Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 8

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 8

..... he broke. "Alright" He said again, interrupting the call because he heard Naseeb's voice calling Omar. He put the phone down slowly and relaxed. "Walima?.....men and women" When the conversation came back to him, he picked up the phone again and started looking for Abdii's number. Until the call went in, he started asking himself what he would say to him. What will he say to him is the reason for the call? "Good Friday obbo" He said with respect and some fun in his voice. "Obbi, I hope everything is fine" "Alhamdulillah, obbo..." "Obbo, maleek will be fine today" "It's not my son's job to give you a call." "Yes.....you should pay attention again" "I pray to God, obbo" He hung up the phone and concentrated on the road that they were passing with the calmness of the salaana driving. When Sanda reached home, he checked the time and saw that there was still time to go to the mosque. He was sitting in the car, looking at his phone as if he was remembering something.

Standalone post2,016 words

πŸ’Ž *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*πŸ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 8*

,kiran da yana shiga bugu uku kawai omar ya daga.

"Me yasa haka omar?" Yayi tambayar cikin sanyi da nutsuwarsa,saidai akwai yanayin da zai nuna maka qorafi yakeyi.

"Noooo captain......you're forgiven fa,dukka nauyin Ethiopia ne a wuyanka......and you need to stay at home......kowa yazo,hakan kuma yana nufin zuwanka gurin baiyi daidai ba,cikin wadanda sukazo din ba kowa bane yasan kana nan ba........dole sai ranar daya kamata ka fita din.......sallah kawai zamuyi yanzun a daurawa wannan angon mara kunya auren nan muma mu huta......sceret mana sir" Murmushi kadan ya saki a boye,ya yadda da maganan omar,dole ya zauna a gidan gudun ballewar wani liqi daga mutanen da sukazo.....amma dai maleek dama sauran duka nashi ne.

"Alright......."

"Akwai wani walima da sukeyi idan an gama daura auren duka maza da mata......inajin harda Madame dinka ma" Shuru ya gilma kadan,kafin haisam yadan waro idanunsa. Kaman zaice wani abu amma sai ya fasa.

"Alright" Ya sake fadi yana katse kiran saboda jin muryar naseeb yana kiran omar din.

Wayar ya ajiye a hankali yana sauke ajiyar zuciya.

"Walima?.....maza da mata" Maganan yadan sake dawo masa akai,sai ya sake daukan wayar ya soma lalubar number abdii. Har kiran ya shiga,sai kuma ya soma tambayar kansa me zaice masa?. Me zaice masa shine dalilin kiran?,bai bawa kansa amsa ba yaji muryar abdii ya daga kiran.

"Barka da juma'a obbo" Ya furta cikin girmamawa da kuma wani nishadi cikin muryarsa.

"Yauwa abdii.......fatan komai lafiya"

"Lafiya alhamdulillah obbo......yau obbo maleek zai angwance"

"Ba shine aikin dana baka ba"

"Obbo ina aikina.....komai lafiya yake obbo" Shuru haisam din ya danyi,kamar meson tambayar wani abu ko kuma tuhumar abdii akan abinda baisan meyeshi ba.

"Yayi.....ka sake kula sosai"

"In sha Allah obbo" Katse wayar yayi a gefe,ya tattara hankalinsa kan titi da suke wucewa da nutsatsen tuqin salaana,salon tuqin daya sanya ya zabeshi cikin kaf drivers dinsa,yakan zabi kuma ya tafi dashi ko ina ne.

Sanda suka isa gida ya duba lokaci sai yaga akwai sauran lokaci na tafiya masallaci. Yayi zaune a motar,yana duban wayarsa kamar meson tuna wani abu daya manta. Sake daukan wayar yayi ya budeta yana lalubar sunan nanay dinsa.

Daidai lokacin da nanay din ke zaune ita da Khansaa tana duba list din komai da aka zuba cikin gidan narkakken ginin gidan haisam.

