Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 7

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 7

.....he blinked, he remembered her with her beauty, her soft words, and the love she showed him. The goods have been collected before two o'clock, two drivers are waiting for them in front of the door of the trucks that will pass and take them to the airport. Everything is going according to plan, as befits people who live in comfort and dignity. It was 2:30 and forty minutes past one on her twin Cartier watch, when the call came in from Habibie. His soft and calm voice filled her ears with a style that energized her even when she was tired. He told her that their flight will leave around 5:00. This made her hurry back to her room to fix her body. She did not take time to choose an Arabian abaya with embroidery like Al-Zahra Collections abaya with embroidery like Amirat with red color and silk lace that covered her body in style and elegance. She hung Van Cleef & Arpels earrings, and sprayed her Oud Royal perfume from the floor to the top. She stood in front of the mirror and looked at herself. Her face is full of radiance, not to mention her smooth skin. Then she took her Chanel handbag.....

Standalone post2,066 words

SHAFI NA BAKWAI

Gaba ?aya zuciyar Ayshatu cike take da rudani da rashin kwanciyar hankali. Duk da cewa tafiyar za ta ba su damar yawon ?asashe masu kyau, bata jin da?in barin Habibie a baya. Kishinta yana ratsa jijiyoyin jikinta kamar wutar lantarki mai ?arfi domin ita ba ta jin za ta iya yin nesa da shi ko da na ?an lokaci ne.

A wannan karon, sai ta lura Habibie yana da wasu abubuwa masu matu?ar muhimmanci da ke gabansa abubuwan da suka fi tafiya a wurinsa. Wannan ne ya saka mata wata irin fargaba da ba ta ta?a ji ba a baya. Kullum bayan tafiyarsa, sai wani labari ya riske ta ko dai an daura masa aure, ko kuma an tsayar masa da wata magana. Saboda haka, wannan karon zuciyarta tana kukan shiru tana tsoron sake kasancewa a sahun baya a rayuwarsa.

Amma duk da haka, tana da tabbacin babu wata mace da ta ?auki gurbi a zuciyarsa irin nata. Saboda haka, kafin tafiyarsu, tana ?o?arin bar masa wani ?amshi wani salo na musamman da zai kasance masa kamar alamar tunawa. Wani abu da duk lokacin da ya ?an lumshe ido, ya tuna da ita da kyanta, da lafuzanta masu taushi, da ?aunar da ta dora masa.

An gama tattara kayayyaki tun kafin ?arfe biyu, direbobi biyu na jiran su a gaban ?ofar manyan motocin da za su wuce su kai su filin jirgi. Komai yana tafiya bisa tsari, kamar yadda ya dace da mutanen da ke rayuwa cikin jin da?i da martaba.

Karfe biyu da rabi da mintuna arba in da ?aya kenan a agogon tagwayenta na Cartier, lokacin da kira ya shigo Habibie ne. Muryarsa mai laushi da nutsuwa ta cika kunnen ta da wani salo da ke sanya mata kuzari ko da ta gaji. Ya shaida mata cewa jirginsu zai tashi da misalin ?arfe hu?u. Wannan ya sa ta hanzarta komawa dakinta domin gyara jikinta.

Ba ta ?auki lokaci ba wajen zabar Arabian abaya mai ?inki irin na Al-Zahra Collections abaya mai dinki irin na Amirat mai launin ja da yadin siliki wanda ya rufe jikinta cikin salo da ladabi. Ta rataya ?an kunne na Van Cleef & Arpels, sannan ta fesa turaren ta na Oud Royal daga kasa har sama turaren da ke saka kowane numfashi ya kasance kamar wata zallar sa?o na ?auna.

Gaban madubi ta tsaya tana duba kanta. Fuskar ta cike da annuri, ba sa?ani da fatar ta mai santsi. Daga nan ta ?auki handbag ?inta na Chanel sannan ta rufe dakin da natsuwa, ta nufi babban bangarensa.

Da ta shiga babban falonsa wanda aka yi wa ado ba ta same shi ba. Ta wuce cikin nutsuwa zuwa ?akinsa, tana bubbuga ?ofar da taushi sannan ta shiga. Ta saki sallama cikin ladabi yayin da idanunta suka sauka a kansa yana waya, fuskar sa cike da annuri da murmushi. Ba sai an gaya mata ba, ta san da Hajja ce mahaifiyarsa yake waya, domin ita ka?ai ce ke da ikon motsa masa zuciya da dariya haka.

Tsit... lokaci kamar ya tsaya. Wani irin salo na ?auna da cikar burin zuciya ya lullube Ayshatu, tana kallon Habibie da wani irin shau?i da ko cikin mafarki ba ta ta?a tunanin za ta iya ji ba. Tana ?arasowa, ?amshin turarenta mai kyau na Oud Royal yana gauraye da dumin sutturar ta, Arabian abaya mai ?inke na sarauta da launin zinariya wanda ke zubewa a jikinta kamar ruwa a kan yashi mai laushi.

Ba tare da wata fa?a ko wani bayani ba, ta fa?a masa jiki. Rungumar da ta fi kowacce magana da kalma, tana nemansa kamar wacce aka ?wacewa iska. Sai da ya gama sallama da mahaifiyarsa cikin ladabi da annuri, sannan ya ?auki lokaci yana kallonta idanuwanta cike da hawaye masu nauyin ?auna.

"Please, Habibie... bana son yin wannan tafiyar... ba tare da kai ba." Ta furta cikin wata irin ra?a mai ?ayatarwa.

Wani murmushi mai ?auke da jin da?i da mamakin zurfin soyayyarta ya bayyana a fuskarsa, yana jawo gefen kuncinta da yatsansa mai sanyi da tsabta. Kafin ya kai ga amsa, sai ta kai bakinta cikin nasa ta masa wata mahaukaciyar sumba mai cike da tsananin da?i da bu?ata. Jikinsa ya birkice. Numfashinsa ya ?ara nauyi. Idanunsa suka lumshe da tsantsar jin da?i.

Yana ?o?arin daidaita kansa ne ya kalli Rolex ?in hannunsa. Mintuna uku suka rage kafin jirgi ya tashi. Yayi ?o?arin zare kansa daga cikin wannan narkakkiyar soyayyar, yana ce mata da murya mai cike da kwantar da hankali

"Ki sani Ayshatu, ko cikin aljihun zuciyata zan tafi da ke."

Sai ya kama hannunta, sannan ya ce

"Mu tafi. Zan rakaki filin jirgi da kaina."

Ta zube masa murmushi mai cike da cin nasara da jin ?auna. Ita dai ta san ta kar?e dukkan tunaninsa. A motar suka wuce motar da aka zana tana masa addu ar samun lafiya da kariya daga sharri.

Yayin da suke yin sallama a Airport ?in, Ayshatu ta jinkirta da gangan tana kallon yadda iska ke ka?awa a rigarsa mai alamar Zegna. Ta kama hannunsa a karo na ?arshe, ta fesa masa ?amshinta, sannan da murya mai ra?a ta furta

"Kada ka bar kowa ya raba ni da kai, Habibie... Allah ya tsare ka."

Daga nan ta juya cikin tafiya mai cike da izza da tausayi, zuciyarta cike da fatan cewa ?aunarta za ta kafa sansani a zuciyarsa har abada.

Ko da ya koma gida, ya yi gaggawar shiga cikin babban ?akinsa mai ?amshi da kwanciyar hankali. Wanka yayi da sabulun Arabian oud mai ?aukar hankali, sannan ya saka riga da wando na tsadaddan yadi kaya masu launin zinariya da shudi, ha?e da takalmansa na Ferragamo. Tufafin da suka ha?u da halittarsa suka ?ara fito da cikakken surarsa ta namiji wanda ya saba da alfarma.

Yayin da ya fito daga ?aton falonsa, ya tsaya gaban layin motocinsa G-Wagon, Maybach da kuma Lamborghini mai launin zinariya. Idanunsa suka sauka a kan wata mace dake tsaye a gefe, cikin shigar abaya mai she?i, gefenta kuma na ?auke da ?aramin bag.

Bilkisu ce.

Zuciyarta ta soma harbawa da ?arfi, kamar zata fito waje. Ta tsare shi da ido, kamar wacce take so ya karanta tunaninta. Murmushi ya kwanta a fuskarta, amma zuciyarta na tsaka da tafasa da addu'a "Ya Allah, ka sa ya ce yana sona... Ya aure ni... Wallahi da na more mijin kirki."

Kamar wanda ya karanta zuciyarta ne, Habibie ya ce da wata murya mai sanyi da izza

"Muje ko?"

Wani sanyi ya ratsa Bilkisu. Zuciyarta ta kada kamar gangar sarauta. Ta ce cikin fara'a

"Tohm, Dady."

Ta ?auka motar da za su shiga ?aya ce. Sai dai sai ta ga shi ya nufi wata daga cikin tsadaddun motarsa Range Rover mai sunan sa a lambar ita kuma direban gida ya bu?e mata wata daban.

Murmushinta ya ?an dushe, amma har yanzu zuciyarta cike take da fatan alheri. Ta ?ora hannunta kan ?irjinta, tana lumshe ido tana cewa a hankali "Ko da ba a tare ba yanzu in Allah ya yarda, zan kasance matar gidan nan."

*******

A cikin kwanaki biyu da suka gabata, gaba ?aya na fara lura da sauyin jikina. Kibar da na tara ta ragu sosai, jikina ya fara komawa yadda yake da. Allah ne masani burina kawai shi ne in ga ni na zama cikakkiya, kamar yadda sauran 'yan ajinmu suke.

Amma fa fargaba nake sosai, domin bayanan da nake karantawa game da illar magungunan ?ara kiba na sa ni jin tsoro har cikin ?ashi.

Yau Juma a ce ranar karshe ta jarabawarmu. Ni dai, Ramlah, nasan ban shirya sosai ba. Ayyuka sun yi mun yawa, har ba zan iya cewa na tsunduma cikin karatu yadda ya kamata ba.

Da na ga har ?arfe shida na safe ne, sai na sa gaggawa. Na shiga kitchen da sauri, na dafa chips da kwai, na zuba a food flask dina. Na rantse ba zan yi girki da Momy ba yau. Jiya ma ta gayyato kawayenta, ni kuma ta tura ni na dafawa musu mandi da kaza da salad amma fa, wallahi, sai da ta rabar musu abinci. Na bar gurin cikin ?acin rai, sai lemo da biscuits kawai na ci. Ina cewa zan yi magana, sai ta watsa mun banzan amsa

"Rashin kunya za ki yi mun ne, Ramlah?"

Abu kafan ya rage, sai na ga zata kai ta hada ni da Abba. Na yi shiru, na janye na bar wajen. Ko gyara gidan banyi ba yau ta san yadda aikin gida yake.

Murmushi ne kawai ya subuce mun yayin da na ?auki kaya kala ?aya, na sanya a cikin jakar makaranta na fita.

A filin gidan na tarar da Abba yana lazumi. Na gaidashi cikin ladabi, sannan na shaida masa

"Abba, yau zamuyi practical a makaranta, za mu gama 6. Malam Idi ne zai zo ya ?auke ni."

Ya ?ago kansa, ya kalleni da kulawa, sannan ya yi mun addu a da fatan alheri. Sai ya ?ara mun ku?in makaranta.

A mota nake cewa da Malam Idi: "Anjima, dan Allah zaka kaini gidan Mama. Bata jin da?i. Amma don Allah, kada ka fa?awa kowa."

Ya saki dariya yana cewa "Haba, kar ki damu, babu wanda zai ji."

Gimbiya Momy bata farka daga baccin hutunta ba sai bayan ?arfe takwas na safe. A hankali ta mi?e daga gadonta, tana lumshe ido kamar wadda ta yi dare tana faman tunani ko gajiya.

A lokacin Abba ma ya tashi, ya kammala shiri yana fatan fita da wuri, sai dai da ya sauko falo, abu na farko da ya lura da shi shine babu breakfast a kan dining table. Ya tsaya cak, ya ?an yatsina fuska yana kallon tagar kitchen.

Momy tana zaune a kan kujera tana gyara zaninta, sai ta ce da shi cikin murmushin rainin hankali

"To, Ramlah batayi bani ba??

Idanun Abba suka ciko da mamaki da ?an ?acin rai, ya ce cikin murya mai ?an ?arfi

"Ramlah ke da hakkin dafa min abinci yanzu? Ita matar gidan ce? Ko ita kike so ta rika rikewa alhakin aikin da ba nata bane?"

Maganar ta yi mata zafi. Bata ce komai ba, sai kawai ta mi?e cikin fushi, ta shige bandaki da hanzari. Brush kawai tayi sannan ta fito, ta sakko ?asa. Da ta sauka, ta tarar da gidan kamar yadda aka bar shi babu gyara, babu motsi, babu tsafta, komai a hargitse.

Wani irin takaici ya tsaya mata a kirji. Ta cika da bacin rai

"Wallahi zan dawo na sameta! Karfe goma sha biyu zamu fita! Wannan shegiyar yarinyar da ke tazamemun karfen kafa, sai na yi maganinta, ni ba zan ?yale ta ba!"

Ta gama masifar ne tana shirin kai abincin karin kumallo wa Abba. Sai dai duk yadda ta ?o?arta, ta kasa nutsuwa. Kitchen ?in da kanta ta bu?e shi sai da ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta na suya kamar ana hura mata wuta.

"Yau zan kar?i ba?i. Bilkisu ma zata dawo. Gidan haka? Kitchen haka? Allah Ka sani, ba zan iya haka kullum ba."

Tana kallon komai a cikin gidan, sai da ta ?an zauna a jikin bango ba saboda gajiya ba, sai don damuwar da ta yi nauyi a jikinta.

Sai ta ?auki waya cikin takaici, ta kira wata lamba.

"Kawata , dan Allah ki zo nan gida anjima... akwai maganar gaggawa."

"Lafiya dai, zainab?" muryar ta fito da damuwa.

"Wallahi sai na ci uban Ramlah! Yarinyar nan ta isheni! Wallahi na gaji da ita!"

Momy kuwa, da ta kai wa Abba abinci ?akinsa, sai ta shigo da sallama da kissa, tana ?auke da fuskar fara a kamar wadda ba ta da wata damuwa.

Ta ajiye flask ?in a gabansa, tana ha?a masa shayi da kulawa, sannan ta ce da sassanyar murya

"Ka yi hakuri Abban Ramlah. Auta ce da kanta ta ce min zata dafa maka kosai da kunu da safe, tunda ta ga kana so."

Ta ?an lumshe ido sannan ta ci gaba da magana "Ina jin ko yau ta makara ne daga bacci, shiyasa bata samu tayi maka ba. Allah ya huci zuciyarka, ayi hakuri."

Ta ?arasa ha?a masa shayin tana kallonsa da tausayi. "Auta ai tana ?o?ari. Allah dai ya albarkace ta, ya kare min ita."

Daga ?arshe sai ta ?arasa da fatan "Allah yasa taci wani abu kafin ta fita, kada ta tafi da yunwa."

Abba dai ya zauna yana sauraren ta ba tare da ya ce uffan ba. Sai kawai ya ?auki shayin ya ?an kur?a.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH