
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 8
..... he was crying because he saw that he liked Nasiru. When the house was full of people and relatives, Abdul-rasheed found himself wiping away tears, seeing that their mother's family was full of people but she was not in this world. His mother's origin is from Maiduguri, so her family all came from there, even his younger sister who was going to get married there will be married off. After tying the knot, the men began to prepare to pass, but the next day the women would go with the bride as well. Abdul-rasheed is among them and is grateful for their efforts even though tomorrow he will be his sister Rakkia Maiduguri. An old man who they call Baba Kalla looked at Abdul-Rasheed and said, "Why don't you come among us and take a wife. That will keep our attention on you and we are lost if we are busy doing something without you. At least the devil is not a lamb, now that your mother is not alive, you see we are busy neglecting your affairs, not even the same hair. But look if you get married. Among us, like how Gana also married Khadijah, there is always no question of forgetting each other.
......... Abdul-rasheed ya cigaba da karatunsa, yana kuma koyon ɗinki da zuwa yanzu ma zamu ce ya iya tunda yana yi ya samu taronsa da kwabo, yana iya ɗinka kowane ɗinki da hannu da kuma yi da keken ɗinki, tsakaninsa da A'isha kuwa sai Alhamdullah, dan zuwa yanzu mutane da yawa a layin sun san alaƙar tasu. Har ma takai ana kiransa da suna Abdul-rasheed ɗin A'isha, dan ko baka ganesa ba da ance maka haka kuwa zaka gane shi ake nufi. Sun sake samun hutu yay shirin zuwa gida Bauchi, zuwan daya samu rakkiyar Nasiru abokinsa, shima zaije yaga tushen Abdul-rasheed a wannan karon yay sati guda sai ya dawo. Hutun nashi kuwa ya haɗa da bikin ƴan uwansa mata biyu da suke uba ɗaya da za'ayi, da ƙanwarsa ɗaya da suke ɗaki ɗaya, sai ɗaya namiji da suke uba ɗaya shima. Hakanne ma yasa Nasirun zai bishi. Nasiru ya samu tarba ta mutuntawa a wajen mahaifin Abdul-rasheed dama ƙannensa, dan sun san sunanshi a bakin Abdul-rasheed. Kai hatta da abokan Abdul-rasheed tunna ƙuruciya dake anguwar kowa iya ƙoƙarin sa yake na ganin ya ƙyautatama Nasiru. Yanda gidan ya cika da mutane da dangi sai Abdul-rasheed ya samu kanshi da share hawaye, ga dai dangin mahaifiyarsu cike taf da gida amma ita babu ita a wannan duniyar. Asalin mahaifiyarsa ƴar Maiduguri ce, dan haka danginta duk daga can suka zo, ƙanwar tasa ma da zatai aure can za'a kaita auren zuminci ne. Bayan ɗaura aurarrakin maza suka fara shirin wucewa, dan sai zuwa gobe matan zasu tafi da amarya itama. Abdul-rasheed yana cikinsu yana godiya akan ƙoƙarin su duk da shima goben da shi za'aima ƙanwarsa rakkiya Maidugurin. Cike da kulawa wani dattijo da suke kira Baba Kalla ya dubi Abdul-rasheed ɗin tare da faɗin, “Kaima kuwa kaga da zaka zo cikinmu ai sai ka ɗauki mata. Hakan zai ƙara dawwamar da hankalinmu a kanku muma batare da mun shagaltu akan yin wani abu babu ku ba. Kasan dai shaiɗan ba rago bane, yanzu yanda babu mahaifiyar nan taku a raye sai gaka muna shagaltuwa da yin sakaci akan lamarinku, balle ma gashi ba gari ɗaya ba. Amma kaga idan ka aura a cikinmu, kamar yanda shima Gana ya auri Khadijah ai kaga koda yaushe babu batun manta juna. Dan lokacin rasuwar mahaifiyarku shima kamar wasa mukai irin wannan zaman da shi ikon ALLAH ashe ma suna tare da ita tuni. Bazamu so ku zauna a ware a cikinmu ba dan mahaifiyarku sanda tana raye mai ƙoƙarin bibiyar al'amarin dangi ce da don ƙyautata musu a kowane motsinta.” Karaf wani a ciki yace, “Ai Baba bama sai an kaita da nisa ba, dan da zasu dai-daita da Yakura ni dai al'amarin su na min kamanni, itama yarinya ce mai sanyin hali da nutsuwa kamar shi. Gashi tana kama da mahaifiyarsu kamar ita ta haife ta. Abdul-rasheed ka fara gwadawa ka gani akan Yakura duk da nasan itama dai bazata ƙika ba.” Tunfa da aka fara maganar nan gaban Abdul-rasheed sai faman faɗuwa yake da dukan uku-uku, dan haka yay shiru na tsawon lokaci har sai da mahaifinsa dake wajen yana lure da yanayinsa ya kira yi sunansa. Ɗan firgigit ya kallesa, sai kuma ya amsa kiran da yay masan. Baba ya zuba masa ido na sakanni, kafin ya furta, “Bakaji abinda ake gaya maka bane?”