
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 1
.....everyone was speechless in the first session of the court and the decision was made. They sentenced Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi to twenty-five years in prison, and Imran Abbas to five years. He said this matter did not only shake the descendants of Mammah and their house Imran, the entire country was shaken, as soon as the young nationalists and other groups started a peaceful protest because they did not accept the sentence given to Zak-Shadow and Imran. This protest brought chaos later, and the chaos was not caused by anyone but the dark group who faced being asked to undo their victory. Strict security measures have been put in place to force the young people to return home and they have gone back to saying what they say in the media, with a prayer asking the Lord to take it, then a warning to the politicians that GOD will take care of the next election, everyone who is intelligent should look at what happened with their own eyes and know that this decision is only political... In Mammah's side, there is no talking. This time, despite all her strength and ability to suppress things, she had to go to bed for treatment. It was almost two months before GOD got sick, but th
KIDA A RUWA
Book 2
1
.........2016
Shekaru uku da wasu watanni kenan da kama Zak-Shadow. Abubuwa da yawa sun faru marasa daɗi harma da masu daɗin ta wani fannin. Sai dai rinjayen marasa daɗin ya danne masu daɗin ta yanda har idanu basa ganinsu. Misalta kalar tashin hankalin da su Mammah suka shiga a wancan lokacin ɓata baki ne. Babu irin shigi da ficin da Imran baiyi ba amma ko damar ganin Zak-Shadow an hana musu har na tsawon watanni. Daga baya shima Imran ɗin suka kama shi. A farko manyan sojoji da yawa sun tsaya akan case ɗin da son ganin abubuwa sun dai-daita Zak-Shadow da Imran sun fito, sai dai daga baya sai suka fara janye jikinsu baya aka bar General Yusuf kawai da gwagwarmaya. Dan har cikin ransa ƙauna ɗaya tak yake ma Zak-Shadow da Imran. Faɗi tashin COAS yasa aka fara shirin miƙa case ɗin kotu, a lokacin Zak-Shadow nada watanni tara a rufe, kuma har lokacin ba'a taɓa barin kowa ya gansa ba sai masu tsaronsa sai shi COAS ɗin kawai. Kasancewar al'amarin shiri ne na musamman da kowa ya rasa bakin zarensa a zaman farko na kotun aka yanke hukunci. Sun yanke ma Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi hukunci zaman gidan yari na shekara ashirin da biyar, shi kuma Imran Abbas shekara biyar. Ya rabbi wannan al'amari ba zuri'ar Mammah da gidan su Imran kawai ya girgiza ba, ƙasa gaba ɗaya ce ta girgiza, dan a take matasa masu kishin ƙasa da wasu kungiyoyi suka fara zanga-zangar lumana akan basu amince da hukuncin da aka yankema Zak-Shadow da Imran ba. Wannan zanga-zanga taso kawo hargitsi daga baya, hargitsin kuma ba kowa ne ya haddasa shi ba sai ƙungiyar duhu da suka fuskanci ana neman warware musu nasararsu. An saka matakan tsaro masu tsauri daya tilasta matasan komawa gida aka koma ka-ce-na-ce a media kawai, tare da addu'ar neman ɗauki ga UBANGIJI, Sai gargaɗi ga ƴan siyasa akan ALLAH ya kaimu zaɓe na gaba, dan duk mai hankali ya kalli abinda ya farun da idon basira yasan lallai hukuncin nan na siyasa ne kawai...
A ɓangaren Mammah ba'a magana. A wannan karon duk dauriyarta da iya danne abu sai da ta kwanta jiyya, kusan watanta biyu kafin ALLAH ya bata lafiya, sai dai ciwon hawan jini ya riga yayi tasiri a gareta. Hakama ƙannensa da sukafi kowa ɗaga hankalinsu, sai da takai har su Ma'aruff suka ce sun fasa aurensu da ake gaf da yi, amma Mammah tace bata yarda ba bata amince ba. Dan haka tana samun lafiya aka hau shirye-shiryen bikinsu, dama gininsu tun kafin a kama Imran ya dawo da shi anan cikin gidan, bayan an kama shi kuma Uncle Nasiru ya tsaya akai aka cigaba bisa shawarar Mammah. Satin Mammah ɗaya da baro asibiti, da yay daidai da sati biyu ciff da yankema su Dada hukunci akai bikin Ma'aruff da Ja'afar, sai dai bikin baiyi wani armashi ba, dan aure kawai aka ɗaura amare suka tare. Idan ka cire yara irinsu Nimrah dake shagalinsu kowa ƙarfin hali kawai yake, har dai akai aka tashi lafiya...
Kasancewar ba wani taro akai sosai ba gidan shiru babu hayaniya, su Gwaggo Khadijah ne dama kawai sai wasu tsiraru daga mutanen Kano suka zo. Tun bayan sallar isha'i aka maida amare sashensu, dan tunda aka kawosu anan sashen Mammah aka ajiye su sai yau da biki ya tashi. Ganin har ƙarfe goma babu Ma'aruff babu Ja'afar Mammah tai kiran Bilal tana tambayarsa su. Amsa ya bata da, “Mammah gasu nan fa a ɗakinsu. Da alama kuma basu da niyyar tafiya sashensu. Wanka ma da ƙyar na samu sukayi suka canja kaya”. Murmurshi Mammah tayi tana ɗan girgiza kai cikin danne damuwa, “Kaga basu wayar”. Da to ya amsa mata, yana nufar ɗakin su Yaya Ma'aruff ɗin dake jikin nasu shi da Ammar. Sai da yay knocking ƙofar suka bashi izinin shiga sannan ya shiga da sallama. Mammah dake saurarensa tace, “Saka wayar a amsa kuwwa”. Sakawar yay kamar yanda ta bashi umarni, ya sanar mata ya saka. Kai tsaye ta furta, “Ma'aruff! Ja'afar!”. A tare suka amsa mata, dan suna zaune ne a bakin gado su duka, “Yanzu kuna ganin abinda kuke shirin yi dai-dai ne kenan?. Karku manta yanzu suna da hakki a kanku, ɗaya kuka tauye sai ALLAH ya tambaye ku. Abinda kukeyi bashi zai dawo da Imran da Muhammad cikinmu ba, miyasa bazamu karɓi ƙaddara muyi haƙuri bane. Addu'a itace maganin komai. Dan haka ina baku umarnin tashi ku wuce Bilal da Ammar su raka ku sai da safe...” Ma'aruff da idonsa ya kaɗe murya a cinkushe ya ce, “Amma Mammah.....” “Bana son jin komai, ku tashi ku wuce kawai. Bilal kaje kai da Ammar ku rakasu.” “To Mammah”. Bilal ya amsa yana share hawayen da suka cika masa ido. Dan Ja'afar ma kuka yake. Haka shima Ma'aruff ɗin gefe ya kauda kansa ya share nashi. Babu abinda ke cizon zukatansu sai tuna yanda suka shirya wannan ranar da ɗokin zuwanta tare da Dadansu da Yaya Imran, amma sai gashi yau anyi komai babu su, kuma suna raye, suna a gari ɗaya amma ƙaddara tai musu shamaki. Ba yanda suka iya dole sukabi umarnin Mammah, dama sunyi wanka, suka shirya cikin kayan barci iri ɗaya dan basa wani buƙatar wasu kaya saɓanin waɗan nan. Ammar da gaba ɗaya baida isashiyar lafiya tunda aka yanke hukuncin nan nasu Dada da ƙyar ya iya binsu saboda umarnin Mammah. Ma'aruff shine babba, shi suka fara takawa har falon sashensa daya ƙawatu da kayan more rayuwa, babu abinda ke tashi sai ƙamshin sabbin kaya dana turare da sabon fenti. A ƙofar bedroom ɗin da yake da tabbacin Lailah na ciki yay knocking, bai jira amsarta ba ya buɗe kaɗan ya leƙa. Hangota can a kan katafaren gadon da aka saka mata ya sashi ɗan sauke numfashi, kafin ya buɗe ƙofar gaba ɗaya yana sallama. Bai damu data amsa ba, ya juyo yana kallon su Ja'afar da ke tsaye. Nuni yay musu su shigo, dan haka suma duk sukai sallama ya amsa sannan suka shiga. A bakin gadon ya zauna kusa da ita, su kuma suka zauna a sofa ɗin ɗakin su duka. Duk da sun girmeta, matsayin ƙanwa take ma a garesu, dan uwa ɗaya uba ɗaya take da Imran, itace autarsu ma. Amma a tare matsayin matar Yayansu a yau suka fara gaisheta. Da sauri ta girgiza kanta tana share hawaye batare data buɗe fuskarta ba. Dan itama dai irin ciwon dake zuciyarsu shine a tata zuciyar. Cikin rawar murya ta gaishesu batare da ta amsa gaisuwar da su sukai mata ba. Dan kai tsaye ta ce, “Yaya ina yininku”. Amsa mata sukai da kulawa, kafin Ja'afar yay mata gajeruwar nasiha da addu'a. Shima Bilal yay mata a taƙaice. Ammar dai kasa cewa komai yayi sai addu'a da fatan zaman lafiya. Cikin abinda bai fi mintuna goma ba suka kammala suka fito zuwa sashen Ja'afar...
A sashen Ja'afar ɗin ma dai shine yay musu jagora har bedroom ɗin Shariffat. Itama dai komai na funichars ɗinta irin na Lailah ne, kala ce kowa wadda yake so aka saka masa. Ga ƙanshin turare na tashi kamar dai sashen Lailah ɗin. Ita kam a kwance suka sameta, sai da Ja'afar ɗin yay sallama sannan ta tashi zaune, fuskarta na lulluɓe itama cikin lifaya. Suna zama ta fara gaishesu. Suka amsa mata da kulawa. Yanzu kam Bilal ne yay mata nasiha ita, Ammar yay addu'a. Anan ma basu wuce mintun goman ba sukai musu sallama suka fito...
Kamar haɗin baki su Ja'afar na fita a sashen Ma'aruff Lailah ta saki kukan da take riƙewa. Haka ma su Bilal na fita Shariffat ta fashe da kuka. Dan su dukansu auren nan tamkar fami ya zama ga damuwar family's ɗin nan nasu guda uku. Sai dai babu yanda aka iya da ƙaddara. Ma'aruff ya haɗiye abu mai nauyi daya tsaya masa a maƙoshi, tare da matsawa kusa da Lailah ya jawota jikinsa a karo na farko a rayuwarsu ya rungumeta. Sai kawai ta sake sakar masa kukan da yafi na farko. Murmurshi yayi mai ciwo. Kafin ya fara magana cikin ɗacin murya sai dai tana fita da sanyin sauti mai tafiya da lallashi... “Yau rana ce ta farin ciki da ɗunbin tarihi a garemu, rana ce da iyayenmu sukaci buri a kanta damu kammu. Sai dai gata ta cika babu waɗanda mukema kallon iyaye na biyu a tare damu. Lailaty ƙaddara batai mana adalci ba, miyasa zata ɓoye mana su a lokacin da mukafi buƙatar su...?”
“Saboda makirci da zaluncin azzalumai ne Yaya Man. Kuma bazamu yafe musu ba..” “Tabbas bazamu yafe musu ba Lailaty, za kuma mu cigaba da gayama UBANGIJI kukanmu da kai ƙararsu gareshi. Dan sun cutar damu.” hawayen da yake riƙewa suka shiga gangarowa suna sauka akan kafaɗarta. Da sauri ta ɗago tana kallonsa a karo na farko, sai ya kauda kai gefe yana murmurshi. “Bafa kuka nake ba, abu ne ya faɗa min a idona”. Hannunta mai ɗauke da lallen da daƙyar suka yarda akai musu ita da Shariffa takai saman kyakkyawar fuskarsa mai kama data Ja'afar matuƙa, dan kamanninsu na saka mutane da yawa yarda su Twins ne. Fuskar ta maido saitin tata dan tabbatar da abinda ta gani, sai dai suna haɗa idon ya ɗaga mata gira kaɗan, cikin son kauda mata zargin dama yanayin nasu ya matsar da fuskar sosai gab da tata. Ƙoƙarin komawa baya tayi yay saurin riƙota ya hana hakan, nan ma tai ƙoƙarin kife kanta a kafaɗar tasa ya sake hanawa ta hanyar riƙo fuskar da duka hannayensa biyu, a bazata taji lips ɗinsa kan nata. Sai kawai jikinta ya kama rawa ta daburce, dan abunda batai zato ko tsammani bane daga garesa. Tun tana mutsu-mutsu harta nutsu dan tuni ya mannata da fuskar gadon dole ta sallama. Sai da ya tabbatar ya tabbatar mata da wannan ranar da sun zama ɗaya ta hanyar sumbatarta yanda ya dace kafin ya haƙura. Gaba ɗaya kunya ta sanyata naɗewa a jikinsa tama kasa tashi. Shi ko murmushi kawai yake yana shafa bayanta. Yo banda ALLAH ya rage ma aya zaƙi ai wannan ranar tanadin da sukai mata shi da Ja'afar ɗinsa ba'a magana. Amma ina ƙaddara tace musu bata yarda ba, sai dai kawai ayi wani abun dan sauke haƙƙi da rahamar UBANGIJI mai sassauta zukatan bayi da ikonsa..........✍️
_Alhamdullahi barkanmu da dawowa a littafi na biyu. Duk da dai na barku da jira, Amin afuwa uzuri ne yasa aka samu dogon hutun. Ina fatan kuna cikin ƙoshin lafiya kuma bakuyi fushi ba 😘. Kar ku damu faka-faka ne in dai naga kuna so kuma. Dan in babu kwarin gwiwa daga gareku rubutun bazaiyi gudu ba kamar yanda muke fata. Karna cikaku da surutu kumuje zuwa kawai dan book 2 ɗin nan hummmm ba'a mana, in sha ALLAHU sai ya tashi kanku fiye da yanda kuke tsammani, na tattaro muku tari-tarin abubuwa a cikinsa da sai kun karanta kawai zaku gane abinda nake nufi 😘😘😘💃._