
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 12
.....yes, he is your life partner and your happy friend." She bowed her head to him with respect, and in a voice that came out from the ground, she said, "There is no pain, and I am ashamed." He smiled very wide and abundant. is it over? Kefa is the wife of Abdul-Rasheed today, one day for three days, why don't you forget?". She shook her head as a sign of no. He said, "Good wife. Men, let's cook the meat so it doesn't get cold, then go to bed and rest. I know there is a lot of fatigue in the party." She just nodded to him, and refused to let them make eye contact with him. He put the chicken in the middle of them. The first time he took one bite, he reached her mouth, but she quickly took it and hid it in the scarf, now she laughed thinly, she was a little shy. Eating this meat, he patiently ate his own, then he stood up and said, "Let me go out, I know if you're not here, you'll eat it, right?"
......Alhamdullah sunyi sallah, Abdul-rasheed kuma ya musu addu'oi sosai, sannan ya ɗora da tambayoyi ga A'isha da baya haufi a kanta. Ta kuwa amsa masa dalla-dalla cike da ƙwazo. Daga haka ya ajiye musu kaza irin ta al'ada, miƙewa tai itama ta ɗakko wani ɗan ƙyaƙyawan kwanon tangaran dake a rufe ta ajiye a gabansa. “Mina samu Matar Abdul-rasheed?”. Ya faɗa cike da zolaya yana murmushi. Kanta a ƙasa muryarta dake a dishe na fita can ƙasa ta amsa masa. “Abinci ne akace na baka idan kazo”. Kansa ya jinjina yana buɗe kwanon tangaran ɗin. Gasassun ƴan shila ne har guda huɗu, sai uban ƙamshi suke na kayan yaji. Yay murmushi yana sauke ajiyar zuciya. Yunƙurawa tayi zata miƙe, ya ko riƙe hannunta yana faɗin, “Koma ki zauna”. Zaman tayi da sauri kodan ya sake mata hannunta. Shima ganin yanda take yi ɗin sai ya saki hannun kawai yana gyara zamansa. Idonsa a kanta ya ce, “A'isha bazaki cire gyalen nan hakanan ba, ko baƙya jin zafi ne?. Ina son ki saki jiki dani dan ALLAH. Ni ba abin tsoronki bane, abokin rayuwarki ne kuma abokin farin cikin ki kinji”. Kanta ta jinjina masa cike da girmamawa, sai kuma cikin murya dake fita can ƙasa ta ce, “Babu zafi fa, kuma ina jin kunya”. Murmushi yayi mai matuƙar faɗi da yalwa. Sai kuma ya kai hannu ya riƙo hannunta a cikin nashi, ɗan matse jikinta tayi kanta a ƙasa, ya sake girgiza kai murmushinsa na sake faɗaɗa, muryarsa na ƙara tausasa ya ce, “Ai'shatul-humairah, yanzu ni da ke ai kunya ta ƙare ko? Kefa matar Abdul-rasheed ce yau kwana ɗai-ɗai har uku kokin manta?”. Kanta ta girgiza alamar a'a. Ya ce, “Yauwa matar kwarai. Maza matso to muci naman kada ya huce, sai kije ki kwanta ki huta abinki nasan akwai gajiyar biki”. Nan ma kai ta jinjina masa kawai, ta kuma ƙi yarda su haɗa ido sam da shi. Ajiye kazar yay ya saka musu kwanon ƴan shilar nan a tsakiyarsu. Laumar farko daya cira ya kai bakinta, amma sai ta duƙe da sauri tare da ɓoyewa cikin gyalen, yanzu kam siririyar dariya yayi, dan kunyar tata tsumashi take. Rarrashin duniya da dabara taƙi cin naman nan, haka ya haƙura yaci iya nashi sai ya miƙe cike da dabara yana faɗin, “Shike nan ni bari na fita, nasan idan bana nan ai zaki ci ko?”. Kai ta jinjina alamar eh. “Oh ni Abdul-rasheed, yau dai Shatu na ta zama kurmar ƙarfi da yaji, nazata yau idan muka haɗu har sai na gaji da surutunki, karki manta kusan mako huɗu kenan fa bamu ga juna ba, kewarki duk ta hanani sukuni ashe ke ba hakan bane”. Cike da yarinya ta ce, “Nima haka, kawai ina jin kunyarka ne”. “Shike nan na yarda hajiyar kunya, ni bara naje muyi sallama da baba sai na dawo. Amma fa kici naman nan, dan in na dawo naga baki cinyeshi duka ba zan miki ɗura ne. Idan kin kammala kiyi kwanciyarki kiyi barci kinji”. Bai jira amsarta ba ya fice. Tana jin takunsa yay nesa da ɗakin ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya, sai kuma a hankali ta ɗago ta leƙo fuskarta tana kallon hanya. Shiru alamar babu shi a kusa, ko da gaske ya fitan. Wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa sannan ta gyara zama ta fara cin naman. Wani daɗi yay mata na musamman, aiko ta shiga lumshe idanu ranta fes. Babu wata fargaba irin ta amare na yanzu, dan su lokacinsu idonsu bai buɗewar sanin mima ake a gidan auren ba balle har ya zame musu fargaba. Tana gama cin naman ta kwashe kwanikan ta maida gefe. Buta ta ɗauka ta fita tsakar gida ta wanke hannunta, sai kuma ta ɗanji tsoro. Da gudu ta koma cikin ɗakin, tana ajiye butar bata dire ko ina ba sai a saman ƙaramin gado, dan su Gwaggonta sun gaya mata shine nata, babban gado mai rumfa kuwa na miji ne. Kamar jira barcin keyi ta kwanta kuwa ya saceta, hankali kwance ta ɓararraje taji sabuwar katifar Rimi ta shiga jan numfashi. Duk abinda take Abdul-rasheed na gidan babu inda yaje, dan da farko ma laɓe yake yana kallonta ta window, sai da zata fito wanke hannu yay saurin komawa bayan ɗakin dan karta ganshi. Sai da ta shige ya koma jikin window ɗin, yanda ta daka tsalle ta faɗa a gadon ya sashi sakin murmushi da girgiza kai. Haka ya cigaba da tsaiwa a wajen har sai da ya tabbatar tayi barcin sannan ya koma ciki. Kwanciya ya gyara mata a hankali dan karta farka, yay mata addu'ar barci. Itama fitilar ƙwan ɗakin ya kasheta, shima ya cire rigarsa kawai ya bar wandon dogo da singlet ya haye babban gadon nan mai rumfa ya kwanta, sai dai ya zuge labulen duka ta yanda zai dinga ganin kowane motsinta ga kuma garin da zafi. Addu'a yay abinsa, ya zuba mata ido daga inda yake kwance zuciyarsa na ƙara shiga a farin ciki da alfaharin jin yau gashi ga A'isha suna barci a ɗaki ɗaya matsayin ma'aurata, ko haka aka tsaya shi kam yaci ribar zuwa kano karatu ai, sai dai a tayashi da sambarka. A haka shima yana tunane-tunanensa barci yay awon gaba da shi.
Washe gari shine ya fara farkawa da asuba, a mamakinsa sai yaga itama ta miƙe cikin lalube tana faɗin, “Inna ki kunna fitilar duhu yayi yawa. Ina son naga hanya naje na tada su Bashir suje massalaci”. Ɓoyayyen murmushi ya saki, kafin ya kama ya saukko a gadon gaba ɗaya hannunsa riƙe da Torchlight sai dai bai kunnata ba. Jikin gadon nata yaje ya tsaya, kafin ya kunna fitilar yana haska kansa kaɗan da faɗin, “Yau ba Inna zaki gani ba a wannan ni'imtacciyar asubahin Humairah. Mijinki ne, rabin tsokar jikinki Abdul-rasheed”. Tunda ya haska kansa A'isha ta daburce, dan cikin kici-kici ta shiga gyara zaninta da tuni ya warware daga jikinta yayi nashi waje, sai dai jikinta akwai ɗan tofi. Ganin yanda ta rikice tama kasa kamo zanin yanda ya dace ya sashi duƙowa yana dafa gadon ya kama mata zanin ya rufa mata, ajiyar zuciya ta saki tana ɗan juya fuskarta ga bango. Sai kuma kamar zatai kuka ta furta, “Na manta ne”. Cikin kwaikwayon ƙaramar muryarta da son tsokanarta ya bata amsa da, “Na sani Ayeshat”. Hannu tasa ta rufe fuskarta gaba ɗaya tana murmushi. Shima dai murmushin yake yana kallonta. Kafin ya bata umarnin sauka a gadon domin fita yin alwala. Ta ɗauki butar roba dake matsayin tata, shi kuma ya ɗauki ta ƙarfe. Yana gaba da fitila tana biye da shi. Fitilar ya bata yace ta fara shiga bayin, shi kuma ya tsaya jiranta a waje. Koda ta fito bai amshi fitilarba ya barta da ita shi ya shiga bayin a haka. Sanda ya fito ta kammala tata alwalar, tsayawa tai ta jirashi yayi, sannan suka koma ɗakin a tare. Ashana