Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 9

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 9

..... It is a small yard that is filled with light. It is not a good day to go to the place because of the availability of some interesting plants in the place. No matter what part of the morsa morning, the window is according to her plan and opinion, and she doesn't know why. Over the years... this is the first time she has come to know the places and corners of her side, which no one knows except her parlor that she enters every time she is forced to come to greet me. It is in the west, sitting on top of some of the most beautiful churches in the country of Turkey. All of them are almost her cousins, then her and then Falaak, they are all close because they are three years apart. Her coming to the place caused surprise in the hearts of almost everyone who was there, until she realized that she started to feel as if she was in a stranger or a new place. They were almost surprised to see her coming out of them, but the way everyone was trying to accept her by dragging her body made her lose a little, and she went to the area where Safeena's grandparents and parents lived and she sat among them. It was Shehnaz who also walked in a beautiful dress that was embroidered with money and

Standalone post1,532 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 9*

"Ubangiji ya tsareminku daga dukkan sharri,ya tsare gabanku da bayanku......kiyi sallah,zan turo birra ki fito farfajiya kema cikin ahalin safeena,cikin jinin safeena 'ya'yan 'yan uwanta,wanda na tabbatar inda tana Raye a yanzu abinda zatayi kenan. Zama cikinsu.....taji ta kalli taron daurin auren 'yar uwarki falaak" Ta qarashe maganan da wani rauni tana zame hannunta daga nan akhnan.

Idanun akhnan akan morsa safiyya din,tana sake jin wani yanayi me kama da karyewar zuciya. Taci gaba da kallon morsa safiyya dake mata murmushi har xuwa sanda ta juya tana fita a dakin.

A sanyaye ta wuce shiyyar da take salla a dakin,ta dauki after dress da yalwataccen mayafin dake ajiye a gurin saboda sallar,ta dora a kanta ta kabbara sallar.

Tana sallamewa birra ta shigo,saita taimaka mata ta fidda after dress din da mayanin,ta gyara mata zaman gown din jikinta komai ta maida mata muhallinta,sannan ta take mata baya dauke da wayoyinta.

'Yar farfajiya ce dake tarwai da haske. Ba hadin rana da zuwa gurin saboda wadatar wasu irin shuke shuke masu daukan hankali a gurin. Komai na sassan morsa safiyya sai taga yayi daidai da tsarinta da ra'ayinta,bata kuma san dalili ba. Tsahon shekarun......wannan shine karon farko data fara sanin gurare da sasanni dake bangarenta,wanda ba daya data sani banda parlour dinta da take shiga a duk sanda aka tilasta mata zuwa gaidata.

'Yammata ne zaune saman wasu lausasan kilisai saqar qasar turkiyya masu tsananin kyau da daukan hankali. Duka kusan cousins dinta ne,sa'anninta da sa'annin falaak,dukka sun saje saboda tazarar shekarun duka uku ne.

Fitowarta gurin ta aza mamaki a zukatan kusan dukka wanda yake gurin,har ta ankara da haka ta soma jinta kamar cikin wani baqo ko sabon guri. Mamaki kusan suke na fitowarta cikinsu,saidai yadda kowa ke qoqarin karbarta da ja a jiki ya bata sakewa kadan,ta kuma taka zuwa shiyyar da kakanni da iyayen safeena suke zaune suma ta zauna cikinsu. Shehnaz ce ta tako itama cikin kyakkyawar shigar shadda da aka yiwa dinkin mali ta zauna gefanta.

"Bansan ina momma takeso kikai wannan kyan ba......karku susuta sheikh fa........kar kisa karatun nan yayi nasa guri". Karon farko magana irin wannan ta sauka saman zuciyarta ta zauna daidai. A hankali sai zuciyarta ta tafi wani tunani na daban,haka kawai ta samu kanta da lumshe idanunta tana jin wani abu ya harba cikin jikinta.

