
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 9
.....here is the royal family, As'ad Babangida! Second to the noble, the grandson of the king, the rich man that the country is proud of! God is great and great!" The palace men looked at the way As'ad walked calmly and respectfully, and he was near the king's hall. Inside the palace, it was already announced to his majesty that As'ad had arrived. The king waved his hand in joy, smiling like a saint. Slowly, As'ad entered the palace hall. He stopped and bowed his head politely, and made the royal salute The king replied with a caring smile, "As'ad, welcome. May God give you success and blessings." As'ad found a place and sat beside the king calmly, watching the fight with the members of the royal family. He noticed how the house has regained more strength than he left it. It has been one and a half years since he went to the palace. It was not because his father and mother Hajja were here, he would not have come. The king corrected his voice, looked at As'ad with care, and said "As'ad, I am blessed. Is it now? So I went to where you are because of a royal habit? Even if I die, you can't come to see me.....
SHAFI NA TARA
Da zarar As'ad Babangida ya iso fadar mai martaba, sai aka fara masa kirari kamar yadda aka saba a gidan sarauta
A hankali ya shiga cikin gidan sarautar, yana kallon ko'ina da idanuwansa. Yau shekara ?aya da rabi kenan rabon da ya taka wannan gida. Gidan da ya tsana fiye da komai da ba don iyayensa na ciki ba, da ko kusa ba zai sake taka shi ba.
Tun da ya kammala karatu, As'ad ya yanke shawarar komawa birnin tarayya, gidan mahaifinsa. Hajja, matar sarki ta biyu, tana zama a can tare da 'ya'yanta guda biyar Mamy Shamsiyya (ta farko), As'ad, Kanwarsa Zaitu (wacce ke zaune a London), Abba, da Fiddausi (?arama kuma fitinanniya). Sauran yaran kuwa na sauran matan sarki ne.
As'ad ya kasance mutum mai ra'ayin kansa wanda baya sha'awar rayuwar sarauta, shiyasa ya fi zama nesa da gidan mai martaba.
Tunda As'ad ya iso harabar fadar mai martaba, ake masa kirari da girmamawa, ana aika masa gaisuwa daga kowanne bangare. Mai sanarwa na fada ya ?aga murya cikin izza "Gaisuwa ta musamman ga ?an gidan sarauta, As'ad Babangida! ?a na biyu ga mai martaba, jikan sarki, hamshakin mai arziki da ?asar ke alfahari da shi! Allah ya ?ara girma da ?aukaka!"
Fadawa suka gyara zane suna kallon yadda As'ad ke takawa cikin natsuwa da girmamawa, ya na kara kusa da zauren sarki. Cikin fadar kuwa, an riga an sanar da mai martaba cewa As'ad ya iso. Sarki ya ?aga hannu cikin jin da?i, yana murmushi irin na mai alfarma.
A hankali, As'ad ya shiga cikin zauren fada. Ya tsaya ya sunkuyar da kai cikin ladabi, sannan ya yi gaisuwar sarauta "Ranka ya da?e, Allah ya ja zamanin sarki." Sarki ya amsa da murmushi mai cike da kulawa "As'ad, maraba da kai. Allah ya ?ara maka nasara da albarka."
As'ad ya samu wuri ya zauna a gefen sarki cikin natsuwa, yana kallon fadawa da 'yan uwa na gidan sarauta. Yana lura da yadda gidan ya sake samun kwarjini fiye da yadda ya barshi. Shekara ?aya da rabi kenan bai taka fadar ba. Shi kam ba don mahaifinsa da mahaifiyarsa Hajja suna nan ba, da bai kara zuwa ba.
Sarki ya yi gyaran murya, ya kalli As'ad da kulawa, sannan ya ce "As'ad, ?ana mai albarka. Yanzu haka ne? Sai ni na je inda kake saboda wata dabi'a ta ?in sarauta? Ko in mutu ma baka da ikon zuwa ka ga iyayenka da yan uwanka? Ku?i ba komai ba ne, As'ad. Ina gaya maka, duk arzikin da kake tunanin ka tara, a nan gidan sarauta ne tushen komai."
Ya ?an numfasa kafin ya ci gaba da magana cikin natsuwa "Kai fa ?an gidan sarauta ne. Meye na gujewa gidan sarauta? Ban ce kada ka je Abuja ba, amma fa dole ka rike martabar gidan nan. Na aura maka mace sau uku, duk ka sake su. Me yasa baka son ?ara aure ne? Ka duba yan uwanka, dukkansu suna da gida, suna da zuri'a sama da ?aya. Wannan magana da nake maka ba shawara ba ce, umarni ne. ?ar gidan Fulani, Maryam, itace nake so ka je ka gani. Wannan magana ta gama karewa."
As'ad ya sunkuyar da kansa cikin jin nauyi, sannan ya ce cikin ladabi "To ranka ya da?e, za a yi yadda kake so."
Sarki ya yi murmushi cikin farin ciki, yana jin da?in yadda As'ad ya amsa. Ya ?aga hannunsa yana addu'ar samun albarka a kan ?ansa. "Allah ya sanya alkhairi. Ka je ka shirya, za a kawo Maryam nan fada gobe, domin ka ganta da idanunka."
Cikin girmamawa, As'ad ya dur?usa gaban mai martaba sannan ya ce da ladabi
"Allah ya taimake, a yi ha?uri, zanje inshaa Allahu."
Wannan ?abi'ar tasa ce ta ladabi da girmamawa bai ta?a yin gardama ko musanta umarnin mai martaba ba, duk da rashin sha'awarsa ga rayuwar sarauta. Har lokacin da ya auri Ayshatu ma, shi ne ya bashi izini, kuma ya amince. Haka kuma sauran matan da ya aura duk da shi ne ya nemi izini kuma aka amince masa.
Cike da farin ciki, mai martaba ya amsa da murmushi mai cike da annuri
"Allah ya yi maka albarka, na baka izinin tafiya."
Da girmamawa As'ad ya mi?e, ya fice daga fadar mai martaba yana yi wa sarki addu'ar albarka da tsawon rai. Cikin zuciyarsa, yana jin da?in yadda aka yi komai cikin sau?i da girmamawa, duk da yana matu?ar guje wa irin wa?annan taruka na gidan sarauta.
As'ad na shiga bangaren mahaifiyarsa, wanda yake da kyau da tsari irin na gidan sarauta, sai ya tarar da kaninsa Abba yana cin abinci. Da ganin shi, Abba ya ajiye kwanon abincin ya mi?e tsaye, yana dur?usawa cikin girmamawa:
"Yaya barka da zuwa."
As'ad ya amsa da fara'a, yana ?agowa da shi tare da ?an runguma. Yana tambayar lafiyar gida da aiki. Abba ya amsa cikin ladabi, sannan suka zauna cikin tsari irin na gidan sarauta.
Bayan sun ?an yi hira, Abba ya fara magana cikin natsuwa "Yaya, da zaka yarda na nufi gidan Fiddausi, wallahi wannan fitsarar nata ta yi yawa. Anty Aysha ma ta kira ni, ta ba ni labarin yadda abin ya faru."
As'ad ya ?an murmusa, yana jin mamakin yadda Aysha ta kira Abba "Ka kwantar da hankalinka, Abba. Na riga na yi maganinta."
Kafin su cigaba da magana, Hajja ta sauko daga bene cikin hanzari, tana dubansu da fuskar rashin jin da?i
"Abba! As'ad! Kuna tattauna Fiddausi kamar ba ku san darajar 'yar uwarku ba? Kun ga ai sai ku ha?u ku yi mana duka tare, ko? Abba, ka kiyaye ni akan Fiddausi. Ni na haife ku, ba ku kuka haife ni ba! Kun damarmun yarinya da maganganunku!"
Ta ?an ja numfashi, sannan ta cigaba da fada cikin takaici "Yanzu har Fiddausi zata je gidan As'ad sai matarsa ta ba da izini kafin ta ga ?an uwanta? Yaushe kuka fara ba wa matanku wannan ?arfi fiye da 'yan uwanku da kuke ciki ?aya?"
Abba ya sunkuyar da kai cikin kunya, yana sauraron mamarsu. As'ad kuwa ya yi shiru, yana kallon yadda Hajja ke nuna damuwarta da ?arfi
Cikin zafin rai, Hajja ta yi magana cikin ?arfin murya "Wallahi bazan ta?a yarda da wannan ba! Ayshatu ba ta da wannan ikon! Na gaya muku, dukanku!"
