
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 25
.....he came in with a smile, carrying a paper and his helmet on, he was beaming, after he finished looking at them, he allowed them to sit down from the greeting they gave him and said, "Before I start the lesson, I have a simple question for the new students in the new class that is ss", he ended his speech looking at the students of the class one by one. They respectfully replied, "Okay Sir!!". "Tell me, when you grow up, what do you want to be?". The children started one by one. "I am a doctor!" "I'm an engineer!" "I'm a pilot!" Some of them couldn't tell me because they didn't know they were going to tell me. Then the teacher's eyes fell on Haysam who was sitting in the middle of the first seat and he kept his eyes on the cover of the book of Elijah the Mighty in front of him. "Haysam ibn Abdul-rasheed Shehu!". He called his name teasingly, his son is a funny man. He continued to say, "What about you? What do you want to be when you grow up?" Haysam slowly raised his head. His eyes were a little dry like someone with heavy thoughts. He took a few breaths before he said calmly: "I... I want to be a SOJA Sir." The class was silent for a few seconds, then some children laughed a
.....A haka Bashir ya nema shiga soja, shiko Tasi'u ya fara shirye-shiryen aure dan gidansu yarinyar sunce zasu masa komai. Hakan kuwa akayi, sun masa komai sun aura masa ƴarsu sun kuma biya musu kuɗin karatu zuwa ƙasar waje, sai dai abin takaici da tausayi ko saka su A'isha a hidimar bikin baiyi ba wai suna masa baƙin ciki ita da Inna, haka akai shagali daga shi sai abokansa sai dangin matar ya tare, bayan sati ɗaya yazo yay musu sallama shi ya wuce ƙasar waje karatu da amaryarsa. A'isha da Inna suka masa addu'a kawai ya buga ƙeyarsa yay gaba abinsa. Bayan tafiyar Tasi'u shima Bashir ya samu aikin soja, dan haka ya wuce ya barsu, sai dai shi da sanya albarkar Inna da ƴar uwarsa A'isha....
<<•>><<•>><<•>>
Lokaci ya ja, shekaru sun matsa Haysam ya kammala js3 ɗinsa ya shiga ss1, a ranar su ta farko a aji wani al'amari ya faru tsakanin malaminsu dasu su Haysam ɗalibai. Suna zaune cikin natsuwa, kowanne da littafinsa a gaban tebur. Malam Sulaiman, wanda ake kira da Mallam Su a kamarantar ya shigo da murmushi yana ɗauke da takarda da kwalkwalinsa kan nan sai ƙyalli yake, bayan ya gama ƙare musu kallo ya basu izinin zama daga gaisuwar da sukai masa ya ce, “Kafin na fara darasi ina da tambaya mai sauƙi ga ɗalibai na sabbi fil a sabon ajin fara girma wato ss”, ya ƙare maganar yana kallon ɗaliban ajin ɗaya bayan ɗaya. Cike da girmamawa suka amsa da, “Okay Sir!!”. “Ku gaya min, idan kun girma me kuke son zama?”. Yara suka fara ɗaya bayan ɗaya. “Ni likita!” “Ni injiniya!” “Ni matuƙin jirgi!” Wasu ko sun kasa faɗa dan basu san mi zasuce ba. Sai idon malam ya sauka kan Haysam dake zaune a tsakiyar kujerar farko yay shiru idonsa akan bangon littafin Iliya ɗan Mai ƙarfi dake gabansa. “Haysam ibn Abdul-rasheed Shehu!”. Ya kira sunansa cike da tsokana dan shi mutum ne mai barkwanci. ya cigaba da faɗin, “kai fa? Me kake so ka zama idan ka girma?” Haysam ya ɗago kai a hankali. Idonsa ya ɗan bushe kamar wanda ke da tunani mai nauyi. Ya ɗan ja numfashi kafin ya ce cikin nutsuwa: “Ni… so nake in zama SOJA Mallam.” Aji ya ɗan yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai wasu yara suka yi ƙaramar dariya, amma Mallam Su ya ɗaga hannu yana nuna musu su yi shiru. Ya ce, “Soja fa? Haysam! Mi yasa soja?” ya maimaita cikin mamaki matuƙa dan a lokacin ba kowa ke son soja ba. Haysam ya maida idonsa ƙasa kamar bazai ce komai ba, sai kuma a hankali muryarsa na canjawa da alamar rauni ya ce, “Abiy na ne... mahaifina. Yana so in zama soja kafin ya rasu shiyasa