Ganin bata amsawa shehnaz din ba,itama sai tabar batun ta maida hankalinta akan nanny dake magana da ita tana gaya.mata yau da dare me jan lallen aure zata shigo gidan har sai ta kammala da dukka amaren.

Ba ita kadai ba,kusan duk wanda ke gurin dama cikin masarautar yana iya jin yadda aka fara siga ta daurin auren falaak a hankali ta daga idanunta a karo na ba adadi tana duban falaak din. Tunda ta shigo gurin ta fahimci wani kwantaccen farinciki a fuskarta.....tunda ta shigo gurin ta karanci sam ta kasa zama guri daya,ko ba'a gaya maka ba kasan cikin farinciki take wanda bata taba irinsa ba cikin rayuwarta.

"Amma kuma.....me ya banbanta ni da ita?" Ta tambayi kanta tana tuna nata yanayin a dukka daurikan aurenta guda biyu da aka taba yi mata. Kuka baqinciki tashin hankali da bacin rai. Bata aminiya ba qawaye idan ka dauke aisa da shehnaz......daga aisan kuma har shehnaz banbancin ra'ayi da fahimta ne ko yaushe a tsakaninsu. Ba kasafai suke fahimtar nata ra'ayin da muhimmancinsa ba.

Lokacin da waliyyin falaak ke shaida cewa ya bada aurenta ga maleek din.....lokacin ta aza idanunta a shiyyarsu. Wani irin qudundunewa taga tayi,tana wani dariya dake bayyana kunya da zallar farincikinta. Qawayenta nata zolayarta,hayaniyar gurin tadan qaru,don ma da alama suna ragewa ne saboda idanun manya dake gurin.

Idanunta ta zare a hankali tana sauke ajiyar zuciya. MENE A CIKIN AUREN?,ta tambayi kanta da kanta,quruciya ke damun falaak din?,har take zaton wani abune babba na jin dadi cikin aure take masa murna haka?. Ko kuma ita dince?,itace bata fahimci komai ba?. Kai ta girgixa a hankali da yanayin da ba wanda zai gane,tafi zaton quruciyarce......tafi kyautata zaton rashin sanin ciwon kaine.

"Auren soyayya dadi.....kaga ikon Allah yarinya zata rigamu shigewa ciki?" Shehnaz ta fada tana kama hab'a gami da duban yadda falaak keta sunne kai da alama dadi ne yake addabarta. Akhnan naji tayi shuru,bata kuma ce komai ba,malamar nan kuma da morsa ta dauko da niyyar mata training ta iso gurin,wanda wannan shine abinda ya tattara hankulan kowa a kanta.

Ba wanda yasan dalilin zuwanta sai data zauna yiwa amare lecture. Tun akhnan naqin bawa maganganunta hankali har wasu daga ciki suka fara shiga kunnuwanta,bata kuma san me yaja hankalinta kacokam zuwa ga malamar ba tunani da hankalin nata suka daina rarrabuwa gurare.

*_K'ARFE TARA NA DARE(A wannan ranar_*

Sanye yake cikin emarati thobe baqa wul me sheqi da daukan idanu,wadda tana cikin sample na sabbin jallabiyyar da kamfaninsu dake dubai zai fidda a shekara me zuwa,sukayi masa tasa suka bashi kaman yadda aka saba. Cloak thobe ce a saman emarati din,wadda ta kasance gray color kalan zaren da aka yiwa emarati din ado dashi. Amama ne saman kanshi daya dace da cloak thobe din jikinsa,ya kuma haska wannan zagayayyar fuskar tasa ma'abociyar kyawawan labba,labban nasa da suka sake bada wani yanayi me kyau sakamon zazzafan black tea din dake cakude da qamshin coffee din da qasarsa take nomawa(Ethiopian oromian coffe da aka nomashi daga yankin jimma.

Tsaye yake cikin sassanyan yanayinsan nan,yayin da khadeem dake zaune cikin da'irar abokansu ke qare masa kallo a nutse.