Cikin girmamawa, As'ad ya tsugunna har ?asa ya gaisheta "Hajja,Za'a kiyayye inshaa Allahu. ?" Ta amsa tana tambayar yadda su Nawal suke. "Alhamdulillah, suna Dubai, Hajja. Ta yi musu fatan dawowa lafiya."
Hajja ta yi gyaran murya, tana magana cikin nuna damuwa "Maganar Fiddausi nake so mu yi. Daman taje kun ci mata mutunci kai da matarka. Duk lokacin da yarinya ta fara kuka game da mijinta, yakamata ku saurareta. Kuna ganin kamar Fiddausi ba ta da kunya, amma ai mace mai rauni ce. Kun san mahaifinku da girmama al'adar gida. Ni kuma bazan zuba ido rayuwar 'yata ta lalace ba. Kun sha gayamata mijinta yana biya mata bu?ata, amma kullum cikin rashin kunya da fitsara take. To tayaya zata girmama namiji mara kuzari agado? Bata fa?a mini ba, sai yanzu da take cewa har magani aka nema babu ci gaba. Kuma duk kwayar da ya sha, ba tashi yake yi ba, sai jiri da kwanciya har asuba! Yaya aure zai yiwu haka?"
As'ad ya sunkuyar da kansa cikin ladabi "Hajja, ki yi ha?uri, Fiddausi ce dai. Mun yi magana da mijinta, ba haka ya sanar da ni ba, shi ya sa na yanke hukunci. Amma duk yadda mai martaba ya fa?a, haka za mu yi. Allah ya za?a musu abin da yafi alkhairi."
Hajja tace "Munif yana son Fiddausi sosai, bana tunanin zai iya sanar da kai matsalar. Amma ku tsaya mata! Ni shekaruna sun ja, ku zaku tsaya kamar iyayenta."
Abba yace "Inshaa Allahu, Hajja, za mu gyara."
Hajja ta yi ?an nishi kadan "Maganar diyar Maryama fa? Ka amince?" As'ad ya yi shiru na ?an lokaci kafin ya ce "Zabinku shine alkhairi, kamar yadda mahaifina ya umurce ni. Inshaa Allahu, da daddare zan je na ganta."
Sai Hajja ta ?aga murya cikin takaici "As'ad! Wannan biyayyar taka tana cutar da kai! Yanzu Haneefa zaka aura? Yarinyar da kowa yasan rashin tarbiyanta, kuma kasan mahaifiyarta makiyata ce! Wallahi tun da mahaifinka ya gaya min sai na ji bata kwanta mun ba! Ina ro?onka ka canja wannan shawarar."
Har sai da Abba ya sa baki "Dan Allah, yaya, kada ka aureta. Haneefa fa? Haba yaya, auren nan da manufa!"
Hajja ta kara nuna damuwarta "Biyayyarka ta yi yawa, As'ad. Yarinyar da aurenta fiye da biyar, duk ta kasa ri?e ?aya. Na ?arshe ma, sata tayi masa ya rabu da ita. Dan Allah, ka kiyaye."
As'ad ya girgiza kai cikin ladabi "Hajja, ki yi mun addu'a. Bazan iya tsallake umarninsa ba."
"To Allah ya duba mu, ya yi muku albarka."
Bayan ya fita, Abba ya kalli Hajja cikin mamaki "Hajja, anya ba asiri aka yi wa yaya ba? Wannan biyayya fa ta yi yawa!" Hajja ta yi dariya "Abba, mahaifinku ne yayi masa amma dai." Abba ya ?an nuna damuwa "A'a Hajja, kar ki sani, dan Allah."
Ta yi shiru na ?an lokaci tana nazari. Abba kuwa ya kalle ta yana mai nuna damuwa "Hajja, wallahi abin da yaya yake yi yana bani mamaki. Wannan biyayyar kamar ba ta al'ada bace. Ko dai akwai wani abu a ?asa ne?"
Hajja ta ja numfashi, ta dube shi da ido cikin natsuwa "Abba, mahaifinku ne ya yi masa wannan Tun yana ?arami, ya horar da shi da biyayya da ladabi. Babu wani sihiri ko asiri a cikin wannan lamari. Amma gaskiya ni kaina ina tsoron irin wannan biyayyar, musamman yadda yake tafiya akan batun Haneefa."
Abba ya girgiza kai cikin takaici "Hajja, idan aka ce mutum ya yi biyayya, ai yana da hankali. Amma wannan kamar an mamaye tunanin sa ne. Haneefa fa? Duk gidan sarauta sun san halinta. Ina ro?on Allah kada wannan aure ya zama matsala."
Hajja ta ?an yi dariya mai ra?a?i "Abba, mahaifinku ya yi imani da soyayyar danginsa da ha?in kai.
******
A cikin falon Maryama, Haneefa na zaune tana daddanna waya yayin da mahaifiyarta ta fito daga ?aki tana kallonta da wani irin yanayi na tsananin takaici. Ta daka mata tsawa
"Dan ubanki! Haneefa, haka zaki fita da wannan shigar? Nayi miki dinki gashi can, show me your body! Ki saka shi ki cika. Ki yi dam! Ki ?akko brazier guda uku ki ha?a. Wannan wandon da na siyo miki na cikon hips ki saka, ki ?auki jan jambakinki ki sa. Wannan kwalliyar da na kar?o miki daga wancan mai gyaran fuska, ki yi amfani da ita. Kuma idan kina magana, kina narkewa, nagaya miki!"
Ta ja numfashi tana gyara gyalen da ke kafadarta
"Matarsa fa yar gayu ce sosai, kuma kyakkyawa ce duk da ba?aramin jiki gareta ba. Da kadan zata girmeki, amma fa dirine da ita! Kina jin ni kuwa? Ki tashi kiyi maza! Yanzu zakiga As'ad."
Haneefa ta gyara zaman rigar da ta saka, tana murmushi mai ?auke da son zuciya. "To Fulany," ta fada tana barin falon cikin jin da?i. Zuciyarta fes, tana tunanin yadda zata burge As'ad. Tuni tunaninta ya tafi ga yadda zata sa shi ya kafe mata ido, yana ganin ita ce mace ta daban da babu kamarta.
Ta dauki wandon da aka kawo mata, ta saka brazier guda uku kamar yadda aka umurta, sannan ta yi make-up mai tsauri, tana mai danna jan jambaki sosai. Ta kalli kanta a madubi, ta gyara gashinta da wani irin salo na matan zamani.
"Yau fa sai As'ad ya san ni ce matar da ta dace da shi," ta fada a hankali tana murmushi mai dauke da kulle-kullen cin nasara.
A cikin zuciyarta, ta yi alkawarin cewa komai zai yiwu domin ta samu matsayin matar As'ad, ko da kuwa ta nemi taimakon Fulany don ganin burinta ya cika. Duk da cewa zuciyarta ta san cewa As'ad mutum ne mai tsari da kamala, hakan ba zai hana ta amfani da duk wani salo don ja hankalinsa ba.
Ta ?auki wayarta, ta danna kira "Mama, na shirya! Yanzu zan fito."
Fulany ta yi murmushi daga nesa tana jin sautin muryar 'yarta "To haka nake so! Yi hakan da kyau ki ga yadda zai zuba miki ido."
Maryama ta fito daga ?akinta tana tafiya da sauri zuwa falon inda ta tarar da Haneefa tana kammala kwalliya. Ta daka mata tsawa da murya mai ?arfi
"Au Haneefa! Maza zo nan! Sarki ya sanar da cewa yana gidan yanzu, yana jiranki. Ga direba can, ki hanzarta ki tafi!"
Ta gabatar da wata ?aramar kwalba na turare mai ?amshi mai ?arfi "Kar?i wannan turaren. Gab da zaki shiga gidan sarauta, ki gogashi a wuyanki da kunnuwanki. Wannan garin kuma ki watsa shi a kafar hagu. Wannan abu sirri ne, na tabbatar da cewa zai ja hankalin As'ad."
Ta tsayar da Haneefa ta kalli ta cikin ido "Haneefa, komai rintsi, kada ki soma magana da kowa sai As'ad. Koda suna gaishe ki, ki yi kamar ba ki ji ba. Kin ji ni? Kada ki ?atamun aiki!"
Haneefa ta gyara tsayuwarta, tana gyada kai "Na ji mama. Zan yi yadda kika ce."
Maryama ta yi ?an murmushi mai ?auke da nasara "Kin ga yan uwanki suna kokari, amma ke kadai na yarda da ke. Ki kula sosai, kada ki yi wani abu da zai bata mana suna. IAs'ad yana da rauni akan mace mai kyau da nutsuwa. Ki nuna masa cewa ke ce za?in da ya dace."
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH