
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 21
.....continue to say, "Tell them. If you neglect to reject me and take my words as a mouthful, then get ready... prepare the game we started without counting the threads of the building of GIZO-GIZO. Tell them. This is the field that they are filling with the preparation for soccer, with the blood that they will soak the ground to make it soft. I will prepare the GAME field, and I will soak the ground with your blood. Instead of playing football, I will tie women's chains on your feet Go around the dance floor. I'm the one who will play this dance. I understand that this message will be the first one from here. Give birth to me with this pride and write my words and put them on the top of the rock. He pushed the chair and got up slowly, letting go of the rest of the country like a king standing up from his throne. He looked at his watch for a few seconds and once again let out a smile with many meanings and then.....
21
........Tunaninsa ya katse sakamakon cigaban kalaman Zak-Shadow masu zafi da sanya zuciya raɗaɗi. “Idan kaje ka sanar da iyayen gidanka saƙo daga ni Haysam Abdul-rasheed Shehu. Ku na mallakar gwamnati, amma ba kwa mallakar ƘASA. Ku na mallakar masu muƙami, amma ba kwa mallakar mutanen da suke amsa sunan KASAR. Ka sanar musu. Idan suna tunanin zasu sarrafa ni kamar karnukan su… to su sake tunani tun kafin lokaci ya ƙure musu. Ka faɗa musu. Wannan ba ƙarshen wasan ba bane, farkon rugujewar su ne, domin kuwa yanzu ne za'a FARA WASA na GASKIYA. Ka faɗa musu. Wanda yake da cikakken iko ba ya zuwa ya gaya wa wanda yake tsoro barazana. Domin wannan zuwan naku tabbatar min yay da kun MATSORATA ne, kuma ni abin tsoronku ne. Na ji ƙamshin wannan tsoron naku tun shigowarka nan. Ka faɗa musu. Idan kun kasance da ikon da kuke ikirari… ku kasheni kawai zai fi muku sauƙi da samun cikar burin ku cikin salama” ya ɗan yi dariyar da ta sake tsokano zuciyar bako. Batare da bashi damar cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Ka faɗa musu. In har kukai sakacin ƙin kasheni da ɗaukar zantukana cika baki, to ku shirya… ku shirya wasan da muka fara ba lissafin saƙar zaren ginin gidan GIZO-GIZO ba. Ka faɗa musu. Shi wannan filin da suke cika bakin samarwa domin ƙwallon ƙafa, da jinin da zasu jiƙa ƙasar domin ta tausasa. Ni ne zan samar da filin WASAN, sannan na jiƙa ƙasar da jinin jikinku. A maimakon buga wasan ƙwallo na ɗaura muku sarƙar mata a ƙafafuwa ku zagaye filin da takun RAWAR ƘOROSO. Ka faɗa musu. Ni nake tsara gangar da masu kiɗanta, kuma tabbas in sha ALLAHU sune zasu taka wannan rawar fa. Ka tafi ka faɗa musu. Na gane kun TSORATA. Sannan wannan SAƘON daka kawo zai zama kuskurenku na farko. Na biyun zai biyo bayan fitowata daga nan. Ka faɗa musu. Idan har iyayensu sun haifesu da alfaharin igiyar aure, kamar yanda ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi A'isha da Abdul-rasheed suka haifeni da wannan alfaharin ku rubuta kalamaina ku ajiye da yaƙini a saman dutse. Sannan ku shirya.” Ya turo kujerar ya tashi a hankali yana sakin murmurshin ƙasaita tamkar sarki ya miƙe daga gadon mulkinsa. Ya zubama agogon hannunsa idanu na sakanni tare da sake sakin murmushi mai ma'anoni da yawa sannan ya fara takun dake nuna alamar barin wajen. Da sauri shima baƙon ya kalla agogon nashi mai ɗauke da camara saboda kallon da Zak-Shadow yay ma agogon ya tabbatar ɗayan biyu ne, ko dai ya fahimci camara ɗin ce ko ya tsargu.... Dada da yay takun da bai gaza biyar ba ya tsaya cak, tare da juyowa a hankali, idanunsa suka sauka a kan mutumin. Fuska ta bogi, amma mugunta ta gaskiya.... Murmushi ya sake saki da ɗan taɓe baki. Cikin salon isar da saƙon ƙarshe a inda yake da tabbacin masu aiken na kallonsa yanda ya dace domin idanunsa kam a kan agogon mutumin ya furta, “Ni bana kare gwamnati. Bana kare hukumar soji. Bana kare kujerun ƴan mulkin mallaka. Amma ku sani. Na kare ƙasa. Na kare mutanen ƙasa. Na kare gaskiya duk da ƙarfin ikon UBANGIJI mai IZZA da cikar mulki na gaskiya. Wannan kuma… Shine abinda kuke tsoro. Zan ƙara tabbar muku, idan har kuka bar Haysam Abdul-rasheed Shehu a raye, zai cigaba da tabbatar muku wannan tsoron a cikin ZUKATA. Bance zan iya komai ba, amma bazan taɓa raina kaina a gaban ALADU irin ku ba”. Ya ɗan yi shiru yana murmurshi mai ciwo, dan kowace kalma yana fitar da ita ne daga zuciyarsa kamar takobi mai kaifin gayawa jini ya wuce. Baƙo da zuciyarsa ke dukan uku-uku cike da ƙarfin hali ya ɗan taɓe baki, numfashinsa dake fita da rawa ya fisgo da ƙyar dan neman ƙwace masa yake. A karo na farko ya ji wani abu ya motsa masa a ƙirji, ba tsoro bane kawai, ba kuma bakin ciki bane kawai. Bayyanan nen rauni ne dake tuna masa, shima fa ɗan ƙasa ne tamkar Zak-Shadow, yana da dangi a ciki ba iyalai kawai ba, yana da ƙarfin ikon kiranta tushe ba son tara dukiya da ƙarfin ikon son mulki kawai ba.... Dada daya gama fahimtar raunin nasa dake son bayyana ya juya zai fita abinsa yana murmurshi, sai kuma ya sake tsayawa tare da juyowa a lokaci guda. Da tabbatar wa ya ce, “Ya kamata na sake jaddada muku domin fita hakki. Kar ku barni a nan domin in gani daga shirin shirin ku. Idan kukai wannan sakacin zan zauna in rubuta yadda zan rushe ku daga cikin ɗakin nan da wawancin ku ke sakaku kallonsa keji”. Ya kammala da murya mai sanyi, amma mai ɗauke da tabbataccen iƙirari. “Kuna da duhu. Ni kuma ina da hasken da yake huda duhun nan naku. Saƙo na ƙarshe, duk wanda ya sake zuwa inda nake da saƙon ku, zan bashi amsar da zai maido muku. Sai dai GAWARSA ce zata dawo da amsar da gangar jikinsa ba BABU RUHI....” Ya saki murmushi tare da salute da yatsa ɗaya kacal sannan ya juya abinsa cikin takun nan nasa da wanda basu fahimcesa ba ke kallon na izgili da izza. Ƙofar ya buɗe ya fita ba tare da ko waiwaye ba yabar baƙo da rawar zuciya da jiƙewar gumi, ga shi ya gagara koda motsi a wajen tamkar wanda gangar jikinsa ta mutu ta barshi da fitar numfashi kawai........
<%><%><%><%>
Cike da nutsuwa take haɗa masa abincin karin a gabansa, duk da kuwa tana daga tsaye ne shi a zaune kan ɗaya daga kujerun daning ɗin. Ya zuba mata idanunsa na girma fuskarsa da murmurshi. Sai da ta kammala zata matsa ya riƙo hannunta. Kallonsa tayi itama a karo na farko, sai dai fuskarta ita sam babu walwala alamar akwai abinda ke damunta ko ranta a ɓace yake. “Juwairiyya mike damunki ne wai?”. Yanda yay maganar cikin taushin murya yana sake tsatstsareta da idanu ya sata sunkiyar da kanta. Sai dai batace komai ba. Numfashi ya ja ya fesar tare da sake matsa hannunta cikin nashi, ya buɗe baki zai magana kenan takun fitowar wani daga cikin yaran ya sashi yin shiru yana sakar mata hannun. Itama matsawa tai kaɗan dan mai fitowar har ya bayyana. Ba kowa bane face Abdul-rasheed da suke kira Imam saboda sunan aboki, amini kuma mahaifi gasu Dada da yaci. Imam shine babban ɗanta a gidan, sa'anni suke shi da Mu'azz koma muce ya girmesa da kusan 2years. Yarone nutsatstse yana tsananin kama da Uncle Nasiru, akwai mai bi masa Halimatus'sa'adiyya. Sai Bintu sa'ar su Nimrah, itama dai ƙawarsu ce dan ƙiriniyarsu ɗaya da ita, idan suka haɗu sam basa jin bari musamman idan an samu hutun makaranta sukan haɗu anan ko gidan Mammah ko gidan Daddy Imran. Adam da Sadiq sune ƙananu a gidan, dan Hajiya Zuwairah ta haifesu ne ma kusa-da-kusa sakamakon gwanne data samu, ta haifi Adam da wata uku ta sake samun cikin Sadiq, hakan yasa tsiransu nasu ba yawa.
“Abba ina kwana? Ummu Ina kwana?”. Imam ya faɗa yana mai kaiwa duƙe. Hannu Uncle Nasiru ya miƙa masa alamar suyi musabaha yana murmurshi, yayinda Hajiya Zuwairah ta amsa masa da kulawa. Fuskar Imam da murmurshi ya bama Abban hannu kamar yanda yake masa kullum. Dai-dai lokacin Sadiyya da Bintu ke fitowa suma dan ɗakinsu ɗaya. Abba ya ce, “Abdul-Rasheed kaifa abokina ne ba suruki ba”. Murmurshi Imam yayi kamar yanda ya saba a duk sanda Abban nasu ya faɗi haka. Hakama Hajiya Zuwairah na tayashi. Imam na kaiwa zaune a kujera shima su Bintu suka ƙaraso dining ɗin, cikin girmamawa suka gaida Abban sannan Ummu da Yaya Imam. Duk sun amsa musu da kulawa, Ummu ta kalli Sadiyya tana faɗin, “Halimatu taso min su Adam suzo suyi kari, dan yanzu haka ma basu tashi ba balle batun tafiya Tahafiz, ni narasa miyasa kukafi ɗaukar tafiya boko da muhimmanci a rayuwarku fiye da islamiyya”. Sadiyya data zama budurwa sosai tai ƴar dariya da faɗin, “Ummu itama islamiyya muna so ALLAH, baga Yaya Imam nan ba har jami'a fannin Islamic ya zaɓa”. “To ai shi dama yana son karatun addini ba irinku ba. Dan magajin mai sunan nashi ne da Haysam.” Hajiya Zuwairah ta bata amsa. Murmurshi Uncle Nasiru yayi, zuciyarsa na tuno masa amininsa kuma ɗan uwa Abdul-rasheed, tare da jin raunin zuciya na gagara taka kowacce irin rawa akan al'amarin babban ɗa na ƙwarai irin Haysam. KIƊA A RUWA 2