
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 7
.....if she is going to pass, likewise when she comes back, she greets them and enters the house. He never asked her name and never spoke to her after the greeting she gave them together. He only sleeps and wakes up until he memorizes her voice, which is full of calmness and no noise. On one Sunday afternoon, he was at the shop alone, sewing for his wife, Yaya Zubair went to buy sewing clothes when the girl's voice reached his ears. He quickly picked up his bike and stopped from his pace. She was standing outside the shop and greeted him on the ground. He answered her carefully, before he said, "Do you want something, my sister?". With her head down she said, "Yes, Yaya, I brought your clothes for Yaya Zubairu, but I see he is not here either". Jokingly, he said, "Oh son, Yaya Zubairu is not here, did you break the seam?". She quickly said, "No, I won't let you save the opportunity for him". He smiled for the first time and said, "Well, he is here". Yay, the word is coming to the door of her son, she is still standing outside. Handing him the letter, she put herself on the ground. For the first time in his life he stared at her hand. She started, her hands covered in red lace that
........Haka kuwa akayi, kamar wasa Abdul-rasheed ya fara zuwa koyon ɗinki, kasancewar yana son abun dan danan sai ga sakamako ya fara bayyana. Baya gajiya duk asabar da Lahadi sai yazo. Da Nasiru yaga yana wahala da kashe kuɗaɗensa ga ɗan makaranta komai nasa a ƙa'ide yake, ga nisa Abdul-rasheed yana jimawa baije gida Bauchi ba sai yace mizai hana duk juma'a ya dinga biyoshi sai Monday su dinga shiga makaranta tare, ya dinga weekend dai a gidansu. Da farko Abdul-rasheed yaso turjewa, sai da Nasiru ya nuna masa fushinsa sannan ya amince amma yana ɗar-ɗar dai, duk da kuwa kowa ya sanshi a gidan su Nasiru zuwa yanzu, kuma suna nuna masa so da kulawa. Amma shi dai baya son takura musu, yana kuma tsoron kar mahaifinsa yay faɗan barinsa makaranta harna kwana uku a kowane mako batare da saninsu ba. Tun dai yana ɗari-ɗari har ya saki jikinsa. Tun a farko fara koyon ɗinkin Abdul-rasheed akwai wata yarinya a maƙwaftan su Nasiru da kullum takan wuce da safe da allo zata makaranta. Takan gaishesu idan zata wuce, hakama idan ta dawo da takan gaishesu ta shige gida. Shi dai bai taɓa tambayar sunanta ba, bai kuma taɓa magana da ita ba bayan gaisuwar nan da take musu a tare. Sai dai a kwana a tashi har ya haddace muryarta mai cike da nutsuwa da rashin hayaniya. Ranar wata Lahadi da yamma yana a shagon shi kaɗai yana ɗinki ogansa Yaya Zubair yaje sayen kayan ɗinki zazzaƙar muryar yarinyar nan ta ratsa kunnensa. Ɗagowa yay da sauri tare da take keke ya tsayar daga takun da yake masa. Tana tsaye daga wajen shagon ta rissina ta gaisheshi kanta a ƙasa. Amsa mata yay da kulawa, kafin ya furta, “Kina son wani abu ne ƙanwata?”. Kanta a ƙasa ta ce, “Eh Yaya, dama kayan ɗinki na kawo ma Yaya Zubairu, naga kuma baya nan ma kamar”. Cike da zolaya ya ce, “Oh dan Yaya Zubairu baya nan kin fasa ɗinkin?”