Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 18

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 18

.....they started to ride to get out of the kingdom.....the car with number six casss.....the car that Haisam and Akhnan were in, the car that she was carrying was carrying some things that are heavy in the standard of her life. Saida smiled and smiled at her because of the vision of success......getting space and getting a full chance to control the SULTANE and the kingdom as a whole. But one thing she didn't know......sanda was lying down when haisam ran away from her with some kind of distance running......sanda started thinking......and then haisam finished his and even closed the chapter waiting for the next chapter. Their cars are finishing leaving the house... the car turns around and goes back inside with a smile of victory... at the same time, the press (journalists) are coming in their car, from the main TV and radio station of the country. *_Spit.......😄, what will happen?_* There was a kind of silence in the car, the silence that Haisam was trying to control his anger. Now there is no time to be angry, it is time to start harvesting after the black seed that has been planted for a long time. His silence is echoed by the repetition of Olive's words in his head. Shameless

Standalone post1,860 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 18*

"Ina fatan dai ka sani.....duk da cewa komai temporary ne......buzuwar mace......tana da cikakken 'yanci,mata ne masu 'yanci,masu son 'yanci.....masuson walwala da barinsu suyi rayuwarsu cikin sakewa,basusan wahala ba ko wasu dokoki da zasu taqaita musu jin dadinsu ko walwalarsu ba.....saboda haka nake cewa,ka kula da ajiyarmu zuwa lokacin da zamu karba.........inaso kayiwa agadez kallon qarshe....don ba lallai ka sake samun dama kwatankwacin wannan a rayuwarka har abada" Ta qarashe maganar da wani irin kallo cikin idanunta.

Nasa kallon ya zurfafa a kanta,kallon da duka duka na sakanni biyar ne,saidai qasa da second biyar din wani abu me qarfin gaske ya nemi rusunar da nata kaifin ganin.

Abu na qarshe daya daketa sosai har cikin jijiyoyinta murmushi ne.....murmushi daga fuskar haisam......murmushin da bata buqatar fashin baqi ko qarin bayani daga gurin kowa. Da baya take ja a hankali amma idanunta suna kan motocin da suka fara hawa saiti don fita daga masarautar.....motar dake dauke da lamba shidda casss.....motar da haisam da akhnan suke ciki,motar da takejin tana dauke wasu abubuwa da suke da nauyi a mizanin Rayuwarta. Saidai kuma murmushi ya subuce mata,murmushi ya kubce mata saboda hangen nasara......samun sarari da kuma samun cikakkiyar dama na sarrafa SULTANE da masarauta gaba daya.

Saidai wani abu guda da bata sani ba......sanda take kwance a lokacin haisam ya tsere mata da wani irin matakin nisa a gudu......sanda take fara tunani......a sannan haisam ya kammala nasa har ma ya rufe babin yana jiran chapter ta gaba.

Sanda motocinsu ke kammala fita daga gidan......sanda ta juya tana komawa ciki cikin murmushin nasara......a daidai wannan lokacin 'yan press(yan jarida) motarsu ke kutso kai,daga babban gidan tv da radio na qasa.

*_Tofa.......😄,me kuma zai faru?_*

Wani irin shuru ne ya ziyarci cikin motar,shurun da haisam yayishine yana qoqarin controlling fushinsa. A yanzu babu muhallin yin fushi,sarari ne da fara shimfida girbi bayan baqar shukar da aka dade ana yinta. Shurunsa yana zarcewa ne da maimaita kalaman zaituna cikin kansa. Mara kunya duk a inda yake mara kunya ne. Bai taba zato zata iya ci gaba da duban idanun wani daya shafi ahmad ba balle ta nuna fake love din da take masa,ciki kuwa harda akhnan din. Akhnan din daya gama fahimtar wasan data shiryayi da Rayuwarta ba qarami bane,CETONTA ko shine ya zama silar tsoma qafafunsa kenan cikin agadez?.

Dab da isarsu airport din ya waiwaya a hankali zuwa sashen da take zaune. Kowacce rana tana sake tabbata ITA DIN MALLAKINSA CE......a yanzun gata sukutum da guda gaba dayanta sultane ya damqa ragamar Rayuwarta a hannunsa da dukkan yarda. Zai iya tsallakewa kuwa?,zai iya cinye wannan jarabawar?.

Baya iya ganin fuskarta......amma yana iya ganin zara zaran yatsunta data gamesu guri daya tana murza zoben dake tsakiyar yatsan nata. Koda baya ganin fuskarta yana jin akwai hawaye me yawa kwance cikin fuskarta. Idan tayi kuka yanzu......idan a yanzu tana kuka kadai saboda barin agadez.......me zataji?,yaya zatayi a sanda tasan wacece mammina?.

