
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 14
.....day, ten days passed and Abdul-Rasheed prepared to return to Kano as soon as his vacation days were over. His hair is at the end of the range and he doesn't need to play with his studies. A'isha cried so much that he felt as if he also congratulated her, and finally he barely persuaded her to leave and leave their hearts full of bitterness. Aisha went back to the wedding with her, and now she only spends the day at her house, but at night, Abdul-Rasheed comes to their house to spend the night. In the morning she returned to her house and at night she went there. She has been bothering herself even more because of his two younger brothers who are almost half an hour away. It doesn't matter to Inna, she only says if we do something wrong. Aisha is very involved in doing homework with Alawiyya, if they go out, Inna forbids them from following them, or if they go to boarding school. Since I said that, you have understood that this is the rule and the law, since the other wives of his aunts don't go out anywhere without a reason, so she relaxed. Since A'isha has been counting the days of Abdul-Rasheed's departure, he has been sleeping for four months. That's when Dad sent him a let
.........Abdul-rasheed bai dawo ba sai bayan sallar isha'i. Yana shigowa Khadijah tai musu sallama ta wuce. Shi kuma ya zauna yana zolayar A'isha akan yau dami-dami tayi da baya nan?. Sai da ta ajiye masa abincin da aka kawo daga gidansu gabanshi sannan ta zauna tana bashi labari cike da farin cikin tabbacin yau ɗin ya mata daɗi. Shima sai yaji nashi farin cikin ya sake girma, da jin damuwar yanda zai tafi ya barta nan da kwanaki kaɗan dan zai koma Kano makaranta. Dole dai ya ture tunanin a ƙarshe ya lallaɓata sukaci abincin tare, daga nan suna hira yaga ta fara hamma yace taje ta kwanta. Shi kuma ya ɗakko kayan karatunsa ya fara nazari. Daga baya shima ya kwanta a nashi gado batare da yau ma yama A'isha komai ba. Kwanakin da suka biyo baya sun cigaba da gudana ne cike da shaƙuwa a tsakanin Abdul-rasheed da A'isha. Domin kuwa cikin hikima irin ta masu ilimi yanata jan ra'ayinta da janta a jiki kamar aboki tana sake sakin jiki da shi. Gayyar yaranta kuwa na anguwa kullum tare da su take yini, a haka suka cika kwanaki goma Abdul-rasheed ya shirya komawa Kano dan kwanakin hutunsa sun ƙare. Gashi yana ƙarshen zango baya buƙatar wasa da karatunsa. A'isha taci kuka sosai har ya dinga jin kamar shima ya tayata, daga ƙarshe dai da ƙyar ya lallasheta ya tafi ya barta zukatansu cike da ɗaci. A'isha ta koma sukuku da ita, kuma yanzu tana yini ne kawai a gidanta, amma da daddare can gidan su Abdul-rasheed take zuwa ta kwana. Da safe sai ta dawo gidanta sai kuma dare taje can. Tun tana tsangwamar kanta harta saki jiki saboda ƙannensa biyu da suke kusan sa'anni ƴammata. Ga Inna ba ruwanta, faɗanta kawai dai idan anyi ba daidai ba. Sosai A'isha take saka hannu suyi aikin gida tare da su Alawiyya, idan zasu fita ne dai Inna ke hanata binsu, ko in zasu tafi makarantar allo. Tun abin na sakata kuka harta fahimci hakan fa shine ƙa'ida da doka, tunda sauran matan yayunsa bataga suna fita ko'ina ba sai da dalili, dan haka sai ta saki jiki. Tun A'isha na ƙirga kwanakin tafiyar Abdul-rasheed harta bari, kwanci tashi sai gashi da watanni har huɗu. A lokacin ne Baba ya aika masa wasiƙar tunatarwar yazo gida ko kwana biyu yayi, koya manta yana da iyali ne yanzu. Ya kamata ya dinga sara yana duban bakin gatari. Wasiƙa ta isa ga Abdul-rasheed. Kuma ya gamsu da tunatarwar Baba, sai dai baya son zuwa gida ne saboda kaucewa abinda zuciyarsa da gangar jikinsa ke raya masa akan A'isha. Yana son ya bata damar ƙara fahimtar kanta har gaɓar kammala karatunsa daya rage watanni biyu rak. Dan haka ya maida saƙon wasiƙar baba da amsar ban haƙuri data neman uzirin bashi damar kaiwa zuwa watannin da suka rage masa. Acewarsa karatunsu ya ɗauki zafi a yanzu kuma suna gab da fara jarabawa. Bayan an kawo wa baba amsar Abdul-rasheed dole ya haƙura ya bishi da addu'a, dan ya fahimci manufarshi kai tsaye. Haka kuwa aka ci gaba da rarrafawa har watanni biyun Abdul-rasheed na karatu suka cika. A lokacin ya shirya baro Kanon dabo zuwa Bauchin Yakubu gida. Sun sha kuka sun sha ruɗani shi da amini kuma ɗan uwa Nasiru da ogansa Yaya Zubairu. Daga ƙarshe dai dole suka sallamawa tunda mai rabawa ta raba, sai dai ance sabo turken wawa ne, a wannan gaɓar wannan turke ne kafe da zukatan su Abdul-rasheed. Yaje yayma Innar A'isha sallama, dan dama yana zuwa duk kwanakin mako da yake yi a anguwar kullum safiya gaisheta, hakan yasa abincinsa daga gidansu A'isha kullum kwano ukun nan babu fashi a kwanakin ƙarshen makon. Shiko baya gajiya da godiya da yin kuma cefane ya kai ma Inna. Ya kuma yi ƙoƙari ya lallaɓata ta yarda ya saka Bashir da Tasi'u a makarantar primary da ƴaƴan gidan su Nasiru ne kawai ke zuwa a layin. Inna ta haɗa tsaraba mai yawa sai ƴar sana'ar da amarya kanyi irinta ƙulle-ƙullen kayan lwaɗayi. Haka Nasiru yay masa rakkiya har tasha tare da su Bashir, basu dawo gida ba sai da motar su Abdul-rasheed ɗin ta ɗaga zuwa Bauchi....
_________________
BAUCHI
A bisa al'adar wannan zamanin zaman mace babu ƙunshi a ƙafa da hannu kamar wani zunubi ne. Kahama kitso ƙa'idane wani na tsufa kina sake wani akai-akai. Wannan wajibi ne ga mace mai aure a kowane yare na arewacin ƙasar. Dan haka koda Abdul-rasheed baya nan a duk sanda ya dace A'isha tayi ƙunshi da kitso Inna na sakata tsefe kai cikin matan yayun Abdul-rasheed wata tai mata kitso. Hakama tana yin ƙunshi tare da su dan sukan shirya yinsa ne a tare. Dan haka da wahala ka samu A'isha babu irin wannan tsaftar. Kamar dai yau a jiya Inna ta sakata yin sabon kitso, inda Magajiya ta zuba mata ƙanana masu ƙyau harda na gaba sak dai irin na barebari. Yau kuma suka shirya yin lalle a ƙafafunsu tun safe. Haka kuwa suka sakashi har yamma yana jikinsu. Sai la'asar suka kunce, A'isha batai niyyar zuwa gidanta ba yau sam dan haka ta ɓararraje suna hira da sauran facalolinta dan a gidan ɗaya daga cikinsu akai ƙunshin. A dai-dai kuma wannan lokaci Abdul-rasheed ya iso. A gidansu ya sauka kamar yanda ya saba, dan haka Inna ta tareshi tarba mai girma. Cike da hikima irin ta manya yana zaman gaisawa da Baba ta aika akai mata kiran babbar surukarta, a soro suka tsaya, bayan ta gaisheta ta shaida mata Abdul-rasheed ne ya dawo, maza su saka A'isha ta koma gida ta gyara jikinta. Sannan su taimaka mata sauri-sauri su tayata gyara gidan shima kafin ya iso. Ta amsa da ladabi ta fice. Tana zuwa ta gwargwaɗama sauran ƴan uwanta dan haka suka tasa A'isha a gaba. Tana son jin ba'asi babu wanda ya bayyana mata, sai dai sunce umarnin Inna ne hakan. Girman suruka koda matsayin kishiyar uwar miji take girma gareshi a wannan lokacin, dan haka A'isha bata sake tari ba ta bisu, dan yanda Innarta zatai mata magana ko bata umarni ta bi haka Inna itama zatayi tabi dole dan matsayin uwar miji take a garesu. Dan danan suka taimaka mata da dukkan abinda ya dace, ruwan wankanta kanshi yasha turare kala-kala a cikinsa. Hakama ɗakin suna kammala gyara mata suka baɗesa da turaren wuta. Basu taɓa mata gadon miji ba suka barta ta gyara da kanta suka fice zuwa nasu gidajen lokacin anata kiraye-kirayen sallar magriba. Hakan yasa cike da mamaki A'isha ta fara kici-kicin gyaran baban gado dake matsayin na mijinta Abdul-rasheed, zuciyarta kuwa cike da wasi-wasi akan mike faruwa ne wai? Gashi kafin su tafi sai da sukai mata kashedi akan ta zauna a gida karta ce zata biyosu ta jira. Bata fahimci mi suke nufi ba sai da Abdul-rasheed yay sallama yara biye da shi da kaya niƙi-niƙi. Ita jitai ma kamar ta firgita, dan haka ta fito wuff da fitilar ƙwai a hannu domin haskawa, hakan ya bama Abdul-rasheed damar ganinta fes a cikin sirritaccen hasken mai cike da ƙayatar da mai kallo. Tayi ƙyau cikin atamfa mai tabarma sabon ɗinki ne daga cikin kayan lefenta da sai yau ta saka. Turus ta tsaya tana kallonsa itama kamar yanda yake kallonta, sai dai shi nashi kallon na shauƙi ne da kewa matsananciya. Itako na mamaki ne da ruɗanin bazatar tasa. Sun zubama juna ido harna fin minti ɗaya har yaran nan suka ajiye kayan suka fice abinsu suka barsu dan saurin komawa suci tsarabar daya bayar a basu a can wajen Inna. Sai da aka kabbara salla ne hankalin Abdul-rasheed ya dawo jikinsa. Numfashi ya furzar a hankali yana janye idanunsa daga cikin na A'isha da suka tara ƙwalla, cike da sanyin murya ya furta, “Bani buta kada na rasa salla gaba ɗaya”. Sukuku ta koma ciki kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta ɗakko masa butarsa ta ƙarfe, tazo gabansa ta durƙusa ta miƙa masa. Amsa yay yana kallonta shi dai, dan harga ALLAH sai ya ga ta ƙara masa cika a ido da girma, shi yana can tunaninta na hanashi sukuni da isasshen barci, itako da alama ko'a jikinta daɗinta take ci, ƙaramin murmushi yayi kawai, kafin ya maida hankali yayi alwalar ya fice gudu-gudu sauri-sauri dan har anyi raka'ar farko ma. Sauƙin ma massalacin kusa ne da su gab. Koda aka idar da magriba bai dawo ba, A'isha ma data idar da tata sallar tana zaune shiru, tama rasa miya kamata tayi ita kam, a haka yaro yayi sallama, ta amsa tana miƙewa hannunta riƙe da fitila. Tire ne da kwanika akan yaron, dan haka ta ajiye fitilar tana faɗin, “A'a Salihu kayan nan basu maka nauyi ba?”. “A'a basuyi ba. Inna ce tace na kawo miki. Tace tana gaisheki sai da safe”. “To na gode Salihu, amma kace mata ai yanzu ma zan taho gidan nima”. Shi dai Salihu ya amsa da to ya fice abinsa. Itama dai ta ɗauki turen ta shige da shi ciki. Tuwo ne da miya sai fura damammiya a kwanon sha, ta tabbatar furan Baba ne aka ɗibo, dan Abdul-rasheed akwai son fura kamar Baban. Baki ta kuskure tai sallar isha'i dan an fara. Bayan ta idar ta miƙe, tabarma dake matsayin ta miji dake can saman babban gadon a maƙale ta taka ƙaramin gado zata zaro. Sai dai hannunta yaƙi ya kai, dan dole sai ta hau gadon zaifi mata daɗi amma bata son hawa ta saɓa a ganinta laifi ne. A yanda take ta amsa masa sallamar da yayi, ta cigaba da ɗiɗɗishenta na son ɗakko tabarmar. Inda take ya ƙaraso, ya tsaya a bayanta gab sosai, cike da kulawa da tausasawa ya ce, “Mizaki ɗauka haka Matar Abdul-rasheed?”. Da yanayin shagwaɓa na wahalar da take sha ta ce, “Tabarman can mana, amma kamar ance ta gudu min na kasa na jawo”. Hannayensa ya harɗe a ƙirji yana kallonta, ya ce, “To banda abin A'ishatu ai ta miki nisa ne, ga hanya mai sauƙi ki taka gado ki hau ki ɗakko kawai, tanan inda kike baƙya tsoron ma ki faɗo”. “A'a zan iya a haka, kuma fa na faɗa maka tun ranar hawan gadon nan babu ƙyau”. “Okay na manta haka ne fa, amma ai nima nace ki hau na yafe miki tun a waccan ranar ko. Kinga nidai sakko na tayaki ni”. Yay maganar yana kamata cak ya sauke ƙasa. Kafin ta ankara ya sakata a jikinsa ya rungume...........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._