Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 10

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 10

...you grabbed three mats and took the bride and her friends to her house. As the corner was also here, they stepped on their feet. We sat down and chatted for a while and everyone asked for their bed, and the bed was this mat that your alwanka answered by turgeza (😂 people, what is Turgeza? Answer in the comment, there is a gift🤣, and what is Alwanka too? That's two questions😂🙏). Two of her friends went to bed, one was lost alone. The next morning, cocoa was bought for them and they were fed with it. After that, they went back under the cedar tree in the house and sat and talked, but the bride who saw her was very happy, sometimes she even wiped away her tears. On Alwanka's part, she prepared her food, which contains up to one and a half bowls, since it is the morning of TURGEZA, and by ten o'clock, she will surely shower the bride's friends with szunguru, and the dishes will contain it for her. The bride's bride's clothes contain the contents of the old lady's quarter (🤣 I hope you know the contents?), and in her hand, a zunguru is put inside her (Who is the zunguru? 😂 Whoever said there is a gift too🤣🙏). After the marriage of the bride, the bride's friends left for their home in

Standalone post2,195 words

.......Bayan ƴan ganin lefe sun kammala kowa ya wuce an adana kaya ma sannan A'isha ta dawo daga maɓoyarta. Ganin yanda aka ɓata gidan ta ɗauka tsintsiya ta hau shara kamar yanda ta saba, tana tsaka da sharar tsakar gida duk da baƙi sun fara cika gidan nasu ƴan biki matar yayansu ɗan ƙanin babansu ta shigo gidan. Cike da shammata ta shiga zazzage mata turare a jiki tana guɗa. Wani irin sakin tsitsiyar A'isha tayi a ƙasa, sai kuma ta fashe da kuka tana mai durƙaushewa a wajen. Kuka take sosai mai ban tausayi, har sai da akazo aka ɗagata a wajen. Abokan wasa kuwa sun samu nayi, sai binta suke da guɗa. An cire mata ƴan kunnenta da tsakiyarta ta wuya (Abin wuya, kamar sarƙa dai a yanzu). Hakama kayan jikinta ta cire an kawo mata tsohon zani da riga ta saka. Wannan alama itace amarya ta shiga lalle kenan, dan kuwa zuwa bayan sallar magriba wadda take matsayin Alwanka ɗinta tazo gidan, ƙawayenta dama tunda akai kamun sun cika gida abinsu domin zaman lalle ya fara kenan. Bayan gaishe-gaishe aka ɗakko ma alwanka tabarmin tirgeza guda uku ta kwashi amarya da ƙawayenta suka tafi gidanta. Da yake itama anan anguwar take da ƙafa suka taka abinsu. An zauna an ɗan taɓa hira kowa ya nema makwancinsa, makwancin kuwa wannan tabarmi ne da alwanka