
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 9
.....vern da ake yo masa aiken kayan abinci. I don't know anything about my family. Peace be upon you. Faten and I were in Qashy Lafiya Abd al-Rashid. Ya kratanko ya jamaar da kaki tarra su. Tu Dan Allah Dak Aghayda Min Da Kua. En pa zen tapa maka krato pa kiyi gokari a satin sama kazo gida kuna kuna bi yin sa ka kuma. Den ina son mi yi majanga, kaga kuma ni ba e ya zu kanun nen tako zen ba ina so they thanked us. Na Barka Lafia. Daga Mahavvenko. Sheikh Isa Kobi Buchi. Assalamu alaikum. What kind of fat can be with you Lafiya Abdul-Rasheed. Oh karatunka ya jama'ar da cake tare da su. Then ALLAH put it in the middle of the room. I don't know what to do when I don't know what to do. There is no money in this world, but there is nothing to do with it, but it does not happen in this way. We are blessed. Daga Mahaifinka. Shehu Isa Kobi Bauchi. Abdul-Rasheed na gama karanta wantn wasiƙa baiyi ƙasa a gwiwa ba sati na zagayowa yayima garinsa na Baushi tsinke tare da asusunsa daya jima yana tarin kuɗin ɗinki a ciki. Sosai kuwa Baba ya nuna jin d.....
Bayan wucewar baƙi dangin Abdul-rasheed iyayen A'isha ɓangaren dangin uwa dana uba suka baje kayan sa rana aka raba. Aka bama Inna nata da danginta, dangin mahaifinta suka ɗauki nasu. Sosai A'isha take a cikin farin ciki, sai dai wani ɓangare kuma jikinta duk yayi sanyi. Ko lokacin da ƙanwar Inna da suke kira Inna Haule tai kiranta akan ta faɗi suwa zata zaɓa matsayin ƙawaye da baranya akai musu kayan saka ranar kasa magana tayi, daga ƙarshe akace taje abinta ta sanar ma da Bashir ko Tasi'u su suzo su faɗa. Haka kuwa akayi, ta gayama Tasi'u ƙawayenta biyu da take son ɗauka matsayin babbar ƙawa Lantana da Jummai, sai baranya kuma, dan haka aka ƙulla kayan sa rana aka kai gidajen iyayensu kamar yanda ake ta rabo gidan sauran dangi da abokai da makwafta. A kwana a tashi ba wuya wajen UBANGIJI, kwanakin aurensa da A'isha nata gabatowa. Domin kuwa sai anyi bikinsu da watanni bakwai ma zai kammala karatunsa. Gabatowar abubuwa dole ya shirya yaje gida Bauchi. Dan ya samu saƙon wasiƙa daga drivern da ake yo masa aiken kayan abinci. Baba ne kuma ya rubuto ta da Ajami.
ٱلسَّلَامُ عَلَيْكُمْ
إِنَا فَاتَن كَانَا فِي قُشِي لَافِيَّا عَبْدُ الرَّشِيدْ. يَا كَرَاتُنْكُو يَا جَمَاعَار دَا كَكَيْ تَرَّة سُو. تَوْ دَنْ ٱللَّهْ دُكْ أَغَايْدَا مِنْ دَا كُوَا.
إِنْ بَا زَنْ تَابَا مَاكَا كَرَاتُو بَا كَيْي قُوكَارِي أَ سَاتِينْ سَمَا كَازُو غِيدَا كُونَا كْوَنَا بِي يَنْ سَا كَا كُوْمَا. دَنْ إِنَا سُون مُي يِ مَاجَنْغَا، كَاغَا كُوْمَا نِي بَا إِي يَا زُو كَانُونْ نَنْ تَاكُو زَنْ بَا إِنَا فَمَا دَا شِكَرُونَا.
نَا بَرْكَا لَافِيَّا. دَاغَا مَهَافِفِنْكُو. شَيْخُ إِيسَا كُوبِي بَوَتْشِي.
Assalamu alaikum.
Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya Abdul-rasheed. Ya karatunka ya jama'ar da kake tare da su. To dan ALLAH duk a gaida min da kowa. Idan ba zan taɓa maka karatu ba kayi ƙoƙari a satin sama kazo gida kona kwana biyu ne sai ka koma. Dan ina son muyi magana, kaga kuma ni ba iya zuwa Kanon nan taku zan ba ina fama da shekaruna.
Na barka lafiya. Daga Mahaifinka. Shehu Isa Kobi Bauchi.
