Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 6

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 6

.....hekaru hasn't done anything like her......" "I need to see the video of the place to know how to collect everything and pay the compensation for the loss" she said, feeling a sweat breaking down her, and she was trying to be strict in all her words, not to say anything that would expose her secret. Is this house consumed by fire like her heart is alive? Is this house the one that she doesn't have in the whole world, or is it just an illusion of her heart? Sanda moved with the intention that something behind them made them look back. If she was told that she had been picked up from the first gate of the place, she would not have tried to lie even once.

Standalone post2,002 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 06*

Wata irin mummunar faduwa gabanta yayi,a hankali sai yanayin karsashin da take da yadda take daga qafafunta sukayi low a hankali. A haka ta qaraso dab da karan bamboo din,ta dakata da wani irin sanyi,sannan ta daga idanunta tana duban tafisu.

"Kina jin abinda suke cewa?" Tayi tambayar kamar wadda keda hope kan tafisu tace mata bataji komai ba.

"Kaman villa road ranki ya dade........"

"Nan ne......jikina yana bani wani abu tafisu.......maza kiyimin magana dasu" Ta fada tana jin qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba,don haka ta sauqaqawa kanta,ta sulale ta zauna saman concrete chair din dake girke a gurin.

A razane da jin kira daga gurin giwa suka iso,suka zube dukkaninsu kansu a qasa,zuciyoyinsu kamar zasu tsinke da fatan ba wani laifi suka aikata ba.

"Ku bani labari.....me yake faruwa a villa road?" Tayi tambayar a sabule duk da tana qoqarin tattala qwarin gwiwarta.

"Gobara ce.......mafi munin gobarar da aka dauki shekaru ba'ayi irinta ba......"

"Ina buqatar ganin video din gurin don asan yadda za'a tari komai da biyan diyyan asara" Ta fada tana jin wani gumi yana yanko mata,can qasan zuciyarta tana sake tsananta takatatsantsan a dukka maganarta,kada ta furta wani abu da zai tona binnnan sirrinta.

"Yanzun in sha Allahu zamu cika umarninki uwar gijiyarmu". Sanda suka tashi suna barin gurin bayansu tabi da kallo,tana jin kamar taje tare dasu ta gani. Gidan nan ne ya cinye da wuta kamar yadda zuciyarta ke raya mata?.....gidan nan ne daya qunshi babban sirrin da bata dashi a duniya gaba daya kamar yadda jikinta da zuciyarta suke bata?,ko kuwa hasashe ne kawai na zuciya.

"Ina tamim qarami?" Ta jefawa tafisu tambayar tana jin tashin hankalin da bata taba jin irinsa ba a kaf rayuwarta,bacewar tamim a karom farko tun bayan faruwarta taji ya zame mata barazana,irin barazanar nan me wawakeken gibin da ba wani abu da zai cikeshi. Sanda tafisu ta motsa da niyyar cewa wani abu takun da sukaji daga bayansu ya sanyasu waiwayawa gaba dayansu.

Idan akace mata anji qugin da cikinta ya debo tun daga qofar gate na farko na gurin ba zatayi yunqurin qaryatawa ba ko sau daya. Iya abinda take gani cikin fuskar tamim kawai qarami kawai ya gaya mata cewa yau tana fuskantar rana mafi muni cikin rayuwarta.

"Ranki ya dade......gidan villa ya qone......ba alamin burbushin me rai......ba babana.......ba kowa cikin mutanenmu" Ya fadi yana kecewa da wani irin kuka tamkar qaramin yaro.

"Gidan villa?,wanne gida ne a villa din dani kaina bansan dashi ba?" Tafisu ta tambayi kanta da kanta,saidai sanda tayi nufin maida dubanta kan mammina ko zata samu wani haske game da gidan........saita tsinciki miqewar mammina din da wani irin hanzari,miqewar kuma da tayi daidai da debeta da jiri yayi,ba zaton tafisu ba zaton tamim qarami ta tafi luuu gefan fuskarta ya daki kujerar. Banda tafisu tayi zafin naman tareta ba abinda zai hanata ta sake kifawa taci da baka. Cikin tashin hankali tafisu ta riqeta sosai tana kiran sunanta a jejjere hankalinta a matuqar tashe.

Duk da cewa ruhinta dama dukka hankalinta suna shirin yin qaura daga ainihin wannan duniyar da muke ciki amma hakan bai hanata tunawa da makomar abubuwa masu dama data binne cikin gidan ba.

"Tamim babba wanda da bayyanarsa gwara alqiyama ta tashi gaba daya......gwara a tattara a wuce zuwa filin hisabi zaifi mata sauqi......JINJIRI da har yanzu bata gama tsaida matsaya akan rayuwarsa ba......duk tana jagwalgwalawa gami da juya akalar rayuwarsa yadda taga dama.......gudaddun masu laifi daga kurkukun qasar Ethiopia masu tarin yawa.......masu muggan laifin da wasuma an rufe file dinsu da sunan sun mutu. Bakinta take son motsawa ta fadi abubuwa masu yawa da suke zuwa kanta a sannan,duk da ta sani wani binnannen abune da koda tafisu saninsa yayi nisa da tunaninta....... Cikin qanqanin lokaci ta sulale tayi relax sosai a jikin tafisu tana fita daga duniyar da muke ciki zuwa wata duniya ta daban.

