
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 22
.....she was a fool who smiled and didn't say anything like this, and then she took a breath and calmly said, "Jiddah's father was talking about yesterday when you didn't listen to Jiddah. After all, you and I both know what Ismat said. Now son of GOD, you let sadness force you to leave these children in the trap of tragedy? Do you hear what is happening; do you think that one day their mother will not be able to overcome them, especially Nabeeha who is carrying I know Nabeeha is a criminal for you, her son did not have her husband's permission to move to another country after being worried about her husband's condition, but what we need to see is whether she is guilty of a part in it. Are they not the ones who chose the kind of life they are in? They are not children, even Ismat, who is considered unmarried, but they follow their mother's ignorance and love for the world. "That's right, but what we have to look at now are the children on us...
22
.........“Wlhy Abba zasu aika kada ka amince da daɗin bakinta. Idan ba haka ba nima sai dai a maida ni makarantar su Asma'u ai ƙawaye basu ƙawaye ba”. Caraf Adam yace, “Muma haka Abba”. Dariya kowa ya sanya. Abba ya shafa kan Adam da Sadiq. “Kenan dai na gane a gidan nan kowa yana jealous da Mamana kawai”. “A da alama kam”. Cewar Ummu tana murmushi. Itako Bintu tayi kicin-kicin da fuska alamar jin haushi. Sai da Ummu ta lallasheta sannan ta yarda ta zuba abinci. Daga haka suka nutsu suka fara karyawa babu mai magana. Sai da suka kammala kowa ya miƙe dan zuwa yay shirin Tahafiz har Imam. A lokacin ne Uncle Nasiru ya sake kallon Hajiya Zuwairah dake gyara gurin duk da su Bintu duk sun kwashe kwanikan sun kai kitchen. “Zamu iya magana yanzu?”. Kallonsa ta ɗanyi, sai kuma ta tura baki kama ƴar yarinya. Dariya yayi yana haɗe hannayensa da faɗin, “To ni dai duk ma laifin da nayi ayi haƙuri ai min afuwa. Amma dan ALLAH a sanar min damuwa kada zuciyata ta sake kumbura.” Kanta ta sunkuyar kawai batare da tayi murmushi data saba yi ba a duk sanda yay irin wannan maganar, sai kuma ta ɗan sauke numfashi cike da nutsuwa ta ce, “Abban Jiddah akan maganar jiya da kaƙi sauraren Jiddah akai ne. Bayan kuma ni da kai duk munji abinda Ismat ta faɗa fa. Yanzu dan ALLAH sai ka bari ɓacin rai ya rinjayeka barin yaran nan a cikin tarkon musiba? Kana jin fa abinda ke faruwa; a tunaninka watarana mahaifiyarsu bazata ci galaba akansu ba musamman ma Nabeeha dake ɗauke da igiyoyin aure a kanta! Nasan Nabeeha mai laifi ce a gareka, dan babu izninka babu na mijinta ta koma wata ƙasa da zama bayan ana cikin damuwa da halin da mijinta ke ciki, amma abinda zamu kalla ko tana da laifi wani kaso ne a ciki Hajiya Hasiba nada wani, saboda tana da tasiri ƙwarai da gaske akan al'amarin yarannan idan ka cire Jiddah da ALLAH yay saurin fargarwa...” Cikin ɗacin murya da sauyawar idanun da ɓacewar murmushin kan fuskarsa ya ce, “Ya kike so nayi Juwairiyya? Shin basu ne suka zaɓi irin rayuwar ba shiyyasa suke ciki? Ai su duka ba yara bane har Ismat ɗin da ake ganin batai aure ba, amma suke biyewa gafalar uwarsu da son duniya ta rufema idanu ko”. “Hakane, amma abinda zamu duba har yanzu su yara ne akanmu. Sannan mata ne. Mufa mata a kowace sigar rayuwa a karkacen nan muke tamkar haƙarƙari. Shekaru basa saka mu canja ko ilimi. Sai wanda UBANGIJI yaso ya gane kawai daga cikinmu. Mu godema ALLAH da yarannan basu tasirantu da huɗubarta ba ma har suka fahimta illar al'amarin. Dan wlhy UBANGIJI ne kawai ke riƙe da igiyoyin auren Nabeeha saboda Haysam mutumin kirki ne, in sha ALLAHU ALLAH bazai haɗa masa zafi biyu a lokaci guda ba. Dan ALLAH kayi wani abu kodan Haysam, saboda koba komai da saka hannunka ya auri Nabeeha, sannan yana sonta”. “Hummm Juwairiyya....” “Dan ALLAH karka ce A'a Abban Jiddah”. Tai maganar cikin katse masa hanzari. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kawai. Tare da faɗin, “Shike nan zan duba. Amma ki sani Adeel yaro ne mai dauɗar duniya a hannu, sannan ya fito daga babbar zuri'ar da yake da ƙarfin aji ako ina a duniya musamman ma ƙasashenmu na Afirika. Barowarsu ƙasar nan zai zama babban al'amari. Amma zan gwada wata hanya idan za'a dace.” “ALLAH yasa a dace, dan duk ƙarfinsa bai kai na UBANGIJI ba ai. Darajar auren dake kan Nabeeha ALLAH zai hanashi dukkan nasara. Itama ALLAH ya shiryar da ita ta gane halakar da take neman jefa yarannan da kanta.” “HUmmm”. Kawai Uncle Nasiru yace, itama sai ta saki zancen ta ɗakko na batun zuwa sake duba Aunty Mimi mai haihuwa duk da kuwa randa ta haihu taje. Amma a matsayinta na kamar uwa koda Mammah na nan dama ita ya kamata ta yi abinda uwa zatayin, saboda ita da Mammah suna jin kansu kamar ya da ƙanwa uwa ɗaya uba ɗaya. Kamar yanda Uncle Nasiru ke ɗaukar Mammah ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗayan. Bai hanata ba, shima ya miƙe yana faɗin zai shirya dan yau yana da ganawa da sanata Yusuf Shu'aibu Tafida tsohon janar. ƘIDA A RUWA 2