
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 10
..... not until he said bismillah and moistened the water and put the cup down. "Everybody should not hold some things" "It's a picture.....a tree" Omar mumbled to Amjad who was closest to him, Amjad was surprised by Haisam and killed him and couldn't speak. Sam Omar forgot his manners......some kind of sharp hearing for him, he didn't know what Haisam heard when he answered with a stick and he was about to leave. "I don't used to share what I own with anyone...everything that he owns will stay in my borders until the stick stops responding to this name". He listens to them.....he listens to their speech and everything about them, he is sure that if he was living among them, they would almost eat him. A little smile appeared on him, his smile itself does not know where it came from....... he just remembers how he showed it. He himself will not respond to what he has done, he will not respond to what has made him react, he only knows one thing, he will not be at peace until he gets the confirmation of his servant, even though he does not blame or blame the servant. "What is that? Jealousy?...." He heard the question come to him. His head shook slowly, leaning his elbows on the hood
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 10*
Kallon kallo aka fara yi tsakaninsi,banda naseeb daya fuske. Har cikin zuciyarsa baiga laifin haisam ba.....ballantana haisam din da tun da can sunsan halinsa. Sarai ba wanda ban sanshi ba akan kishi,diya mace kadai wadda bai hada alaqar komai da ita ba kishinta yake ballantana wannan da igiyar aure ta gilma tsakaninsu koda ba soyayya?. Mutumin da kishinsa ya hanashi yayi soyayya da kowacce mace?. Saboda bazai so ba kuma sannna ya sakarwa wani?. Shi a karan kansa kallon haisam yake da yake fadin auren Akhnan tsani ne kawai zai zame masa.......amma ya sani,wani aure ne da Allah kadai yasan yaushe zai qare.......ga alamu nan kuma shi da kansa yana barwa kansa da kansa ba tare ma da yasan me yake aikatawa ba.
"Da alama hoton dai yana da muhimmanci sosai". Khadeem ya fadi wanda idan bai tsokani haisam ba tun da can dama shi baya jin dadi.
Ya jishi sarai,ya kuma fahimci inda ya dosa,amma sai yayi banza dashi,bai bashi amsa ba har sai da yayi bismillah ya dansha ruwan ya ajiye cup din.
"Ba kowane ya kamata ya riqe wasu abubuwa ba"
"Bafa hoton bane.....itace" Omar yayi gulmar da amjad da yafi kusa dashi,amjad din da mamakin haisam duka ya kasheshi ya kasa magana.
Sam omar ya manta dabi'arsa......wani irin kaifin ji gareshi,bai kuma san haisam din yaji ba sai sanda ya bashi amsa sanda yake dab da fita.
"Ban saba raba abinda na mallaka ba da kowa......komai da yake mallakata zai zauna a iyakokina har sai sanda ya daina amsa wannan sunan".
Yana jinsu.....yana jin kakacinsu da komai nasu,ya tabbatar idan da yana zaune a cikinsu sai sun kusa cinyeshi,tsiya kam ya barsu a yanzu suyi son ransu.
Murmushi kadan ya subuce masa,murmushin dashi kansa baisan daga ina ya taso ba.......kawai ya tuna yadda ya nuna ne. Shi kansa bazaice ga abinda ya jashi ba,bazaice ga abinda ya sanyashi yayi wani reaction din ba,abu daya kawai ya sani,bai samu salama har sai daya samu tabbacin abdii ya goge,duk da baida zargi ko haufi akan abdii din.
"Me kenan?,kishi?....." Yaji tambayar ta subuce masa. Kansa ya girgiza a hankali yana dogare gwiwar hannunsa jikin murfin motor din.
"Ba kishi bane wannan.....dom ba irin wanna feeling din na saba ji ba....."
"Eh qarfin wannan ya d'ara na kishin da kake zaton kana dashi?.....saboda wannan din zahiri ne ba gaibu ba". Kai ya sake kadawa a hankali,ya aza dukkan qarfinsa yana ture tunanin gefe,don yana ganin maganan wani qofa daban da babu ita takeson bude masa,sai ya fidda wayarsa ya turawa omar gajeran saqo.
_Zan shiga gurin sultane_ ya aike masa yana maida dubansa kan titunan da suke wucewa.
_Ka sanar dani idan akwai buqatarmu a kusa,zan zama cikin shiri kusa da wayata_
Amsa ta shigo masa da gaggawa daga omar. Murmushi ya saki dan siriri,wanda har ya sanya har kyawawan labbansa suka bude kadan.
Masoyin gaskiya ba qarya bane,ubangiji yana iya hada zukata suso junansu da tsaftatacciyar soyayya da aminci. Kaman dai......su bakwai din tamkar uwarsu daya ubansu daya,ba wanda keson ganin kuka ko damuwar daya,hakanan dukka team dinsa da yayi aiki dasu,da wani abu ya sameshi har abada suna zabar su ya samesu.
Idonsa ya lumshe sannan ya bude,baisan yadda sultane zai karbi maganar ba..... Zai iya jurewa?......ko kuma bazai iya dauka ba?. Ya fidda numfashi a hankali yana tuna maganganunsa dazu da almaz.
"Ka bari muje tare,na bayyanawa duniya na santa,nasan adadin fuskokin da take dasu......ta batamin hotona a fuskokin al'umma.........ta yaya sultane hankalinsa zai fara daukan ni d'ansa ne bayan na amsa sunan surukinsa na kwanaki uku?".
Ya sani,abune me matuqar nauyin gaske,amma a yadda Ahmad din ya sauya a yanzu,ba kowa bane zai gane farat daya shine wancan almaz din ba,uwa uba sai Allah yayi wani abu cikin hikimarsa,ya hana sultane da duk wani me ruwa da tsaki ganawa da almaz a wancan lokacin,so da yawa basusan fuskarsa ba.....idan kuwa har mammina ta zama na farko da zata bankada maganar......zaiso haka,don zata burmawa kanta wuqa kakkaifa idan har hakan ta kasance.
_Tofa......sheikh haisam........ko sultane zai yarda dakai?,ko sultane zai gasgataka?_
Tun daga bakin babban gate din daya mallaki manyan katangun masarautar ya sanya salaana ya saukeshi. Cikin nutsuwa da kamala ya dinga takawa zuwa cikin gidan,yana kuma gaisawa da dukkan hadimai,tun daga masu tsaron qofofi har zuwa masu kai kawo don tabbatar da komai na tafiya lafiya cikin masarautar dama wadanda uzurorinsu ne suka fito dasu.
Komai yana nan akan tsari doka da qa'idar daya bayar. Hakanan kowa yana bakin aikinsa daidai da yadda ya dace. Ya sani komai zai tafi daidai din,dom fiye da rabin masu tsaron dukka sun fito ne daga qarqashinsa da kuma horonsa.
Daga iyakar da yasan labarin shigowarsa masarautar zai iya kai mata......daga nan ya danna wani device don bawa mutanensa umarnin dauke hankula da masu kula da doguwar hanyar nan dake shimfide da interlocking,doguwar hanyar data zama kebantacciya da ba kowa ke da ikon binta ba,doguwar hanyar kuma da zata iya sadaka da sasannin sultane akhnan morsa mammina dama sashen baqi na musamman makusanta.
A nutse ya bude qofar ya maidata kamar yadda take,ya kuma soma takawa a nutse yana kutsawa ciki.
*A K H N A N*
Bayan dukka tarin hayaniya da shiga cikin jama'a data jima batayi irinsa ba a yau.......ta zare jikinta daga cikinsu tun bayan sallar isha'i awa daya da rabi data wuce,ta kuma zabi dawowa dakinta da nufin tayi sallan magariba ta kwanta ko bacci zai dauketa.(haramunne bacci bayan sallar magariba,manzan Allah yace duk wanda yayishi bayan ya farka duk abinda ya sameshi ya zargi kansa).
Alwala tayi kawai sannan ta rage kayan jikinta da taimakon birra kamar kullum. Ta tayar da sallah sannan ta idar bayan ta cewa birra bata buqatar kowa da komai.
Da gaske take data fadi hakan,har yanzu wani nauyi takeji cikin zuciyarta,nauyin da batasan na meye ba......saidai bayan wucewar kowacce awa tana duban agogo.....kuma lissafin KWANA HUDU ZUWA YAU bai tsinke daga kanta ba,duk da qoqarin manta hakan da takeyi.
Zaune tayi saman abun sallar bayan ta kammala sallar. Zuciyarta ta nace da tambayar
"Kwanakin sun qaru" Idonta ta lumshe,tanason sanin ainihin damuwarta akan zancan.
"Ba wanda ke maganar qaruwar kwanakin........ko sultane baiyi wani magana ba akai......"
"Me yake damunki ne akhnan?.....me yasa kika damu da qarin kwanakinsa?.....me yasa kika damu da rashin jin motsinsa......da rashin jin komai ma daya shafeshi?" Zuciyarta ta jefa mata tuhumar data tilastata bude dukkanin idanunta tana kallon guri daya. Guri dayan da take ganin kamar a kallonsa kadai zata samu amsar tuhumar da takewa kanta da kanta.