Yadda tayi a jikin tafisun ya bawa tafisu tsoro,lamari ne na matar maimartaba gaba daya. Ta tabbatar inda cikin hayyacinta mammina take ko jingina da jikinta ba zatayi ba duk da yadda tayi imanin tana amfanarta ne kawai,dole tsoro ya shigeta,ta kurma ihun kawo dauki,cikin sakannin da basufi qiftawar ido ba gurin ya samu daukin hadiman dake da ikn yin zirga zirga a rea din

*A K H N A N*

Ko kadan bataji wani abuba wai don ta dakatar da mammina daga gurinta ba,hasalima karatun da takeyi sai ya mantar da ita komai da kowa.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sanda ta kammala littafin,ta lumshe idanunta a hankali tana rungume littafin a qirjinta. Ba abinda ke mata yawo akai sai dabi'un ma'aiki masu ban sha'awa da qayatarwa. Dabi'un sanyin hali,kawaici haquri tausayi kyauta da martabawa mutum koda bawa ne. A hankali ta koma kan mu'amalarsa da iyalinsa,bata taba karanta labarin madaukakin mutum wanda bai dauki kansa komai ba a gurin iyalinsa ba irin annabin rahama. Ta saki murmushi kadan sanda ta tuna inda ta karanta,nana aisha tabi sahunsa sanda ya zame jikinsa daga makwancinsa don zuwa ziyara maqabartar baqee'a(yakanje nemawa al'ummarsa da suka rasu sassauci),ta dauka zaije dakin daya daga cikin kishiyoyinta ne,sanda yake dawowa ta dawo da gudu gudu don ta rigashi isowa daki,ta koma ta kwanta luf,saidai yana kallonta da yanayin yadda qirjinta yake dagawa ya fahimci komai,yayi murmushi. Sake murmusawa itama tayi tana shafa lallausar sumar saman kanta da dankwalin yadan zame kadan.

"Kishi?" Ta fada a hankali kamar tana tambayar kanta da kanta. Saita juya idanunta kadan,tana sake tambayar kanta......akan waye zataji irin wanna kishin?,ko akwai lokaci?,ko akwai wani da zata iya jin halittar kishi haka a kansa?.

"Muhammad haisam ne" Kai tsaye taji zuciyarta ta jefa mata amsar. Guri daya ta zubawa ido,tana jin shakka akan hakan.

Wanne matsayi ya taka a ranta da zuciyarta da zataji irin haka a kansa?,DABI'U ta yarda dabi'unsa nargartattu ne......musamman a yanzu data sake karanto daga inda yake koyinsu......suna masa kyau kuma.......ta yarda da haka,suna qara masa wata irin kamala.......amma shike nufin lallai zata soshi.

"Allah ya taimakeki" Taji an fadi daga gefanta. A nutse ta daga idanunta tana duban birra dake rusune daga gefanta.

"Inata magana......amma kin zurfafa a tunani.....ban taba ganin irin wannan zurfin tunanin daga gareki ba......Allah yasa lafiya" Idanu ta zubewa birra din,a tsakanin awannin nan......tsakanin awannin da komai ya wakana zuwa yanzu wasu irin sauye sauye take gani. Basarakiya ce ita.....wadda ta rayu cikin sarauta da mulki,tana iya karantar kowanne motsi hali da dabi'ar abinda ke kewaye da ita idan ya sauya.

Da yawan hadiman dake mata tattaki yayin fita wani guri ko cikin gida idan ka debe su birra basu bane yanzu. Yaushe aka canzasu?,waye yayi canjin ba tare da masaniyarta ba batasan wannan ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Yaushe kika koyi bin qwaqwqwafina?" Rusunawa birra tayi sosai.

"Tuba nake.......kawai ina qoqarin kiyaye amanar da sheikh yabar mana ne". Shuru ta sakeyi,kamar kowanne lokaci idan birran ta fadi wani abu daya dangaceshi.

Tafiyar kwana uku yace zaiyi......amma batasan ina zaije ba.....wa ya sani cikin qasarsu?.

"Yaushe kika fara damuwa da abubuwan da basu shefaki ba?" Taji zuciyarta tana mata tambayar data sanya komai nata tsaiwa cak. Siririn tsaki taja......ya akayi take dulmiya kanta a hankali akan lamarinsa?.

"Ki bawa barratu litattafan nan ta wuce dasu.......zamu qarasa sassan morsa safiyya" Ta furta tana jin ya kamata ta amsa kiran nata.

*M O R S A S A F I Y Y A*

Kusan komai ma da yake faruwa cikin gidan a yanzu ba damuwarta bane......kusan duk wani abu dake wanzuwa batajin yana cikin damuwarta. Damuwarta daya ce AKHNAN biftun safeena.......kuma ta tabbatar ta shiga hannun da koda ita daya ta rage a duniya ba zata wulaqanta ba muddin shine mijinta.

