Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 17

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 17

.....Only her mother knew about it on the day when the daughter would be taken from her hand to someone else's house. Sheshsheqar's cry of Falaak created a kind of silence between them, a kind of silence that carries a weight that only the heart can measure. No matter what, she hears it like a fairy tale, no matter what she watches it like a movie or a book. Today is she akhnan?, is she a man who will take her completely?, from her motherland?, from her kingdom?, from the family she grew up in?. She will not leave only Niamey..... she will not leave only Agadez..... aah, she will leave her country and her entire continent. The first time she heard the cry of Falaak put a wound in her heart, the first time she held Morsa Safiyya's hands and felt them in her bones and heart. "It's enough falaak... it's enough ha..." Then the morning morsa's voice started, and Salin Alin swallowed the rest of her words to avoid tears, and broke the promise she was preparing for them. "Momma... what about the sultan?" Ahmad's voice, walking into the room, fell on their ears. She smiled and started trying to slip her hands, thinking that she was just going to argue, but to her surprise, she heard a...

Standalone post1,621 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 17*

*M O R S A S A F I Y Y A*

Zaune suka a gabanta dukka su biyun,sanye kowaccensu da abaya data banbamta gurin launi da design din ma gaba daya.

Falaaq na sanye da dark mint green,wadda aka saqata da ainihin satin material me kyau da tsada. Yayin da akhnan ke sanye da baqar abaya,Japanese nida da aka saqata daga asalin yadin silk me yauqi dake shaking yana sake qawata farar fatarta dama ainihin kalar baqi wul din da abayar ke dashi.

Zaune suke gaban morsa safiyya,a kebantaccen dakin kwananta da babu kowa a cikinsa,daga ita sai 'ya'yan nata guda biyu.

Dukkaninsu tafukan hannuwansu suna cikin nata,na tsahon wani lokaci suka dauka a hakan,duk wani magana da zata musu koda kalma daya bata bari ta fadeta suna nesa da ita ba,ta damqesu sosai cikin nata hannuwan,tana jin kamar ba zata iya zame hannun nasu daga cikin nata ba.

Wani emotion ne me nauyi tun daga idanunta zuwa zuciyarta,irin wannan yanayin da UWA data aurar da d'iyarta ne kawai ta sanshi a ranar da za'a karbe diyar daga hannunta zuwa gidan wani.

Sheshsheqar kukan falaak ita ta haifar da wani irin shuru a tsakaninsu,wani irin shuru dake dauke da nauyin da zuciya ce kadai tasan iya adadin mizaninsa.

Komai akhnan tana jinsa ne kamar almara,komai tana kallonsa ne kamar wani shirin film ko a littafi. Yau ita akhnan?,itace wani d'a namiji zai dauketa cancakat?,daga mahaifarta?,daga masarautarta?,daga cikin iyali da ahalin data taso a ciki?. Ba Niamey kawai zata bari ba.....ba agadez kawai zata bari ba.....aah,zatabar qasarta da nahiyarta ne gaba daya.

Karon farko da taji kukan falaak ya sanya wani rauni cikin zuciyarta,lokaci na farko da riqon da morsa safiyya ta yiwa hannuwanta take jinsu har cikin qasusuwanta da zuciyarta.

"Ya isa falaak.....ya isa ha...." Sai muryar morsa safiyya din ta maqale,salin alin kuma ta hadiye sauran maganganunta gudun kada hawaye ya balle mata,ta karya musu qwarin gwiwar da take musu tattalinta.

"Momma......sultane fa" Muryar ahmad dake takowa cikin dakin ta sauka a kunnuwansu gaba daya. Murmushi ta qaqalo,ta soma qoqarin zame hannuwanta da take zaton falaak ce kawai zatayi gardama,saidai ga mamakinta tsam taji akhnan ta riqe yatsunta cikin nata.

A hankali ta daga idanunta tana duban morsa safiyya din,sai a sannan taga damshin hawayen daya jiqa zara zaran eye lashes dinta.

"Kiyi haquri" Akhnan din ta furta a hankali labbanta suna motsawa. Kai morsa safiyya ta soma girgiza mata,akwai tarin abubuwan data karanta tattare da ita,saidai a yanzun a wannan lokacin ba muhallinsu bane gaba daya.