ya ɗauka ya kunna mata fitilar kwai, ya ɗauki Torchlight ɗin ya wuce massalaci. Bayan ta idar da sallar asuba bata jira komai ba ta sake hayewa gadon tai kwanciyarta, dan barcin kwana biyun nan dake cin idonta ne ke damunta. Amma ita bata san wani barcin safe ba dan bata yi, a gida ma suna idar da sallar asuba ita da Inna su Tasi'u suka dawo massalaci makarantar allo suke tafiya, sai takwas hantsi ya haska suke dawowa. Suyi kari su sake tafiya wata makarantar sai kuma ƙarfe sha biyu. Daga nan sai ta yamma kuma. Amma yau sai ga Hajiya Indo ƴan gidan miji daɗi ana shan barcin safe cike da freedom. Shiko Abdul-rasheed ma bai dawo gidan ba koda aka idar da sallar, dan suna tare da Baba, bayan sun bar massalacin Baba ya tarkatasu da sauran yayunsa suka tafi gaishe da wani makwafcinsu da jiya yaji ciwo a ƙafa. Daga can kuma suka wuce gidansu....
Wajen ƙarfe takwas hantsi ya ɗaga. Rana ta leƙo mai ɗumi da hasken safiya ta ratsa cikin ɗakin da ke da ɗan sauran ƙanshin turaren wutar jiya da aka kunna mata da dare. Fitilar ƙwan harta gaji ta mutu alamar kalanzir ya ƙare a cikinta. Dai-dai nan amarya A'isha ta tashi saboda ɗumin hasken rana dake taɓa mata fuska, zaune ta tashi tana miƙa da kiran sunan ALLAH. Ɗakin ta fara bi da kallo daga inda take zaune a bakin gadon, sai kuma tai murmushi tana raya (Yanzu fa komai ba ɗakin nan nawa ne kona fasa Inna bazata min gaɗa ba) kawai sai abin ya bata dariya, ta tashi ta buga tsallen farin ciki, kafin ta sake hayewa gadon tana juyi. Sai da tayi mai isarta sannan ta sake tashi zaune, tunanin gidane kuma yazo mata, zuciyarta na sake ayyana mata yanzu fa su Inna sunyi nesa da ita da su Bashir, shike nan bata da kowa anan kusa. Shar hawaye suka fara rige-rigen sauka a fuskarta, a haka ta fara kici-kicin gyaran gadon, tana yi tana share su da sharɓar majina harta kammala. Inna ta gaya mata tana tashi a barci ta dinga fara gyara ɗakinta kafin komai, karta sake tabar gadajenta ba'a gyare ba har wani ya gani koda Abdul-rasheed ne. Gadon nasa ta kalla, ba wani yayi barkatai bane, amma duk wanda ya kalla yasan an kwanta a kansa, gashi ya zuge labulen ana ganin kan gadon, kuma ina tace babu ƙyau wani ya gammaka sirrin gadon mijinka, rage darajar miji ne. Maza-maza ta ajiye batun kuka a gefe ta ɗakko kujera ƴar tsugunno ta ajiye a gabansa ta taka ta hau, sai kuma tai tsaye shiru cikin ɓata fuska, a fili ta furta, “To yanzu a yaya zan gyara masa, gaskiya ina jin kunyar hawa masa gado, karma yaga kamar na rainashi, kuma za'a iya rubuta min zunubi”. Dariya sosai kalamanta suka saka Abdul-rasheed dake tsaye a bakin ƙofa batare data sani ba, dan tun sanda ta ja kujera ya iso wajen. Da ƙyar ya iya danne dariyar yana cigaba da kallonta, sai kuma ya koma kallon ɗakin ya murmusa kaɗan, komai tsaftatacce yake, kamar yadda aka bar shi a jiya, idan ka cire gadajen da suka kwanta kawai. Sai kazar al’adar ta jiya tana gefe tare da kwanikan abincin da suka ci.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 13_
__________________
https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6
*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*
*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*
*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*
*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*
_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃
*_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 💃_*
20k monthly kayan 100k 10k monthly kayan 50k
*_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. 💃 Ga sauƙi abaka tamkar ƙyauta 💃💃😀_*
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________