Ta kammala komai.......idan akace komai ciki harda rabon lafiyayyen invitation din gayyatar bikin da ta tsara yi na kwana biyu kacal. Bikin da tayi wani irin gayyatar girma da ba wanda yasan plan dinta na hidimar. Kowa ma tanason masa ba zata ne,wani irin bikin na zallar gargajiya da al'ada wanda aka haura shekaru hamsim ba'ayi irinsa ba.

Komai da komai cikin gidan ta tsara za'a yishi ba tare da an fita ko ina ba. Ta gama tanadarwa akhnan komai.......idan akace komai komai da uwa ke tanadarwa d'iyarta da zata aurar auren ma irin auren farko dinnan.

Lokacin da suka tattauna da sultane kuma akan falaak,akan maleek dakeson a yarje masa auren falaak sai taji hawaye yana taruwa cikin idanunta. Wane irin karamci wannan daga ubangijinta?......irin karamcin da bata taba zato ko tunani ba?. Aminin sheikh haisam ta tabbata sheikh haisam dinne,banbancin da zai zama a tsakaninsu d'an qanqani ne.

"Me zamu jira Allah ya taimakeka?.......me zai hana a daura auren ayi hidimar dukka lokaci daya?" Ta fada tana jin nutsuwa da gamsuwa har cikin ruhinta. Ko ba komai ta sani.....aminin haisam komai nasu zai iya zama daya kaman yadda qasarsu take daya.......kasancewar falaak tare da maleek zai zama tamkar kasancewar falaak din da akhnan ne. Wannan kadai zai sassauta zai kuma ragewa akhnan kewar gida......zai kuma sake bata daman tattara hankalinta gami da rage qiyayyar auren a ranta.

Murmushi sultane ya saki yana jin wani farinciki shima......farincikin da ya tabbatar ya haura wanda morsa safiyya keji.

"Da sauri haka safiyya?". Qasa tayi da kanta tana murmushi.

" Ba domin ita ba......sai don jin dadin d'iyata.....saidon diyata taji cewa ba ita kadai bace tabar gida" Murmushi ya sake kubce masa,yana mamakin yadda a komai morsa safiyya ke fifita masalahar akhnan sama data kowa......koda kuwa d'iyan cikinta ne......anya akwai qanwar uwa a zamin nan irinta?.

"Wato harda ke hairaan.......aka hadu aka yiwa diyata fashin miji.......sheikh ta gani takeso......amma kuka mata taron dangi kuka hadata da abokin sheikh?". Murmushi da yafi kama da dariya dukkansu sukayi,morsa safiyya na mamakin yadda yaji zancan. Duk da tasani,shi din aminin 'ya'yansa ne,mulki ko wani abu makamancinsa bai hanashi jan yaransa a jiki ba.

"A duk sanda bawa yabar wani abu saboda girman zatin Allah.........a duk sanda wani bawa yabar wani abu saboda maslahar dan uwansa........saboda danuwansa ya samu.......to lallai Allah zai musanya masa da abinda yafi zama alkhairi" Kai sultane yake jinjinawa. Wannan hankali da nutsuwa ta hairaan ya sanya ko yaushe yake jin kamar daga jikinsa ta fito itama.

"Haka yake.......munyi magana da Muhammad........kuma na samu gamsuwar shida maleek duk daya ne.......a ranar juma'ar nan,iyayen maleek zasu iso daga masarautar gera,inda mahaifin maleek ke sarautar yankin.......abokina bobbo muhammad dawud ya sake bani tabbaci a kansa......ranar juma'ar zai d'aurawa falaak aure da maleek......kwana shida suka rage kacal a yanzu......amma kuma.......inason suma saudiyya ya zamana guri na farko da zasu fara zuwa itama don su nemawa kansu da kansu albarkar aurensu.......zan bude ticket na sheikh da akhnan da qarin kwanaki daban......zan baki dama ki gudanar da bikinki don nasan kina da buqatar hakan......zan hada tafiyarsu tare kwana biyu da gama bikinki". Wasu irin hawaye morsa safiyya taji......wani hawaye me yawa da wani irin d'umi yana bin kuncinta. Ba zatace sultane baida wani alkhairi a tattare da ita ba......ba zatace sultane bai mata kowanne alkhairi ba iya zamansu.......amma dai wannan......wannan damar da wannan abun da yayi mata yana cikin manyan abubuwan da idan zata lissafa zasu kasance cikin sahu da list na gaba gaba.

A ranta takejin dukkanin burikanta sun fara cika.........burikanta burikan safeena......tana jin kamar ta fara cikawa safeena wani sashe na burinta.......idan har ta kammala da wannan........ranta zai zama fansa ne gurin bankado inda AHMED da jaririn safeena na ajani suka bace......koda hakan shine zai zama fansa kuma sanadin ranta.

*Akhnasaim tales*🤍

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