Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 3

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 3

...from the top of the wooden table of Indian Wood. The phone flashed the logo of his company SILIFAS Group, a company that manages jewelry, luxury houses and men's perfumes. His company Silifas is one of the biggest companies that attract the attention of buyers across the country. Every man who has enough, knows the perfume of slippers. He also knows that Asad Babangida's hand or blessing is a valuable person, with limits and honor. He went to sit in the main living room chair, where his assistants brought in papers and phones for him to look at. He looked at the clock. His two servants came in quietly, each wearing a shirt and turban, and bowed respectfully. "You're welcome, your slippers company in Lagos said they have completed the new goods you are waiting to import," said one of them. As he saw the hand, he understood, he didn't have to say anything. In Asad's case, talking is not a lot, but it is internal, looking and breathing. He took his special two-digit phone, which was designed as "AB-Exclusive", a type of phone that is given to people who are proud. He was looking and he saw the message from the oil company in Sokoto, they are looking for cooperation with one of the

Standalone post1,869 words

SHAFI NA UKU

A cikin wani katafaren gida da ke tsakiyar babban birni, gidan da gini guda ya fi kwatankwacin wani ?auye, wani mutum ne ya fito daga cikin toilet ?insa na alfarma. Bango na marmara ne mai she?i, bene na zinariya da fari mai haske, tagogi na gilashi masu ?aukar hasken rana, da madubai masu bayyana komai da kyan gani.

Shi ne As ad Babangida, ?an sarkin Zubairu. Mutum ne mai kamala da mazantaka, cikakken jarumi mai ?asaita. Shekarunsa kusan hamsin a duniya, amma kyawunsa da lafiyarsa na jikin samari ne. Jikinsa yana da lura da kulawa, fatarsa na she?i, ga murya mai ?aukar hankali, da tabbas a cikin tafiyarsa.

A lokacin da ya fito daga wanka yana ta share fuska da tawul ?in fata mai launin zinariya, mutum na iya gane cewa wannan bawan Allah ya taso a cikin ni ima da arziki. Daga nan ya nufi babban ?akinsa na kaya, wanda ke cike da rigunan Al?ebulan da turaren Dubai, agogo masu daraja, da takalma daga turai.

Ya zura jalabiyya mai nauyin zinariya, sannan ya ?auki wayarsa mai tsada daga saman table din katako na Itacen India. Wayar ta haska logon kamfanin sa na SILIFAS Group, kamfani da ke sarrafa kayan ado, gidajen alfarma da ?era turaren maza.

Kamfanin Silifas ?in nasa yana daya daga cikin manyan kamfanoni da ke jan hankalin masu ku?i a fadin ?asar. Duk wani namiji da ya ?oshi, to ya san turaren Silifas. Ya kuma san cewa daga hannu ko albarkacin As ad Babangida ne mutum mai kima, mai iyaka da daraja.

Ya tafi ya zauna a babban kujerar falo, inda masu taimakonsa suka shigo da takardu da wayoyi da zai duba. Ya duba agogo.

Hadimansa biyu suka shigo cikin natsuwa, kowanne sanye da shadda da rawani, suka dur?usa da girmamawa.

"Ranka ya da?e, kamfanin silifas ?inka na Legas sun ce sun kammala sabbin kaya da kake jiran shigo da su," in ji ?aya daga cikinsu.

As ad ya ?aga hannu alamar ya fahimta, ba sai ya ce komai ba. A wajen As ad, magana ba sai mai yawa ba isa na ciki ne, da kallo da numfashi.

Ya ?auki wayarsa mai lamba biyu ta musamman, wanda aka tsara da suna "AB-Exclusive", wata nau'in waya ce da ake yiwa mutane 'yan takama.

Yana dubawa, ya ga sakon daga kamfanin mai mai a Sokoto, suna neman ha?in gwiwa da wani daga cikin kamfanonin gine-gine mallakinsa AB Construction & Prestige Estate.

As ad ya lumshe ido. Wannan ba sabon abu bane a gare shi. Ko da yake ya gaji dukiya daga mahaifinsa, shi ya ninka ta sau goma bisa gogewa kasuwanci.

Bayan ya gama karanta sa?on, sai ya mi?e tsaye. Jikinsa yana she?i da lafiya, da karfi. Kallon da zaka masa ya isa ka fahimci cewa yana daga cikin manyan mutanen da kasa kiji dasu.

?ofar babban falo, wani dattijo mai murya da ?an kaifi yana jira shi.

"Ranka ya da?e, Masarautar Rano sun ce za su zo gobe da safe neman ha?in gwiwa akan gina sabuwar cibiyar kasuwanci da banki a yankin su."