Wani radadi takeji da zugi cikin ranta....wannan tsohuwar aqidar wannan tsohon ra'ayin yanason yunquro mata. Ya rabata da mahaifarta......ya rabata da kowa nata......ya dauketa cancakat zai kaita qasarsa garinsa ba tare da tasan wayeshi ba....zai kaita inda ba idanuwan sultane babu kulawarsa......dukka don kawai buqatar kansa?,duk kawai don shi yazo a NAMIJI?. Tun daga mataki na farko.....tun a yanzun da mintuna da awannin kasancewarsu tare suka fara harbawa,ta fara lissafawa da qididdige yadda abubuwa masu tarin yawa nata suka fara juyewa zuwa MALLAKINSA ciki harda nasabarta da sunanta.

Iya wannan abun tunanin dake zukatansu ya wanzar da wani irin shuru,wanda bai yanke ba sai sanda suka isa airport din bangaren private parking lot na airport din.

Dukka motocin suka tsaya,sai a sannan ta daga blue eyes dinta a hankali tana duban airport din. Mamaki kadan ya kamata,kaman idan taji daidai zasu wuce Niamey ne a mota saboda ba jirgin da zai tashi a daidai wannan lokacin,amma me sukeyi cikin airport din.

Bata kalleshi ba,amma tana jin sanda driver ya fice daga motar daga can bangarensa,motar ya zamana daga shi sai ita kadai.

Wani shurun ya sake ratsawa tsakani,tana jin kamar wani sabonshi ne,ya kuma zame masa jiki. Jinkirin fita a duk sanda sukazo wani guri,har sai kusan wanda ke dakon fitowarsu hankalinsa yakau. A baya yana bata haushi da hakan da yakeyi,amma a yanzun saita tsinci kanta da lalubar dalili?.

Izza ce ko kuwa?. Qasaita ce ta masa yawa?,wanne irin izza ne wai a jininsa?. Tambayar data fusgeta har takai ga daga idanunta da har yanzu taketa ririta hawayen cikinsu ta kalleshi.

Kaman ko yaushe,kaman yadda ya saba mata,wannam attitude din nashi dake bata haushi. Ba ita yake.kalla ba......wayarsa yake kalla. Ba ita yake kalla ba,hankalinsa ba'a kanta yake ba. Me yasa sai ita zata dinga kallonsa?,me yasa sai ita zata dinga satar kallonsa?. Hasalima ai sultane tasan ya basa amanarta. Me yasa bazai damu da ita ba?. Irin duk motsinta dinnan idanunsa yana kai?,irin duk wani tari nata ko qanqani ne ya tamabaya.

Wuf tayi ta zare idanunta daga kansa sanda yake motsa manyan idanunsa yana dagasu xuwa kanta. Kafeta yayi da kallo sanda take dauke idanunta cikin basarwa. Ya jita.....yaji duk wani kallonta a kansa,har iya tsahon mintunan data dauka din.

Bata zata ba batayi tsammani ba taji hannuwansa saman kanta.....dukka hannuwansa guda biyu inda yasa yatsunsa yana jan bannan veil da tayi rolling dashi saman kanta.

A nutse ya ajiye idanunsa gaban goshinta,inda wani sashe gashinta me santsi da baqi ke kwance luf gaban goshinta. Irin sumar nan ta cikakkiyar buzuwa da tayi gadon suma ta kowanne bangare.

Bugun zuciyarta ya tsaya na wucin gadi,ta dauke numfashinta dif tana jin yadda zuciyarta ta dawo aiki da wani irin gudun wuce sa'a sanda ya sanya yatsansa a hankali kamar me tsoron taba qirjinta yana sakin tattara tattarar da mayafin yayi saman qirjinta.

"Bazan iya jure wannan shigar ba......material na abayar nan yana showing........" Sai kuma ya dakata yana jan jikinsa baya.

Ko da ba gaya mata ba,tana jin yadda kalmomin da haruffan suka fito a rarrabe,kamar bugun zuciyarsa keson hana sautinsa fita daidai.

"Subhanallahil azeem" Yake fadi idanunsa a lumshe,yana jin yadda bugun zuciyarsa ke rarraba numfashinsa. Tsahon wasu sakanni,sannan ya bude idanunsa a hankali. Abubuwa da yawa,abubuwa da yawa ya gani saman fuskarta saboda wani irin kusanci daya wanzu tsakaninsu sanda yake qoqarin daidaita komai nata kada wani sashe na Jikinta ya bayyana.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Wata irin glowing skin dake shimfide saman fuskarta,wasu irin eye lashes da eye brows da suka kusa hadewa da junansu. Wata irin lobawa daga tsakiyar habarta harma da gefan kuncinta guda daya.....ga kwantaccen sumar data yiwa goshinta ado daya tabbatar ta sauka har kusa da kunnenta.

A nutse ya bude murfin motar,ya fice,ta bude idanunta a sace tana kallonsa. Takunsa na dabanne......wani irin taku da tunda take ganin nau'in isassun maza bata taba katarin ganin wani da irinsa ba. Tayi gaggawar kauda kanta sanda ya iso bakin qofar da take zaune,ya saka hannu ya bude mata murfin motar kamar yadda ya saba yana ja da baya don bata hanya.

Ta gefe ta sake satar kallonsa,still ba ita yake kalla ba,ya tsaya kawai daga bayan qofar da wannan wayar dai a hannunsa. Saita dauke kanta ta hadiyi wani yawu da haka kawai taji ya mata tauri da d'aci.

Ranta taji ya dan jagule,ta motsa a nutse tana sako qafafunta waje,daidai nan ya matso da sauri,ya sanya hannunsa da nufin ja mata rigarta ta sauka ga qafafunta,idanunsa suka sauka saman fararen qafafunta masu dogayen yatsu wadanda jan lalle ya yiwa wani irin ado me daukan hankali..

*M A M M I N A*

Bayan juyawarta zuwa cikin gidan sai takejin iskar gidan yau kawai ta dabance,kaman yadda ta tabbatar nishadinta zai zama na dabanne.

Almaz yana maqale a ranta,saidai tana ganin abune me sauqi bazai zame mata matsala ba. Ta sanshi tun yana qanqaninsa,duk wata tarbiyya da raino nasa itace ta bada wannan horon,ta yaya dabbar daka raineta da hannunka ta isa ta zame maka barazana?.

Ta tabbata ta kuma yi imani haisam baisan me yakeyi ba.....kodai lissafi ya kwance masa,ko kuma tsananin murnar samun akhnan......akhnan din da yake kalla kamar banza ta samu sama taka ya sanya ya soma daburcewa a lissafinsa. Wanda ita hakan yayi mata daidai,akhnan zata zama tamkar fatsar da zata kamashi a hannunta tayi wasa sa rayuwarsa har sai yayi nadamar ajiye malinta ya dauki bangaren bin diddiqinta.

"Allah yaja da ran giwa.....Allah shi riqa miki" Maher.....maher d'aya daga cikin irin da haisam ya bari agadez......maher din da a yanzu mammina ke hasashen sakashi a gaba ya maye wasu gurabe na mutanen data rasa ya furta maganan cikin tsananin girmamawa.

Murmushin jin dadi ta saki,yaron yana ranta tana jin kuma wani aminci a kansa,saidai duk da haka ta dakata ne ta gama karantarsa. Sau da dama yana cikin wadanda ba'a gulmarta idan an ganshi,saboda yadda yake girmama sunanta ma kadai da duk wani abu daya rabeta ballantana ita kanta.

"Me yake tafe dakai?" Tafisu ta tambayi maher.

"Yan jarida ne.....daga gidan talabijin da radio na qasa.....sukeson tattaunawa dake" Ta danyi jim tana duban maher din.

"Tattaunawa?" Ta tambaya cikin son qarin bayani. Kai ya gyada.

"Itafa Allah ya baki yawan rai......qoqarinki da jajircewarki akan mutanen qasarki da yankinki.....labarin alkhairanki daya karade ko ina shine silar zuwa su tattauna dake,sunce ki musu afuwa basu sanar ba basu nemi izni ba kafin yanzu.....amma a yanzun ma idan kina ganin saidai suje su dawo a basu lokaci zasu aikata hakan" Ya qarasa fada yana karantar yanayinta. Shuru tayi na daqiqu,shurun da tafisu ta katseshi ta hanyar fadin.

"Ba girmanki bane....karamci ne a tare dake ki karbi baqin da suka zabeki ke kadai,duk da ba ke kadai bace matar sultane amma sukace dake sukeson ganawa". Murmushi ta sake saki a hankali,tafisu tazo da magana. Wannan dalilin ya sanya takeson tafisu sama da kowa cikin mutanenta. Tana da wani irin hasashe da hangen nesa me zurfi.

"A basu guri mafi kyawun dauka.....zan shiga ciki na canza saina fito".

"An gama Allah ya taimakeki sarkin karamci" Maher ya fadi yana miqewa sa gaggawa.

A yau sai ta sakejin kanta yana fasuwa.....bawai don bata taba hira a kafar yada labarai ba.....aah,saidai wannan din tazo mata akan gabobi masu yawa,tazo mata da wata babbar dama da zata isar da wani saqo cikin sanyin rai.

Sutura ta alfarma tasa aka sake ware mata,tasa kuma akayi aiken kabakin arziqi ga tarin masu daukan rahoto da labarai daga gidajen tv da radio masu yawa bisa jagorancin babban gidan jarida na qasa. Tasa a shaidawa sultane zatayi ganawa da 'yan jarida,bai kuma hanata ba tunda kusan lokaci lokaci tana yi din.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