ta amso na turgeza (😂mutane na miye Turgeza? A amsa a comment akwai ƙyauta🤣, sannan miye Alwanka ma? Tambaya biyu kenan😂🙏). Biyu ƙawayenta suka kwanta, ɗaya aka bata ita kaɗai. Washe gari da safe aka dama musu koko aka sayo ƙosai aka basu sukai kari da shi. Daga haka suka koma ƙarƙashin bishiyar ceɗiya dake gidan suka zauna suna hirarsu, sai dai amarya daka ganta duk tayi sukuku, lokaci-lokaci ma takan share hawaye abinta. A ɓangaren Alwanka kuwa ta tanadi lallenta na ƙunshi har kwano ɗaya da rabi ta kwaɓa tunda safe na TURGEZA kenan, zuwa goma ta bama ƙawayen amarya lalle da zunguru sai ledoji su ƙunsa mata. Tsaf ƙawayen amarya suka ƙunsheta kuwa da ƙunshi na tsohuwa ta faɗa kwata (🤣ina fatan kun san ƙunshin dai?), hakama a hannunta sannan aka saka mata zunguru a ciki (Miye zunguru?😂 Wanda ya faɗa akwai ƙyauta shima🤣🙏). Bayan an gama sakama amarya lalle ƙawayen amarya suka fice zuwa gidan su Nasiru, dan kuwa ance duk abinda ake badawa na gidan anguna suje can su amsa. Bayan gaida Innar su Nasiru da baƙin Bauchi da suka samu a gidan aka danƙa musu shinkafa da manyan zakaru har huɗu, sai kayan miya da kayan magi da iccen girki da man gyaɗa, sai kuɗi wannan sune kayan kamu. Koda suka dawo gidan alwanka ɗanta Ibro ne ya yanka musu kajin, su kuma suka shiga hidimar girki amma dai Alwanka na duba musu da nuna musu yanda duk ya dace ace sunyi. Amarya kuwa na zaune da ƙunshinta har lokacin abinta. Zuwa azahar aka kammala abinci, shinkafa da miya da naman kaji zuɗu-zuɗu, mai kuwa. A ƙyallan har kana iya ganin fuskarka a ciki fes. Umarnin cire ƙunshi Alwanka ta bama amarya, dan haka ƙawayenta suka fara taimaka mata tai zaman cirewa kamar abin arziƙi, gefe kuwa manyan ƙawayen amarya sun shimfiɗa tabarma a tsakar gida, wanda suka taimaka mata ta cire ƙunshi suna gamawa ta miƙe da nufin barin wajen kawai taji an rufu a kanta, cak suka ɗagata sai kan tabarmar nan da aka shimfiɗa. A take ta birkice musu ta shiga bibbigesu da son ƙwace kanta, amma ina sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, tuni suka danneta a wajen, dama gashi daga ita sai zani ɗaurin ƙirji, dan sanda za'a saka ƙunshi sakata akai ta cire rigar. Tsaf ƙawayen amarya suka cire zanin nan kuwa daga jikinta aka barta zir sai ɗan kamfai (😂wato mutanen da anyi shagali da ɗanyen aiki gaskiya🤣). Sauran lallan da aka saka mata ya rage da wanda aka cire matan Alwanka ta kawo musu, nan fa ƙawayen amarya suka shiga ɗiba suna saka mata a jiki ana murjeta da shi. Itako tana kai musu duka da harbinsu ƙafa da hannu tana kuka. Har cikin gashin kanta ana raira waƙa, bari na ɗan raira muku💃🤣.