As ad ya tsaya, ya ?an lumshe ido sannan ya ce da muryarsa mai sanyi amma mai ?auke da izza

"Ku amsa musu. Ku shirya tsare-tsaren da ya dace. In na ce zan shiga abu, to tilas ya ?auki martaba."

Dattijon ya rusuna, ya amsa da To, ranka ya da?e, sannan ya juya da sauri.

Bayan As ad Babangida ya kammala ganawa da masu shigowa , sai ga Sarauniyar gidan Hajiya Aisha ta bayyana cikin natsuwa da kamun kai. Ta shigo da sallama mai nauyin izza, wadda ta cika dakin da kwarjini. A jikinta ado ne na sarauta, tufafi masu kyan gani, da turare mai ?aukar zuciya. Kallon da ta masa ya bayyana girmamawa da kauna, kirarin da ta kwarara kuwa sai da ya sa zuciyarsa ta narke.

Shi kuwa yana zaune a babban kujerarsa da kamanni irin na manyan maza. Ya kalleta yana murmushi mai nauyi, wanda ba kowa ke samu ba. Hannunsa ya daga a alamar izini, ya nuna mata kujera kusa da shi.

Ta ?araso kamar sarauniya, ta zauna da girmamawa, ta ?an latsa ?asa da tafin hannunta kafin ta furta da nutsuwa Ranka ya da?e, dama ina so in ji batun tafiyarmu gobe. Yaran sun ce har yanzu baka basu amsa ba.

As ad ya ?an yi shiru, yana kallon gabansa, kamar mai tunanin manyan al amura. Daga bisani ya ce cikin murya mai ?arfi da nutsuwa Akwai tafiya.

Aisha ta saki addu ar albarka a gare shi, da harshen mace mai sanin girman mijinta. Ta ce Dama Bilkisu ce zata je gida gobe. Nace mata ta jira, mu tafi tare. Tana son ganawa da iyayenta.

Ya ?an jinjina kai cikin karfin hali, ya ce Tashirya. Da safe zan shiga garin, in ga mai martaba. Sai mu tafi tare.

Ta sunkuyar da kai cikin girmamawa, ta ce Na gode, ranka ya da?e. Ta mi?e da kyau, ta fita.

Shekaru kusan 45 kenan da As ad Babangida yake cikin aure. Matar sa ta farko ta rasu tun da wuri, ta bar masa ?a guda ?aya mai suna Umar. Umar yanzu gaba ?aya rayuwarsa yana yi ne a Dubai tare da iyalansa. Yana da kyau, yana da natsuwa, amma ya fi son zaman can fiye da dawowa gida.

Bayan mutuwar matarsa ta farko, As ad ya sake aure. Wannan matar kuwa ita ce Hajiya Aisha, mace kyakkyawa, mai aji, da nutsuwa. Yanzu haka tana da shekaru 37 a duniya, kuma tana da yara guda uku yan mata biyu. Daya daga cikin yan matan ta rigaya an daura mata aure. Ita kuma ?ayar tana nan a gabanta, suna kiranta da Nawal.

Nawal yarinya ce ta musamman sangartacciya ce da gata. Kyawu, tarbiyya da jin da?in rayuwa duk suna tare da ita. Kusan ba ka fiye ganinta a Najeriya ba, saboda tana cika zama ne a Dubai tare da yayanta Can ne ta fi so, can ne ke faranta mata rai.

Hajiya Aisha, matar As ad ta biyu, ce uwar gida. Ita ce mace mai hankali, mai cike da izza da daraja. Yar gayu ce ta gaske, wadda duk ta shiga za ka girmama ta. Bayan aurenta, As ad ya sake auren wasu mata har guda biyar, amma abun mamaki babu ko ?aya da ta ta?a haihuwa.

Ba sa jure zama da shi. Yana yiwuwa su zauna wata shida ko shekara daya, sai kowacce da kanta ta nemi saki. Wannan lamari ne da ya ba kowa mamaki, har ya sa As ad ya fasa neman karin aure, duk da cewa zuciyarsa na da bu?ata.

Wata rana yarinyar da ya aura a ?arshe mai suna Maryam, ta zauna da shi, ta ce

"Ka ji tsoron ?aukar hakkin yaran da ba su ji ba, ba su gani ba. Dan Allah ka zauna da matarka "

Kafin ma ta gama, maganar ta tsaya masa a zuciya. Wannan kalma ?aya ta sauya masa tunani. Ya fasa tunanin karin aure gaba ?aya.

Sai dai har yanzu babu wanda ya gane dalilin da yasa ba matarsa ?aya da ta da?e da shi. Wasu na cewa halinsa ne mutum ne mai ra ayin kansa da tsaurin hali. Ko da yake, mutum ne mai ibada da addu a sosai, amma idan ya ce abu, sai Allah ne ka?ai zai iya sa ya canza.

Aisha kuwa, duk da cewar ta fi kowacce mace samun daraja a gidan, akwai abu ?aya da ta kasa samu daga As ad mulkinsa. Duk yadda ta ?o?arta ta mallake shi, ta janyo hankalinsa, ko da ta hanyar ?auna ne ko magana mai taushi, As ad bai sauka a karkashinta ba.

Sai dai ita Hajiya Aisha ta san inda zata taka. Ta san yadda ake tafiyar da namiji mai taurin kai. Da hankali da ha?uri, da kishi, da maganar mace mai wayo, ta kasance ita ke ri?e da gidan da komai ke gudana kamar yadda take so.

Rayuwar cikin gidan As ad Babangida cike take da sirrika da ru?ani, amma a tsakiyarta, ita ce ta fi kowa shahara. Ita ce matar da ta fi iya jure halinsa. Ita ce ginshi?in gidan.

Daga babban shashen mijinta, Hajiya Aisha ta nufi nata sashen wani ?angare na gidan da ke nuna sarauta da jin da?in rayuwa. Falo ne mai girma, cike da kayan alatu daga ?asashen waje, fitilun gilashi suna haskawa cikin shudi da zinariya, sannu a hankali AC ke busar iska mai ?an?ano da ?umi.

Ta shigo tana tafiya da kwarjini kamar sarauniyar gida, sai kamshin turarenta ya cika wajen. Ta tarar da Nawal zaune a kan kujera tana danna wayarta, ana mata tausa da mai ruwan sanyi. Daga gefenta kuma Bilkisu ke kallo Korean film ke tashi a giant screen ?in plasma TV, wanda ke manne da bangon da aka lullu?e da fatun fata.

Ta tsaya tana kallonsu, sannan da muryarta mai natsuwa da iko ta ce Bilkisu, ki shirya. Inji Habibie, gobe da safe zai shiga garin, zai tafi dake.

Bilkisu ta kalleta cikin girmamawa, sannan ta ce To, mamah.

Nawal kuwa ta ?an turo baki, ta kalli yar uwarta da ?uruciyar shagwa?a. Yanzu sis, kina nufin ba zaki bimu ba? Please mana

Bilkisu ta ?an murmusa, ta ce cikin taushi Ki yi ha?uri sis, next time. I really want to see my parents.

Hajiya Aisha dai ba ta ce komai ba. Sai zuciyarta ta ji wata ?igon bakin ciki, musamman da jin cewa Habibie zai tafi tare da Bilkisu. Anya kuwa zata fasa tafiyarta ta Paris da ta shirya makonni? Sai kuma ta sake ta. Wata dariya ta su?uce mata tana fadin cikin zuciya:

Itama ai ba zata fara ba. Tasan wacece ni.

Ta juya da fara arta mai ?aukar hankali, ta bar su cikin dakin, sai kamshin turarenta da sautin takalminta suka rage.

Bayan ta bar falon da 'ya'yan suke, Hajiya Aisha ta shiga ?aya daga cikin dakunan nata na sirri wuri ne na musamman da ba kowa ke da damar shiga ba. Daki ne mai fadi, an kawata shi da madubai masu haske, fitilun kwali, da kwalabe masu launi na kayan mata daga ?asashen waje.

Ta nufi wajen da take ajiye kayan mata na gyaran jiki, tsumi, turare da hadin gargajiya. Tana tafiya a hankali, tana tsiyaya a zuciyarta. Daya daga cikin kwanukan matsinta ta ?auko, ta dora shi gabanta a kan faifan , sannan ta zauna, ta kwantar da hankalinta.

Cikin nutsuwa da kwarewa, ta shiga shan hadin tsumi, tana shafawa jikinta da tsari da salo irin na mata masu gata. Wannan ba shan kaya bane, wannan kula da martaba ce.

Tana kallon fuskarta a madubi, ta dan yi ajiyar zuciya. Bata jin dadin yadda take mu'amala da Habibie kwanan nan. Ko da yake tana da daraja a idanunsa, amma yana yawan kau da kai daga kusa da ita. Tana jin magungunan da take amfani da su, da hadin da take turawa jikinta, kamar suna ?ara nisantar da shi ba tare da dalili ba.

Shin ko ya gaji da ni? Ko akwai wata can da ke jawo masa hankali? Zuciyarta ta tambaya, amma ta goge tambayar da murmushin mace mai karfin zuciya. Ta dora turaren kwalliya a gefe, ta furta a hankali

Ba zan ja da wata ba, sai dai ta gaji da kallo. Ni ?adaice matarsa.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH