita hadiye maganarta ta juya tana wucewa ciki.

Ta jima zaune da rigar jikinta tana kallon yadda ruwa ke zuba ta glass door din data ratsa bangon,kafin a hankali ta zameta daga kafadarta ta miqe don hadata da 'yar uwarta. Wancan rigar daya bata aro wancan karon bata maida masa ba......a yanzu ga wata ta qaru,saita hadesu guri daya tana zubasu cikin wata 'yar jaka. Har yanzun koda rigar farko ma bata daina qamshin da takeyi ba bare riga ta biyu.

*H A I S A M*

Samun tabbacin ta rufe qofar ya sanyashi maida wayar aljihunsa a hankali,ya juya a nutse yana takawa zuwa sassan sultane da yake iya hangowa dab da shi.

Tun daga qofan farko amintattun hadiman me martaba suke masa iso. Shiga shiga shiga yau sai gashi har qaramin parlor dake manne da bedroom dinsa,parlor din da daga shi sai matansa sai yaransa duk iya tsanin shaquwarka dashi batakai ka iso nan ba.

Da sallama ya shiga,duk da bai sameshi zaune a gurin ba,sai yayi tsaye yana goye da hannuwansa a qirjinsa yana qarewa parlor din kallo a nutse.

Mutum har mutum......mutum ma basarake,me jagorantar dubbai kuma miliyoyin al'umma,ya sarrafa ko wane lamari da sha'ani,amma ya wayi gari cikin juyawa da kuma makircin mace qwaya daya tal. Ya kwashi shekaru cikin duhu,cikin rashin sani da makanta me tarin yawa.

"Yaya zaka tsaya muhammad?,shin ka manta a muhallin mahaifinka kake?" Muryar sultane ya katse masa dogon nazarin da yakeyi.

Wannan murmushin......wannan murmushin mai cike da tarin nutsuwa ya sakar masa. Cikin girmamawa ya furta.

"Barka da fitowa".

"Barka kade Muhammad.......zauna" Sultane ya sake masa tayin zama sanda yake zama shima saman kujerar.

Cikin mutuntawa haisam ya bashi hannu sukayi musabaha me dan tsaho,sultane yana tambayarsa batun tafiyar.

"Tafiya ta kammala.....ta kuma zo da bayanai na abubuwa masu nauyi da girma" Sosai maganar ta sauka a zuciyar sultane cikin wani gurbi na zuciyarsa,sai yaji wani abu yana lullubeshi kasalarsa tana ninkuwa.

"Allah ya tabbatar da dukkan alkhairi" Ya fada haka kawai yana jin zuciyarsa tana laushi.

"Ameen ameen"

"Dukka hadimai sunyi nisa da gurin hidimarsu......akwai duk wani nau'in abu da kake buqata kaci ko kasha daga can" Murmushi haisam yayi kadan,ko yaya mutum me karamci yake sai ya nuna karamcin nan nasa.

"Alhamdulillah,godiya nake" Ya fadi yana sake nuna girmamawarsa a gareshi,shuru ya ratsa na wani dan lokaci,sultane yana jin wani nauyi yana jin akwai abinda ya kawo haisam din,akwai abinda haisam yakesonyin magana akai amma kuma shima ya gagara tambayarsa.

Gyaran muryar haisam taja hankalinsa.

"Allah ya taimakeka.....nace ayimin afuwa,na nema ganinka a lokacin daya kamata ace kana hutawa......Musamman kwana biyun da akace bakajin dadin jikinka". Murmushi yayi mai cike da dattako.

" A duk sanda d'a keson ganin ubansa daidai ne,hakan bazai zama laifi ba sam sam".

"Haka ne.....akwai wata gaskiya ce data jima tana boye......kuma yanzu lokacin boyewarta ya wuce" Yayi maganan a hankali yana duban sultane.

Sanyaya jikinsa yayi,zuciyarsa tana rawa kadan. Fatansa kawai Allah yasa ba wani mummunan abu bane.......fatansa kawai Allah yasa koma meye bai shafi aurensa da akhnan ba.

"Ina jinka muhammad" Ya fadi yana sallamawa cikin ransa.

"Ni ba malami bane kawai kamar yadda ka sani,kamar kuma yadda kowa yake kallona.......ina da wani aiki na daban da nakeyi tun daga qasata". Yakai maganan qarshe shuru yana maye gurbin dakin.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