
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 15
.....nun his, something melted her heart very much the first time. She recognized the sultan's fingers on his hand, their length and the shape of their fingers, even the size of his thumb was the sultan's. "Even if you go to the police station, I will come, I hope that I will be like a sultan for you, right? I heard you say that he is a substitute for a father" She felt a cold feeling that was slowly passing through her heart. In the past, where is he here?, where is he living, is he going to give her advice?, is she going to complain to him? His eyes are not open, but his ears are in the same place, especially when the stick reaches in front of them... especially when the stick puts her hand in his and he feels something standing on his neck. It is halal...not haram, he is my blood cousin, same mother, same father, but just like that, a fire of jealousy was planted on top of his soul. "I have made peace with Muhammad.......let me say goodbye until tomorrow?" The Sultane said something great coming out of his eyes to Haisam. He feels a kind of love for Haisam more than he loves his children, he doesn't know if in the future he will love Ahmad like this or more than that?. Miqewa ma
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 15*
"Ni sunana ahmad,kefa kefa?" Ya fada yana dubansu dukka su biyun.
Murmushi ya kubcewa falaak sosai da yafi kama da qaramar dariya.
"Yaya ahmad.......ni sunana falaak.....ita kuma khadeeja,akhnan ko biftu,daa itace babba,amma yanzu tunda ka dawo kaine babban" Saida sukayi murmushi dukkansu harda ahmad din. Ya maida dubansa akan akhnan,har yanzu batayi magana ba. Da gaske dai haka dabi'arta take.....haka yanayinta yake,ba wani abu bane daban da a baya ya dauka. Ya hadiye wani yawu mai tauri da quna......ya dinga maimaita furta.
"Alhamdulillah" Da tuni qanwarsa yake aure?,da tuni zuwa yanzu alaqa da mu'amala tsakaninsu tayi nisa?. Da mummunan nufin wancan shaidaniyar ya cika da yanzu me kenan?.
Hannunsa ya miqa musu dukka sun biyun son suyi musabaha,sai falaak ta dora nata akai,amma akhnan saita noqe.
"Ehemmm......ko har yanzu ban shiga cikin ahali ba?" Ya tambayi akhnan yana dubanta. A hankali ta sauke idanunta akan hannun nasa,wani abu ya narka zuciyarta sosai tashin farko.
Yatsun sultane take gane a nasa hannun,tsahonsu da yanayin zubinsu,hatta da girman babban yatsansa na sultane ne,sai ta miqa masa nata hannun a hankali dukka ya hadesu guri guda nashi dana falaak da akhnan din.
"Duk da zaku tafi a sanda ni nazo,ina fatan zan zame muku kamar sultane ko?,babban yaya naji kuna cewa shine madadin uba" Wani sanyi taji yana ratsa zuciyarta a hankali.
A baya inda yana nan?,inda yana rayuwar ta qila shine zai dinga bata shawara?,shine zata dinga kaiwa kokenta?,shine zai duba daidai daba daidai ba qilan sama da yadda sultane yayi?.
Idanunsa basa kansu,amna kunnuwansa suna gurin,musamman sanda ya isa gabansu......musamman sanda ta sanya hannunta cikin nasa sai yaji wani abu ya masa tsaye a wuya. Halal ce......ba haramun ba,dan uwnata ne na jini,uwa daya uba daya,to amma haka kawai wani wutar kishi ta d'isa saman ransa.
"Na tsaidaka muhammad.......bari na barka haka sai gobe?" Sultane ya fadi wani girma yana fita daga idanunsa zuwa ga haisam. Wata irin qaunar haisam din yakeji sama da yadda yakejin ta yaransa,bai sani ba ko a nan gaba zai qaunaci ahmad kamar irin haka ko sama da haka?.
Miqewa yayi fuskarsa adan sake,yana bawa sultane hannu sannan ya juya a nutse ya fara takawa don ficewa daga gurin.
"Biftu......tashi ki bishi" Morsa safiyya ta furta da muryarta data dakushe kadan saboda kukan dazu. Tana ankare da ita......kamar bata gaidashi ba,hakanan bata bashi attention din daya dace ta bashi ba. Tana tsoron yadda akhnan din zatayi zaman aure......irin zaman auren nan da ake cewa iya zama ya sanya mace ta kame zuciyar mijinta. Ta sani akwai tarin naqasu dama gyare gyare,amma abinda yake bata nutsuwa da kwanciyar hankali nau'in mijin data aura din.
A hankali take takawa,iskar da tun da yamma bata yankewa duniya ba tana ci gaba da kadawa cakude da qamshin qasa da kuma sanyin da hadarin ya bari,saidai sanyin ya yiwa halittu da dama dadi,saboda baiyi yawa sosai ba saima wani shiga jiki da yake yana sanyayar da zukata.
Kamar yadda hanyar take a baya,shuru don ba hanyar shigar kowa bace.....shimfide interlock da bishiyoyi hagu da dama dake sake bawa gurin yanayi me kyau.
Duk taku daya sai taji zuciyarta ta buga kafin a hankali ta soma jiyo wannan mayataccen qamshin. Cak ta tsaya,don idanuwanta dai basu gano mata shi ba,a hankali ta soma juyawa zuwa bayanta zuciyarta na wani motsawa da wani irin yanayi.
Yana tsaye tsaf daga bayanta. Dukkanin hannuwansa cikin aljihun kuftar jikinsa.
Lafiyayyen tsadajjen yadin kuftar da aka yiwa aikin sarauta wuya da hannu da bakin aljihu qasan wando harma da gefe da gefan rigar.
Yayi wani irin sassanyan kyau.....karon farko data ganshi cikin shigar da bata taba ganinsa da ita ba. Shigar ta wani amsheshi,tabi jikinsa.....zaka dauka ya hada jini da al'ummar nigeria......qasar hausa,bakano wanda cikin jerin jinsin mazan da sukafi mazan kowanne gari sanin haqqin wanka,saidai kuma kash.....wannan sassalkan gashin nasa dake kwance saman kansa.......wannan zubin nasa daya banbanta da qira da siffar kanawa ko qasar nigeria......shine abu daya da zai gaya maka wani qabila ne daban da bahaushe ba.
Inda zata iya buda baki tayi magana,abinda zatace masa shine.
"Kaci gaba da saka irin wadannan kayan.....suma sunayi maka kyau kamar yadda cloak thobe ke maka" Saidai bugawar da zuciyarta keyi ma bazai bari komai ya fita a bakinta ba.
Tana jin nauyin idanunsa a kanta sosai.....suna mata wani irin tasiri da taji kaman tana son daburcewa,ta rasa wanne irin idanu ya mallaka masu kaifi da kwarjini har haka?.
Wani abu yake gani cikin idanunta,wani abu da yaja ra'ayinsa kadan,ya sanyashi sake cusa hannuwansa a aljihun rigarsa. Kansa ya karkatar kadan yanason lalubo qwayar idanunta,amma kuma ya gaza yin hakan sam saboda yadda taqi daga fuskarta da kyau.
Ya kafeta da idanu....baice mata komai ba......bai kuma bata hanya ba,hakanan ya daureta sosai da wannan idanun nasa masu tsananin kwarjini.
Daburcewa ta soma ji sosai cikin jikinta......ta soma complain ita daya qasan ranta.
"Yasan kaifin idanunsa akan dan adam kuwa?" Ta tambayi kanta da kanta,tambayar da babu abinda ta qara mata sai rudewa.
Can qasan ranta kuma har yanzu da wannan feeling din,kwana biyar yayi maimakon hudu,a kwana biyar din bai nemi koda wayarta ba,bayan sun hadu kuma by incident sai ya sake bace mata?. Sai a yanzu ta ganshi a gaban kowa?. Kuma ko bayan ya gama zamanshi bataga ya kalli koda inda take ba?,hasalima sai ita aka yiwa tayin binsa?.
"Kaman girmana ya tabu" Taji can qasan ranta wata zuciyar tana gaya mata,hakan yasan ranta yadan tabu kadan.
"Ko zan iya komawa?" Ta fada da muryar nan tata me wani irin laushi.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Iska sosai yaja,wata irin iska data zuqo masa dukkan qamshin dake fita a sanyaye tun daga gashin kanta zuwa sassan jikinta. Ya fesar da iskar a hankali yana lumshe idanunsa gami da budesu.
Yadda take avoiding kallonshi tun a wancan ranar.....akwai wani abu cikin idanunta da yake karantarsa tas. Yana da wannan baiwar......baiwar iya karantar dan adam da tunaninsa ta cikin ido.
Sosai take sake jin yana aza mata nauyi,tana jin kamar ta daga idanunta ta kalleshi......kamar ta daga kanta taga meye ya tsaidashi?......bai amsa mata ba,kuma bai tafi ba,bai kuma barta ta samu daman tafiya ba.
Tarin da taji yadan fara yi kaman ya qwarene ya sakata daga kanta da sauri,saurin daya haifar da shigar qwayar idanunta cikin nasa,fuskarta a dan yamutse da alamun tsoro na tarin daya sarqeshi,saidai suna hada idanun saita sameshi qyam a tsaye,ba wani alamun jigata ko kuma sarqewar tarin kamar yadda taji sautin.
Wani irin riqe qwayar idanunta yayi cikin nasa. Sosai ya nutsa qwayar idanunsa cikin nata,ya lumshesu sau uku yana budesu duka cikin nata da wani irin yanayi na qwarewa wajen sarrafa dan adam ta cikin idanuwa kadai.
"Duka fushin na meye?" Ya furta da wani irin soft and cool voice,ba taushi da sanyin muryar ba kawai.......can cikin sound dinsa akwai wani irin deep abu dake ajiye magana sosai cikin kunnuwa da qirjin me sauraro.
Ji tayi kaman qafafunta suna lanqwashewa,kallon yayi mata nauyi da zurfi da yawa,inda ace tana kusa da wani abunne tabbas da zai taimaka mata qwarai,don zata dafashi don ta samu daidaito gurin tsaiwa.
"Ehmmmm?" Ya fada still yana hana idanunta motsawa daga cikin nasa. Kallon kallo ne ya sake wanzuwa tsakaninsu,kallon da ita daya tasan me yake ajiye mata a gangar jikinta da zuciyarta,sawa yake kowacce gaba ta jikinta tana laushi.
"Akhnan ce fa?,princess akhnan" Wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita. Wannan shine ya bata wani qwarin gwiwa,qwarin gwiwar zame idanunta sannan taja da baya kafin ta juya da nufin saka nisan tazara tsakaninsu. Saidai kuma kyawawan taku uku kawai ya cike tazarar,ya kuma sha gabanta da kyau,har yana mamaye tsahonta gaba daya,yana kuma lullubeta da faffadan kafada da qirjinsa.
Haka kawai sassanyan qamshinta ya masa....haka kawai yaji kaman yayi sauri ace ta koma ciki yanzu.....kamar akwai ragowar mintuna.....kamar akwai abinda yakeson ya fada.
"Gaisuwa.......gaisuwa sai ance kiyi?" Ya fadi yana dubanta har yanzun.
"Barka da dare" Ta samu kanta da hanzarin fada. Ba don maganansa ba,sai don tana buqatar ya tallafeta ya bata hanya kafin ta gagara mallakar kanta. Koda wasa bata bari ta sake kallonsa ba,hanya kawai take nema,bata kuma ganta ba muddin bai matsa mata hanya ba.
A hankali ya sauke idanunta kan yatsunta,karo na farko daya sake ganinsu a zahiri ba a allon computer ba irin jiya. Sosai ya zube musu idanunsa. Ya sani,tun ranar daya karanta cikar sunna ga jan lalle,umarnin ma'aiki ga mata dasu zama masuyin lalle,tun daga wannan rana son abun ya shiga ransa,musamman daya tashi ya samu Nanay dinsa ma'abociyar yinsa ce,ta kuma koyawa kowa cikinsu rumaisa Anaani noorah yinsu,hatta da khansaa'u dake gidan aure.
Motsa yatsun tayi kadan,kamar tasan su yake kalla,hakan sai ya sake daukan hankalinsa,yabi yatsun da kallo yana jin kamar ya miqa hannu ya shafa yaji yaya suke?,yaya lallen yake a hannunta?.
"Zan iya samun hanya?" Ta sake fada still ba tare data kalleshi ba.
A hankali ya janye gefe yana bata isashiyar hanyar da zata wuce din. Ta qasa......ta qasan da idanunta ke zube saman rufaffun takalman qafarsa taga yaja bayan,wani abune yayi mata tsaye a rai,don tace zata tafi?,sai kawai ya bata hanya ta sauqi irin haka?.
"Kina lafiya?,ba wani matsala?" Ya sake fadi da muryar da tafi ta dazu laushi. Kai kawai ta gyada masa a hankali taci gaba takawa tana wucewa.
Baisan me ya tsaidashi a gurin ba,yaci gaba da bin takunta da kallo,abinda a yau karon farko ya fara noticing. Wani irin cat walking,kowacce qafa kaman akwai qa'dar ajiyeta.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