Khansaa da tafi kusa da wayar ita ta miqa hannu ta dauki wayar,ta saki qaramin murmushi ganin sunan dake rubuce. Amini kuma abokin shawara qaninta haisam,duk kuwa da cewa ta girme mishi,amma ta bashi dukkan girman da komai ma. Kallon wani babban yaaya ko kuma uba take masa,yana kan dukkan damuwarsu da matsalarsu da shawarwari dama dukan abinda ya dace ace yayi.

"Obbo ne" Tace da nanay tana dariya,sannan kai tsaye ta daga wayar tana sakata a kunnenta.

"Assalamu alaikum......i missed you" Ya fada yana jin rauninsa yana dawowa. Indai a gaban nanay ne.....indai nanay tana nan to yana jinsa shi ba komai bane.....shi ba kowa bane.....yana jinsa ne tamkar d'an jariri. Duk wani power tarin tawaga.....manyan ayyuka masu munin hatsari da yake aiwatarwa a gaban nanay yana jinsa kamar ba shi ba.....kamar ba wannan Al_saamit din ba.....the silent one.

"Dan nanay.....ba nanay din bace" Khansaa ta fada tana murmushi mai sauti. Fuskarsa ta saki kadan,ya dora hannunsa saman sumarsa me santsi yana shafawa a nutse idanunsa suka lumshe sannan suka bude duka lokaci guda.

"Oum maheer" Ya furta a nutse.

"Captain obbo.....munyi kewarka,kowa ya shirya.....dukka masarauta kai ake jira,surukarmu mukeson gani,duk shirye shirye suna dab da kammala" Ta fadi cikin zumudi gami da son ganin matar captain sheikh din.

Murmushi mara sauti ya sakeyi,da girma haka suka dauki lamarin?.

"Sati uku captain kamar yayi nisa"

"Kubi komai a hankali obbolettii(sister)" Ido ta juya kadan tana duban nanay. Ba su kadai ba,daidai da nanay din tasan yadda ta dauki abun kadai bazai sanya kowa ya zauna ya nutsu ba har sai sunga isowarsu.

"Karka damu qanina......kaidai kawa kayi qoqari ku iso da wuri"

"In sha Allah" Ya amsa mata sannan ta miqawa nanay.

Cikin muryoyinsu yakejin wani irin shauqin abun,cikin muryoyinsu kadai yana iyajin dokin auren da kuma son iswarsu Ethiopia. Ya sake shuru bayan sun gama wayar dasu. Har yanzu yana jin wani emptiness da baisan daga inda yake ba,irin yanayin nan da mutum yakejin kamar akwai wani abu daya kamata kayishi amma ka rasa meneshi.

Siririyar ajiyar zuciya ya sauke,sannan ya kwashi wayoyinsa kawai,ya zura qafafunsa a nutse yana fita a motar.

Cikin gidan ya shige kansa tsaye,yau sai yaji gidan ya masa shuru da yawa. Cook dinsa ya soma tambayarsa me yake buqatar a zuba masa.

"Black tea da dabino" Shi din kawai ya karba yasha yana hadawa da dabinon ajwa da yasan shine dabinon haisam din,duk da yana cinsu kala kala amma yafi mu'amala da ajwa din.

Wanka ya shiga yayi,ya kuma shirya tsaf cikin Moroccan thobe olive green data masa wani irin sassanyan kyau. Wayarsa ya sake dauka yana dube dube,shi kansa baisan dube duben me yakeyi ba,sai yaja dan siririn tsaki ya sakasu a flight mode duka biyun,ya dauki abun sallah ya zura lausasan flip flops a qafarsa masu sauqi ya feshe jikinsa da wannan lallausan turaren nasa sannan ya doshi qofar fita. Akwai masallacin juma'a daya gani gaban anguwarsu kadan,basu da wani nisa,sai ya yanke zuwa can din yayi tattaki da qafa ya samu juma'arsa a can.

Sanda aka kammala juma'ar sai yayi zamansa cikin masallacin. Lokacin sai ya zame masa wani dan taqaitaccen lokaci na samu nutsuwa da kebe kai daga mutanen da suka sanshi. Emptiness din da yakeji yayi yawa,don haka ya dauki qur'ani cikin drawers na masallacin da aka adana ya soma tilawa da wannan sautin qira'ar tasa me matuqar jan hankali da sanya nutsuwa.

Awa daya kawai yayi ya rufe,ya miqe a hankali yana maida qur'anin sai ya fahimci akwai idanuwa sosai dake satar kallonsa a masallacin. Inde irin wannan kallon ne ya saba dashi,ballantana a yanzun da ya tabbatar yayi daban da qabilar da yake rayuwa a cikinsu,so dole ya samu wannan qalubalen.

A nutse yake takawa zuwa gida,saidai still yana jin wannan yanayin. Ya furzar da iska daga bakinsa a hankali maganan abdii tana dawo masa.

"Walima zaayi maza da mata.....bayan gama daurin auren" Hakan na nufin kowa ma zai fito.....kowa ma zai halatta.

"Amma ita fa?" Ya tambayi kansa. Shuru ya gilma ta cikin kansa,ba wani amsa ko motsi daya dawo masa da sunan amsa,sai kawai ya samu kansa da sauya akalar tafiyarsa zuwa gida.

*A G A D E Z P A L A C E*

Cike masarautar take a wannan juma'ar da ninkin jama'a baqi da 'yan gari da suka saba zuwa sallah babban masallacin juma'ar na gidan sarkin. Cikar yau ta banbanta data kullum,saboda gudanar da d'aurin auren falaak sultane muhammad hammud da kuma maleek motii ja'afar.

Wata irin qauna da soyayya mutanen yankin agadez suke nunawa sultane din,wanda adalcinsa da soyayyarsa ga jama'arsa duka ya siya masa wannan. A qurataccen lokaci aka sanar da daurin auren......amma adadin jama'ar da suka halatta zaka dauka abu ne da aka jima ana shelar daurashi.

Masarautar ta cika da baqi...ko ina kai kawon al'umma ne da kuma hidimomi da zasu tabbatar maka babban sha'ani ne ya samu masarautar.

Tsaye take gaban babban mirror din dake girke cikin dakin daya zama mallakinta tun sanda ta dawo da kwana sassan morsa safiyya. Wani irin daki ne dake da wani irin tsari da kyau me daukan hankali,dakin da bata taba zaton akwai me yanayinsa cikin gidan ba.

Ba wannan bane.....abinda yafi daukan hankalinta da kuma sanyata yawaita zubawa morsa safiyya idanu a duk sanda ta shigo gurinta shine. Tasan komai da tafi buqata cikin dakin baccinta.......tasan kowanne tsari nata.....tasan komai da yake qayatar da ita yake kuma burgeta,tun daga kan color na dakin da duka tarkacen furniture da aka zuba cikin tsari da burgewa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Akwai wani yanayi me dadi da dakin yake dashi.......yanayin kuma daya hada da sassanyan qamshin turarukan da kowanne rana ake cudesu dashi ita da falaak din,duk da falaak din tana nata dakin daban,amma komai iri daya,komai tare momma take musu.

Wasu irin turaruka ne daga asalin gargajiya. Turarukan nan dai na kamfanin *INCENSE BY KABO DAUGHTER 803 211 9803*

Wani irin mayen qamshi da hatta da numfashin dake fita a daga hancinsu da hucin qamshin yake fita. Baya barin sutura da gangar jiki da wuri,sannan a sake dora musu wani.

Saidai duk da haka.....duk da nutsuwa da dadin da wannan qamshin yake mata......duk da irin yadda qamshin ya mata dari bisa dari......har yanzu dai. Har yanzu akwai wani qamshi guda daya da tayi kewarsa.......tana jin akwai wani qamshi qwalli daya da kamar ta rasashi a dukka tarin qamshe qamshen dake zagaye da ita.

Ko yanzun da take tsaye gaban madubin.....a shirye cikin wata irin doguwar riga ta alfarma da aka saqata daga qasar dubai......wani qamshin ne a jikinta na musamman yake tashi,amma kuma tana jin akwai sauran wani gurbi daban......kamar akwai abinda take jiran samu......kamar akwai abinda take jira taji.

Ta soma zargin kanta sanda lasifiqar babban masallacin ta fara motsawa,muryar na'ibi ta fara tashi yana tayar da iqama,sai ta samu kanta da tattara dukka hankalinta akan kowanne furuci na iqamar da yakeyi,ta miqa hannu ta jawo stool ta ajiye gaban mirror din,ta kuma zauna akai a hankali zuciyarta tana bugawa kadan kadan da wani irin yanayi da batasan me ya kawoshi ba.

Idanunta zube saman fuskarta tana duban kanta da kanta. Taga irin kyan da tayi ita kanta,....taga yadda fatarta ta sauya daga ainihin fatarta data sani zuwa wata lafiyayyar fata da ita kanta burgeta takeyi. Ita kanta burge kanta takeyi,to amma duk da haka a daidai wannan lokacin sauraren da kunnuwanta sukeyi sunfi ganin kyan jikinta dana kwalliyarta muhimmanci.

"Allahu akhbar......bismillahir rahmanir raheem......alhamdulillahi rabbil Aalameen....." Muryar limamin dake jan sallah a daidai wannan lokacin ta shiga cikin kunnuwanta.

Idanunta ta mayar ta lumshesu a hankali,tana ci gaba da sauraren karatun sallar juma'ar amma kuma wani abu yana mata nauyi yana danne zuciyarta.

Kamar wata murya ta daban take buqatar ji ba wannan ba......kamar wata murya daban tayi tsamamanin ji ba wannan muryar da ake karatu da ita yanzu ba.

"Yau.....Kwana hudu kenan" Ta fadi can qasan zuciyarta,sai kuma ta ware idanunta da dan sauri

"Me yasa nake irgawa?me yasa na irga?" Ta samu kanta da tuhumar kanta da kanta. Miqewa tayi a hankali tanason watsar da komai,kunnuwanta suna iya jiye mata saututtuka kala kala,wanda kusan fin rabinsu na karadin falaak ne da qawayenta da kusan duka cousins dinsu ne.

Ajiyar zuciya ta sauke,daidai sanda aka turo qofar dakin,saita waiwaya a nutse don ganin wanda yake shigowa.

Morsa safiyya ce......morsa safiyyan da a yau tayi mata wani zuzzurfan kallo.....zuzzurfan kallon daya nuna wasu kamanni nata da na safeena. Kamannin da ita ta sansu ne kawai ta hoto,hoton da ta hannun morsa safiyya,ta silar morsa safiyya kadai ta mallakeshi,sai taji zuciyarta ta mata nauyi,wani abu me kama da nauyin maraici yanason ya saukar mata,amma kaman safiyyan ta fahimci haka saita qaraso gabanta,ta kamo kafadarta tana rungumeta cikik jikinta.

"Alhamdulillahi......Alhamdulillahi" Ta maimaita har sau uku,sautin muryarta yana yiwa akhnan zurfi tana jin a yau kamar muryar safeena ce cikin tata,muryar data mallaketa ta wannan tsohon cassette din recording din,cassette din daya zame mata abokin hira takan maimaitashi a rana sau babu adadi.

Rungumar da momma din tayi mata saita dinga ji kamar ana sauke mata wani abu......sai taji kaman wannan damuwar data mata yawa tana raguwa. Saitaji wani irin sassauci yana saukar mata a hankali. Wani yanayi da bata taba jin irinsa ba ballantana makamancinsa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