Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 6

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 6

....for that, he stumbled upon him. Malam Shehu responded with excitement. The thing impressed the king at that time, because there was nothing more disgusting to the poor people than the issue of the priest at this time. Because everyone is afraid of losing their family tradition and religion. Malam Shehu was excited and went home, gathered his children and his two wives and told them his decision and the good news that the King gave him. He also assured them that he will take all three of his older children to school. In other words, those are the children of Inna, the lady. But then the children started crying and they were not interested in that. Also, their mother Inna showed that she didn't want it, she cried for him and she didn't want her children to learn disbelief, persuasion of the world and explanation of satisfaction of Malam Shehu to Inna but she didn't listen to him without understanding him. He was so sad that he went out and left the house for them. Abdul-Rasheed is among the middle children, the third son in their father's family, and the first born in their family. He has three younger brothers, two women in the middle and the youngest. Malam Shehu's displeasure

Standalone post2,108 words

TUSHIYA MAFARIN DAWA >>>>>1940s<<<<<

Abdul-rasheed Shehu Isa ɗan asalin jihar Bauchi ne, an haifesa cikin anguwar Kobi. Mahaifinsu malam Shehu baban hadimi ne a masarautar Bauchi ƙarƙashin mulkin Sarkin Bauchi Alhaji Yakubun Bauchi. Amintaccen hadimi ne kwarai da gaske, dan yana kusa da sarki saboda mutum ne mai aminci da gaskiya da amana. Gashi dai talaka amma akwai dattako da dattijantaka irin ta mutanen kirki. Matan Malam Shehu biyu ne, yaransa kuwa tara cif. Matarsa ta farko nada yara biyar, uku maza biyu mata. Yaran na kiranta da suna Inna. Matarsa ta biyu nada yara huɗu, biyu mata, biyu maza. Yara na kiranta da Iya. Malam Shehu nada sha'awar yaransa maza suyi karatun boko, sai dai kasancewar sa talaka da yanda tsarin karatu yake a lokacin sai ƴaƴan sarakuna yasa bai fidda burin nasa a fili ba. Amma kullum yaga ƴaƴan sarki zasu makaranta sai ya tsaya yayta kallonsu yana murmushi abinsa da jera musu addu'ar nasara. Yau da gobe sai mai-martaba ya fahimci kamar Malam Shehu nada sha'awar hakan, dan haka ya tuntuɓesa. Babu ko musu Malam Shehu ya amsa da zumuɗinsa. Abun ya burge sarki a lokacin, domin kuwa da yawan talakawa babu abinda sukafi ƙyama kamar batun bokon a wannan lokaci. Saboda kowa na tsoron a ɓata masa al'adar iyalinsa da addininsa. Cike da zumuɗi Malam Shehu ya nufi gida, ya tara yaransa da matansa biyu ya gaya musu ƙudirinsa da albishir ɗin da Sarki ya masa. Ya kuma tabbatar musu zai kai yaransa manya duka uku a sakasu boko. Wato ƴaƴan Inna kenan uwargida. Amma sai su yaran suka saka masa kuka dan basu da sha'awar hakan. Hakama mahaifiyarsu Inna ta nuna bata so, dan kuka ta saka masa ita bata so akai mata ƴaƴa su koyi kafirci, lallashin duniya da bayanin gamsuwa Malam Shehu yama Inna amma taƙi saurarensa bare ta fahimceshi. Har takai ransa ya ɓaci ma ya fita ya bar musu gidan. Abdul-rasheed yana cikin yaran tsakkiya, dan a wajen mahaifinsu shine na uku, a ɗakinsu kuwa shine na fari da Iya ta haifa. Yana da ƙanne uku, mata biyu a tsakkiya sai autansu. Ɓacin ran da Malam Shehu ya nuna ya dami Iya, duk da kuwa bai ambaci Abdul-rasheed a cikin wanda zai saka makaranta ba, tasan kuma saboda yana ganin shekarunsa basu kai bane. Dan a lokacin shekarar Abdul-rasheed 5 ne kawai. Haka ta yini tana saƙe-saƙe, sai dai batace da kowa komai ba har washe gari Malam Shehu ya dawo ɗakinta. (Ranar kwananta kenan). Bata tada zancen ba ko a ranar sai dare, bayan ta bashi abinci yaci ya gode ALLAH ta kwashe akushin daga gabansa sannan ta dawo ta zauna gefensa cike da ladabi. Da yake lokacin ɗari ne kowa ya shige ɗakinsa, baka jin motsin kowa sam. Cikin nutsuwa da girmamawa tace, “Malam niko in zaka bani dama ina da shawara”. Kallonta yayi da dukkan hankalinsa, kafin ya amsa mata da, “Ina jinki Halimatu, wace shawara ce? Kuma akan minene?”. Iya ta ƙara duƙar da kai irin na girmamawa. “Malam akan maganar jiyane na batun makaranta. Naga ranka ya ɓaci daga kai har Yaya. Dan ALLAH kayi haƙuri ka fahimceta, kasan batun bokon nan yana bama kowa tsoro, ba kuma kowa ke fahimta ba kai tsaye. Amma tunda kana so, kuma kaji ka gamsu da saka ƴaƴanka, mizai hana kafin Yaya ta sakko itama ta fahimta ka ɗauki shi wannan yaron (haka take kiran Abdul-rasheed saboda karar kasancewarsa ɗan fari) ka saka kawai. Daga baya itama nasan idan ta fahimta zata bari a saka su Bilyaminu ɗin”. Shiru Malam Shehu yay cike da nazarin maganar Iya. Kafin ya nisa tare da sakin murmushi irin nasu na manya. “Nagode sosai Halimatu, ALLAH yayi miki albarka. Tabbas naji daɗi matuƙa akan wannan shawara taki. Duk da da farko ina duba ƙanƙantar Abdul-rasheed ne shiyyasa ban sakashi a lissafi ba, dama sai gaba nake son kaishi shi bayan su sun fara. To amma maganarki sai ta min daɗi, kuma ya bani mafita dan dama a cikin tunanin yanda zan fuskanci mai martaba nake akan hakan. Kinga yanzu dai kawai na kai Abdul-rasheed a sakashi, su kuma tunda basa so bazan matsa musu ba, su cigaba da karatunsu na mahammadiya da noma. ALLAH ya sanya musu albarka gaba ɗayansu”. “Amin malam. Idan hakan kayi ma dai-dai ne. Amma zuwa nan gaba ɗin dai suma a sake tuntuɓarsu ko zasu canja shawara bayan sunga shi wannan yaron ɗin ya fara”. Bai musa mata ba akan hakan. Washe gari cike da farin ciki ya kama hannun Abdul-rasheed suka nufi gidan sarki. Wannan shine mafarin fara karatun bokon Abdul-rasheed. A lokacin yana da shekara 5 a duniya, dan an haifesa a 1947 ne. A shekara ta 1953 aka saka shi a makarantar Bauchi Native Authority Primary School (wacce daga baya ta zama Kobi Primary School). Kuma Alhamdullahi sai ya kasance shima yana son karatun kuma yana maida hankali. Malama Shehu yaji matuƙar farin cikin ganin Abdul-rasheed yana da himma akan karatun, dan haka ya ƙara tsayawa a kansa sosai. Ba'a boko Abdul-rasheed ya tsaya kawai ba, har ilimin addinin ma yana ƙoƙari akai dan suna zuwa malarantar allo kamar sauran yan uwansa, saɓanin ƴan uwan nasa da sunfi maida hankali dai akan ƴan abubuwansu na yara na yau da kullum, sai kuma makarantar allo da suma suna zuwa kamar shi. Makarantar tana kusa da ƙofar gidan sarki, cikin unguwar da ke cike da yara masu sanya riga doguwa da rawani ƙarami, wasu kuma ke tafe da allo. Malamai suna koyar da aji da harshen Hausa a farko, amma daga baya aka fara musu harshen turanci a matsayin harshen karatu. Ya koyi rubutu da karatu, ya kuma fara sha’awar duniyar da ta wuce yankinsu. A kwana a tashi ba wuya wajen UBANGIJI. Abdul-rasheed ya kammala primary ɗinsa aji shida (Standard 6) a 1959, yana ɗauke da babban burin samun ilimin da zai sa ya taimaka wa garinsu. A Shekarar 1960 ta kawo masa sabon babi. An tafi da shi Zaria tare da sauran ƴaƴan manyan Arewa, inda ya shiga Government College Zaria (Barewa College), makarantar da aka san ta fi kowace a Arewa. Ya tafi yana kuka Iya nayi. Yayinda Inna ke dariyar ƙeta ita da ƴan uwansa, a ganinsu dai ya saka kansa a wani bala'i ne shi da uwarsa. Amma ita Iya addu'a tabishi da shi kawai, sai kewar rashinsa a kusa da ita matsayinsa na babba dake taimaka mata da aike da abubuwa na yau da kullum dake tsakanin uwa da ɗa. Zama a boarding school ya koya masa nisa da iyaye da wahalar rabuwa da gida. Ya saba da rana da safiya da bugun ƙaho, shiga aji da sautin turanci daga bakin malamai na Ingila, da kuma yin motsa jiki da yamma a filin kwallo. A can ne ya haɗu da wasu ƙananan jaruman Arewa, waɗanda daga baya za su iya zama manyan shugabanni idan UBANGIJI ya ƙaddara hakan a littafinsu. Tun a zuwa hutunsa na farko ƴan uwansa suka fara hango canji a tare da rayuwarsa, sai dai hakan baisa sunji suna son yin karatun boko ba, hasalima babban su ana shirin masa aure ne wato Bilyaminu. Shekaru sun miƙa a rayuwar karatu ta Abdul-rasheed, yana zuwa hutu a duk lokacin da aka basu, yayi kwanaki ya koma cike da kewar gida da ƴan uwansa da iyaye. A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gashi ya kammala a 1966, yana da shaidar Cambridge School Certificate, wadda aka fi darajawa sosai a lokacin. Ya dawo gida Bauchi cike da farin ciki da nasarori, nasarorin da suka saka iyayensa a farin ciki mara misalin kwatance. Abdul-rasheed ya kammala Secondary school cike da nasarori da suka sake faranta ran mahaifinsa, dan haka ya sake tsaya masa akan cigaba da karatun nasa. Bayan kai kawo da taimakon wani malamin su na Boarding ya samu gurbin shiga jami'a a Kano. A wannan gaɓar ma dai kowa ya bishi da addu'a musamman mahaifinsa da mahaifiyarsa. Yayinda sauran ƴan uwansa ke masa dariya da kallonsa a matsayin wahalalle mara aikin yi, hakama Inna mahaifiyarsu kallon abin ta dinga yi kamar wani rashin aikin yi ne, sai dai duk habaicin da take da dariya iya bata kulata ba. Haka akai masa shiri ya taho Kano karatu a shekara ta 1967, ya shiga Ahmadu Bello College a Kano, wanda daga baya aka fi sani da Abdullahi Bayero College, har ya zama Bayero University Kano (BUK) a cikin 1975. Yana karantar History and Political Science, yana ƙara fahimtar tarihin mulkin mallaka da rawar da Arewa ke ciki a Nigeria data samu nasarar ƴanci kai a 1962. Cikin makaranta yake zaune, dan basu da kowa da suka sani na dangi a cikin Kano ɗin sam, hasali ma a cikin gidansu kaf babu wanda ya taɓa zuwa garin Kano sai shi yau da ALLAH ya kawo matsayin ɗalibin ilimi. Zaman Kano ya buɗe masa ido, ya kuma sake koya masa iya zama da mutane, ya kuma haɗashi da abokai na ƙwarai na amana... Rayuwar Abdul-rasheed a Kano wata irin rayuwa ce mai cike da ƙalubale da darasin rayuwa. Domin kuwa ba karatu kawai ya maida hankali ayi ba harda koyon ɗinki. Ya fara koyon ɗinki ne a dalilin abokinsa Nasiru. Wanda suka haɗu acikin makarantar department ɗinsu ɗaya. Da farko dai babu wata abota a tsakaninsu sai gaisuwa, sai da Abdul-rasheed ya fahimci Nasiru ƙuru ne dan akwai fahimtar karatu sai dai bashi da hayaniya sam sannan suka fara abota, dan kuwa Abdul-rasheed bashi da girman kai, duk abinda bai iya ba idan ya fahimci wanda ya iya koda mace ce sai ya nema taimakon a nuna masa, ta haka ne ya samu kusanci da Nasiru, a hankali suka zama abokai dan shima dai rashin girman kan Abdul-rasheed ɗin ya burge Nasiru sosai. Kamar wasa ya jashi suka je gidansu wani weekend, dan kuwa Nasiru ɗan garin Kano ne a anguwar ƙofar mata. A ƙofar gidan su Nasiru kuwa akwai shago da ake ɗinki kasancewar a bakin titi suke kusa da kasuwa, shagon kuma na yayansa ne. Tunda Abdul-rasheed ya ƙyalla ido yaga shagon sai abin ya bashi sha'awa, baiyi ƙauron baki ba da suka shiga gaida yayan Nasiru yay ta yaba abin, shi ko Yayan Nasiru yaji daɗi ya kuma fahimci kamar Abdul-rasheed na son harkar, sai yay masa tayi. Babu musu yace aiko yana son koyar kuma ya gode. Daga haka suka saita zai dinga zuwa duk weekend koyon ɗinki...........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 7_

_Amin afuwa wlhy gaba ɗaya banda nutsuwa ne an mana haihu bana yini a gida, jiya ma shaf na manta da batun posting ALLAH 😂. Kuyi haƙuri ayi suna gobe idan ALLAH ya kaimu sai na dawo gaba ɗaya hankali kwance, ga pages babu nutsuwar editing. Ina ƙara neman afuwa😀🙏._ __________________

*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana 💃 fulanin asali ke nan 😘._*

*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*

_Maza kuzo ku sha labari da ɗumi-ɗuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buɗe muku gidan gyara da ƙalƙale jikin mata ƴan kwalisa a kusa da ku gabb._

*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na👇_*

*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*

_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_

*_Zaku same mu a wannan numbers ɗin kamar haka👇_* *07068210505* *09133081313*

_DEALER IN all kind of skin care products such as:_

moisturizer Sun screen Face Toner Eye cream Face serum Face wash Face scrub Face cream Face marsk Body lotion Body cream Shower gel Body scrub Tube Body oil Body spray Perfume Hair crm Hair spray and many more

*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne 💃_*

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________