Tunda yake bai taba ganin mutumin da wannan shigar kewa kyau irin haisam din ba. A duk sanda ya kalleshi sai yaga kaman saboda shi aka halicci shigar,a kuma duk lokacin da zai kalleshin limaman harami yake tuna masa irinsu sheikh yasir rashid addusary dasu abdurrahmanis sudais.

Hira kawai ke tashi a parlor din da yaren oromo,sai turanci jifa jifa don bai daga cikin tilashinsu a yaruka. A farinciki suke dukkansu,kuma maleek ya hana kowa sakat kaman ba dare ne yakeyi ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Qamshin turarukansu masu aji ne cakude da parlor din,da sassanyan freshener din data zama tilas ga duk wani muhalli da zai rayu koda na qayyadaddun awanni ne,amma shigowarsa da tsaiwarsa a parlor din yana shan black tea din sai qamshinsa ya rinjayi kowanne qamshi dake parlor din da wani lallausan yanayi.

Wayar abdii ce a hannunsa na hagu,yana viewing pictures din cikin wayar daya bayan daya,wanda duka wadanda akayisu ne dazu harda family din falaak a ciki sosai.

Har xai ajiye wayar ya sake tafiya next picture,sai ya tsaya cak akan hoton yana dubansa. Daga baya ta fito ba daga cikin hoton ba,hasalima alamu dukka sun nuna batasan an dauki hoton ba,don fuskarta bata fita sosai ba.

Haka kawai yaji wani abu yana sauka tsakani yatsunsa da tafukan hannunsa dana qafarsa. Sai.ya zame cup din da yakai bakinsa a hankali ya azashi saman table din da yake kusa dashi sosai.

Yatsunsa ya sanya yayi zooming hoton,take fuskarta tayi kusa dashi sosai fiye da dazu,sai yayi clicking fuskar wyaar har sau biyu yana maida hoton anihin girmansa.

A nutse ya daga wannan zagayayyun manyan idanun nasa ya zubesu akan maleek.

"Maleek?" Ya kirashi da tone din daya sanya kowa a cikinsu ya maida hankalinsa kanshi. Wayar abdii ya daga masa,har yanzu idanunsa suna cikin nasa.

Qanqance idanu maleek yayi,yanason ganin me haisam yake nuna masa. Ya gane hakan sai ya sake karkatar da wayar saitin fuskarsa shi kadai yana sake tsuke fuskarsa,bayan ya saka yatsansa daya yayi clicking sau biyu hoto yayi zooming.

Second uku kawai ya bawa maleek dim ya dauke fuskar wayar daga idanun maleek din.

"Matarka ba haja bace a kasuwa da zaka bada daman daukan hoto da ita......koda hoton mene bana tarihi ba.....ka kiyaye hakan" Ya fada da wani irin izza wani abu yana tasiri tun daga zuciyarsa zuwa saman fuskarsa.

"Goge" Yace da abdii yana cilla masa wayar. Yadda ya cilla wayar banda abdii din ya nuna zafin naman cafeta ba abinda zai hanata faduwa ta fashe a qasa.

"Amma......" Abdii ya bude baki zai magana,yanason gaya masa hoton tarihine,kuma ba kowa bane ya fito a ciki,yanason ya ganar dashi ba komai a cikin irin wanna hoton,amma kallo daya.....kallo daya daga haisam din ya kulle bakin abdii.

"Tashin hankali" Omar ya fada qasa qasa yanayi sosa sumar kansa. Irin wannan kallon na haisam dukkaninsu sun sanshi. Kallo ne dake daureka da dukka wata jijiya ta jikinka,ya hanaka musu ko motsi har sai kayi abinda yace maka.

"Obbo na goge"

"Ka gogeshi daga trash ma" Ya fadi yana isa bakin fridge ya fidda ruwa mara sanyi ya soma zubawa a glass cup.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