"Qila saboda shima ya nuna damuwa a kanta a sanda buqatar hakan ta taso......qila saboda yayi mata wani gagarumin taimako na kubutar da rayuwarta.....qila....qila qila din da yawa,saidai abu daya daya sanya komai dauke mata dif shine......qila tana jin wani kadaici.....wannan kular......wannan kulawar wadda ke mata kamanni da takura da tsanani a wasu lokutan duka babu su. Taji wannan sosai yau a jikinta,a taron walimar.....ta dinga jin cewa inda yana kusa.....inda yana tare dasu a sannan,qila lullubinta......rigarta data dinga zamewa dukka idanu da hankulansa suna kai. A yanzu fa?duk da kulawar birra.....duk da tarin hadimai amma sai takejin kaman ta rasa wannan bangaren.
A hankali saita kifa kanta saman cinyarta,sai takejin kamar wani abu ta rasa me girma. Amma duk da hakan zuciyarta taqi amanna dari bisa dari,zuciyarta hujjoji kawai take bata mabanbanta. Hujjar an mata aure a sanda bata shirya ba.....hujjar aure da mijin da bata shiryawa ba.....hujjar zata bar qasarta......kamfaninta......sultane dinta dama komai nata.
A yau da kanta ta hadawa kanta ruwan wanka,saidai rashin sabo dayin hakan ruwan yayi zafi da yawa harsai data fita ta qara tara na sanyi,shi kuma ya kusa salamcewa,a haka tayi wankan,ta fito kuma ta shirya cikin farar gown cotton me yankakken hannu,rigar da saboda rashin kaurinta kana iya hangen shatar bra dinta idan ka sanya idanu sosai.
Iskar dake ratsowa ta tsakanin labulen dakin ya tabbatar mata hadarin dake ta hada kansa dazun a yanzu ya kammala wannan aikin. Ta shaqi iskar can cikin hunhunta da zummar fesarwa,saidai cak ta tsaya da iskar cikin hancinta saboda gauraya datayi mata da wannan qamshin.
Wannan qamshin dai daya zame mata jarrabi.....wannan qamshin dai dake sama mata wata dukkan nutsuwa ya kuma birkita mata tunani a wadansu lokuta....wannan qamshin.......wannan qamshin,saita saki iskar da sauri,ta sake shaqar wata da hanzari da nufin tantancewa.....shin da gaske qamshin takeji ko kuma gizo ne hancinta yake mata?.
Sake bude idanunta tayi tana sakin iskar a karo na biyu. Qamshin dai da gaske takeji,hancinta bai mata qarya ba a dukka karo ukun,to amma bataga koda alamar gilmawar kowa ba ballantana tayi tsammanin shine.
"Shine wa?.....har kin fara imagination......anya bakya matakin farko na fadawa soyayya?" Zuciyarta ta sake tuhumarta. Siririn tsaki taja,duka wannan shirme ne takeyi,ta sani tun ba yau ba turaren ke mata dadi,kuma tabbas daga sanda ta mallakeshi shikenan komai ya qare,so ba wani hasashe ko tuhuma na daban.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Haka kawai taji sha'awar fita ta shaqi daddadar iskar dake kadawa a sararin subhana,siririn mayafi kawai ta aza saman kanta,saboda tasan inda zata tsaya din ba guri bane na shige da ficen kowa ba,ta zura lausasan bedroom slippers dinta da morsa safiyya ta tilasta musu zama dashi.
Tana takowa a hankali tana sake jin kamar tana kusantar qamshin,a duk sanda ya jashi zuwa hunhunta kuma bugun zuciyarta ke tsananta. Wani memories suka dinga dawo mata a hankali. Ranaku irin wannan tsakaninsu na haduwar hadari da siraram yayyafi dama saukar ruwan sama me qarfi. Ta dinga tuna komai daki daki,kawai sai taji gabbanta suna saki a hankali.
Sosai ya jawo cloak thobe dinsa yana tattareta cikin jikinsa sosai saboda iskar dake tasowa me qarfi,ya miqa hannu ya jawo amam din kansa yana lullube fuskarsa har zuwa kan hancinsa kamar yadda ya saba a yawancin lokuta. Yafi zabar barin zagayayyun idanunsa da hadaddiyar girarsa a waje akan barin dukkanin fuskarsa gaba daya.
Sosai ta ware hannuwanta dukka biyun,iskar tana kada gangar jikinta sosai,tana kuma kwaso mata qamshi iri biyu tana dawo mata dashi hancinta. Na farko qamshin ta ne,wannan sassanyan qamshin na INCENSE BY KABO DAUGHTER daya kama jikinta sosai,0803 211 9803,cikin kowacce kafa ta jikinta ta saba jinsa,ya zauna ya manne da fatarta da wasu kalar turaruka da momma ta zube ake musu amfani dashi. Na biyun kuma wannan turaren dai....wannan qamshin dai da zuwa yanzu ya sanya ta fara tunanin ANYA BATA SAMU MATSALA BA?. Me yasa ko yaushe yake manne da ita?,me yasa ko yaushe take jinsa a kusa da ita?. Me yasa?.....me yasa?....me yasa?.
Daidai sanda tambayar ke kaiwa qarshe cikin kwanyarta......daidai lokacin da wata qaqqarfar iska ta taso ta kuma yaye dan yalolon mayafin kan nata tayi gaba dashi,bata kuma damu ta bude idanunta ba ballantana tabi ba'asin mayafin,don tasan a duk inda zai sauka zai sauka ne a amintaccen gurin da zata dauki abinta tayi gaba. Iskar dake ratsata da qamshin dake shiga hancinta wani yanayi ne da batason ya katse mata.
Da wani irin sanyi mayafin ya sauka saman kafadarsa sanda yake takawa da ginshirar nan tasa zuwa kebantaccen sassan sultane.
Ya daga kansa a hankali yana duban kafadar tasa da dan mamaki shimfide saman fuskarsa na saukar mayafin. Hannu ya miqa a nutse don saukeshi,saidai sanda hannuwansa ke sauka akan kafadar sai idanunsa suma sukayi kyakkyawan gani da ita.
Iska ce ke kada rigar jikinta kamar yadda take kada gashin kanta yadda taga dama. A nutse yabi siraran hannuwanta dake warwatse cikin iska.
Da wani irin sanyi ya sauke mayafin daka saman kafadar tasa.....saidai a maimakon neman inda zai ajiyeshi.......sai ya damqeshi sosai cikin tafin hannunsa sulbin material din yana ratsa fatarsa.
"Qila a irin haka?......a irin wannan yanayin tamim yasha ganinta har zuciyarsa ta fara saqa masa mummunan tunani?"
Wani irin motsi zuciyarsa takeyi. Tana tsaye ne ba hijabi a jikinta.......tana tsaye a inda idan amintaccen hadimi hidimarsa ta kama ya biyo ta gurin xai biyo.....me zai faru idan haka ta kasance?.
A hankali ya saki mayafin,ya kuma tashi yabi iska kaman yasan inda akeson aikashi,daidai sanda ya iska saman qafafunta......daidai sanda take bude idanunta da sauri jin saukar abu saman qafarta.....kuma daidai lokacin da yayi qoqarin sajewa da inuwar bishiyar dogon yaro dake gurin.
Tabbas taga inuwar mutum.....sannan taga gilmawarsa......abinda ya hadu ya cakude mata a zuciya kenan,ya haifar mata da wani irin tsoro me nauyi,tsoron daya sanyata ta fara tafiya da baya da baya zuciyarta na tsananta bugu,tamim ya fado mata da komai daya faru,sai taji kamar tana shirin firgewa gaba daya.
Ya gani,ya kuma lura da yanayin,abinda ya sanyashi takawa da wani irin zafin nama ta cikin shukokin,ya kuma zagaya ta bayanta ba tare da ta lura da faruwar hakan ba,saiji tayi tayi karo da wani abu,ta kumayi dungureshi ta baya.
Tsoro fargaba da dimuwa ya sanyata juyawa da wani irin sauri numfashinta yana neman daukewa,tanason tantance waye?.
Yadda ta juyo a razane ya tabbatar idan bai riqeta ba zatayi mummunar faduwa ne......tana juyowar ya sanya hannuwansa dukka biyun ya zagaye qugunta dashi.
Firgici da lakarta data sabule sakamakon tsoro ya gusar da duk wani karsashi nata,wannan ya sanya ta samu kyakkyawan masauki cikin qirjinsa ba tare da tasan waye ba.
Wani irin dumin daga anihin fatarta.....tudun jikinta dake tsakanin faffadan qirjinsa......wani irin dimautaccen qamshi dake fita daga sassalkar sumarsa dake barazanar rufe masa fuska sakamakon iskar dake kadawa da qarfinta.....wani irin sautin bugun zuciyarta dukka suka hadu lokaci guda suka soma ratsa fatarsa suna kaiwa zuwa ga kowacce jijiya dake jikinsa........wani irin abune yaji yana neman tafiyar da nasa numfashin,sai da yayi qoqarin riqeta da kyau gudun kada ta subuce ta kuma sulale.....sannan yayi jarumtar qwato numfashinsa daya qwace masa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