Ayye yara iye TURGEZA. Ga Turgeza yazo, Turgeza.

A wanketa da sauri, turgeza.

Lallen iya ƙamshi, turgeza.

Ayye yara amarya turgeza.

Sai da ni bilyn ku😂 (magana ta gaskiya ni na ƙirƙiro muku waƙar, amma ta gaskiyar ba haka take ba, baitin farko ne kawai na gaskiya kada kakanin mu suce na musu sharri😂🤣🤣).

Sosai amarya ta dirzu da lalle. Masha ALLAH kuma sai tayi ƙyau abinta, sai dai fa kowa ya daku gwargwadon iko cikin ƙawayenta. Itama kanta ta jigata da kuka da harbe-harben data sha. Ana sakinta taja zaninta ta ɗaura, data rarumi icce tai kan ƙawayen nan nata sai gudu Malam. Tuni fa kowa yay waje, masu neman wajen ɓuya suka nema, masu haura katanga nayi masu yin hanyar zaure nayi. Da ƙyar Alwanka ta kamata ta riƙe, sai da duk suka baje sannan ta saketa, babu batun wanka, wannan lalle na jikinta haka kuma zai cigaba da zama a jikin nata har sai gobe, gefe ta koma ta dasa sabon kuka. Babu wanda ya hanata har tayi mai isarta ta gaji dan kanta ta haƙura. Bayan komai ya lafa ƙawayen amarya suka daddawo sai kuma aka ɗakko abinci da miya aka baje kuma a tsakar gida da turirrika na rabo. Haka aka raba abincin ƙunshi da nama kowa ya samu har maƙwafta, aka baje kuma aka fara ci ana hira da wasa da dariya. Bayan sun kammala aka aiko baranya ɗakko igiyar shillo, babu jimawa ta dawo, amarya ta tashi ta saka rigarta da kallabi suka kwashi igiyar nan suka fice bayan gidan wajen wata bishiyar ɓaure ƙatuwar gaske. Anan aka ɗaura wannan igiya ta ɗauru kam sannan aka fara shillo, idan wannan ya sauka wannan ya hau, har yamma suna a wajen suna waƙe-waƙensu na ƴanmata cike da nishaɗi. Sai gab da magriba suka dawo gidan Alwanka. Washe gari alhamis ma haka suka sha shagalinsu aka ƙara yima amarya wankan lalle kamar jiya, dan kuwa yau ma zir akai mata sai ɗan kamfai aka shafeta da lalle har cikin kanta, tasha kukanta kamar jiya har yamma. Zuwa dare bayan sallar isha'i Alwanka ta tattarasu tai musu rakkiya aka maidasu gidan su A'isha. Gida kam ya gama cika da dangi tako ina. Bayan gaisuwa Alwanka tace “Ga aro na maido, ALLAH ya sanya alkairi ya fiddamu kunyar gobe. ALLAH Kuma yasa takai mutuncinta ɗakinta. Nagode, Nagode ALLAH yabar zuminci”. Atare aka amsa mata da amin. Dangi sukai godiya suma sosai ta wuce. A ranar anan gidan su A'isha suka kwana, dan kuwa ɗaki guda aka ware musu ita da ƙawayenta. Washe gari juma'a ɗaurin aure, ta ko ina dangi maza sunata isowa, hakama tawagar ango da danginsa daga Bauchi, da abokansa na Bauchi dana Kano duk sun iso, zuwa ƙarfe sha ɗaya aka ɗaura auren A'isha da Abdul-rasheed akan kuɗi sule na gugar sule har sule goma cas. Lallai wannan yawan sadaki ya girgiza mutane, dan kuwa sule goma ba kuɗin wasan yaro bane a lokacin. Abinci kala-kala tako ina ƙamshin ke tashi na miyar taushe ga nama kamar a banza. Dangi kowa ka gani bakinsa a washe anatama juna sambarka, balle kuma ace Inna ai ba'a magana, tayi shar da ita cikin sabon ɗinki. Amarya kuwa na can tare da ƙawayenta a ɗaki, sai dai a miƙa musu abinci. Ƙawaye sunyi wanka da kwalliya, amarya kam dai tana nan ba wanka har yanzu dai tsoffin kayanta ne a jikinta na zaman lalle, sai bayan sallar azhar kuma aka shirya yima amarya wanka dan za'a shiryata domin tafiya Bauchi. An shirya ruwan wankan amarya a cikin ƙaton masaki da yasha addu'oi daga tsoffi, aka zuba lalle sai kuma ruwan turare kala uku masu ƙamshi sosai, sai sabulu shima mai shegen ƙamshin tsiya. Bayi aka kaishi sannan aka kira alwanka da zatai mata wanka. Aifa nan abokan wasa suka miƙe domin rakkiyar amarya bayi, tana kuka aka dannata ciki bayin, dama Alwanka an kiranta. Waƙa abokan wasan nan nata suka fara rairawa suna tafi yara na tayasu....

Tsohuwa iki wanke, kin saki Kwankwaso yeee a ƙofar soro💃....

(😂Ehem-ehem lamarin fa ba'a cewa komai, amma wannan waƙar ta gaskiya ce walle bani na ƙirƙira ba😎😂).

Kuka sosai itako amarya keyi, Alwanka kuwa na wanketa lungu da saƙo har gashinta dake danƙare da lalle. Duk wannan dattin ya fita da suke kira (Saiɓi), sai ga amarya na sheƙi da ƙyalli da ƙamshi kamar ka lasheta. Zani aka bata ta ɗauro aka rufeta da wani aka fito da ita sai ɗakin Inna. Acan aka shafa mata mai mai ƙamshin tsiya mai gurguwa, aka shafe ta da turarruka kala-kala Sannan aka bata sabon zani da riga na atamfar.... Ta saka daga cikin lefe yake, sai ɗan kwali disko da wani fallen zanin na lulluɓi. Aka shafa mata hoda aka saka mata jan baki amarya ta fito tsaf da ita masha ALLAH. To daga nan fa iyaye suka zagayeta aka shiga faɗa da nasiha, itako tana ƙunshe a zanin nan da take lulluɓe tana kuka sosai. Bayan sun gama akasa Inna tai mata addu'a tana kuka sosai, dan yau ne karo na farko da zatai nesa da ƴarta. Bayan ta kammala aka kamata aka fito da ita soro inda iyaye maza suke suma suna jira. Nan ma sabon faɗa da nasiha aka buɗe, gargaɗi dai kam amarya ta shashi gwargwadon iko kafin a kamata zuwa ƙofa gida inda motor da za'a ɗauki amarya take. Kanta ce guda biyu, sai ƙarama ɗaya da za'a saka amarya. Tuni masu zuwa sun cika kantar kuwa harda ƙawayen amarya, dan haka aka sakata cikin ƙaramar Innarta da Gwaggon na ɓangaren uwa da uba suka shiga kusa da ita, sai a gaba direba da Nasiru ne, ango da sauran abokai kuwa tuni sun ɗauki hanyar Bauchi su dama da iyaye ƴan ɗaurin aure. Motoci na ɗagawa ƴammatan amarya suka fara raira waƙa da yara....

Ayye yaraye dide, ayye yaraye naye, ayye yara iye naye yaraye!!.

Ƴammata kuzo roni, mi zamuyo roni? Aiko zaman lallen A'isha lale laya!.

Ke kikace kinayi da shi, shi yakace yanayi dake, har magana takai ga manya kibar mana koke-koken tsiya.

Babu mararraba ba rabawa, iccen wurma yasha harara, yasha rarraɓar masu ƴaƴa, tunda ya kada goɗiya.

Iye yaraye, ke kikace kinayi da shi, shi yakace yanayi dake!.

💃🏼💃🏼😂😂Iya nan za'a tsaya, (😎kuma itama ta gaskiya ce ehe😂).

Su suna raira waƙa amarya na kuka mai ban tausayi. Haka motoci suka wuce jama'ar anguwa na binta da addu'ar fatan zama lafiya na har abada. Ahaka aka ɗauki hanyar Bauchi. Tun masu waƙa nayi har suka gaji wasu ma suka fara barci, cikin amincin ALLAH bayan magariba suka iso Bauchi. Kai tsaye kuma gidan iyayen Abdul-rasheed aka wuce da amarya, inda suka samu tarba ta mutuntawa da girmamawa. Tarba dai kam dangin Abdul-rasheed sun yima amarya ta gata ita da danginta, yayinda take ƙunshe cikin gyauton zanin da aka lulluɓa mata na atamfarta mai barewa datai mata ƙyau. An kawo musu abincin maraba kala-kala sukaci suka ƙoshi, daga haka suka baje barci dan kowa ya gaji matuƙa, ita kanta amarya tuni ta ɓingire da ƙyar ma aka samu taci abincin.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 11_

__________________

*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana 💃 fulanin asali ke nan 😘._*

*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*

_Maza kuzo ku sha labari da ɗumi-ɗuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buɗe muku gidan gyara da ƙalƙale jikin mata ƴan kwalisa a kusa da ku gabb._

*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na👇_*

*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*

_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_

*_Zaku same mu a wannan numbers ɗin kamar haka👇_* *07068210505* *09133081313*

_DEALER IN all kind of skin care products such as:_

moisturizer Sun screen Face Toner Eye cream Face serum Face wash Face scrub Face cream Face marsk Body lotion Body cream Shower gel Body scrub Tube Body oil Body spray Perfume Hair crm Hair spray and many more

*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne 💃_*

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________