Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 16

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 16

.....n is the HUSBAND?. The last question she asked herself broke her heart, and she felt a warmth in her eyes as if tears were about to gather. She noticed the changes in everything about her parts, like from above, the security situation and so on, even if she didn't ask, it was from....... but then she felt like this was not satisfactory. "Why are you worried.....it's only a husband who is married to you without your approval" A part of her heart whispered this to her slowly, what made her look at the wall of her room even though it was dark, as if she wanted to remember something different. And as if waiting for you to do that, her phone which was on silent started to light up. Her eyes were fixed on the phone, her heart was beating slowly. That's how she was hoping someone was making her believe about the phone call...so she was thinking something about someone calling her on the phone at the same time. It should be a little bit surprising....when she opened her eyes, is it at such a time?. She knew that it was not her nature to call so late at night, if she would ask her like that when it was late at night, she would tell her to leave.....

Standalone post1,770 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 16*

*_A K H N A N_*

Tun daga wankanta zuwa kammala shirin baccinta komai ne yake dawo mata cikin kanta daki daki. Wannan kusancin......wannan kallon......wannan qamshin nasa da yake sake mannewa cikin zuciyarta da rayuwarta gaba daya.

"Me yasa yake da izza har haka?" Ta sake nanata tambayar da har yanzu ta gagara samun amsarta.

Tunda take a rayuwarta,ba zata iya tuna wani namiji da izza ke nunawa cikin komai nasa ba irin haisam din,haka malaman suke?,ko kuma daga shi dinne?.

Sake qanqame jikinta tayi guri guda gami da cusa pillow tsakanin qirjinta kamar zata maidashi cikinta.

"Me yasa yake saurin surrender?......me yasa idan nace abu baya kafewa akai?" Ta sake tambayar kanta tana jin wani rashin dadi. Kaman dazu,ta dauka zaice ba zata tafi ba,ta dauka zai gaya mata uzurinsa na qarin kwanakin da yayi akan wadanda yace zayayi din,amma babu ko daya a ciki. Hasalima sai daga qarshen qarshe yake tambayarta lafiyarta......wannan shine MIJIN?.

Tambayar data yiwa kanta na qarshe ya karyar mata da zuciya,sai taji wani dumi cikin idanunta kamar hawaye yana son taruwa. Ta lura da sauye sauye kan komai na sassanta,kama daga cima,yanayin tsaro da sauransu,koda bata tambaya ba tasan daga shine.......amma kuma sai taji duka kamar wannan bai gamsar ba.

"Me yasa kike damuwa.....miji ne fa kawai da aka aura miki ba amincewarki" Wani sashe na zuciyarta ya rada mata hakan a hankali,abinda ya sanyata ware dukkanin idanunta tana kallon bangon dakinta duk da duhun daya mamayeshi,kamar meson tuna wani abun na daban. Kuma kamar jira akeyi tayi hakan wayarta dake silent ta fara haske.

Idanu ta zubawa wayar,zuciyarta na bugawa a hankali a hankali. Haka kawai takejin wani fata yana shigarta game da kiran wayar......haka kurum take raya wani abu kan kiran daya shigo mata wayar a daidai wannan lokacin,wannan fatan da saka ran ya sanya ta miqa hannunta da hanzari tana daukan wayar,saidai kuma sunan aisa ta gani baro baro saman wayar.

Mamaki kadan ya kamata........tadan ware idanunta,aisa a irin wannan lokacin?. Ta sani sam ba dabi'arta bace kira late da dare haka,idanma zata nemeta irin haka inde dare yayi saidai ta shaidawa barratu ko birra su sanar da ita ta duba watsapp dinta.

Dab da kiran zai katse ta dauka,ta saka wayar a kunnenta ba tare da tace komai ba.

"Biftu" Taji muryar aisa da tayi wani irin mugun sanyi ta kira sunanta.

"Aisa?" Ta maimaita sunanta itama tana jin wani yanayi.

"Kiyi haquri biftu.....na kasa.....na gaza riqe wannan amanar,komai yafi qarfina biftu bazan iya ba,zan ajiye zan dawo agadez" Tayi maganan muryarta wani iri. Shuru akhnan tayi,zuciyarta na faffasa yadda taji sautin muryar aisa. Muryar aisa ba haka take ba.....ba haka yanayin aisa yake ba,bata da wannan raunin,tana da taurin zuciya da kafiya shigen nata,duk da cewa ita ta fita sauqin sarrafuwa da sassauci.

"Mene ne aisa?"

"Komai ma biftu,komai ma,amma kiyi haquri ki yafemin,zanzo zamu zauna,komai nawa yana gayamin KIN GAZA AISA.....komai nawa yana gayamin kaman naci amanarki ne,kamar ban kyauta ba,kamar zunubina bazai wanku ba,kamar na zama sanadi.....kamar nice sila" Dukka tayi maganan muryarta tana sake raunana sosai.

Maganganun sunwa akhnan nauyi da girma da yawa,tana qoqarin magana taji alamun aisa ta datse kiran,ta kalli screen din,saita soma yunqurin kiranta amma na'ura ta shaida mata wayar a kashe take gaba daya.

Bata natsu ba,ta miqe ta zauna ta fara kiran shehnaz. Kaman dama wayar na hannunta ne tana jiran kiran akhnan din ta daga.

"Shehi....Qu'est-ce qui se passe avec Aïsa?(me yake faruwa da aisa?" Ta tambayeta da french.

"Je ne sais pas.mmmmc'est étrange,je me demande pourquoi elle pleaurait(Ban sani ba nima,baqon abune wannan.....inata mamakin me yasata kuka)" Ta fada da alamun damuwa sosai cikin muryar shehnaz din.

Shuru akhnan tayi,tana sauraren bayanan shehnaz.

"Tun kwanakin can nake jin yanayinta kamar ba'a daidai ba,bata fadamin ba bata kuma nuna tanaso naji ba shi yasa ban matsa mata ba,amma koma meye gobe ko jibi tace zata taho,ko bata sameki ba ni zan jirata naji" Kai ta gyada a hankali

"Allah ya kaimu". Ta katse wayar sannan ta koma a hankali ta kwanta,saidai har zuwa sanda bacci ya dauketa aisa ce a ranta.

*M A M M I N A*

Bata taba jin tana so tayi kuka a rayuwarta ba irin yau........ta jima kuma bataji kuka yana neman hallaka numfashinta ba irin yau din.

Duk wani hadimi da hadima dake kusa kusa da dakunan baccinta ta sallamesu,ta kuma kulle kanta a daki tayi wani irin kuka harda ihu daidai da yadda take jin baqincikinta zai ragu.

Batasan adadin tsahon lokutan data dauka ba a haka ba,har sai data tabbatar ta samu sassaucin abinda takeji qasan ranta,sannan ta shiga bandaki tayi wanka da ruwan sanyi waiko zata samu sassaucin abinda takeji cikin jikinta.

Dawowa tayi dakin,tayi zaman dirshan,zaman 'yan bori tana qoqarin farfasa tunaninta daya bayan daya.

Ayau,ta samu dukkan tabbaci da yaqinin sheikh muhammad haisam yana cikin jerin sahun mutanen da suka shigo agadez don farmakarta

"Idan ba haka bane?,me ya hadashi da almaz?......kenan dama can almaz din yana hannunsa?,idan haka ne dukka al'ummar villa street suna hannunsa kenan". Wani irin zazzafan gumi taji ya karyo mata,haka kawai takejinta kamar ita kadai ce.....haka kawai takeji kamar ita kadai ta rage a wannan sansanin,......a wannan filin. Batasan me yake damun tafsu ba,cikin kwanaki gaba daya wani nesa takeyi da ita wanda ta bada uzuri da juyawar ciki da har yanzu ta kasa saurara mata. Da waye zatayi shawara?,waye zai hango wata mafitar da ba lallai ita din ta hangota ba?.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Tambayar da tayi mata tsaiwar mashi aka,bata kuma samo amsarta ba......sai wani courage daban da takeji daga wani sashe na zuciyarta.

"Karki yadda ki fadi.....karki yadda kaikai qasa......koda yanzu kina tunani motsinki zai iya zama barazana.......ki bashi lokaci,sanda zai tashi daga agadez zuwa qasarsa......wannan futar ki tabbatar ta zame masa fita ta qarshe daga qasar......daga yankin nan. Fitar da zata sama nisa na har abada tsakaninsa da agadez da kuma sultane.

"Ki daure......a qarasa komai dashi......ya fita yabar qasar,komai zaizo da sauqi" Wani murmushi ta saki,murmushin dake da alaqa da sassaucin data samu da 'yan qanqanuwar mafitar da zuciyarta ta bata.

Burinta a yanzu ba control bane......babban burinta a yanzu shine ta qarasa aikinta na ture kaza daga kan qwai ta kwashe qwan.....kauda sultane me gaba daya,ta kuma tumbuke bishiya daga tushenta,tayi rantsuwa........ta kuma lashi takobin tabbatar da wannan aikin,a kusa ko kuma a nesa.

Wayarta dake gefe ta dauki qara da tsuwwa,ta waiwaya ta zuba mata ido kamar ma ta manta da ita. Kamar ta shareta,kaman kada ta dauka,amma sai sunan dake harbawa saman screen din yaja hankalinta,ta miqa hannu ya daga ta saka a kunne.

Batace komai ba,amma maganan da ake mata daga wancan bangaren ya sanya wani shu'umin murmushi subuce mata.

"Ko a iya nan kun kammala aikinku......inaso kowacce hujja ta bata ta salwanta kamar komai bai taba faruwa ba.....burina akan sahel couture ya gama cika........aiki ya kammala.......ku jira sakamakonku........ina alfahari dakai" Takai qarshe tana cije labbanta da haqorinta irin na zallar muguntar nan,sannan ta zare wayar a kunnenta har yanzu murmushi yana sauka saman fuskarta.

"Kafin na tafi......ya kamata kowa ma ace anbar masa wani babban tabo.....babbar barakar da bazata taba gyaruwa ba" Ta fada a bayyane tana jin alamun nasara na tare da ita kena,tunda har a sanda take zaton faduwa babban labarin nasara yazo mata.

*_RANA BATA QARYA_*

Cikin wani irin tarin nutsuwa yake zaune gaban sultane,wanda ya kebe ne daga shi saishi,duk da cewa shi da maleek ya fara yin magana dasu.

Sanye yake cikin wata qayatacciyar jallabiyya da asalin kudinta ita da cloak thobe din jikinsa yake isa babban jari da tarin al'umma marasa qarfi. Wasu irin thobe da a idanu kawai idan ka kallesu kasan an nunawa kudi iyakarsa wajen mallakarsu.

"Na aura maka biftu ne......saboda fadin manzan Allah.......mu aurar da diyoyinmu ga maza irinka,idan ka sota zaka mutuntata ka mutunta ahalinta,idan ka qyamaceta kuma ba zaka wulaqantata ba........haisam,bazan boye maka ba,ba kuma don ban aminta dakai ba aah......ina sake jaddada maka ne kaji tsoron Allah akan khadeeja.....bazan boye maka ba,inason khadeeja sama da kowa cikin 'ya'yana.....amma hakan........" Sai zuciyar sultane dake kashingide saboda rashin qwarin jiki da yake fama dashi ta raunana. Ya yunqura ya miqe ya kuma zauna sosai,rabon da yaji alamun taruwar hawaye cikin idanunsa tun rasuwar mahaifiyarsa.

"Amma hakan bazai hana na aurar da ita ba,saboda hakan shine cikar kamalar mace.........ina sake baka amanarta......ba don ina kokwanto kan cikar kamalarka ba,a yanzun duk duniya,ba wani d'an adam dana aminta dashi sama dakai" Wani irin nauyi yakeji sultane yana sake aza masa.......wani irin sanyi dukka yake ji yana bin jikinsa. Yana jin kamar bazai iya ba.....kamar bazai kai labari ba. Ya sani,idan ana maganar amana wata abace me girman gaske......abace da idan ba ita tsallake siradi kansa baya yiwuwa a gurin bawa. Zata kasance abu mafi santsi a tafin hannun bawa ranar qiyama,ita zaa aza maka a hannunka ka tsallake wannan siririn zaren da ko kaurin gashi baikai ba.....siririn zaren dake tsakanin wutar jahannama,ka tsallaketa da ita,tana santsi kamar tarwada a hannunka. Duk sanda ta subuce ta fada to zaka bita ne ka daukota don ba zaka wuce ba sai da ita,idan kaci amana zaka yita sintirin daukota daga wuta Allah ya tsaremu,idan kuwa ka kiyayeta lafiya qalau shikenan zaka wuce,wucewar da babu wani bawa da yake da tabbas a kanta. (Ya Allah,ka bamu ikon kiyaye amana....Allah ka tsallakar damu siradi lafiya).

"Muhammad" Sultane ya kira sunan haisam da yanayin daya sanyashi daga manyan idanunsa kadan ya kalleshi.

"Akwai wasu abubuwa a wancan ranar dana gani......akwai abubuwa da yawa dana saka musu ayar tambaya.....akwai abubuwa masu yawan gaske daya kamata ace na sani inaji a jikina hakanan......inason nasan gaskiya muhammad......inaji a jikina akwai wani boyayyen abu......shin zaka iya riqo da hannayena na sauka daga mulkina na damqawa ahmad?......zaka iya dafawa raunina ka fiddani daga cikin duhu zuwa haske?" Maganan ta zowa haisam a bazata,magana data sake tilastashi daga kansa a hankali yana duban sultane,yana masa wani kallo ne dake bayyana gaskiyar magana manufa da abinda yake fadi daga tsakiyar zuciyarsa ne

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