ma yake kirana da ZAKINSA, nima kuma tunda ya fara bani labarin su waye soja naji ina so, ina son na zama jarumi, kozan iya kwatantawa daga jarumtar magabatan da suka shuɗe a zamanin MANZON ALLAH da wanda suka biyo baya irin su Iliya ɗan mai ƙarfi”. Ya ɗan yi shiru kaɗan, yana wasa da yatsun sa. “Ban san ko zan iya ba, amma kullum ina jin kamar idan nayi hakan Abiy zai yi alfahari idan na cika burin nan nasa, dan shi yaso zama soja amma gida baza'a barshi ba, shiyasa yay fatan ni na zama na cika masa burinsa.” Malam Su ya ɗan ɗaga kai yana kallonsa da murmushi mai cike da birgewa, dan harga ALLAH yaron ya ƙara ƙayatar da shi. Cike da son ƙarfafawa ya ce, “Zaka iya Zaki mazan fama, in sha ALLAHU sai ka iya, sai ka zama abin alfahari ga babanka damu al'ummar ƙasa. Na maka alƙawarin zan taimaka maka in ALLAH Ya yarda.” Abinda ya bama kowa mamaki sai akaga Haysam yayi murumushi, abinda kuma bai cika yi ba, cike da farin ciki ya ce, “Malam kayi alƙawari?”. “In sha ALLAHU Zakin babansa in dai ina rayuwa nayi alƙawari. Dan ina da ɗan uwa soja daga yau ɗin nan ma zan bashi labarinka”. A wannan lokacin babu wanda ya sake dariya. Kowa ya kalli Haysam da wani sabon kallo na girmamawa da tausayi. Shiko ya koma gida da farin ciki ya sanarma Mammah da Inna. A kuma dalilin wannan alƙawari shaƙuwa ta shiga tsakanin Malam Sulaiman da Haysam, har ofishinsa yake zuwa suyita hira da labarin aikin soja. A haka rayuwa ta shuɗa yau da gobe kayan ALLAH. Ranar da Haysam ya kammala Secondary School, Aisha ta kasa boye hawayenta na farin ciki da na tsoron duk a lokaci ɗaya. Domin tana ganin ɗanta zai tashi neman hanyar rayuwa ta girma da gwagwarmayar da tafi ta shekarun ƙuruciyarsa girma da haɗari. Domin zuwa yanzu Haysam ya gama yanke shawarar shiga aikin soja kamar yanda yasha faɗa mata tun bayan alƙawarin da malaminsu yay masa. A duk lokacin da ya faɗa mata haka, sai ta yi shiru na dogon lokaci kafin ta ce: “Ka tafi idan hakan ne ka ga daidai, amma ka tuna da addu’a. Rayuwar soja ba wasa bace Muhammad, sai dai bazan hana ka ba, ba kuma zan tunɓuke maka burin mahaifinka a zuciyarka ba saboda ina jin tsoro, zan cigaba da maka addu'a da karfafawata ALLAH ya fimu sanin abinda ke ɓoye ai, sannan kowane bawa yana rayuwa ne da ƙaddararsa, kwazonsa a cin jarabawarsa ne ke bashi makoma bisa ga rahamar mahaliccinmu.” To a yau ma aka kammala bikin gama Secondary ɗinsu daya tuna mata cewar lokacin zama soja yayi amsar data bashi kenan. Sai kawai ya durƙusa ya rungumeta tare da faɗin, “Mammah na gode da ƙarfafawarki a gareni a koda yaushe, amma ki sani ni bana zuwa neman suna, amma zanje neman ƙarfi da adalci. Na ga yadda rashin adalci ke cinye mutane, zan so in tashi da takobin gaskiya, ko da zai zama ƙarshena, daga karshen dai na cika burin Abiy na kuma cika nawa burin, na kuma maida sunanki UWAR GWANI ko UWAR MAYAƘI.” Murmushi Aisha tayi da share hawaye, ta ɗagosa daga jikinta tana mai ɗan dungure masa kai. Murmushi yayi yana mai risinar da idanunsa ƙasa, dama idan kaga sakewa ta musamman ga Haysam to yana a gaban Mammah ne. A'isha dake hawaye itama ta kamo hannayensa cikin nata ta runtse tana addu’a kamar haka, “ALLAH ya taimake ka Muhammad. Ka zama zaki mai adalci kamar yanda mahaifinku ke fata ba wanda ke cin mutane ba. Ka zama ZAKI mai amsa sunan SARKI a rundunar adalci ba Sarkin dabbobi mai mulkinsu ta ƙarfi yana halakasu matsayin abincinsa ba. Ka zama ZAKI mai kassara maƙiya da karya mugayen burunsu da manufofin su. ina fatan wannan jarumin na Abiy da Umman-Haysam (Yakura) ya zama Zaki wanda rayuwarsa ta samo asali daga haske da nagarta, daga hawaye da fata, daga ƙaunar iyaye da ƴan uwa da nauyin al’umma. Kaje soja da fatana da addu'ata Muhammad, kaje soja da amincewata da farin cikina Muhammad Haysam. Amma ina mai gargaɗinka da shaye-shaye, bana so! Bana so! Bana so Muhammad. Ka kiyaye Zina, tana ruguza bawa da zuri'arsa, bana so! Bana so! Bana so Haysam. Ka yaɗa ilimi ka cigaba da neman ilimi musamman na bautama UBANGIJI, kaga dai zuwa yanzu kayi saukar Alkur'ani, ka samu ilimin hadisi mai yawan gaske, ka haddace litattafai da yawa na addini da koni mahaifiyarku kana koyar dani a yanzu. Ka tuna yan uwanka suna kiranka da suna (DADA) a yanzu saboda kai suke gani madadin mahaifinsu, idan ka ɓata ɗan wani kaima za'aci nasarar ɓata maka su Haysam. Yau babu Innata a duniya shekararta ɗaya kenan da rasuwa, tunda Tasi'u yabar ƙasar nan bamu sake jin labarinsa ba shekara huɗu kenan, an kashe mana Bashir a aikin soja, wanda labarin rasuwarsa yasa Inna yanke jiki ta faɗi bata sake lafiya ba sai da ta koma ga UBANGIJI. Haysam banda kowa sai ALLAH NA, sai ku ƴaƴana guda takwas, kune uwata kune ubana, kune dangina. Babu kalar zagin da bana sha saboda naƙi yin aure, ni kuma bana son nayi aure ne wani yazo ya ƙuntata min rayuwarku koda da harara. A kowace rayuwa zaka tsinta kanka ka tuna kai wanene dan ALLAH Haysam ka tuna”. Kuka ya sarƙeta, shima sai ya kwantar da kansa a cinyarta yana hawaye. Sun jima a haka kafin ta koma lallashinsu, sai kuma ta koma bashi labarai masu daɗi na rayuwarta da mahaifinsu Abdul-rasheed. A haka su Ma'aruff da a yanzu suma suke js 1 Secondary suka shigo, ba jimawa Ummi da Bilal da Momy suma suka dawo. Ammar da Mimi kuwa ba'a sakasu a makaranta ba har yanzu dai. Aiko zama sukai suka zagaye Haysam da a yanzu suka maida sunansa Dada suna taya shi murnar gama Secondary. Idan ka gansu dole su burgeka su kuma baka tausayi. Akwai zuminci mai ƙarfi a tsakaninsu, akwai ginanniyar soyayyar juna mai tsafta a zukatansu, akwai shaƙuwa mai rahama a tsakaninsu, akwai tausayi mai yalwa a tsakaninsu. Su ba masu arziƙi bane, amma ALLAH ya basu arziƙin farin ciki da so da ƙaunar junansu, ALLAH ya basu arziƙin JARUMAR UWA mai sadaukar da farin cikinta domin gina nasu. Sun rasa uba amma suna kallon babban yayansu madadin uba a wannan lokacin. Dan kuwa shine ke musu ɗawainiya irin ta uba. A dalilin gwagwarmayar talla daya sha ta kayan koli da kayan karatu dama wasu wahalhalu, da aikatau na mahaifiya da wankau, dama wasu abubuwa da tayi bayan nan, dan akwai gaɓar da aka koreta a aikatau ɗin ma, wankin ya daina yiwuwa saboda ciwo daya kwantar da ita, ɗan abinda suka samu ta koma yin abincin sayarwa safe da rana wani lokacin har tuwo da dare ta fita da shi bakin kasuwa. Kai har dakau A'isha tayi domin iyalanta, haka zatayi surfe ta maida dakan gari hannunta na baroro da fashewa amma bazata kula ba, aikin gona tasha yi ta tasa yaranta gaba suyi a biyasu, sussukar hatsi na gona ta ɗure a buhu a biyata. Ga jiyyar Innarta da ciwo ya kayar, da al'amarin ya ƙwaɓe har itace A'isha tayo a daji ta sayar dan samun abinci da kuɗin maganin Inna dan abinda Haysam ke samowa a kasuwa bawai zai wadacesu bane duka amma yana rage musu sosai dan dashi ake biyan komai na karatunsa dana ƙannensa. Da kuma ALLAH ya sakama abin albarka har ya kafa jarin kansa sai yazama har anan gida ana zuwa nema a saya kayan kolin, daga haka ya barma Mammahnsa wannan sanar kolin har ma da kayan karatu na yara ya maida hankali a zana jarabawar ƙarshe da sukayi yau suka kammala. Sai kuma Alhmdllh yaga a gida ma kamar ALLAH yafi sanyama sanar kayan kolin ma albarka, wannan ƙwarin gwiwa ne ya ƙarfafashi a yau ya sake tabbatar ma Mammah zai je aikin sojan da yake ji da kamar zai fasa saboda kar ya barta da nauyi, amma yanzu yana fata wannan sanar tasa data dawo gida zata taimaka musu sosai.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 26_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________