
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 10
..... He didn't say anything, he just nodded, then said in a calm voice, "Goodbye." Haneefa felt her heart break because of the way he spoke calmly and respectfully, but without showing interest at all. A heart in her head said, "If I marry this one, I will surely increase. With him, I will be a perfect queen!" Badara, who did not have the strength to speak, sat next to him, trying to attract his attention. There was a long silence before As'ad looked at her carefully and said, "Are you worried?" Terrified! Haneefa acted as if her breath had been stopped. In a trembling voice, she said, "No, your soul is old." As'ad took a deep breath, then stood up, looking at the clock on the wall. He turned and looked at her without showing any concern, then said "Let's have a good night." Haneefa felt like she was drowning. The way he stood up, his posture full of respect and dignity, her heart began to waver. Before she knew it, she said loudly "Woow!" As'ad turned and looked at her for a bit, but he didn't say anything. As he was leaving the hall, she felt her heart beating fast. A kind of love and desire enveloped her. "Oh God! This is a man. By God, As'ad.....
SHAFI NA GOMA
Da Haneefa ta shiga babban falon gidan sarauta, ta yi sallama cikin wani irin salo na kissa, muryarta na rawa tamkar wadda aka koya mata. Ta tsaya a gaban As'ad, tana zuba masa ido da murmushi mai ?auke da natsuwa. Amma abin mamaki, ko kallonta bai yi ba. Ya ci gaba da duban takardun da ke gabansa tamkar ba ta ma wanzu a cikin ?akin.
Haneefa ta ji zuciyarta na bugawa da ?arfi, fuskarta na ?aukar wani irin yanayi na rashin jin da?i. Ita kam, ba ta saba da irin wannan wulakancin ba. A daidai wannan lokacin ne ta sake ?arfafa zuciyarta, ta gyara tsaiwarta, tana murza hannunta cikin rashin gaskiya.
"Ranka ya da?e, barka da yamma," ta fa?a cikin sanyi, tana matsa maganarta da wata irin murya mai sanyi da salon lalama.
Sai a wannan lokacin ne As'ad ya ?aga kai ya kalleta, idonsa na yin wata irin ?ya?y?yawar gani. Ya lura da yadda ta yi shigar da ba ta dace ba kaya masu matu?ar ?aukar hankali, nonuwanta suna bayyana sosai, ga kuma uban kwalliyar da ta yi tamkar mai shirin rawa. Bai ce komai ba sai kawai ya yi ?an share murya, sannan ya ce cikin sanyin murya "Barka."
Haneefa ta ji zuciyarta na tsinkewa saboda yadda ya yi magana cikin natsuwa da girmamawa, amma ba tare da nuna sha'awa ko ka?an ba. Wata zuciya a cikin kanta ta ce, "Idan na auri wannan, lallai izzata za ta karu. A tare da shi, zan zama cikakkiyar sarauniya!"
Batare da ta samu ?arfin yin wata magana ba, sai ta zauna kusa da shi, tana ?o?arin jan hankalinsa. Sai da aka ?an yi shiru mai tsawo kafin As'ad ya dube ta a hankali ya ce "Akwai damuwa ne?"
Firgigit! Haneefa ta yi kamar wadda aka tsayar da numfashinta. Cikin rawar murya ta ce "A'a, ranka ya da?e."
As'ad ya yi wani irin numfashi, sannan ya mi?e tsaye, yana kallon agogon bango. Ya juya ya kalleta ba tare da nuna wata damuwa ba, sannan ya ce "Mu kwana lafiya."
Haneefa ta ji tamkar ta nutse. Yadda ya mi?e tsaye, tsayuwarsa mai cike da kima da mutunci, sai zuciyarta ta shiga karkarwa. Kafin ta ankara, ta furta da ?asa da murya "Woow!"
As'ad ya juyo ya dubi ta ka?an, amma bai ce komai ba. Yana fita daga falon, ta ji zuciyarta na bugawa da sauri. Wata irin soyayya da sha'awa suka lullube ta. "Wayyo Allah! Wannan kuwa namiji ne. Wallahi, As'ad ba kamar sauran maza ba ne," ta furta cikin ranta.
---
Da Haneefa ta koma gida, tana cikin farin ciki mai cike da fargaba. Fulany Maryam na zaune tana jiran ta dawo. Da ganin yanayinta, ta gane cewa al amura sun fara tafiya dai-dai. "Mama! Wallahi As'ad ya ha?u, kai... ai a hoto baiyi kyau ba! Yana da kwarjini, yana da kyau! Wallahi wannan fa hadaddan mutum ne, kai!"