. Da sauri ta ce, “A'a zan baka ka ajiye masa daman”. Murmushi yayi a karo na farko, ya ce, “To shike nan”. Yay maganar yana tasowa yazo bakin ƙofar dan ita tana daga waje har yanzu. Miƙa masa ledar tayi kanta a ƙasa. Karo na farko a rayuwarsa ya zubama hannunta ido. Fara ce sol, hannunta da ƙunshin jan lalli da yay mata shegen ƙyau. Harga ALLAH sai da gabansa ya faɗi, mazantakar ta motsa amma sai ya kauda kansa kawai ya amsa yana ɗan murmushi da duba kayan ledar. Yadi ne irin nasu na maza. Ɗagowa yay ya sake ɗan kallonta. “A ajiye kawai kenan zaki dawo ki masa bayani?”. “A'a basai na dawo ba. Ɗinkin Bashir da Tasi'u ne daman. Inna tace dan ALLAH idan bata takura masa ba zuwa jibi a ɗinka. Dan zamuyi tafiya ne biki”. “In sha ALLAHU za'a ɗinka, nima zan ɗinka musu da kaina. Idan kin shiga ki turo min su yanzu naga girmansu a daren nan zan yishi dan da safe zan wuce makaranta”. Godiya tai masa cike da girmamawa, sannan ya wuce kanta a ƙasa. Samun kansa yay da binta da kallo. Doguwa ce sosai masha ALLAH, shekarunta bazasu wuce 14 ba, tana da ɗan jiki, hakan ya nuna ne kuwa sakamakon kayan dake jikinta, zani da riga t-shirt sai kallabi disko, Tayi ɗammara da gyale a ƙugunta, kasa ɗauke idonsa yay harta shige gidansu, a mamakinsa ya ɗan juya zai koma yana sauke ajiyar zuciyar da tazo masa a bazata kamar ance sake waigawa sai ya ganta tana leƙensa. Wuff ta shige kamar walƙiya kuwa, tana turo ƙyauren zauren gidansu na katako burum. Ɗan tsai yay yana kallon ƙofar kamar mai tunani, sai kuma yay murmushi ya juya ya koma cikin shagon. Yana zama su Tasi'u ƙannenta sukai sallama. Yara ne matasa da bazasu wuce 9/7years ba. Sun gaishesa da girmamawa, ya amsa musu da kulawa yana musu murmushi. Dan sun sanshi ya sansu tunda yanzu ya zama ɗan anguwar duk da kwana 3 kawai yake a duk sati. Amma sauƙin kansa da son kula yara yasa duk suka sanshi. A karo na farko a rayuwarsa ya tambaye su miye sunan yayarsu?. Caraf Bashir dake matsayin ƙarami ya ce, “Indo”. Samun kansa yay da faɗin, “Masha ALLAH A'ishatu kenan. Wace makarantar kuke zuwa?”. Yanzu kam Tasi'u ne ya ce, “Muna zuwa makarantar Malam Sallau. Yaya Indo nada ƙoƙari sosai, dan duk wata tana wanke allon ta sau biyu, yanzu haka tana izu kusan ashirin. “Kai kai kuce dai yayarku Malama ce kawai?”. Wannan kalma ta saka Bashir da Tasi'u tsuge masa da surutu akan yayarsu Indo. Abu kamar wasa hirar yaran ta dinga masa tasiri a zuciya, yana tare da su har akai kiran magriba, shi ya jasu suka je massalaci. An idar da salla sun dawo sai ga Indo tana nemansu. Karo na farko da Abdul-rasheed ya samu kansa da yima Indo kallon ƙurulla sosai. Ƙyaƙyƙyawar yarinya mai cikar zatin fuska da hasken fata. Suna haɗa ido tai saurin juyawa zata shige gida. Amma sai ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. “A'ishah!”. Cak ta tsaya amma ta kasa juyowa, dan haka ya ƙarasa inda take riƙe da hannun su Bashir. Sai da ya ɗan ƙara kallon fuskarta sannan ya furta, “Amin afuwa nine na riƙesu a shago suna tayani taɗi, Inna ma ki bata haƙuri”. Batare data ɗago ba ta jinjina masa kai tana kama hannunsu suka shige. Yanzu ma sai ta juyo da tunanin yabar wajan zata saci kallonsa suka haɗa ido. Da sauri ta shige. Murmushi yayi yana girgiza kansa ya koma shago yana yaba halittar UBANGIJI a ransa, dan tabbas A'isha kyakkyawar yarinya ce kam. Kyawunta a bayyane yake ga mai kallonta kuma.
★Tun daga wannan rana al'amarin Indo ya fara saƙar zare a zuciyar Abdul-rasheed, har takai Nasiru ya fara harbo jirginsa. Haka ma Yaya Zubairu ya fara fahimta halin da Abdul-rasheed yake ciki akan Indo da yanda itama in zata wuce yanzu takan saci kallon cikin shagon bakamar da da zata wuce kanta a ƙasa ba koda zata gaishesu. Ƙannent kuwa koda yaushe suna manne da Abdul-rasheed, tun mahaifiyarsu na jin sunansa a labarinsu ko idan ya saya musu abu irin na yara sun kai gida har dai ranar ta nema sanin wanene shi, dan bai kamata ta saki jiki da wannan shaƙuwa dake tsakaninsa da yaranta ba batare da tasan wanene shi da halayyarsa ba. Yaranta marayu ne mahaifinsu ya rasu shekara biyu data wuce. Kasancewar sun gaya mata a shagon Yaya Zubairu yake yasa ta nema Zubairu kai tsaye, aiko yay mata bayani na gamsuwa har ma ya ɗora da batun Indo daya shin-shino. Inna mace ce ba mai damuwa ba, sai kawai tai fatan alkairi cikin al'amarin. Nasiru da Yaya Zubairu sune suka fito fili suka fara kwaɗaitawa Abdul-rasheed batun karfa yayi sake akan Indo in dai sonta yake da gaske, idan ko ya tsaya kallon ruwa lallai kwaɗo zai iya masa ƙafa. Tun yana dojewa har shima dai ya fahimci gaskiya suke faɗa masa, dan haka ya fito fili ya nema shawarar Nasiru akan ta ina ya kamata ya fara ne?. Tsaf Nasiru ya tsara masa komai kuwa. Dan haka a cikin satin suka je ga Inna domin basu damar fara zuwa hira. Sosai Inna tayi farin ciki da hakan, domin ta fahimci wasu ƙyawawan halayya daga Abdul-rasheed ɗin a sanin data fara masa na watanni, taji kuma hankalinta ya kwanta da shi akan ƴarta Hadiza. Sannan yanda Abdul-rasheed ya gaya mata komai daya shafesa babu wani ɓoye-ɓoye nan ma taji daɗi. Ta tabbatar musu ita dai uwa ce, kuma taji ta gamsu da shi, amma suje ga ƙanin mahaifin su Indo matsayinsa na namiji shima. Suma sun gamsu da shawarar tata, sunyi godiya sosai kuma. A wajen ƙanin mahaifin Indo ma dai bata canja zani ba, dan shima dai a anguwar yake basu ma da nisa da su, yasan Abdul-rasheed ɗin fiye ma da sanin da Inna tai masa matsayinta na mace. Bai wani jasu da nisa ba shima ya basu damar da suke buƙata tare da addu'a da fatan alkairi. Wannan shine sanadin fara tarayyar A'isha da Abdul-rasheed. Duk da tarayya ce mai tsafta da mutunta juna cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa ta shiga tsakaninsu. Yana zuwa hira wajenta duk ranar juma'a da yamma idan ya shigo anguwar, dan kuwa ranar take da lokacin hutun makaranta. A cikin soron gidansu suke zama kuma. Wani lokacin da Nasiru, wani lokacin shi kaɗai, ita kuma tana tare da rakkiyar ƙaninta Bashir. Dan haka hirar take kasancewa mai tsafta sosai a ciki da nagarta, wani lokacin ma ɓigewa suke da ƙarin karatun islamiyya. Dan tunda ta fahimci yana da sani sosai akan ilimin addini duk wani tambaya ko neman sani takan rubuta da ajami ta bashi ko tayi da baki. A haka Abdul-rasheed yaje gida wani hutu, tafiyar da yaje ya yi ta ya dawo zuciya babu daɗi dan kuwa ALLAH yay ma mahaifiyarsu Iya rasuwa. Yaje ya sameta cikin jiyya ashe ta daɗe a hakan batare daya sani ba, kwanansa huɗu a daren juma'a ALLAH ya amshi abarsa. Yayi kuka sosai dan yana son mahaifiyarsu matuƙa, mace ce mai abubuwan mamaki sosai, sannan mahaifiya ce abar alfaharin kowane ɗa na kwarai. Tana da sati uku da rasuwa hutunsu ya ƙare, haka ya tattaro ya dawo zuciya babu daɗi, sai dai nasihar mahaifinsu ta ɗan ƙarfafa shi. Amma ransa fal yake da tausayin ƙannensa uku daya tsallako ya baro. Duk da A'isha bata san mahaifiyarsa ba daya gaya mata tasha kuka, ta mata addu'a kuma sosai hakama duk wani wanda suke huɗɗa ta arziƙi ya masa gaisuwa da ban haƙuri. Yaso a zuwan da yay gida hutu yayma iyayensa batun A'isha da alaƙarsu da damar daya samu daga iyayenta, sai dai kuma ALLAH bai ƙaddara ba rasuwa ta gitta, dan haka ya haƙura har sai nan gaba kuma idan ALLAH ya bashi ikon komawa wani hutun...........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 8_
__________________
*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana 💃 fulanin asali ke nan 😘._*
*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*
_Maza kuzo ku sha labari da ɗumi-ɗuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buɗe muku gidan gyara da ƙalƙale jikin mata ƴan kwalisa a kusa da ku gabb._
*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na👇_*
*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*
_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_
*_Zaku same mu a wannan numbers ɗin kamar haka👇_* *07068210505* *09133081313*
_DEALER IN all kind of skin care products such as:_
moisturizer Sun screen Face Toner Eye cream Face serum Face wash Face scrub Face cream Face marsk Body lotion Body cream Shower gel Body scrub Tube Body oil Body spray Perfume Hair crm Hair spray and many more
*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne 💃_*
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________