Abdul-rasheed na gama karanta wannan wasiƙa baiyi ƙasa a gwiwa ba sati na zagayowa yayima garinsa na Baushi tsinke tare da asusunsa daya jima yana tarin kuɗin ɗinki a ciki. Sosai kuwa Baba ya nuna jin daɗinsa da zuwan nan. Dan a matse yake da son ganinsa. Bayan ya huta sun taɓa hira da Inna da ƙannensa ya fita gidajen yayunsa duk suka gaisa da matansu da su suma. Daga nan ya leƙa abokansa, sai bayan sallar isha'i ya dawo kasancewar yasan zuwa lokacin Baba ya shigo gida cin abinci. Hakan kuwa akayi, ya sameshi zaune a ƙofar ɗakinsa kan tabarmar karauni yana cin abincinsa a akushinsa. Sannu yay masa ya nema waje ya zauna, bai ƙara magana ba har sai da Baba ya kammala ya fuskanceshi dan kansa. Sun tattauna sosai akan batun bikinsa dake tunkarowa nan da wata ɗaya, sai batun gida da aka gina masa kamar sauran ƴan uwansa anan jikin gidansu, gini ne dai irin na wannan zamanin, wato ginin laka (ƙasa) kamar yanda aka sani ga talaka, an shafeshi da farar ƙasa ƴar aliya daga cikin ɗakunan, a waje an yarfa abin gwanin ƙyau. Abdul-rasheed yayi godiya sosai ga mahaifinsa harda hawaye, yay masa addu'ar tsahon rai da lafiya mai ɗorewa. Bayan ya lafa Baba ya ɗora masa da batun kayan lefe da dangin mahaifiyarsu suka kawo daga Maiduguri. Akwatin ƙarfe ne da irin na mutan da guda ɗaya ƙaton gaske, akwai kaya a ciki wato atamfofi irin na mutanen da sai takalma da kayan shafa kamar dai yanda ake haɗa lefe a wancan zamani. Baba ya sake da nuna masa kwalla guda biyu daga wajensa shima kuma kayan lefen ne dai a ciki, kamar yanda yayma sauran ƴan uwansa shima yayi masa tunda na dangin mahaifiyarsa daban nashi daban matsayin uba. Rasama tacewa Abdul-rasheed yayi sai hawaye kawai yake sharewa da godiya. Daga ƙarshe ya ɗakko asusun nan gaba ɗaya ya dire a gaban Baba. Baba ya ɗan zubama asusu ido sannan ya kalli Abdul-rasheed a nutse. “Wannan asusun fa Abdul-rasheed?”. “Baba kuɗaɗen da nake tarawa ne na ɗinki a ciki daman”. “Masha ALLAH, ALLAH yayi maka albarka, amma ai naka ne, miyyasa zaka kawo min nan?”. “Baba naka ne, kai amfani da shi domin rage nauyin abubuwa sun maka yawa. Nasan dai bazasuyi maka komai ba, amma dai za'a rage wani abu”. Murmushi Baba yayi a karo na farko, ya sake saka masa albarka sannan ya ɗauki asusun ya miƙa mishi. “Abdul-rasheed bazanƙi amsar ƙyauta daga hannunku ba. Domin hakan ba nufin jinƙai da neman albarka. Kuma hakan da kai min ya sakani jin daɗi ƙwarai da gaske. ALLAH yayi maka albarka da sauran ƴan uwanka duka. Amma kaje da asusun nan ka cigaba da tara abinda kake samu, bayan ka kammala karatunka ka dawo gida akwai abinda zamuyi da kuɗin ni da kai. Dan haka ka cigaba da ajiye min su a hannunka kaji”. Batare da Abdul-rasheed yay tunanin komai ba ya ce, “To Baba. In sha ALLAHU yanda kace haka za'ayi”. Daga haka suka cigaba da hira har lokacin barci..
>>>>>>>•<<<<<<<
Kwanakin Abdul-rasheed biyu ya dawo Kano makaranta, bai shiga anguwar su A'isha ba sai da sati ya zagayo kamar yanda ya saba. Sai dai suna tare da Nasiru a makaranta kullum. Shi ya bama tsaraba ma da ƙanwarsa ta bada a kawoma A'isha ya kai mata shi kuma sai ƙarshen sati ya shiga suka gaisa.. Rayuwa ta cigaba da tafiya bikin Abdul-rasheed da A'isha nata ƙara matsowa, ana shirye-shirye shi kuma hankalinsa nakan jarabawar da suka fara, wadda bai kammalata ba kuwa sai ana saura kwana huɗu ɗaurin aure. Zuwa lokacin gidan su A'isha ya gama cika da danginsu na nesa, har ma am sakata a lalle a safiyar yau ko muce da hantsi, wato an saka mata turare irin na al'ada matsayin kamu. Wannan yasa shima Abdul-rasheed bai ganta ba, dan a wannan zamani idan aka saka amarya a lalle keda ango kuma sai a ɗakin aurenku. Sam Abdul-rasheed bai so haka ba, dan tunda ya fara jarabawar nan basa wani samun zama da A'isha, zai iya cewa rabonsa da ita ma tun mako uku da suka wuce randa sukai hira harda Nasiru suka bata kuɗin ƙarshen zance da ake bama budurwa sule na gugar sule har sule biyar cif. To gashi kuma yau da yake son ganinta bamai yiwuwa bane, dole ya haƙura ya kama hanyar Bauchi tare da Nasiru ɗan amanarsa. Sai ana gobe ɗaurin aure zasu dawo Kano su sake komawa tare da amarya. Koda su Abdul-rasheed suka isa Bauchi a can ma sai ya tadda gidansu taf da dangin mahaifiyarsa dana Baba, kai har ma da dangin Inna duk da ta kasance kishiyar uwa. Tuni an baje buhu-buhu na masara dana gero anata faman daka domin samar da garin tuwo harma dana MASA ƳAR BAUCHI, sai fura dama sauran nau'in abinci irin na wannan ƙarni da su shinkafa. Sun sami tarba ta farin ciki, inda abokan wasa dake dakon isowar ango dama suka lulluɓeshi aka fara zazzage masa kwalaben turare masu ƙamshi irin su ɗan duwala ana guɗa, hakan kuwa na nufin shima an saka shi a lalle kamar amarya.
*_KANO_*
A nan Kano ma dai ɓangaren amarya bari muɗan dawo baya kaɗan miji a yanda aka sakata a lalle da yanda suke shagalinsu da ƙawayenta. Zamuce amarya da ƙawayenta sun fara shagali tun a ranar data kasance saura kwanaki bakwai ɗaurin aure. Amma an sakata a lalle ana saura kwana uku. Ranar litinin Inna Zainabu ta bata umarnin tsefe kanta kamar yanda yake a al'ada, da taimakon ƙawarta Jummala ta samu ta tsefe shi. Daga haka suka cigaba da sabgarsu. Washe garin ranar laraba da mutanen Bauchi suka iso da lefen A'ishatu a washe garin randa su Abdul-rasheed suka tafi kenan, akwatin ƙarfe da kwalla biyu sai tabarmi karauni guda huɗu. Gidan ya cika sosai da maƙwafta, bayan an cika baƙi da shatara ta arziƙi na abinci, anyi gaisuwa irin ta mutunta juna, dama gidan su Nasiru suka sauka, dan haka suna kammala bada lefe suka koma can abinsu, kasancewar nisa dama su huɗu ne kawai suka kawo kayan, zasu zauna kuma har a ɗaura aure sannan. Masha ALLAHU kaya sai sambarka. Dan kuwa dai amarya tayi goshi. Atamfofi ne nagartattu irinsu mai tabarma, mai barewa, akwai oni-ƴasu, sai joji da ƴalle gwaggwaro, sai t-shirt masu ƙyau, sai sufa gwaldin, sufa shadda, akori-kura, kai kaya dai sai sambarka. Kayan kwalliya da sabulai suma dai tsaf, sai turaren alwalar uwar ɗiya ƙatuwar kwalba sosai, sai ƴarduwala, miski da sauran irin yan feshi. Sai kuma gyale da su takalma kaya dai rigijib-jib komai ka taɓa akwai irin na wannan zamanin..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 10_
__________________
*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana 💃 fulanin asali ke nan 😘._*
*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*
_Maza kuzo ku sha labari da ɗumi-ɗuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buɗe muku gidan gyara da ƙalƙale jikin mata ƴan kwalisa a kusa da ku gabb._
*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na👇_*
*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*
_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_
*_Zaku same mu a wannan numbers ɗin kamar haka👇_* *07068210505* *09133081313*
_DEALER IN all kind of skin care products such as:_
moisturizer Sun screen Face Toner Eye cream Face serum Face wash Face scrub Face cream Face marsk Body lotion Body cream Shower gel Body scrub Tube Body oil Body spray Perfume Hair crm Hair spray and many more
*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne 💃_*
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________