. Ajiyar zuciya mai nauyi Abdul-rasheed ya sauke, kafin ya ce, “Baba duk naji”. “Shine kuma kai shiru Abdul-rasheed. Sufa shawara suka baka bawai sunce dole bane. Kuma tun a ɗazun nima suka sameni da batun amma nace su maimaita a gabanka saboda gudun halin ɗan yau dana sani”. “Kayi haƙuri Baba, ni mai karɓa ne ga dukkanin umarnin ku. Kawai dama......” Yayi shiru ya kasa ci-gaba. “Dama mi? Kayi magana mana. Dare keyi su suna son su ɗauki hanya ne ka sani”. Yawu Abdul-rasheed ya sake haɗiyewa, ya muskuta zamansa kansa a ƙasa. “Baba dama akwai zancen wata yarinya ne da muka haɗu acan Kano kusan shekara ɗaya da rabi kenan, tun wancan zuwan naso samunka da batun sai rasuwar Inna ta gitta. Amma zan haƙura da batunta ɗin kawai. Sai dai damuwata ta yanda zan ma iyayenta bayani ne bayan su kuma sun riga sun bani yarda da aminci. Ban fara neman ta ba kuma sai da naje garesu suka amince min. Wannan ne kawai damuwata amma ba ƙin karɓar umarnin ku ba”. Sosai zauren yay shiru. Baba ya zubama Abdul-rasheed ido kawai kamar mai nazari. Baba Kalla ne ya katse shirun da faɗin, “Tabbas maganarka abar a kalleta ne Abdul-rasheed, kuma bazamu saka ka zama ƙaramin mutum ba tunda har magana ta gitta haka. Zamu baka goyon baya kuma idan har ta kasance irin yarinyar da muke maka fata. ALLAH yasa haka shi yafi alkairi.” Gaba ɗaya aka amsa da amin. Daga haka kuwa babu wanda ya sake motsa wannan zance har akai biki aka tashi lafiya. Koda yaje Maiduguri shi da Nasiru ma babu wanda yay masa maganar. Yaga kuma Yakura da akai masa magana a kanta. Itama dai yarinya ce ƙarama kamar Ai'sha, ko muce ma A'isha ta girmeta dan ita bazata ma wuce 12 ba da wasu watanni. Kwanansu biyu suka dawo, Nasiru ya koma Kano da shatara ta arziƙi daga dangin Abdul-rasheed, sai wasiƙa daya bashi ya kaima A'isha da kayan biki aba Inna da Gwaggon su Nasiru da Babansu da Yaya Zubairu suma. Abdul-rasheed ya cigaba da shan hutunsa daya rage harna sati biyu kafin ya fara shirin komawa Kano. Ana gobe zai wuce bayan sallar isha'i baba yasa aka kirashi. Dama dai yana da shirin zuwa wajensa, yana jira ne ya gama cin abinci, sai kuma ga kiranshi. Daga tsugunne ya gaishe da Baba, ya amsa masa yana masa nunin ya zauna. Inda ya nuna masan ya zauna. “Gobe ne tafiya ko?”. “Eh Baba in sha ALLAHU”. “To ALLAH ya taimaka, ya kuma bada sa'a, sai a ƙara dagewa da karatu, bani da haufi akan ka Abdul-rasheed, sannan na yarda da tarbiyyar dana baku ku dukanku. A kowane motsina kuma ina bin ku da addu'a ne musamman kai dake nesa da ni a yanzu. Dan duk sauran ƴan uwanka ina tare da su idan ka cire Hadiza da aure ya ɗauke min yanzu itama. Nasa an min bincike akan batun yarinyar dakai magana....” Karo na farko Abdul-rasheed ya ɗago a firgice yana kallon Baba. Cike da rawar murya yace, “Baba A'isha!?”. Murmushi Baba yayi kaɗan shima yana kallonsa, sai Abdul-rasheed yay saurin yin ƙasa da kansa. “Kwarai kuwa A'ishatu Abdul-rasheed, dan na fahimci kana sonta sosai. Shiyyasa banyi ƙasa a gwiwa ba na tada ɗan aike takanas yayo min bincike. Kuma Alhamdullah dukkan abinda ka faɗa min shi aka dawo aka sanar min babu ƙarya a ciki. Harma da wanda baka sani ba game da halayyar mahaifinta da mahaifiyarta da ita kanta. Abdul-rasheed na amince ka auri A'isha. ALLAH ya sanya albarka a cikin tarayyarku. Idan kaje sai ka sanar musu nan da sabon wata idan yayi kwana biyu iyayenka zasuzo garesu. Babanka Kalla zaizo su haɗu da iyayenku na nan su Nuhu sai suje, tunda karatunka saura shekara ɗaya kaga sai a tsaida magana kawai su tabbatar da gaske muke ko”. Sosai wani irin farin ciki mai girma ya baibaiye rayuwa da zuciyar Abdul-rasheed, sai dai kunya ta hanashi bayyanawa, murmushi dai yake ta faman yi haƙoransa a buɗe. A zuciyarsa kuwa ji yake kamar ya tashi yayta rawa dan daɗi. Baba ne ya katse masa murmushin da faɗin, “Sai dai ina da wata shawara a gareka guda ɗaya”. Cikin nutsuwarsa ya koma sosai. Ya ce, “To