
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 7
.....he returned to her as if he had never squatted in a place in her heart. No matter how early morning she wakes up, she concentrates her attention on the akhnan. Her face with a little smile that she felt something broke her today and she showed her side. "Sit here" She sat down and all the servants in the place came down and greeted me with respect. She gave them the same answer, each of them put down their handiwork, lined up and left. "Welcome to you tent" Falaak said with her voice that was kind of funny and hoarse. He nodded slowly, "Goodbye." "Welcome to this time". It was good for everyone, it was something that Falak had never done between her and her husband. "Goodbye, my little one...momma, let's go out and have a good time," Hairaan said as she stretched out, just as Anwaar was entering the parlor. Akhnan was watching and hugging his big ball. Ever since we gave him some big chocolates, he hasn't forgotten her face, even though she missed him, she didn't talk to him but he didn't forget. Good morning, she woke up and felt some happiness.....
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 07*
A yanzun da akhnan ke takowa zuwa babban parlor din daya zamana kusan a yanzu morsa ke yini saboda shiryen da suka zame mata linki biyu,na akhnan din dana falaak,falaak din da a gobe juma'a ne zai zamana cikar ranar daurin aurenta da maleek,sai akhnan din ke dubansu tun daga nesa ba tare da sunsan da shigowarta gurin ba.
Cikin tsakiyar suke da wasu irin akwatina da ba zatace ga abinda yake ciki ba. Tarin Invitation da tana iya ganin qyallinsu daga inda take takowa,da wasu suturu a gefe da amintattun hadimanta ke ninkesu suna shiryasu.
Ta maida dubanta kan hairaan da falaak,sai takejin kamar ita daya ce bare a cikinsu. Farinciki ne kwance saman fuskokinsu,hairaan din ta kaiwa falaak duka tana fadin.
"Mara kunyar amarya kawai" Sai falaak ta saki dariya tana boye fuskarta.
Ko alama bata taba kawowa zataso wani a kusa irin son da taji tana yiwa sheikh Muhammad haisam ba,amma daga randa ya zama mallakin bifttunta sai duka ya koma mata kamar bai taba tsugunnawa a wani gurbi na zuciyarta ba.
Komai da morsa safiyya keyi ta saki tana tattara hankalinta akan akhnan. Fuskarta da wani kalan murmushi da taji wani abu ya tsarga mata a yau ta nuna mata gefanta.
"Zauna a nan" Tana zama kuma dukka hadiman dake gurin suka zube suna gaidata da girmamawa. Amsawa daya tayi musu,kowacce ta ajiye aikin hannunta suka jera layi suka fice.
"Barka da warhaka tanti" Falaak ta fadi da muryarta da tayi wani irin wasai kuma tarwai. Kai ya gyada a hankali
"Barka" Ta amsa mata,saita maida idonta kan hairaan.
"Barka da wannan lokaci". Abun ya yiwa kowa dadi,wani abu ne da falaak din bata taba yi ba tsakaninta da hairaan din ba.
"Barka kade qanwata......momma mufa fita zamuyi mu baki guri" Hairaan din ta fada tana miqewa,daidai sanda anwaar ke shigowa parlor din. Akhnan yaketa kallo yana rungume da qatuwar ball dinsa. Tun rabar data bashi wasu chocolate manya shikenan bai manta fuskarta ba,duk da batace masa komai ba batayi magana dashi ba amma shi bai manta ba,saita saki murmushi ta miqa masa hannu,take ya tajo da saurinsa,ta kama hannun nasa tana zaunar dashi saman cinyarta. Kai morsa safiyya ta dauke tana jin wani farinciki yana ratsaya,zuciyarta ta karye kaman kuka zai kubce mata. Sannu a sannu dai Allah yanata jefa soyayyar yaran a zuciyarta,wanda tana da yaqinin zamowa sa zasu yi da falaak a qasa daya zai sake kawo kusanci a tsakaninsu,tunda dukkaninsu basu da kowa basu da wanda yakai junansu.
"Zai bata miki fa wannan kyakkyawan farar doguwar rigar.....yaje sumayya tayi masa wanka" Kai ta girgizawa hairaan alamun ta barshi,saita daga idanunta take kuma suka hada ido da morsa safiyya alamun ita take kallo tun dazun.
"Barka da yamma,kin yini lafiya?" Morsa safiyya ta fada kai tsaye sanda dakin ya dauki shuru bayan kowa ya fice ya barsu.
Karo na farko.......lokaci na farko da taji wani nauyinta ya kamata. Karo na farko da taji kaman hakan bai dace ba..... Murmushi morsa din ta saki,boyayyen murmushi dake fassara farincikin da takeji,ta gama karantar me takeji,kunya da rashin sakewa......yau ita akhnan kejin kunya?,yau ita akhnan ke qin sakewa a gabanta don ita ta fara gaidata?.
"Kada kiji wata kunyata......hakan ba mummunan abu bane.....uwa tana iya gaida diyarta ta kyakkyawan hanyar tambayar lafiyarta irin haka.......yanzu ba wannan ba....." Morsa ta fada tana jawo wani qaramin akwati. Sai data saka hannu ta dauke anwaar tana dubansa.
"Kaje gurin sumayya ta karbi madara" Batama qarasa ba yayi jifa da ball din nasa yana nufar qofa,sai akhnan din ta bishi da kallo har ya bace kafin ta dawo da dubanta ga morsa.
Saman cinyarta ta aza mata akwatin.
"Ina me fatan sauke wannan nauyin da amanar dake wuyana shekara da shekaru....." Morsa ta fada muryarta tana rawa.
Haka kawai tunda ta kalli akwatin taji ta dokanta ta budeta,bawai don kyanta ba,aah hasalima kana kallonta kasan tsohuwar akwati ce. Ta danyi kiciniya kadan da ita sannan ta gano gurin budeta ta bude,don daga maganan farko morsa safiyya bata iya sake cewa komai ba,hasalima hawaye take daukewa a dabarance da tissue din hannunta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Bracelet ne na danyan gold......(dan uwan wannan bracelet din dake hannun mammina da haisam ya sauya mata da fake dinsa). Abun wuya da dan kunnaye da sauran kayan tarkacen kwalliya na gold data tabbatar na mahaifiyarta ne,don koda ba'a gaya mata ba tasan tsohon gold ne don dukka tsaffin design aka masa. Haka ta dinga fita dasu daga qarshe kuma taci karo da wata takarda da littafi.
Littafi ne na addu'o me shafuka kusan hamsin,wanda aka rubuta da yaruka uku,oromo da yaren Tuareg wato yarensu na buzaye sai yaren larabci da shine asalin rubutun. Ta sauka zuwa ga mawallafin sai sunan safeena din baro baro ya bayyana. Mamaki ya sanyata daga kai kadan ta kalli morsa safiyya,alamun tambayoyine fal cikin idanunta.
"Mahaifiyarki macace me Tarin ilimin addini.....ilimin addinin daya zame mata jagora gurin karbar dukka qaddarar rayuwarta.......wannan littafin shine abu na qarshe data wallafa sanda ya rage mata kwana casa'in kacal tabar duniya". Wani nauyi ya sauka a zuciyar akhnan,ta aza idanunta akan takardar dake da gajeran rubutu cikin yaren Tuareg.
_Wadannan sune kadai abinda na mallaka yake 'yata,kuma sune abinda nabar miki,ina fata su isa gareka sanda kike shirin tafiya dakin mijinki.......ZAMANKI MACE TA GARI SHINE CIKAR BURIN RUHINA da salamar gangar jikina_. Damqe takardun tayi a hannunta tanajin hawaye yanason taruwa cikin idanunta.
"Alfarma nakeso kiyimin......ki kafa tarihin zama kusa da safiyya......ki kafa tarihin kin rayu cikin gidan safiyya koda na iya kwanakin nan ne......inason ki qarasa kwanakin a nan sashe na cikin 'yan uwanki,hairaan da falaak da zata amsa sunan matar aure juma'ar nan itama......wannan ta zama alfarma guda daya da zan dinga tunawa da cewa kinyimin ita a rayuwarki". Idanunta dukka ta bude a hankali tana duban morsa safiyya,idanunta da a yau sai take ganin suna hango wani abu daban da dukka shekarun baya bata taba ganinsu a fuska da idanun morsa safiyya din ba. Ta yaya ma zata iya cewa a'ah.....matar data sake kusantata da wani abu daya shafi mahaifiyarta?.
★★★
"Bansan wacce irin sa'a ce dakai ba har da mukayi nasarar samun hayyacinta ka tatsi dukka wadannan bayanan daga gareta ba" Dr na'eem ya fadi yana share gumin goshinsa da qaramin lallausan handkerchief na towel din dake hannunsa. Kujera yaja ya zauna,ya sake daga idanunsa yana duban haisam dake tsaye qiqam gaban gadon da yalwa ke kwance akai kamar sojan da aka bugawa kugen yaqi. Gadon da a dazu ya dinga jijjiga da jijjigar da gangar jikin yalwa keyi.
"Sun riga sun ciyar da ita wani abu da zai dinga kashe mata organs dinta,kowacce rana zatayita mutuwa ne ba tare da tasan mutuwa takeyi ba.......idan da ta dauki wani lokaci a haka,za'a je ne kawai a tsinci gawarta ba tare da ansan meye yayi ajalinta ba" Dr na'eem ya qarasa bayanin yana bude gorar ruwa yakai bakinsa.
Da wannan nutsuwar tasa dai ya sauke dukka hannuwansa biyu qasa. Da wannan nutsuwar tasa yayi tattaki ya jawo kujera ya zauna,da wannan zaman nasa dake nuna izzar mulkinsa.
A dukka bayanan daya qarqare samunsu......ya fahimci wasan da mammina tayi da hankula masu tarin yawa.....ciki kuwa harda hankulansu yalwa din. A iya saninsu da abinda suke iya gani,a iya mu'amalar da takeyi dasu suna zaton sune na gaba gaba abokan sirrinta,tunda sune sukafi kusanci da ita,saidai wani abu da basu sani ba......wadannan wulaqantattun bayin......wadannan hadiman da ko kusa da ita basu isa suzo ba sune mafi kusanci da ita. Ya gane hakanne bayan ya qwamushe mutumin dake kula da duk wani kwandunan shara na sassan nata,ya wankesu bayan an yasar da sharar,ya kuma maidasu muhallinsu.
Miqewa dr na'eem yayi,suka bawa juna hannu shida haisam kafin su rankaya tare da haisam din su fice suna sake tattaunawa.
Tafiya me dan tazara sukayi kafin su kawo ainihin muhallin ajiyar motoci inda Dr na'eem yayi parking motarsa,ya bude ya shiga sukayi sallama,sannan shima yayi taku biyu baya yana duba agogon hannunsa.
Juma'a ce......juma'ar daya kamata ace yana masallacin masarauta......ya samu jam'i kamar yadda ya saba. Juma'ar ita ya tsara zai koma masarauta.....juma'ar a ita ya lissafa aikinsa ya kammala. Eh aikinsa ya kammala.....saidai yanason budewa mammina qofa daya tal cikin tarin dubban qofofinta daya bude kowacce ya zare maqullin kuma ya yasar........don haka yana buqayar ranar LAHADI.
A ranar lahadin ta sace Ahmad din ta rabashi da tsatsonsa ta kuma batar dashi......a wannan ranar.....a daidai lokacin yakeso ya maido mata da saqonta.
"Zamu iya tafiya?" Salana ya tambayi haisam cikin girmamawa. Dauke idanunsa yayi daga kan agogon,bayan ya duba lokaci harda kwanan wata ya duba yana lissafin watannin daya share a agadez......yana lissafa watannin daya diba baiga nanay dinsa ba.
Yana kewarta.....yana tsananin kewarta sosai,wannan aikin na kwanakin nan daya sakashi a gaba ma ya sanya ko waya basuyi ba kwata kwata,saidai time to time yana ganin saqonnin noorah rumaisa da Anaani,musamman noorah dimma,kamar ita da taufeeq sunfi damuwa da nisan da yayi dasu,duk da yasan kowa a cikinsu ma hakan ya keji,sun fisu dauriyar boyewa ne kawai.
"Su khadeem fa?" Ya tambayi salana a nutse.
"Yau daurin aure,dukkaninsu suna cikin agadez......sunce na barka ka kammala uzurinka".
"Ya salam" Ya furta yana nutsa yatsunsa cikin sassalkan gashinsa.
Bai taba hango daurin auren maleek ba babu shi a gurin......bai taba hango maleek zaiyi aure bai halacci daurin auren ba.
Wayarsa ya soma laluba,me yasa zasu masa haka?,suce kada a tuna masa?. Duk yadda aikin yake da muhimmanci nasu muhimmancin na dabanne,bayajin akwai wani abu da zai shiga cikin wannan alaqar......ya kuma tabbatar kowa da kowa cikin team 7 din yaje banda shi.
Bai kira maleek kai tsaye ba,don bayason raba masa hankali a irin yanayin nan daya tabbatar zumudi ne fal cikin maleek,sai ya kira omar
*Akhnasaim tales*🤍
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