
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 13
..... she said that it was straight up immorality and lack of morals, and she testified that her Abdul-Rasheed was calm and disciplined, he never touched a woman or a stick when they were in Kano. Gwaggo's advice came to her on Wednesday, where she was telling her that her husband had touched her now, as soon as they were married. Her heart dropped for the first time, just as her mind came back to her body, her eyes connected with his, seeing the way he looked at her as if he had a picture, she was overwhelmed with intense shame. She bowed her head, her voice shaking like she was about to cry and said, "Welcome back". "Kema hello and home". He said with the coolness of a person who has entered a state. Then he separated their bodies and lifted her up and laid her down on her feet. She moved back quickly, her head was on the ground and she was struggling to intertwine her fingers in each other's. He smiled and looked at her toes, then he pulled back and returned to the bed saying, "Let me help you fix the bed. And from now on, I promise you to keep climbing, there will be no sin for you. You are also going to scold me while I climb, right?". Yay's last words and turning to look at h
.......Ganin ta fara kici-kicin gyara gadon batare data hau ba sai nishi take alamar wahala ya sashi ƙarasa shigowa cikin ɗakin, yay sallama a hankali yanda bazataji ba, tare da ajiye kofin hannunsa na ƙarfe mai murfi da leda baƙa. Inda take ya ƙarasa, ya tsaya daf da ita sannan ya furta, “Kin tashi lafiya?”. Kamar wadda ta tsorata ta juyo firgigit har tana neman gocewa daga kujerar, duk da kuwa muryar sa ta fita cike da taushi ne, amma ita tajita a bazata kuma gab da ita. Da sauri yasa hannu ya tareta, hakan yasa ta faɗa masa a jiki gaba ɗaya, ya naɗe hannayensa kuwa duka a bayanta ta koma rungume a jikin nasa sosai. Sake rikicewa tai, ta shiga ƙoƙarin fita a jikinsa tana bashi haƙuri. “Shiiii ya isa, ni baki min laifin komai ba”. Ya faɗa cike da raɗa yana bin fuskarta da kallo, a yanda yay magana yasata nutsuwa, sai dai jikinta rawa yake na rashin sabo, zuciyarta na ɗan bugawa ƙasa-ƙasa. Idanunta dake cika da ƙwalla ta ɗago kaɗan da mamakinsa, dan ita dai tasan idan namiji ya taɓa mace iskanci ne da rashin tarbiyya kai tsaye, kuma ita ta shaida Abdul-rasheed ɗinta mai nutsuwa da tarbiyya ne, dan bai taɓa kwatanta taɓa mata ko hannu ba sanda suke Kano. Nasihar Gwaggo Laraba ce ta faɗo mata, inda take gaya mata halak ne mijinta ya taɓata yanzu, dan an ɗaura musu aure. Ajiyar zuciya ta sauke a karo na farko, dai-dai hankalinta ya dawo jikinta, ido suka haɗa da shi, ganin kallon da yake mata kamar ya samu hoto sai kunya ta mamaye ta mai tsanani. Ta sunkuyar da kai, muryarta tana rawa kamar mai shirin kuka ta ce, “Sannu da dawowa”. “Kema sannu da gida”. Ya faɗa da sanyi irin na wanda ya shiga yanayi. Sai kuma ya raba jikin nasu tare da ɗagata cak ya direta ƙasa akan ƙafafunta. Baya ta matsa da sauri, kanta dai na ƙasa sai faman cuɗa yatsunta take a cikin na juna. Murmushi yayi idonsa akan yatsun nata, sai kuma ya janye ya maida ga gadon yana faɗin, “Bari na tayaki gyara gadon ko. Kuma ni daga yau na yarje miki ki dinga hawa babu wani zunubi da zaki samu. Nima ai zaki dinga ara min naki ina hawa ko?”. Yay maganar ƙarshe da juyowa yana kallonta. Murmushi tayi da saka hannayenta duk biyu ta rufe fuska, sai kuma ta jinjina masa kanta alamar eh. Ya ce, “A'a ban yarda ba magana zakiyi da baki. Dan dole ki koya surutu yanzu babu maganar shiru-shiru sai na maidaki akku”. Dariya sosai ta sanya, tare da janye hannun ta ce, “Akku fa?”. “Eh mana, ai kin san shine sarkin subaɗi. Ni kuma irinsa ne bana gajiya da zance amma idan ina tare da Gimbiya A'isha”. Sosai sunan ya sata nishaɗi, dan haka cike da ƙuruciya ta ce, “Kai kuma Sarki”. “Shike nan kuwa, ga Sarki ga Gimbiyarsa”. Ya bata amsa yana murmurshi da ƙarasa gyara gadon. Ganin zai bar wajen batare daya zuge labulen ba ta ce, “Inna tace haramun ne barin gadon miji a buɗe kowa ya gani, tace kullum na zuge labulen nan, kozan wanke in yayi datti ina cirewa na canja da wani kafin su bushe”. Shi kam dai wannan batu na bashi dariya, amma sai ya biye mata ya ce, “To Amin afuwa, bara na zuge”. Ya juya ya mata yanda take so, gado ya koma ruff abinsa. Daga nan ya ce, “Jeki wanke ido na kawo miki wannan. Shayi ne, da ɗan madara. Ki sha kafin ki ci wani abu ko” Kai ta jinjina masa cike da ladabi da sanyin murya ta ce, “Na gode.” Murmushi ya mata, ita kuma ta ɗauka buta ta fice da ƴar battar garin gawayi da aka niƙa da gishiri a waje guda, sai asuwaki a cikin leda ta ɗauki ɗaya. Ta ɗan jima kafin ta koma ɗakin, yana zaune a tabarma daya shimfiɗa. A gabansa kofin shayin ne ya ɗakko ƙarami yana haɗa madara ta gwangwani da sauran kayan haɗin. Ta koma can ƙarshen bango zata zauna ya ce ta dawo kan tabarmar. Haka ta zo ta zauna a ɗarare dan biyayya amma daka gani kasan a takure take bata saba zama da namiji a irin yanayin ba, gashi su biyu a ɗaki kawai tun jiya. Shiru ya kasance a tsakaninsu na wasu mintuna harya kammala, ya miƙa mata kofin shayin da farantin ƙosai daya juye daga leda, sai biredi guɗa ɗaya da kazar jiya da basuci ba. Shima nashi daya haɗa ya ɗauka yana kallon ta. “Ɗauka kisha mana”. Kanta ta girgiza masa alamar a'a tana wasa da gefen zanenta”. Shima sai ya ajiye nashi yana faɗin, “Saboda mi?”. “Ina jin kunya”. “Aisha kunyar nan dole a ajiye batunta. Abdul-rasheed ɗinki ne fa ba wani daban ba. Yi haƙuri muci tare mu sami ladan juna. Ko kina son mutane su fara shigowa su sameni a gidan bayan ya kamata ace nayi na fita na basu waje”. Kanta ta girgiza. Ya ce, “Yauwa to maza muci kinji ƴar albarkata. Ai yanzu mu komai mukayi a tare lada za'a saka mana a samu a aljanna kuma. Sai ta ɗago kai, ta amsa da murmushi kaɗan. Wannan karon, idanuwanta sun ɗan shige cikin nasa. Kallon su ya haɗu, har ta kai kowa ya kasa fara janye wa, nutsuwa ce mai girma da daraja ke ratsasu a tare, zukatamsu na ƙara jin fahimtar wata sabuwar hanya ta rayuwa da suka shiga, rayuwa irin ta soyayya mai ladabi da ƙarfi da haske fiye data da, rayuwa wadda take farawa da kunya, sannan ta cigaba da aminci da yarda. Yatsa Abdul-rasheed ya kai kamar zai tsone mata idon, dan haka tasa hannu da sauri ta kare. Sai ya saki dariya, itama murmushi tayi mai cike da kunya. Zuciyarta na faɗa mata abin da bakinta bai iya faɗa, cewa sabuwar rayuwa ta fara a garesu kamar yanda Inna ta faɗa mata, kuma shi mutum ne da nutsuwarsa ke girmama kwarjininsa a idanun kowa a bayyane. “Kin tafi tunanin miye kuma Matar Abdul-rasheed?”. Kai tsaye ta ce, “Tunanin ka”. “Masha ALLAH akan mi?”. Babu kwalo-kwalo ta zayyane masa kalaman Innar tata. Ya ɗan tsaya kawai yana kallonta da murmushi. Kafin ya cigaba da cin abincinsa yana jin girma da kimar Inna na ƙaruwa a ransa. Haka dai suka karya, ya taimaka mata suka gyara wajen, ta kwashi kwanikan zuwa waje danta wanke a gaban rijiya. Shi kuma sai ya ɗauki botikin ƙarfe ya fara jawo mata ruwan wanke-wanken, sannan ya fara ɗiba a botikin yana kaiwa randunan ruwansu ɗaya bayan ɗaya. A haka suka kammala aikin yace zai yi wanka. Ita da kanta ta ɗauki ruwan takai masa bayi tare da kwandon soson wanka. Ta dawo ɗakin ta saka turaren wuta ta share. A lokacin ne kuma yaro yay sallama cikin gidan ɗauke da kwanika akan ture. Bata yayi tare da mata bayanin cewa Inna ce tace ya kawo. Bata san wacece Innar ba, amma taji a ranta daga gidan su Abdul-rasheed ɗin ne. Godiya tayi da sannu, dan haka yaron bai zauna ba ya juya ya koma. Fitarsa babu jimawa Abdul-rasheed ya shigo. Ya ce, “Sallamar wa nake ji ne kamar Amadu?”. “Wani yaro ne dai, ban sani ba ko sunansa kenan, abinci ne ya kawo yace inji Inna”. “Oh daga gidanmu ne. To ki zauna sai ki karya”. Idannunta a ɗan ware ta ce, “Ba yanzu muka gama karyawa ba? Naƙoshi ALLAH”. “To Alhamdullahi, ki ajiye sai zuwa anjima. Amma kije kema kiyi wanka kada mutane su fara shigowa suna ganinki da kaya tun na jiya”. Babu ko musu, sai ma amsa masa da tai cike da ladabi, daga haka ta ɗiba ruwan itama ta wuce bayi. Lokacin data fito harya shirya, dan haka bai zauna ba yay mata sallama ya fice dan har yara sun fara shigowa gidan. Aiko itama A'isha a gurguje ta kammala saka kaya, ta zauna tai kwalliya gwargwadon iyakarta kuma dai-dai da lokacinsa. Daga nan ta fiddo ma yaran da suka fara taruwa a gidan tabarmin karauni, sai kuma ta kwaso shantu duk ta zube dan harda ƴammata. Ai daga nan suka kafa shiriritar kiɗan shantu da ƴammata sa'anninta a tsakar gidan nan suna raira waƙoƙin gaɗa. Kafin kace mi gidan ya cika da yara. Manya dake shigowa ganin ɗakin amarya kota kansu basa bi ma, sai dai su shiga su gano su saka albarka su fice abinsu batare da sun damu ba, dan wannan ba komai bane daga amaren wannan zamanin nasu saboda ƙuruciya da ƙarancin shekaru..
Amarya A'isha bata sake tunawa da batun Abdul-rasheed ba har yamma ta samu abokan shargalle, abincin rana da aka sake kawowa ma daga gidansu, dana safen duk sun cinye ita da ƙawayen nata. Sai gab da magriba an kawo mata tuwon dare mai kawowar data kasance ƙanwar Abdul-rasheed ce Khadijah da bata koma Maiduguri ba ta kora yaran duka, sannan ta saka A'isha yin wankan dole ita kuma ta rufo gidan ta hau gyara tsakar gidan da sukama kaca-kaca. Ɗakin dai da yake ba zama sukai ba a ciki da haskensa, sai ƴan ganin ɗaki da ke shiga. Amma duk da haka shima sai da Khadijah ta sake sharo mata shi ta kunna turaren wuta, zata kunna fitila taga babu kalanzir. Dole ta ɗauki kalbar da aka aje dan sayen kalanzir ɗin ta fita samun yaro ya bada a suyo sukaci karo da Abdul-rasheed ya dawo. Koda ya tambayeta ina zata haka ta sanar masa sai shi ya amshi kwalbar yace ta koma shi bari ya sayo. Haka kuwa akayi, dan haka a gurguje Khadijah ta taya A'isha shiryawa. Sai gata ta fito tsaff kamar ba itace tai buɗu-buɗu ba. Ta bajeta da turare. Sai ga ango ya dawo. A tare suka masa sannu suka gaisheshi, Khadijah ta amshi kalanzir ɗin tana zubawa a fitila shiko yana satar kallon A'isha datai masa ƙyau a cikin jojin da Khadijah ta sakata sakawa. Yasan wannan kwalliya haka sai da taimakon Khadijan, dan ta fita wayo kuma ta girmeta. Khadijah na gama kunna musu fitilar tai musu sallama zata wuce. Amma ya tsaidata kan ta zauna har ya dawo massalaci dan kar A'isha taji tsoro. Haka dole ta zauna sukai salla tare, shi ko yay alwala da ruwan da A'ishan ta kawo masa a butar karfe ya fice massalacin...........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 14_
__________________
https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6
*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*
*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*
*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*
*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*
_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃
*_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 💃_*
20k monthly kayan 100k 10k monthly kayan 50k
*_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. 💃 Ga sauƙi abaka tamkar ƙyauta 💃💃😀_*
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv