
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 26
..... he was very happy and said that he went to prepare tomorrow for them to go to Kaduna to his brother who is a Major in the Nigerian Army, and who is related to the examiners of NDA (Nigerian Defense Academy). And so it happened, Mammah was a bit of a bitch and she got Haysam the money for the car and the son to eat, the next morning they took the road to Kaduna. They received a warm welcome, and after they had eaten Malam Sulaiman met his younger brother. After he told him who Haysam was, he said with the boy's enthusiasm and the attitude of adults, "This boy does not have a father, as I told you years ago, but he has a character that is more valuable than gold. Please help to check his documents, not for honor, but to qualify and confirm the kind that our country needs. The son has built this goal in his heart since his brain and heart. You yourself will ensure that and be proud to build this child's life on this work one day, God willing." Major Abdullahi said, "God willing, I promise there won't be any kind of problem. I can only confirm that he is a hard worker in the child's documents. And in the hours I spent with him, I understood a lot of things about...
.......Addu'ar mahaifiya ba wasa ba, dan kuwa dai Haysam ya tsallaka ajin jarabawa ko muce ƙaddararsa ta uku bayan rayuwar jin daɗi da iyaye, data maraici da uwa ɗaya tilo, zuwa soja a yanzu, sojan ƙasa mai girma irin ƙasarsa. Matakin ƙaddarar soja dake tafiya da fara shekarun hankali da mallakar kai da kai matsayin cikakken mutum, dan kuwa ya ɗauki hanyar tsallake shekaru ashirin ɗin farko zuwa matakin rayuwa ta biyu a masomin cikar hankali da fara sanin ainahin micece ma duniyar, dan a wancan matakin an san duniyar ne a gaɓar banbance iya abinda ƙwaƙwalwa da zuciya kawai ke iya fuskanta da karamin nisan tunani da hange. Matakin farko na samun gurbi a NDA (Nigerian Defence Academy), Haysam Abdul-rasheed Shehu ya samu wannan gurbin Karatu da taimakon Malamin nan nasu da yay alƙawari tun shekaru uku da suka shuɗe wato Malam Su. Bayan Haysam ya gama Secondary School da ƙwazo da halin kirki ya samu result ɗinsa na SSCE yayi ƙyau sosai. Cike da zumuɗi ya nufi ofishin Malam Su ya kai masa, ai ko ya tayashi murna ya kuma ce yaje ya shirya a gobe zasuje Kaduna wajen ƙaninsa wanda yake Major a Nigerian Army, wanda kuma yake da alaƙa da masu duba takardun shiga NDA (Nigerian Defence Academy). Haka kuwa akayi, Mammah tai ɗan cuku-cukunta ta samawa Haysam kuɗin mota da ɗan na guzirin cin abinci, washe gari suka ɗauki hanyar Kaduna. Sun samu tarba ta muntatawa kuwa, bayan sunci sun sha Malam Sulaiman ya gana da ƙaninsa. Bayan ya ƙara tisa masa wanene Haysam, da kwazon yaron da halin manya ya ce, “Wannan yaron bai da uba kamar yanda na gaya maka tun shekarun baya, amma yana da hali irin wanda ya fi zinariya daraja. Ka taimaka a duba takardunsa ba don alfarma ba, sai don cancanta da tabbatarwa irinsu ƙasarmu ke buƙata, dan an gina wannan burin a zuciyarsa tun kwakwalwar sa na jinjira ita da zuciyarsa. Kai da kanka zaka tabbatar da hakan kuma kayi alfahari da gina rayuwar wannan yaron akan wannan aikin watarana in sha ALLAHU”. Cikin jinjina kai Major Abdullahi ya ce, “In sha ALLAHU Yaya, nama alƙawarin baza'a samu kowace irin matsala ba. Dan a takardun yaron kawai na tabbatar shi ɗin mai ƙwazo ne. Sannan a wannan zaman awannin da nayi da shi na fahimci abubuwa da yawa atare da shi masu girma da daraja. Kaje in ALLAH ya yarda zakaji labari mai daɗi”. “Alhamdullahi Na gode Abdullahi, idan kaimin hakan bazan gushe ba ina mai maka addu'a, domin kuwa ka taimakeni wajen cika alƙawarin dana ɗaukama marayan ALLAH.” Aranar suka koma kano akan za'a neme su...
><><><><><
Bayan bincike da gwaji, an sake kiran Haysam zuwa interview a Kaduna, inda ya nuna basira, nutsuwa, da ilimi mai zurfi har ma jami’an da sukai interviewn ya basu mamaki suka kuma yabama kwazonsa kwarai da gaske. Kamar wasa, sai sakamakon shigar NDA ya fito, sunan Haysam Abdul-rasheed Shehu ya fito cikin jerin waɗanda aka ɗauka. Kwatanta muku irin farin cikin da A'isha da Haysam da ƴan uwansa harma da Malam Sulaiman sukayi ɓata lokaci ne a wannan gaɓar, amma dan musamu mu wuce kowa ya ƙiyarsa a tashi zuciyar kawai..
^^^^^^^^^^^^^
3/12/1992 shirin tafiyar Haysam ya kammala zuwa NDA, inda A'isha tai ƙoƙari matuƙa ta haɗa masa dukkan abinda aka buƙata daga iyaye. Ta ƙara tisa masa nasihar da a kullum bata gajiya dayi masa shi da ƴan uwansa. Ranar farin ciki ga Haysam ga ahalinsa, ranar kuma kuka da alfahari. Haysam ya shirya cikin shigar kamala, ya goya jakarsa a baya. Cikin nutsuwarsa yazo gaban Mammah ya durƙusa, gefe A'isha ta kauda kanta kaɗan tana ƙoƙarin maida ƙwallar da suka cika mata idanu, kafin ta dawo da fuskarta garesa tana kallonsa zuciyarta cike da ƙauna da fargabar rabuwa da shi, tunda ta haifesa bai taɓa yin nesa da ita na abinda ya wuce sati biyu ba. Dama dai Mama Yakura ce kan ɗaukeshi suje Maiduguri suyi kwanaki sannan tana raye. Tunda kuma mutuwa ta ɗauke mata ita ta ɗauke mata mahaifinsu kuma bata taɓa nesa da su ba, shine abokinta a yanzu, shene babban ɗa, shine ƙani, shine yaya, shine uba ga ƙannensa, shine ƙawa, dole taji raɗaɗin nesantarsu da zai yi, sai dai bazata iya daƙile hakan ba dan tana matuƙar son shima ya samu cikar burinsa ya kuma cika burin mahaifinsu. Addu'a ta sake masa mai ratsa zuciya cikin danne kuka. “ALLAH ya sa wannan tafiya ta zama alheri a garemu baki ɗaya. Ka tuna da addu’a, ka tuna da asalinka. Idan ka zama soja, ka zama soja mai gaskiya.” Karo na farko Haysam ya kalleta da idanunsa da sukai jaa, murmushi yay mata irin na kwantar da hankali da ƙarfafawa. “Mammah in sha ALLAHU zan yi kamar yadda kike so koma fiye da hakan. Zan zama soja don na kare ƙasata da al'ummar kamar yanda kika zame mana garkuwa bayan rasa iyaye guda biyu, zanyi haƙuri koda banci ba domin wasu suci, zan sadaukar da farin ciki na dan wasu suyi, zanyi komai da ƙarfin zuciya da ƙarfin addu'arki. Zan kiyaye dokin UBANGIJI da biyayya ga umarnin MANZONSA.” “ALLAH yay maka albarka”. Ta faɗa kuka na ƙwace mata. Shima idanunsa sun sake yin jazur sai dai babu hawayen. Ƙannensa ma duk sun masa addu'a. Cikin share hawaye Bilal ya ce Dada kada ka daɗe fa... ka dawo da wuri!” “In sha ALLAHU Bilalu na zan dawo da wuri, kai dai kaimin addu'a”. Yay maganar cike da kulawa yana rungume yaron. Suma sauran duk sai suka matso suka rungume juna, “Ku kula da Mammah, kada ku barta tayi tunani ko damuwa. Kada ku sakata yawan magana ko ɓacin rai. Duk wanda ya dinga mata laifin da zai ɓata ranta babu ruwana da shi kona dawo, sannan bazan masa tsarabar komai ba”. Kawuna suka shiga ɗaga masa. Ya ɗan jajja musu hanci cikin so da jin kewarsu. Sai suka shiga yin dariya ga hawaye. Shima murmushi yay musu mai sanyi, kafin ya miƙe, kallo ɗaya yay Mammah yaga yanda ta duƙar da kai yasan kuka take, sai ya fice da sauri shima nashi idon na tara hawaye...
>>>>>>•<<<<<<<
*_NIGERIAN DEFENCE ACADEMY, KADUNA_*
Haysam ya fito daga motar da jakarsa a kafaɗa, jakar da Mammah ta zuba masa kayan da duk ta tanadar masa, bakinsa da addu'a ya shiga bin tarin sabin ɗaliban dake cike tam da ƙofar gate ɗin tamkar ba safiya ba da kallo. Yaron da aka saba gani cikin damuwar maraici da wahalhalun rayuwa da yawan shiru, yau zuciyarsa cike take da jin daɗin samun cikar buri, da alfahari. Jinsa yake a yau tamkar ya fara wata sabuwar rayuwa, inama Abiy na raye ya gansa a wannan mataki, inama idan ya ɗaga kai ya faɗa domin shi ace kunnensa zasu iya jinsa... A bakin ƙofar gate ɗin akwai jami’an soja dake tsaye. Kowanne sabon ɗalibi sai an bincika jakarsa, an duba sunansa a cikin jerin waɗanda suka samu shiga. Haysam kuwa na cikin ƴan farko-farko da aka fara kira. Dan dai-dai yana tunaninsa akan Abiy aka ambaci cikakken sunan nasa Haysam Abdul-rasheed Shehu. A karo na farko sai zuciyarsa ta buga da ƙarfi, goshinsa ya ɗan tara zufa, amma cikin dakewarsa ya ɗaga kai da girmamawa ya amsa da nufar inda ake buƙatar ganinsa yana ɗaukar matakin soja na farko a rayuwarsa, shekarar farkon balaga dan yanzu yana da 17years a duniya da wasu watanni. A dai-dai nan kuma yay sallama da Malam Sulaiman da yay masa rakkiya. Hannunsa Malam Su ya riƙe cike da so da ƙauna da jin alfaharin cika masa alƙawari, fuskarsa da murmurshi ya furta, “ALLAH ya tsare ka ɗana, banda wasa, banda biyema abokan banza, ka zama jarumin da ƙasa zatai alfahari da kai ba kuka ba”. Kan Haysam a ƙasa cike da girmamawa ya ce, “In sha ALLAHU Malam zakayi alfahari dani kai da su Mammah..” “ALLAH ya tabbatar da hakan Haysam”. Malam Sulaiman ya faɗa yana sakar masa hannu da shafa kansa.....
Haysam na shiga ciki sai duniya ta canza. Cikin nutsuwarsa ya shiga layin ƴan uwansa da wasu sojoji suketa duba su, suna karɓar takardu, suna aika su wurin medical check-up. Ana duba nauyinsu, tsayinsu, tare da basu lambar cadet. Sannan suka bi jerin sabon layin da ake rabawa sababbin ɗalibai uniform da kayan horo. Sai amsar uniform ɗin suke kuwa cike da farin ciki da zumuɗi, sai manyan takalma da sauran abubuwan buƙata na kwanakin farko. Sai da aka kammala musu komai daya dace a wannan lokacin Sannan aka tafi mataki na gaba. Bayan karɓar kaya, an kai su wani babban hall mai ɗauke da gadaje da yawa da zasu iya kai 200 ma. Kowane gado akwai katifa sabuwa fil. Nanfa bakunan wasunsu suka shiga washewar farin ciki. Wasu suna dariya, wasu suna kallon juna da murmushi. Shaƙiyan ciki masu rawar kai suka fara rawa suna ɗaga hannuwa cikin nishaɗi, yayinda wasu suka fara kiɗa da ƙarfen gado wasu cokula da plate da aka raba musu. Dariya suka bama Sojojin da ke kula da su, dan haka suka tsaya suna kallon suna murmushi kawai. Dan basu da zaɓin daya wuce su bar su suyi farin cikin farko kafin a fara horo na gaskiya, a wannan gaɓar idan ma ance suyi wannan nanayen bazasu yin ba. Duk wannan abin da ake Haysam na zaune ne kawai a gefe bakin wani gado yana kallonsu, bai yi waka ba balle rawa, amma murmushin da ke gefen fuskarsa ya tabbatar da shima yana jin irin farin cikin da suke ji. Kai da ka kalla idanunsa kasan akwai tsananin buri amma a zuciyarsa akwai tambayoyi da yawa. Sai faman ayyanawa yake a zuciyarsa (Zan iya jure wannan sabuwar rayuwar kuwa? Yanzu ko mi Mammah take yi da su Ja'afar. Ƙilama Ammar da Mimi sunyi kukan rashin ganin yau bani zan kaisu makarantar allo ba, bani zan musu wankan dare ba, bazamu ci abinci tare ba. Ƙilama suna can sunama Mammah rigimar kuka). Haka dai ya zurfafa a tunani shaƙiyancin ƴan uwansa ɗalibai na yin nesa da kunensa.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 27_
__________________
LADY'S BEAUTY PALACE
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Lace Hijabs Supplements Kayan yara Saloon Kunshi na salatap Dana zane Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko Sari
Zamuyi promo din kayan mu na hijabs da Kuma zuma
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
Whatsapp or call 08169307477
Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)
Instagram Hajara Rabiu
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________