Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 8

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 8

.....I am also very disturbed by this. As you can see, Bilkisu is still not stable, until she finished university. Bye, Nabila, I hate Ramla! I just want to see her life ruined. Even if I stay in this house, by the way, I don't love her." Nabila sat down, studying. "If that's the case, here are three things you should do, Zainab, stop joining her completely. Be open and show her your lack of love. Do bad things to her in front of her father every day until he hates her. For example, like today when you said that she didn't work for you, then you told him that she didn't come into the house until around eight o'clock. Make sure that his mind is very clear about her." She also laughed a little. "Since you managed to reunite with her mother's family, ruining her life will not be difficult for you. ****** We went out for a break. My aunt Fatima, she is close to my heart, she keeps giving me advice about Momy. "Ramlah, from the beginning I knew that this woman doesn't love you. You just trusted her, but by the way, your opposite mother doesn't love you. She is showing you that she cares about you, it's a lie! Oh, she says that you are like a maid in the house, you don't have any rest de

Standalone post3,572 words

SHAFI NA TAKWAS

Bayan fitar Abba, duk yadda Momy ta so ta gyara gidan, ta kasa. Ba karamin baci gidan yayi ba, hakan ya bata damar komawa baccinta. Ba a ga bakuwarta ba sai wajen karfe goma ko sha daya na rana. Da ta iso, rai a bace ta samu Momy.

"Kawata, ki daina wannan fushin," Nabila ta fara da lallashi. "Tun farko na hango miki haka. Ai ke kika dage cewa kece za ki rike yarinyar nan. Da kin bari kakarta ta dauketa tun farko, da ba haka ba."

Momy ta harareta, tana mai jin haushi. "Nabila, kinsan wanene Abbansu kuwa? Wallahi, da na bari ta rike yarinyar nan, hidimar da zai dinga yi musu ba karama bace. Ni kuma sai na dinga kuka da kaina. Tun da aka haifi Ramla, na ga yadda yake mutukar sonta. A lokacin, na so na fara lalata rayuwarta, amma sai na tuna cewa hakan zai iya raba mu, tunda ita ce weakness dinsa. Sai na yi amfani da ita wajen kara samun soyayyarsa da kaunarsa."

Ta dan ja numfashi kafin ta cigaba. "Yanzu haka, jiya yake ce min yaran abokansa kowa sai ya ce yana rikon Ramla. Ni kuma hakan na dagamun hankali sosai. Kina dai gani, Bilkisu har yanzu babu tsayayye, gashi har ta gama jami'a. Wallahi, Nabila, na tsani Ramla! Ina so kawai naga rayuwarta ta lalace. Ko zama a cikin gidan nan ma, wallahi, bana kaunarta."

Nabila ta gyara zama, tana mai nazari. "To idan haka ne, ga abubuwa uku da zakiyi, Zainab Ki daina shiga sabgarta gaba daya. Ki fito fili ki nuna mata rashin kauna da kyara. Ki hada mata sharri a gaban mahaifinta kullum har sai ya tsaneta. Misali, kamar yau da kika ce bata yi miki aiki ba, sai ki ce masa bata shigo gidan ba har sai wajen karfe takwas. Ki tabbatar da cewa hankalinsa yana yashi sosai game da ita."

Ta kuma yi dariya kadan. "Tun da kin yi nasarar rabata da dangin uwarta, lalata rayuwarta ba zai yi miki wahala ba.

******

Mun fito break. Fatima kawata, tana kusa dani ranta a bace, tana ta bani shawarwari game da Momy.

"Ramlah, tun farko na sani cewa matar nan ba ta kaunarki. Ke kawai kin yi trusting dinta ne, amma wallahi, kishiyar mamanki ba ta sonki. Wannan da take nuna miki kamar tana kulawa da ke, karyane! Ai, tana mai dake tamkar 'yar aiki a cikin gida, ba ki da wani hutu duk da irin shekarunki. Babanki kuma yana da kudin da zai ba ki gata, amma wannan ba soyayya bace. Wallahi, da kin yi hankali, da kin farka ki gane gaskiya."

"Kawata!" Fatima ta fara magana cikin zafafa, "me ya sa kike zama haka kamar wata 'yar kauye? A yanzu fa, rayuwa ba haka ake yi ba! Ai wayewa ce ke kawo farin ciki."

Na kalle ta da mamaki, "Me kike nufi, Fatima?"

Fatima ta dan dara, tana mai ciro wayarta daga jaka. "Wallahi, Ramlah, wannan tsarin rayuwa naki ya tsufa! Kina gida kullum, babu wayewa, babu nishadi. Ga wayarki nan, sai ajiye ta kike wai saboda karatu. Wallahi, mu yanzu muna TikTok da Instagram kullum! Sai ka ga mun yi bidiyo, kowa yana yabawa. Me yasa kika mayar da kanki kamar wata tsohuwa?"

Ni Ramla na gyara zama, ina jin maganganun Fatima suna bani mamaki. "Fatima, ai ba haka aka tarbiyantar dani ba. Wallahi, bana ganin dacewar mace ta dinga fita barkatai ko kuma ta yi abubuwan da ba su dace ba."

Fatima ta tabe baki, tana dariyar raini. "Ai sai ki cigaba da zama haka, ke kadai. Wallahi, ki ga ni yanzu, har hotel nake kwana da saurayina, amma babu wanda ya sani a gida. Saurayina babban mutum ne, yana kula da ni sosai. Duk wata damuwa, yana dauke min ita. Ke kuwa, ai ko saurayi ba ki da shi. Wata rana zuciyarki zata buga saboda babu soyayya, babu shakuwa."

Cikin takaici, Nace, "Fatima, ba kya tsoron Allah kuwa? Wannan salon rayuwar da kike yi ba shi ne daidai ba. Hulda da maza haramun ce, kina iya jawo wa kanki matsala."

Fatima ta girgiza kai, tana mai basarwa. "Ke dai ki cigaba da zama haka. Ki daina nuna kamar ke kadai ce mai tarbiyya a duniya. Wallahi, babu wata wayewa a haka. Ai 'yan mata masu wayo yanzu sun san yadda ake more rayuwa. Kin ga wannan katin? Birthday dina ne gobe, amma ban gayyace ki ba saboda ba zan iya daukar rashin wayewarki a wurin ba. Dress code dinmu kuwa? Mini skirt da top! Kizo ki ga yadda big girls suke rayuwa."

Na kalli Fatima cikin tausayawa. "Fatima, duk wannan ba zai amfane ki da komai ba sai nadama. Ki tuna, wayewa ba ita ce rashin kunya ko sakaci da tarbiyya ba."

Fatima ta yi dariya, ta kada kai. "Ke dai sai a hankali, Ramla. Da kin gane yadda duniya take, da kin daina wannan sakarci naki.

Fatima ta tabe baki, tana mai nuna halin ko in kula. "Ke dai ki cigaba da zama haka. Ai yanzu, har TikTok da Instagram sun zama wajibi a rayuwar 'yan mata masu wayewa. Ke kuwa, duk lokacin da na ga wayarki, sai dai ki rufe ta saboda karatu. Wallahi, akwai guys masu kyau a nan makaranta suna son ki, amma kina zama kamar wata 'yar kauye."

Na girgiza kai. "Fatima, ai ba saurayi ya kawo ni makaranta ba. Kuma wannan salon rayuwa da kuke yi ba shi ne daidai ba. Ki daina bin abin da zai bata miki suna.

Fatima ta mike, tana mai kada kai. **"Sai ki cigaba da zama haka, Ramla. Ni dai ban san yadda za ki iya rayuwa ba babu soyayya da shakuwa. Ai da kin san yadda duniya take, da kin daina wannan girmama kai da tarbiyya naki

Bayan an tashi daga aji, na tattara littafaina cikin jaka. Na jingina da kujerar karfe da ke bakin kofar ajin, cike da tunani. Ashe dai duniya cike take da rudani. Ni dai ban taba tunanin cewa Fatima, wadda na dauka a matsayin ustaziya a cikinmu, za ta iya aikata irin abubuwan da ta gaya min ba.

Ina cikin wannan tunanin sai ga Fatima ta dawo, tana murmushi kamar babu abin da ya faru. Na kalle ta cike da mamaki. "Wallahi, Fatima, ni mutuwa nayi da mamaki! Wai haka kike yi? Ni fa ke na dauka ustaziya ce a cikinmu. Ai su Maryam da Farida kullum suna cewa ni 'yar kauye ce, amma ke ce kadai kike kulani cikin ajin. Ashe duk abin nan wasa kike yi?"

Ta yi dariya, ta dafa kafadata. "Oh Ramla, ke dai ba kya wayewa ne. Ai ba dole sai mutum ya yi ta nuna tsoron Allah a fili ba. Wayewa daban take da irin wannan kamun kai. Kuma ai zama 'yar zamani ba yana nufin an daina tarbiyya ba."

Na gyara zamana, ina cigaba da nazari. Wallahi, ban gane ba. Ashe dai Fatima tana ganin wayewa daban, ni kuma nake ganin ta da wata fuska. "To amma Fatima," na ce mata, "ni fa ban taba saka mini skirt ba, kuma gaskiya ba zan zo birthday dinki ba. Wai kuma fa karfe shida na yamma?"

A nan ta zabura cikin gaggawa, tana kallona da ido waje. "Kai Ramla, kada ki ce haka! Wallahi, ba zan ji dadi ba idan baki zo ba. Ki daina wannan tunanin kamar wata 'yar ?auye. Ai ba komai bane, dama kawai kizo ki ga yadda ake nishadi. Zan siyo miki kaya da kaina, kibiyo ta gidanmu, mu tafi tare. Don Allah kada ki ki yarda."

Na tsinci kaina cikin mamaki sosai. Ashe ba kawai burinta na ganin na zo bane, har ma tana shirin yi min hidimar kayan sawa! "Fatima, kiyi hakuri," na fada cikin sanyin murya. "Ai ba zan iya saka mini skirt ba. Kuma duk da kince wayewa ce, ai ba lallai ba ne in canza halina saboda ina son na yi kama da wasu. Ni dai ban saba ba, kuma ba zan fara ba."

Sai ta marairaice, ta rike hannuna kamar yadda take yi idan tana so ta lallaba ni. "Dan Allah, Ramla! Ki taimaka min fa, kawai ki zo. Ni fa ba zan ji dadi ba idan kin ki. Aje muyi nishadi, ki ga yadda manyan 'yan mata da samari suke hutu."

Na sake jan numfashi, ina jin nauyin yadda take matsa min. Ashe dai Fatima tana ganin cewa zan iya canzawa saboda kawai na more abin da take kira "nishadi." "Fatima," na ce mata a hankali, "koda kuwa zan zo, ba zan iya saka irin wannan kayan ba. Kuma gaskiya, ki daina ganin cewa rayuwa ta dace ta zama irin wadda wasu suke yi. Ni dai ban dace da irin wannan rayuwa ba."

Na ga yadda fuskar Fatima ta canza, kamar ta dau fushi. Ta kada kai cikin jin haushi. "To shikenan, ki cigaba da zama haka. Sai ki gane a gaba cewa wayewa ba ta nufin zama mai tsaurin kai ba."

Ta bar wurin, tana mai nuna damuwa. Amma ni kuwa na zauna a wurin, zuciyata cike da tunani. Ashe haka Fatima take? Duk wannan "wayewar" da take magana akai ba komai bane face jefa kai cikin fitina. Wallahi, idan wannan ce wayewa, to na fi son zama haka da ake ganin cewa ni 'yar kauye ce.

Ina cikin wannan nazari, zuciyata tana tsananta bugawa. Fatima dai tana ganin cewa tana taimaka min ne, amma a gaskiya, ni kam ganin nake tana jefa kanta cikin bala'i. Wallahi, zan cigaba da rokon Allah ya shiryar da ita, don kawai ta gane cewa wannan rayuwar da take dauka "wayewa" ba komai bace face yaudarar kai.

Bayan da Malam Idi ya zo ya dauke ni, na ji wani irin sanyi a zuciyata. Yau kam, Mama zan je gidanta. Na dade ban ganta ba, kuma yau duk yadda za ayi sai na ganta. Tun safe nake shirya yadda zan bullo wa Abba. Karshe na yanke shawarar yi masa karyar cewa muna da practical a makaranta. Na san cewa idan na ce masa haka, ba zai yi jayayya ba.

Da muka fito, Malam Idi ya bude min kofar mota. Na zauna a ciki, zuciyata na bugawa da farin ciki. Ban san dalili ba, amma idan na ga Mama, nakan ji natsuwa sosai. Duk yadda zan yi, sai na je gidanta yau.

Kakata cikakkiyar haifaffiyar kasar Jordan ce. Allah ya ba ta yara biyu kacal a duniya Uncle Kareem da Mamana Najlat. Shi Uncle Kareem yana rayuwarsa a Dubai. A gaskiya, sau daya kacal na taba ganinsa a rayuwata. Amma tun lokacin da Mamana tana raye, har bayan mutuwarta, duk sallar duniya sai ya aikomin da kayayyaki.

Uncle Kareem na son ya dauke ni tun bayan rasuwar Mamana, amma Abba ya ki yarda. Ya ce sam-sam, ba zai taba barina in tafi Dubai ba. Tsananin taurin kansa ne ya hana Uncle Kareem zuwa gidanmu har sau daya. Shi kuma Kakana ya rasu tun ina karama, don haka ban ma san shi sosai ba.

Mama ita ce kadai ta rage daga bangaren mahaifiyata. Duk da cewa asalin kasarta Jordan ce, ba ta koma can ba. Ta fi son zama a nan, sai dai ta je can ta dawo, ko kuma ta je gidan Uncle Kareem ta dade sannan ta dawo.

Tun daga nesa na ji hankalin gida ya sauya. Malam Idi ya danna horn din mota, aka bude mana gate. Ya shigar da motar cikin harabar gidan, cike da annashuwa. Na fito daga mota da sauri, zuciyata na bugawa da murna. Na wuce ma aikatan gidan ina ta kwalawa Mama kira.

Da na shiga babban kitchen dinta, sai na ganta tsaye tana girki. Tana ta jujjuya wani tukunyar da ke kan wuta. Na tako a hankali daga bayanta, na dafata ba tare da ta lura ba.

Ta waiga da sauri, idanunta suka yi karo da fuskata. Nan take ta saki murmushi, ta rungume ni da karfi. "Kai, Ramlah! Ke ce haka? Ashe zaki zo inda nake?!"

Na yi dariya, na manne mata kamar yadda nake yi tun ina karama. "Mama, na yi kewarki sosai!"

Ta shafa kaina cikin kulawa, fuskarta cike da farin ciki. "Nima haka, Ramlah. Yau kuma Abbanki ya barki kin zo?"

Na saki murmushi kadan, na sunkuyar da kai. Ban so in fada mata cewa karya nayi wa Abba ba, don ba zan so ta ji haushinsa ba. "Eh, ya barni," na fada a hankali, don bana son Mama ta fahimci wani abu..

Ina tsaye kusa da ita, tana cigaba da yi min magana, tana tambayata ko nayi karatu sosai. Na ce mata eh, don na san ba ta son raini a harkar ilimi. Ta rike hannuna cikin kulawa, tana sake tambayata komai lafiya a makaranta.? "Mama, komai lafiya lau," na fada, cike da natsuwa.

Ta taba hancina da yatsanta, tana dariya. "To ai yau kin zo, kuma kin san gidan nan naki ne. Ko yaushe ki zo babu wata matsala hakan zaisa naji dadi."

Na ji dadin kalamanta sosai. Duk da cewa zuciyata na dan dukan tsoro saboda yadda na yi wa Abba karya, kasancewa tare da Mama tana sa na manta da duk wata damuwa. Mama tana da wani irin hali na musamman da ya bambanta ta da kowa..

Sai ta juya cikin jin dadi, ta fara magana da harshen Larabci tana cewa "Ahlan wa sahlan! Ya ahlan bik!" Ta yi min kiss a gefen fuska, ta rungume ni sosai. Daga nan ta kama hannuna, ta ja ni zuwa babban palonta. Har yanzu, yaron da take rike da shi yana ta gaida ni cikin ladabi.

Bayan mun zauna, Mama ta dubeni cike da mamaki. "Ya akayi Abbanki ya barki? Kin yi sa a yau!" Na yi sauri na fada mata gaskiya kafin ta yi wani tunani. "Ai Mama, baisan nan zan zo ba. Na ce masa muna da practical ne a makaranta, shi yasa nayo nan. Wallahi na yi kewarki sosai!"

Mama ta yi murmushi tana jin dadin maganata. Duk da cewa bata iya Hausa sosai ba, tana jin kadan-kadan. "Nima na yi kewarki sosai, Ramlah. Lokacin da nake kiran wayarki a baya ba ki dauka ba, sai na yi tunanin wani abu." Na dan yi dariya, na ce "Mama, wallahi yau zan kunna wayar, na kashe ne saboda na fi mayar da hankali kan karatu."

Na ji wata irin kauna tana taso min daga zuciyata. Soyayyar da nake jin cewa nayi asara a gida, yau na same ta a wajen Mama. Mama ta ce na zauna sosai, sannan ta kawo min abinci. Ta ce sunansa Makluba. Ba na jin sunan sosai, amma kamshin abincin yana tayar min da kwadayi. Ta ajiye faranti a gabana, ta ce "Kici, Ramlah. Wannan abincin Larabawa ne."

Na fara ci, zuciyata na jin sanyi. Ban taba cin irin wannan abinci mai dadi ba a gida. Sai na ga Mama tana kallona da murmushi. "Ramlah," ta ce, "yau zan yi miki gyaran gashi. Ki daina zama da kazanta. Mamata yar gayu ce!"

Sai ta kai hannu ta shafa kaina, sannan ta ce "Zo nan, mu wanke gashinki." Na ji kamar in yi kuka. Ban saba da irin wannan kulawa ba. Mama ta shiga wanke min gashi da ruwan dumi, tana yi min magana cikin Larabci, tana lallashina. Sai da ta gama wankewa, sannan ta shafa min wani scrub na gyaran jiki, ta ce "Ki shafa nan da nan kafin ki yi wanka, yana kyau sosai."

Ta nuna min wata me kitso da ta kira daga waje. Ta ce za ta yi min kitso mai kyau da tsari. Wallahi, sai da na yi kuka. A zuciyata, na ji maganar Fatima tana dawo min. Da ace na san menene soyayyar mahaifiya, tabbas da ba zan taba kiran Momy da masoyiyata ba. Yadda Mama ta kula dani cikin wadannan awanni kadan ya sa na yi nadamar cewa ba tare da ita na taso ba.

Da ta ga ina kuka, sai ta zaunar da ni a kusa da ita, tana shafa bayana. "Ramlah, ki daina kuka. Duk komai zai zama labari. Kin ga kuwa?"

Ta goge min hawaye da lullubenta, sannan ta ce "Zan tafi Dubai nan da sati daya. Zan je gidan Uncle Kareem. In sha Allah, bayan watanni uku zan dawo."

Na yi shiru, zuciyata na jin nauyi. sai ta bude wardrobe dinta, ta dakko rafar dubu daya guda biyu, ta miko min tana cewa "Gashi nan, ki yi amfani da su idan kin bukata. Ki rage tambayar kudi a gida."

Na ji dadi sosai, na ji cewa zan iya amfani da kudin ba tare da jiran Mumy ta bani ba. Sannan Mama ta zaro kaya daga cikin wardrobe abaya guda biyu masu kyau, sannan ta hada da wasu turaruka, takalma da jaka guda daya. Ta cika su a leda, ta miko min tana murmushi. "Gashi nan, Ramlah. Ina so ki kula da kanki sosai."

Na yi mata godiya sosai, tana yi min addu'a, tana cewa "Allah ya taimake ki, Ramlah. Ki yi kokari a makaranta. Ki zama 'yar albarka!"

Ta kuma zuba min ragowar abincin Makluba cikin take away, ta ce "Ki kai gida, kici."

Bayan na gama shiryawa, Malam Idi ya zo ya ce min mu tafi. Na yi wa Mama sallama cike da kewar cewa ba zan sake ganinta ba har na tsawon watanni uku.

Da Malam Idi ya ajiye ni a kofar gida, na fito daga mota ina dauke da akwati karama da Mama ta bani. Na dan tsaya a farfajiyar gidan, sai na hangi Abba yana zaune a kan kujerar filawa, yana rubuce-rubuce a wata takarda.

Na yi tunanin ko in juya na koma cikih gida, don zuciyata na bugawa. Amma a karshe na nufi inda yake, na takawa a hankali har na karasa kusa da shi.

"Abba, sannu da gida." Ya dago kai ya kalle ni, sannan ya ce: "Sai yanzu kuka gama, auta?" Na yi murmushi kadan. "Eh, Abba. Na zo tafiya muka hadu da Mama. Shine ta bani wannan." Na bude akwatin da ke gabana, na nuna masa wasu kaya da ta bani. Na ga yadda ya yi murmushi, ya girgiza kai. A waje daya kuma, na san cewa ya gane cewa bansan gidanta ba kafin wannan zuwan. Amma ba yace komai ba, sai dai ya ce "Angode. Allah ya saka da alheri."

Kudin da Mama ta bani na boye, don na san idan ya gani, sai ya yi fada. Abba ba ya son in karbi kudi daga kowa. Yakan ce: "Me ya rage ni dashi?" Shi yasa nayi hankali kada ya gani.

Na juya ina kokarin komawa cikin gida, sai na tuna da take away din abincin da Mama ta bani. Na dawo na bude ledar a gabansa. "Abba, Mama ta zuba min wannan. Shinkafa ce da kaji da salad, harda wata gurasa." Na ajiye a gabansa. Na ga yadda murmushi ya sake bayyana a fuskarsa. "Sai dai ki bude mu ci tare ko?" Na yi dariya. "Abba, ai na ci wani a mota dazu. Ma har na bai wa kawata da Malam Idi."

Na lura da yadda ya share hawayensa a hankali, sannan ya ce da karyewar murya "Hakan sai ya tunamun da mahaifiyarki, Ramla. Allah ya ji kan Najlat, ya mata rahama. Ke kuma, Allah ya yi miki abin da ba ki taba zato ba, ya tsare ki, auta." A lokacin nima sai hawaye suka cika idona. Na amsa masa da muryar kuka, sannan na mike na shige cikin gida.

Ina shiga cikin gidan, sai na ji zuciyata ta danyi sanyi. Amma sai na hangi hamshakiyar gidanmu, kamar sabon gyara aka yi wa gida. Ina cikin rukunin falon, sai ga Yaya Bilkisu ta fito daga daki, tana bariki irin nasu na 'yan zamani. Na yi sauri na nufi wurinta ina rungume ta. Ita kuwa tana dariya, ta ce "Daman kin dawo kenan, auta? You look beautiful! Har yanzu dai babu kiba!" Na yi dariya ina sosa kai. "Yaya Bilkisu, sannu da gida."

Ina cikin jin dadin ganin ta, sai ga Mumy ta shigo cikin falon. Na tsinci kaina cikin tsoro, don yadda take kallona da wani irin ido. "Mumy, sannu da gida," na fada a hankali. Amma sai ta harare ni, ba tare da ta amsa ba. Na dau jakata na nufi dakina cikin sauri, amma kafin na kai dakin, sai na ji Yaya Bilkisu tana cewa "Auta, zo ki gyara min dakina. Ki wanke toilet din ciki. Kuma ina jin yunwa, Mumy jollof rice ta yi, ki zo ki soyamin chips."

Na tsaya na kalleta, zuciyata cike da takaici. Na san cewa Yaya Bilkisu ba ta ganin komai a matsayin matsala. Duk abin da take so, sai ta sa ni na yi mata. Sai na ja numfashi a hankali, nace "To shikenan." A raina kuwa, nace "Shugaban masu saka aiki ta dawo fa!"

Na dau jaka ta na nufi dakin Yaya Bilkisu, zuciyata na ta tunani. Ni kadai ce a gidan da ake juya kamar 'yar aiki. Na rasa me yasa Mumy da Yaya Bilkisu ke kallona haka. Duk da cewa na yi kokarin ganin an karbe ni da kauna a gidan nan, har yanzu ba su canza hali ba.

Na tuna da kalaman Fatima a makaranta "Da kin san menene soyayyar uwa, da ba za ki taba ganin Mumy a matsayin masoyiyarki ba." A yanzu, na fara fahimtar abin da take nufi. Duk da cewa ban yarda da dabi unsu ba, amma maganarta tana da wata nasaba da gaskiya. Na fi jin soyayya daga wajen Mama fiye da yadda nakeji agidanmu.

Na cigaba da gyaran dakin Yaya Bilkisu, zuciyata cike da tunani.