"Biftu" Ahmad ya fada a nutse yana tsugunnawa a tsakiyarsu yana sanya hannunsa cikin dabara yana raba tsakanin hannuwansu dana morsa safiyya

"Ya isa.....muje sultane yana son ganinku" Ya fada da wani irin yanayi da yasa ba wadda ta masa musu a ciki,ya bude musu nashi tafin hannuwan suka saka hannunsu a ciki ya miqe tare dasu gaba daya.

*_HAISAM/SULTANE_*

"Ina kyautata maka zato fiye da yadda kake tunani" Sultane ya sake fadi bayan gajeran kallon kallon daya ratsa tsakaninsu shida sultane din.

Sallamar ahmad itace ta katse ragowan dukka tattaunawar data rage tsakaninsu.

"Wa'alaikumussalam" Sultane ya amsa sallamar murmushi yana subuce masa daga saman fuskarsa. Idanunsa akan ahmad din wanda ke riqe da hannuwan akhnan da falaak.

Cikin girmamawa ya isa gaban sultane dasu,ya ajiye masa su,a daidai lokacin kuma haisam ya miqe a nutse ya taka yana fita daga dakin. Basai sultane ya fada masa ba,a yanzu a wannan lokacin,baya buqatar izinin sultane waje fita a gurin,lokaci ne na uba da 'ya'yansa,lokaci ne na ganawar mahaifi da yaransa cikin sirrin da su kadai ya shafa.

"Allah yayi muku albarka,Allah ya albarkaci rayuwarku da aurenku gaba daya......bakuyimin komai ba tsahon zamanku tare dani,idanma kunyimin din na yafe......saidai kuma akwai abu guda daya da zaku iyayimin wanda ba lallai na iya yafeshi ba". Dukkaninsu......daga falaak har akhnan sai da suka daga kai a gigice suna dubansa. Da murmushi a fuskarsa yake jinjina kansa.

"Eh,kuqi zaman aure,kuqi biyayya wa mazajenku......ku bijire musu,kuqi binsu cikin abinda Allah da manzonsa suka shard'anta....inde ba cutarwa ba zalunci ba tauye haqqi......ku zauna a gidajenku,kuyi biyayyawa mazajenku,wannan shine abu guda daya da nake buri,nake kuma buqata daga gareku" Ya qarasa fada da wani irin sanyi a muryarsa.

"In sha Allah bappi.....in sha Allah zakayi alfahari damu" Falaak ta fada muryarta na rawa tana kama tafin hannun akhnan tana riqewa cikin nata,kamar tanason ta bata tabbacin maganan data gayawa sultane.

"Allah yayi muku albarka,yasa aljanna ce makomarku"

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Ameen" Labban akhnan suka motsa da qyar ta amsa,kafin muryarta can qasa tace.

"Bappi......ka yafemin" Kalmar ta fito tare da silalowar hawaye daga cikin idanunta. Murmushi ya sake saki,yana jin yadda jikinsa a kowacce rana yakeyin weak.

"Kisa a ranki baki taba batamin ba akhnan......baki tabamin laifi ba......amma nan gaba zaki iya yimin matuqar baki tsaya kin yiwa Muhammad biyayya ba......a yanzu duk wani hasashe naki na ido bazai iya gaya miki waye muhammad haisam ba......amma zan fada miki wayeshi,qila a nan gaba idan kin tuna da kalmata koda bana raye zaki ga ta hau daidai da mizanin dana fada miki......muhammad haisam LU'U LU'U ne......LU'U LU'U n da ke lullube cikin wani guri da hankulan mutane da iyaye baikai kanshi ba.....amma hakan yayimin.....inda hankula sunkai kansa da wurwuri.......qila a yau da banyi nasarar zama surukinsa kamar haka ba" Ya qarasa fadar maganan murmushi yana balle masa. Dukkan alamunsa sun nuna sosai yakejin dadin yanayin......sosai abun yake masa dadi har qasan zuciyarsa.

"Ko bayan bana raye....ko bayan na mutu ki tuna wannan" Kalmar mutuwar daya ambata saita zame mata kaman wani babban abun barazana daya birkitata,ya kuma sanyata fashewa da kukan da tun dazu take neman control dinshi dama,ta fada jikin sultane ta riqeshi da kyau kaman ba gobe.