Baba”. “A kan maganar da su Babanku Kalla sukayi ranar auren ƴan uwanka. Mizai hana ka auri itama tasun ka haɗa biyu tunda namiji na mata huɗu ne. Koba komai ka sake samun kusanci da ƴan uwan mahaifiyarku, ka kuma samu abinda kake so. Yarinyar da suke faɗa yarinya ce nutsatstsiya sosai, dan kasan da ita akai jiyyar mahaifiyarku gaba ɗaya da uwarta. Nidai a ɗan zaman da tayi na kusan watanni biyar damu banga wani abin ashsha a tare da ita ba sam. Ga yarinyar kasan itama mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama, inda uwar ke aure yanzu sam mijin bashi da halin kwarai, nuna mata yake kullum ya gaji da yarinyar bayan kuma kafin ya aureta yay alƙawarin riƙeta shiyyasa ma su Kallan suka barta taje da ita. Kaga idan akai hakan itama an taimaketa ai ko? Amma shawara ce dai kamar yanda na faɗa maka ba tilastawa ko umarni ba. Dan ko ƴaƴana mata bazan ma auren dole ba balle ku maza. Kaje kayi tunani ka yanke hukunci da kanka. Duk kuma wanda ka zaɓa ni mai goya maka bayane a ciki”. Daga haka Baba yay masa doguwar addu'a tare da ɗaukar kuɗi ya bashi. Amma sai yaƙi amsa, ya sanar masa yanzu ɗinkin da yake yi na kawo masa kuɗin amfani harma dana asusu da yake yi. Ko gudunmawar daya bama ƴan uwansa ta aure duk da kuɗin ɗinkin ne. Baba ya ƙara jin daɗi sosai, ya ƙara saka masa albarka. Ya bashi kuɗin kuma yace yaje dai dasu, dan wannan hakkine a kansa. Dole badan Abdul-rasheed yaso ba ya amsa yay godiya tare da addu'a sosai shima. Washe gari ya ɗauki kuma hanyar Kanon dabo, mai mata mai mota, mai dala da gwauron ɗutse, garin da ba Kano ba dajin ALLAH, hankaka maida ɗan wani naka, duk wanda ya shigo ƙasar kanon mu ya zama namu, jalla babbar Hausa yaro ko dami kazo an fika.
★Alhamdullahi Abdul-rasheed dai ya dawo Kano, ya kuma isar da saƙon Baba ga mahaifin su Nasiru, shi kuma ya samu Inna da kawun A'isha da maganar. Sunyi farin ciki sosai dan har zuci suke son Abdul-rasheed. Kamar yanda kuma baba yasa akai masa bincike akansu suma batare da sun sani ba sun aika har garin Bauchi an yi musu bincike akan Abdul-rasheed da ahalinsa. Kuma Alhamdullahi suma basu sami wani abin ashsha ko aibu ba sai nagarta. Ba iyayen A'isha kawai ba, hatta itama A'isha tayi farin ciki sosai, dan tunda ya gaya mata take ta faman murmushi tana ɓoye fuska..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 9_
__________________
*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*
*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*
*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*
*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*
_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Ahalin Abdul-rasheed sun cika alƙawari, dan kuwa a karo na farko suka iso garin Kano biyu ga sabon wata kamar yanda suka faɗa. Abdul-rasheed da kansa yaje tasha ya taho dasu. Ya fara kaisu makarantar su sannan suka nufo Ƙofar mata anguwar su Nasiru. A gidan su Nasirun suka fara yada zango. Bayan anyi gaisuwa da godiya bisa ga ɗawainiyar ahalin Nasiru. Suma sunyi godiya da hidimar da akai da Nasiru da yaje. Daga haka sukaci suka sha sannan mahaifin Nasiru ya shiga cikinsu aka wuce gidan kawun A'isha. Acan akai komai cike da mutunta juna da karamci. Abinka da mutanen da, ba alfahari babu fariyya babu ƙyale-ƙyale mara amfani, an bada kuɗin da hatsi har buhu uku na nagani ina so dana gaisuwar iyaye, a take akai baiko. Da za'a rabu an rabu cike da dattako da godiya ma juna. Nasiru da Abdul-rasheed suka rakasu tasha suka wuce. Dan sunce bazasu kwana a Kano ba. Abinka kuma da duniya na kwance ba'a tsoron komai.. Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI. Karatun Abdul-rasheed nata miƙawa, an kuma sake kawo kuɗi na biyu gidan su A'isha, tare da kayan sa rana. Huhun goro, farar alewa, sai cakuleti, sai cingam bazuka, sai alewa daima. Sai kuma tabarma karauni guda biyar, sai katifa da botikin ƙarfe da butar ƙarfe, sai zanin gado da barguna guda huɗu rigis abinsu. Kayan sarana dai sambarka dan duk wanda ya gani yasan dangin Abdul-rasheed sunyi ƙoƙari. Dan haka aka saka ranar aure watanni huɗu.
____________