Fulany Maryam ta yi murmushi mai cike da tsokana, amma a zuciyarta tana sake nazarin yadda Haneefa ke magana tamkar wadda ta ji ?auna. "Ke kam, ki nutsu. As'ad mutum ne mai ra'ayi da natsuwa. Dole ne ki kula da yadda kike magana a gabansa. Kada ki nuna damuwarki ko ka?an. Ki kwantar da hankalinki. Ranar daura aure na kusa, kuma As'ad ba zai iya tsallake umarnin sarki ba. Kina da lokaci ki tabbatar da cewa ya kalle ki da idanun sha'awa. Ki yi amfani da turaren da malam ya ba ki."
---
Da dare, Fulany Maryam ta ?auki motarta, ta nufi gidan babban malaminta, wanda ake kira "Mai Iko." Ta shiga falonsa cikin girmamawa, tana sunkuyar da kanta. Malamin ya kalle ta cikin murmushi mai cike da ru?u. "Tunda na ganki na san cewa labari ne mai kyau kike ?auke da shi."
Fulany ta gyara zaman gyalenta, tana murmushi. "Mai Iko, gobe za a daura auren!"
Mai Iko ya yi wata irin dariya mai ban tsoro. "Na gaya miki babu wanda zai iya tsallake wannan auren. As'ad yana a hannunki yanzu."
Sai dai Fulany ta nuna ?an damuwa. "Amma Hajja tana tsaye kan lamarin. Bana son matsala idan har ta gano wani abu."
Malamin ya kwashe da dariya. "Hajja ba ta isa ba. Tsohuwa ce, bata da ?arfin karya maganata. Ai ita ba ta isa ba! Wata?ila tana da wani ?arfin addu'a, amma kin san me? Wannan turare ki yi amfani da shi gobe. Ki turara kayanki duka da shi, sannan ki shiga cikin gidan sarki. Zaki ga yadda As'ad zai zama naki. Amma kuma akwai wani abu da ya dame ni." Fulany ta ?aga gira cikin tsoro. "Wane abu kenan?" Malamin ya lumshe idanu, yana nazari. "Ina gani kamar wata inuwa tana tsaye kusa da As'ad. Wata?ila ba matarsa ba ce, amma ba zan iya ganin komai ba."
Fulany tace. "Innalillahi! Wata kila matarsa ce! Na gaya maka tun da farko cewa ita ce ke kawo matsala a duk lokacin da aka ce za a yi wani abu."
Malamin ya yi murmushi ya yi wata dariya mai cike da mugunta. "Na ha?a aikinta ita tun tuni, amma ina ganin cewa wannan inuwar tana da ala?a da wani abu mai girma. Ki yi duk yadda na fa?a miki, burinki zai cika."
Fulany ta gyada kai tana jin ?arfin gwiwa. "Babu wata matsala mai iko. Duk abin da kake bu?ata zan kawo."
Malam ya gyara zama, yana murmushi mai cike da mugunta. "Bukata ta dai a biya kamar yadda na fa?a miki. Zan ?ara bincike, amma ki tabbata burinki zai cika."
Fulany ta yi murmushi mai cike da jin da?i. "Ba zan yi wata-wata ba, Mai Iko. Ga wannan, ka ci gaba da aikin."
----
A gida, Haneefa na gaban madubi tana tunanin As'ad. Ta rungumi kanta cikin shau?i. "Mama, wannan mutumin ai kamar jarumin fim ne! Wallahi, idan na aureshi, rayuwata ta gama kyau!" Fulany Maryam ta kalli 'yarta, tana jin cewa ta kusa cika burinta. Amma tana da ?an fargaba game da yadda Haneefa ta fara shiga ru?ani. Ta san cewa As'ad ba mutum bane mai rauni ga kyawawan mata, sai dai wanda ya samu matsayi a zuciyarsa.
---
Washegari da safe na tashi da uban aiki. Tun farkon tashina na fara gyaran gida, saboda Abba yace kosai yakeso, ita kuma ya Billy shawarma. Ai kuwa saboda tsabar iyayinta har da caramel ma, ba tea ba. Momy kuwa tace in hada mata teba. Na tsinci kaina cikin wani irin aikin wahala, amma duk da haka ban nuna komai a fuska ba, na ci gaba da gyaran gidan.
Wajen karfe tara na gama duk wani aiki. Na yi wanka, sannan na dauko system dina da wayata, na saka su caji. Tun jiya maganganun Fatima ke yawo a cikin zuciyata. Na rasa yaya zanyi da kaina. Kai! Ni Instagram din nan da TikTok din ma, na rasa yadda suke. Ai ko bantaba shiga ba. Na zauna ina tunanin yadda zan fita yau zuwa birthday din Fatima. Duk da cewa tsoro nake ji, amma irin yadda Fatima ta rika bani kwarin gwiwa yasa naji kamar zan iya zuwa.
Na tsaya na tsara yadda zan fada wa Abba. Na tabbatar idan nace birthday din kawata ne, ba zai bari ba. Sai kawai na tsara cewa zan fada masa cewa babbar kawata ce aka kwantar a asibiti, kuma mu da yan ajinmu na Islamiyya zamuje dubata. Nasan zai fi sauki idan haka na fada masa.
Ina cikin tunani sai naji muryar Momy tana cewa, "Ke Ramlah, meye haka? Ki dafa mun tuwo, ki kuma hada wannan abincin." Na tsinci kaina ina jin haushi amma na dake, nace, "Momy kiyi hakuri, nazata shi kikeso in dafa."
A nan take ta sake cewa, "Wai me yasa kika canza ne?" Cikin jin haushin kalamanta, amma ina danne zuciyata nace, "Wallahi Momy, na zata shi kikeso."
Nan fa naji takun Abba yana sakkowa. Ina tsaye cikin nutsuwa, sai naji Momy ta soma canza magana tana cewa, "To ai addu'a nake mata akan kokarin da take yi. Ka san idan na fada 'ke Ramlah,' nasan bata karya ba. Shine nazo yin mata fada."
Abba yayi murmushi, sannan ya ce, "Haba Zainab, duk aikin da yarinyar nan tayi, ki ci abin da ya samu. Kada ki matsa mata."
Momy kuwa sai ta saki marairaice fuska tana cewa, "Abban auta, addu'a fa nake mata akan wannan kokarin nata."
Na ji dadin kalaman Abba sosai. Bayan ya gama magana, sai na shiga gaisheshi cikin ladabi. Nan take na fada masa cewa mu da yan ajinmu na Islamiyya zamuje dubiya da yamma. Abba yace "Adawo lafiya."
Bayan haka ya zaro dubu biyar daga aljihunsa ya mikomin yace, "Ki siyo lemo, ki kai mata."
Na tsaya kaina ya dauki nauyi. Yau nice zan yi wa Abba karya? Amma kuma idan ban fita ba, Fatima zata ji haushi. Na karba cikin ladabi, na gode masa har ya fita, zuciyata kuwa na cike da damuwa.
Wata muguwar harara Momy ta watsa min, har naji mamaki. Kamar ba ita ce ta gama yabona ba a baya. Cikin wata irin murya mai cike da takaici, sai naji ta ce, "Ba zaki tashi ki je ki gyara saman ba? Ko ni zan gyara miki?"
Bance komai ba, na mike cikin jin nauyi na nufi dakin. Na gyara ko ina yadda nasaba, hatta wandonta da breziyarta na wanke musu kamar kullum. Ina gamawa, na duba agogo, naga karfe daya har ta wuce. Na sauko kasa, sai naji yaya Billy ta kira ni, "Auta, ga undies dina can ki wanke min, please. Na bar pad a dustbin, kinsan ban son kazanta."
Wata irin zuciya ce ta taso min. Kamar in kifa mata mari wallahi.
Ina tsaye cikin mamaki sai naji muryar Momy tana cewa, "Kiyi sauri kizo ki dora mana abincin rana."
Na cije baki, amma na kasa boye haushina, sai nace, "Wallahi Momy nagaji, sallah nake shirin yi."
Cikin tsawa ta ce, "Dan ubanki! Ni kike gayawa kingaji? Uban wanene zai yi mun aiki? Gaki agida, meye amfaninki? To wallahi baki isa ba! Fitsararriya mara kunya! Dalla, shige kije ki dora abinci. Sha sha sha!"
Baiwuya na fashe da kuka. Yaya Billy ta ce, "Haba Momy, is okay mana." Amma Momy bata kulata ba. Na shiga kicin din cikin kuka, na dora musu abincin rana, sannan na tsaya nayi sallah a can cikin kicin din.
Dakyar na gama aikin duk sai karfe hudu na rana. Ina kunna wayata sai ga kira daga Fatima yana shigowa. Na daga, ina sallama, ta ce, "Haba Auta, dan Allah kizo mana. Ina ta jiranki tun dazu."
Bacin rai ya gama mamaye zuciyata. Na ce mata, "Gani nan."
Nan take na fita na sayi kati a banki, sannan na yi download din Instagram da TikTok har da WhatsApp. Ban gama bude su ba sai ga sakonni daga Khalil sun fara shigowa. Khalil dai tun ina yarinya yake kaunata. Dan uwana ne, dan uwansu Abba da Babansa cikinsu daya. Yanzu kuwa ya gama karatunsa har yana aiki, amma Abba bai yarda da soyayyarsa a gareni ba.
Ban bude sakonninsa ba, sai na duba wasu group chats da aka kara ni. Na lura akwai wani group da sunansa "Bad Boys and Girls", sai nayi mamaki. Ban dade da shiga ba, naji wani irin tashin hankali saboda kalmomin batsa da suke ciki. A take na fita daga group din, sauran group din ma na fita gaba daya.
Cikin fargaba da mamaki naji wayata ta sake daukar kira daga Fatima. Zuciyata na dukan uku-uku, da alama yau akwai zance.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH