Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 22

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 22

.....except from Inna and Gwaggo Lara and even A'isha herself. Haysam completed his primary school, then Ma'aruff and one should be banned, but none of Abdul-Rasheed's brothers spoke. When Nasiru came and saw that there was a lot of silence, he took them and put them in, and he said that we have to wait for Haysam's paper to come out and he also went to Secondary, and the younger ones Ummi, Mommy, Bilal. They were put through the screen as Haysam was coming. Then he turned back to Kano. Abdul-Rasheed's seven months in the country, may God make Yakura safe. However, childbirth comes with stress and tension, since the womb is old and privileged, there is not enough health. Today, when she gave birth, she started bleeding. It's like a joke that Inna Salame can stop him, and Inna Aisha and Gwaggo Araba help her until it gets too bad and they say to go to the hospital. But I don't have enough money to go to the hospital, Aisha went to their elder brother Abdul-rasheed's house to tell him, but he showed him why he didn't have money. Even when she went in, his wife said he was not here. Her mind woke up and she came back home, she didn't know.....

Standalone post2,043 words

........Anyi addu'ar uku, ranar addu'a mutane sun cika fal harma da wanda ba'a sani ba abokan aiki dana kasuwanci na Abdul-rasheed daga gari-gari. A washe garin cikon kwana na huɗu mutane suka fara raguwa. Sai ƴan uwa na jiki kawai da danginsu na Maiduguri sai su Innar A'isha ƴan kano. Bayan addu'ar bakwai ma kowa ya wuce sai su A'isha kawai da Innarta da zata zauna da su. Sai wata ana kiranta Gwaggo Laraba ƴar Maiduguri dake matsayin kamar kaka a wajen su Abdul-rasheed ɗin. Zasu zauna da su har su kammala takaba, koda yake A'isha ce mai gama takaban a kusa. Yakura kam sai in ALLAH ya sauketa lafiya kuma. Gashi cikin ƙarami ne zubar jinin da tayi kuma zai iya sakawa ma ya koma baya. A yanzu kam Alhamdullah, basu da matsalar abinci da abubuwan buƙatu na rayuwa, dan suna samun ɗauki daga ƴan uwa da abokan arziƙi, musamman ma Nasiru dake yin iya bakin ƙoƙarinsa. Bai gajiya da yawo tsakanin Kano da Bauchi. A haka A'isha ta kammala takaba, sai Yakura dake jan ciki, tana kuma samun kulawa sosai daga Inna da Gwaggo Laraba har ma da A'isha kanta. A tsakanin Haysam ya kammala primary ɗinsa, sai su Ma'aruff kuma daya kamata ace anyi haramar sakasu, amma a ƴan uwan na Abdul-rasheed babu wanda yayi magana. Sai da Nasiru yazo yaga shirun yayi yawa shi ya ɗaukesu ya sakasu, ya kuma ce saura a jira takardar Haysam ta fito shima ya wuce Secondary, ƙananun kuwa Ummi, Mommy, Bilal. Aka sakasu ta allo kamar yanda Haysam ke zuwa. Daga haka ya juya ya koma Kano. Watan Abdul-rasheed bakwai a cikin ƙasa ALLAH ya sauki Yakura lafiya. Sai dai kuma haihuwa tazo da tangarɗa da tashin hankali, dan tunda dama cikin ya tsufa gata nan ne dai babu isashiyar lafiya. Yau kuma data haihu sai jini ya ɓalle mata. Abu kamar wasa Inna Salame anguwar zoma zata iya tsaida shi, ga su Innar A'isha da Gwaggo Laraba na taimaka mata har abu yaci ƙarfi akace a wuce asibiti. Amma mi babu isasshen kuɗin zuwa asibitin, A'isha ta fita hankali a tashe zuwa gidan babban Yayan su Abdul-rasheed sanar masa, amma sai ya nuna shi wlhy baida kuɗi, hasalima yau haka ya tashi baida ko sisi, sai dai taje wajen ƙaninsa mai bi masa. Shima koda ta shiga ma sai matarsa tace baya nan. Hankalinta ya tashi ta dawo gida, bama ta iya sanar ma su Inna yanda akai ba ta sake fitowa, abinka da babu waya balle ta kira Nasiru dake tsaye akan al'amarin su. Wajen makwafcinsu dake saida dabbobi ta nufa, tace ya taimaketa ya bata kuɗi zasu kai Yakura asibiti idan sun dawo yazo ya kama akuyarta da take kiyo. Bai musa ba ya bata kuɗin, cikin farin ciki ta juya zuwa gida, tana isa aka ɗauki Yakura aka nufi asibiti. Likitoci sunyi faɗa sosai, daga ƙarshe dai suka amsheta. To ashe wasa farin girki, dan kuwa dai Yakura jiyya ce mai girma a tare da ita. Dan abu tun ana ɗaukarsa na marmari har ya wuce gaban kwatance. Tun ƴan uwa na zarya da bada ɗan taimako har kowa ya naɗe hannunsa ya bar A'isha da Nasiru kawai da Innar A'isha akan al'amarin Yakura. Sai Khadijah da autan su Abdul-rasheed angon da sukai haɗari ran aurensa da suma suke nasu ƙoƙarin duk da ba masu ƙarfi bane, dama dai ƴaƴansu Abdul-rasheed ɗin ne taƙamarsu, yanzu kuma ya tafi abubuwa duk sun tsaya musu. Shima Nasiru ƙarfin hali ne kawai ba wani ƙarfi ne da shi ba, gashi yana shirin tafiya ƙara karatu daya samu scholarship a ƙasar waje. Ana cikin wannan kai-kawo maganar tafiyar tashi kuma ta tashi, da farko yace ya haƙura A'isha taita roƙonsa akan yaje dan ALLAH kada ya fasa. Nan dai su Inna ma suka saka baki haka ya tafi bayan ya ajiye musu ɗan abinda zai iya na iya ƙarfinsa, bayan tafiyarsa matarsa da ƴarsa ɗaya Raihana da bata wuce shekara biyu ba sukabi bayansa. Tun ana zaman asibiti da Yakura har rashin kuɗi yasa suka tattaro suka dawo da ita gida, Gwaggo Laraba ma ta sulale ta tafi abinta, sai A'isha kawai da Innarta, ga yara har takwas dan yarinyar da Fauziyya ta haifa ma sai A'isha ke shayar da ita. A wannan halin A'isha ta ƙuƙuta ta saka Abdul-rasheed a Secondary school, ta fara sana'ar masa da safe. Sai kuma ƙananun tsogumin ya fara tashi akan zaman Inna, wai ya kamata ya tattara ta koma Kano, rasuwa shekara ɗaya da rabi amma ta tare a gidan ƴarta. ALLAH sarki Inna uwa mai dattaku, haka ta tattara ta wuce A'isha na kuka Yakura dake kwance komai sai an mata da yara nayi ta wuce. Tafiyar Inna baifi da wata guda ba Babban yayan su Abdul-rasheed ya lallaɓo yazo wa A'isha da batun wai yana son ya aureta, dan su haɗu su riƙe ziri'ar Abdul-rasheed. Takaici ya saka A'isha rufe ido tai masa tass, wannan abu da tayi kuma babu bincike mutane da dangin Abdul-rasheed suka sakata gaba saboda shi ya juya maganar a baibai. Haka aka dinga zuwa har gida ana cin mutuncin A'isha, sai dai su haɗe kai da Yakura da bata ɓoye ma komai ba suyita kuka. Ana tsaka da wannan rikicin jikin Yakuran ya rikice matuƙa, A'isha ta dinga bin dangi tana neman taimakonsu amma kowa ya nuna bazai iya ba bai da shi. Sai kawai ta yanke shawarar saida gidan da suke domin takai Yakura asibiti. Abinda ya bata mamaki sai ga ƴan uwan Abdul-rasheed sunyi uwa sunyi maɗaukiya, ƙarshe ma Yayan nan nashi da suke kira da Yayan gandu daya ce yana son aurenta ne ya sai gidan. Haka ta share bata nuna ta damu ba takai Yakura asibiti, ta biya kuɗi za'a mata aiki da tun farko likitoci suka faɗa rashin kuɗi ya hana. Sai dai UBANGIJI mai hikima bayan yin aikin da kwana biyu ALLAH ya ɗauki ran Yakura😭. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wato gigita da magagin tashin hankalin da A'isha ta shiga da Haysam mai ɗan wayo a cikin ƴaƴan ɓata lokaci ne ma wajen zana shi. Dan Yakura haihuwar Haysam ne kawai batai ba. Amma komai da uwa take ma ɗa ta masa. Haka tsakanin Yakura da A'isha zamane na amana da ba'a batun wani kishi. A ranar da Yakura zata koma ga ALLAH ta kama hannun A'isha dana Haysam ta jaddada musu ta bar musu amanar ƴaƴanta. Bata yarda A'isha ta bama wani su Ma'aruff ba a duniya koda ƴan uwanta ne da suke uwa ɗaya. Tace ta baiwa A'isha har abada, ta kuma bama Haysam dake matsayin Babban yaya ya koma Uba a yanzu. A haka ALLAH ya ɗauki rayuwarta hannayensu riƙe a hannunta. A wannan rasuwa A'isha ta sake tabbatar da lallai suna cikin halin shiga uku ita da waɗan nan yara har takwas, dan kuwa Yakura batai wata biyu da rasuwa ba Yayan gandu ya sake zuwama A'isha da batun auren da yay mata a wancan karon, da tace bata yarda ba yace to ta tattara yara ta bar masa gidansa, ya bata sati ɗaya kacal. Hankalinta ya tashi, ta kira Jamilu autan su Abdul-rasheed ta sanar masa komai dake faruwa, harna sharrin farko da Yayan gandu yay mata, shima hankalinsa ya tashi, dan basu taɓa sanin gaskiyar zancen ba sai yanzu, amma sai yace su koma gidansa dan babu yanda zai yi tunda yayansa ne. Dan haka suka shiga tattare kayansu, abinda zai zama kaya A'isha ta saida shi, sai kayan sakawarsu da abubuwa masu muhimmanci kawai suka koma gidan Jamilu da zama. Sai dai ko wata basu cikaba sabon kalubale ya ɓullo daga matar Jamilu, dan ƙiri-ƙiri ta nuna ita bata yarda da wannan zama ba. Taya tana amaryarya haihuwa ɗaya (dan zuwa yanzu itama ta haihu) ace azo a cika mata gida da ƴaƴa. Rikici ita da mijinta A'isha taga aurensu na neman mutuwa ta shiga tsakani da roƙon Jamilu ya barta ta wuce Kano. Zai tada hankalinsa ta lallaɓasa da nuna masa muhimmancin yin hakan. Badan yaso ba haka A'isha ta hau shiri, da taimakonsa da rakiyarsa A'isha da ƴaƴanta takwas tai bankwana da garin Bauchi ta koma garinta na haihuwa Kanon dabo....

Babu zato babu tsammani Inna ta wayi gari da baƙin Bauchi. Al'amarin ya girgiza mata zuciya, duk da kuwa kullum dama addu'arta ALLAH ya kawo ma A'isha mafita, dan tunda taje rasuwar Yakura ta sake tabbatar da Bauchi bazata zaunu ga ƴar tata ba. ALLAH sarki rayuwa, bayan shekaru goma sha shida A'isha ta dawo gidansu babu Abdul-rasheed a duniya. Tayi aure tana da shekara sha huɗu. Shekararsu goma sha huɗu da Abdul-rasheed, yanzu yana shekara biyu da wasu wattani da rasuwa. Haysam nada shekara goma sha uku da wasu watanni a duniya. Ja'afar da Ma'aruff nada shekara takwas, Bilal nada shida, Ummi nada biyar. Mommy nada huɗu da wata takwas, Ammar nada uku da wata huɗu, sai ƴar da Yakura ta haifa a ƙarshe da taci sunan A'isha suna kiranta MiMi nada ɗaya da rabi. A yanzu A'isha nada shekara talatin da ɗaya ne cif a duniya. Inna ma ba mai ƙarfi bace, dama Abdul-rasheed ne ke mata komai a yanzu, hatta da karatun su Bashir, dan tunda ya rasu suma su Bashir ɗin karatun ma ya nema taɓarɓarewa sai da Nasiru ya shiga ya fita ya samar musu wani taimako sannan. Ƴar sana'ar koko Inna keyi da safe yanzu, sai daddawa, da itace take ruƙe su ita da su Tasi'u da yake ba zama suke ba a gida koyaushe suna ma makaranta ne a Zaria, yanzu ga A'isha da iyalanta sun ƙaru. Lissafin ya canja ƙwarai da gaske. Ita kanta A'isha tunda ta shigo gidan take tattauna abubuwa a zuciyarta, da yanda rayuwa zata sake kasancewa. Amma dai tasan zama bashi yiyuwa, babban tashin hankalinta karatun yaran, duk rintsi bata fatan karatun yaran ya tsaya musamman Haysam dake jss 2 zai tafi jss 3 ne nan da ƴan watanni. Haka taita lissafi tun a daren da suka iso Kano ko rintsawa batayi ba. Washe gari karatun ya fara mata maimaicin kansa a cikin ƙwaƙwalwa. Ga Haysam tunda suka zo ya tsangwami kansa sai dai ka gansa zaune gefe shiru. Koda yake tunda Yakura ta rasu rashin maganarsa ta sake girmama fiye da bayan rasa mahaifinsu. Ya sake zama mara fara'a da yawan walwala.........✍🏼

_Rayuwa kenan, akowane motsi bawa baya rabo da jarabawa da sabbin ƙaddariri, ALLAH ya baki wuyan ɗauka A'isha🥲._

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 23_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________