"Ba zaka mutu ba bappi na......ba zaka mutu ba......zan fasa tafiya na zauna da kai" Riqeta yayi sosai yana share mata hawayen da hannuwansa,Shima tana sake kashe masa zuciya da gangar jiki bayan kasalar dake sake mamayarsa a kowacce rana.

"Kin manta na fada miki farinciki na?,......farincikina shine zamanki gidan aurenki,kibi umarnin mijinki ki samu aljanna khadeejatu"

Kusan a cike farfajiyar gidan take da jama'an da suke da kusanci da ahalin sultane muhammad hammud,yan uwa bayi da hadimai da suka zama tamkar 'yan uwa na jini ga iyalin me martaba.

Motoci ne na alfarma guda goma aka ware don tafiya daga agadez zuwa Niamey,cike da hadimai da zasuyi masu rakiya har zuwa sanda zasu tashi daha babban filin sauka da tashin jiragen sama na Niamey Diori hamani international airport,wanda daga can suka tsara yadda zasu tashi zuwa jedda

Sultane ne da kansa riqe da hannuwansu yana takawa ta jerin mutanen dake tsaitsayi hagu da dama suna bankwana dasu cikin nuna kulawa da soyayyar da ta samo asali daga adalin mahaifinsu.

Haisam da maleek din dukkaninsu suna bayan sultane din,cikin kamala da shigar dake sake nuna zallar haibarsu.

Motocinsu ya banbanta,kamar yadda sultane ya sanya kowacce cikin motar da aka tanada don tafiya da ita ita da mijinta.

Janyewar sultane baya ya soma takawa don barin gurin gudun tsinkewar zuciya shi ya bawa mammina daman matsowa. Cikin wannan shigar dake nuna alfahari fariya da izzarta.....cikin suturar da kowanne lokaci take zabar mafi qyalqyali da jan hankalin sutura don nuna tarin girman isarta.

Idanunta cak saman fuskar haisam......saman fuskar haisam din da ko sashen da take bai kalla ba,hasalima ya maida hankalinsa wajen tura saqo ga dukka ayarin ta hanyar na'urar dake cikin wayarsa na cewa airport din agadez zasu nufa maimakon bin kwalta zuwa Niamey kamar yadda aka shirya da farko.

"Yata......ba shakka zanyi kewarki......irin kewar da ban taba irinta ba,banda aure ba wani abu da zai iya yimin wannan yankar qaunar tsakanina dake,saidai na godewa Allah daya sanya komai zai zamana na gajeran lokaci ne........kada wani yanayi ya rudeki ki manta da mafarkanki......jajirtacciyar mace bata yin barcin da zai kaita ga mantawa da mafarkanta dama burikanta........ka tsaya tsayin daka,ka gina mafarkinka......ka gina burinka......karka bari wannan mafarkin ya rushe.....wannan shine cikar jajirtacciyar mace........kina da dama.....kina da fili.....kina da gurbi.....kuma kina da sarari na gina mafarkanki,koda hakan yana nufin zaki canza hanya da mutane masu yawa". Tayi maganan tana runtse hannunta cikin na akhnan.

Haka kawai akhnan takejin bataji wannan kewar ba......haka kawai takejin bataji wannan yanayin ba da taji a tare da morsa safiyya sanda hannunta yake cikin nata.

Ba komai da takeji illa burin zame hannunta cikin nata,haduwar hannuwansu guri guda baya tuna mata da komai sai alqawuranta......wadannan alqawuran da sukaso rudar da ita.....suka jefata wani mummunan yanayin da har yanzu bata da tabbacin ta fita ko tana ciki?. Banda nutsuwar da take samu a yanzun batasan wanne suna zata kira kanta ba,batasan wanne suna zata kira rayuwarta dama dukka sauran burikanta ba.

"Sheikh muhammad haisam" Ta kira sunan haisam kai tsaye. A nutse cikin wani irin yanayi da kallon dake dauke da ma'anar BAKI DA MUHIMMANCI ya zube idanuwa fes saman fuskar mammina din. Fuskar daya tabbatar shi yaga dama ya barta har zuwa yanzu......harma takejin tana da zarra da qarfin halin furta wadannan kalaman.......amma ya tabbatar yayi imani abinda ya tanadar mata saita gwammace bata taba walqawa cikin rayuwarsa shi muhammad haisam ba.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