Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 23

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 23

..... he was so shocked by what happened that he could hardly suppress it while he was recovering. They caught Mammah in the middle of the car. When she entered, Ammar entered as well. Seeing that Uncle Tasi'un did not enter, Mammah told him to talk to him to enter. They looked at her as if they were going to cry. But the look she gave them of warning made my uncle Jaafar go out and talk to him. Sum-sum like a hypocrite went near her and they put him and Ammar in the middle... They arrived at the house which was quiet because all of them were in school. They are the only workers except Aunty Shariffa and Aunty Lailah and her brother who did not go to the maternity hospital because of Mammah's return. Hasalima themselves went into the kitchen to make her the food that they knew she loved and loved. The workers who are also happy with her return, thank them with small works. From Aunty Shariffa to Aunty Lailah every struggle has a small pregnancy, a child in the power of ALLAH just like how they gave birth to Abees with theirs Afrah and Ayyan, this pregnancy is not far away. But Aunty Lailah was the first to get it before Shariffa. So her son is more prominent and can be seen. Mu'azz

Standalone post1,668 words

23

.........A wannan rana ƙarfe sha biyu na rana jirgin su Mammah ya sauka, tare take da Ammar ɗinta sai ƙaninta Tasi'u da Ammar ke kira Uncle. A tsakkiya suka sakata har inda motoci suke. Aiko cikin sa'a sukai arba da tagwaye biyu Yaya Ma'aruff da Ja'afar da suka zo ɗaukarsu da kansu. Sai dai me suna yunƙurowa a tare suka koma suka ƙame kamar gunkinaye idanunsu akan Uncle Tasi'un. Dan duk da suma suna yara sosai ya aikata abinda ya aikata hakan bai sa sun mance wannan fuskar tasa ba. Dan bayan mahaifin Biebah shine mutum na biyu daya bar musu tabo a zuciya na zahiri. Abinda dangin mahaifinsu suka aikata duk a labari suka sanshi, a labarin ma ba komai ba daga bakin Mammah ko Dadansu. Gwaggo Alawiyya ce ta gaya musu komai. Ganin yanda sukai ɗin ya saka Mammah cikin dakewa furta, “Oh bakwa farin ciki da ni na koma kenan ko?”. Jikinsu ne yay sanyi, cikin dauriya da danne zukata suka nufota, batare da ko kallon Uncle ɗin nasu sun sake yi ba suka rungumeta ita da Ammar suka manta da shi. Ammar daya tsargu da abinda ya farun da ƙyar ya iya dannewa yana murmurshi. Haka suka kama Mammah a tsakkiya har mota. Sai da ta shiga suma suka shiga Ammar ya shiga, ganin Uncle Tasi'un bai shigo ba Mammah tace su masa magana ya shigo. Kallonta sukai kamar zasu fasa kuka. Amma kallon da itama tai musu na gargaɗi ya sasu risinar da kawuna Ja'afar ya fita yay masa magana. Sum-sum kamar munafuki ya shiga kusa da ita suka sakata a tsakiya shi da Ammar......

Sun iso gida da yake shiru kasancewar basawan cikinsu duk ana makaranta. Masu aiki ne kawai sai Aunty Shariffa da Aunty Lailah da yay basu je gidan haihuwa ba saboda dawowar Mammah. Hasalima da kansu suka shiga kicin yi mata abincin da suka san tafi so da ƙauna. Masu aiki da suma ke farin ciki da dawowarta na tayasu da ƙananun ayyuka. Daga Aunty Shariffa har Aunty Lailah kowace fama take da ƙaramin ciki, dan cikin ikon ALLAH kamar yanda sukai haihuwar su Abees a tare da tasu Afrah da Ayyan haka wannan cikin ma basu da nisa a samu. Sai dai Aunty Lailah ce ta fara samu kafin Shariffa. Dan haka nata yafi fitowa sosai har ana iya gani. Mu'azz ya fita akan batun karatunsa dan Imam ne yazo har gida suka fita a mashin ɗinsa. Wannan ya ƙara haifar ma da gidan shiru. Motar su Mammah na gama tsayawa Lailah da Shariffa suka fito cike da ɗoki da farin ciki dan Mammah uwa ce a garesu ba uwar miji ba. Itama fuskata ƙawace da murmushi ta fito da taimakon Ammar. A tare ta kamosu jikinta ta rungume tana mai jin farin cikin ganinsu da sanya musu albarka. Yayinda suma suka zame suka zube cike da girmamawa suna mata barka da dawowa. Ta amsa musu da kulawa tana kamasu ta miƙar. Cike da tsokana Ammar ya ce, “Wato kunga Mamanku ni in ma na ɓata a can babu ruwanku ko Auntys?”. Yanda yay maganar yana cika baki da iska har su Ma'aruff dake faman haɗe fuska saboda Uncle Tasi'u Sai da suka dara. Suma cike da tsokana sukace, “Mu mun isa muso kawun yara ya ɓata. Ai sai suyi mana bore suma Yaya Ammar”. “Ato naga ba'a wani ji dani ne sai Mammah kawai”. “To ayi haƙuri, kasan rashin ta ya maida mu kamar marayu a gidan cike muke da ƙaguwar son ganinta. Kaima bari kaga ƴaƴanka su dawo duk kanka zasuyi”. “Ai shiyyasa ma ban damun ba. Dan da kaina zanje na ɗakkosu a schools”. Duk hirar da suke zugawa Uncle Tasi'u na kallonsu ne kawai cikin damuwar kallon banzar da su Ja'afar ke masa a kaikaice. Su ko su Lailah basu lura da shi ba sai daga baya. Kamaninsa da Mammah dake a bayyane ya sakasu kasa jurewa suka bishi da kallon sakanni. Sai kuma suka duƙar da kawuna cikin ƙaulani da rashin tabbaci suka shiga masa barka da zuwa. A karo na farko yaɗan sauke ajiyar zuciya. Dan koba komai girmamawar tasu ta ɗan sakashi jin sanyi a ransa. Ya amsa musu da kulawa shima. Mammah ta katse su da faɗin, “Kumuje ciki kun san fa ni bana jurar tsaiwa”. Da to suka amsa mata suna sakata a tsakkiya, dai-dai nan kuma maigadi da sabon driver suka iso wajen cike da girmamawa suka duƙa har ƙasa suna gaida Mammah. Tabbas Mammah zata iya haihuwarsu idan muka musalta da yanayin auren da na ƙarancin shekaru musamman ma itama da akai mata tana ƴar 14. Dan driver dai zai iya zama sa'an Dada, maigadi ko bai wuce sa'an su Yaya Ja'afar ba, idan ma Dada zai girme ma sabon driver ɗin kaɗan ne, sai dai yanayin jin daɗi ba ɗaya ba, duk da a yanzu basu san yaya Dadan yake ba amma ya fishi ƙyawun jiki da ƙuruciyar zahiri. Dan shi wannan ma har furfura ta cika masa gemu duk da dai kansa akwai hula tashi da ƙwaƙwa baƙa data ɓoye gashin kan nasa, sai na iya fuskar zaka shaida zuwa gemu dan yana da saje... “A'a bawan ALLAH tashi-tashi kaji, mun sameku lafiya ko Almu. Ka yi baƙo ne?”. Maigadi ya bata amsa da mata bayanin ba baƙonshi bane su Yaya Ma'aruff ne suka kawo shi. Kafin tace wani abu sabon driver wanda shima a karo na biyu fuskarsa da murmurshi ya amsa mata, kafin ya miƙe yana sake mata barka da dawowa da sannu da jiki. Sannan ya juya yana gaida Uncle Tasi'u da Ammar. Ma'aruff ne ya juyo yana kallon Mammah ya ce, “Sabon driver ne daya maye gurbin Baba Ari. Sunansa Buba kwana uku da tafiyarku ya fara aiki”. Fuskar Mammah da fara'a sosai ta ce, “Masha ALLAH. Sannu da zuwa Malam Buba. ALLAH yasa zamanmu tare ya zama alkairin da zamu shiga aljanna gaba ɗaya. Ina dai fatan babu wani damuwa a zamanka tare da mu ɗin?”. “Amin Hajiya. Amin Amin. Babu wata damuwa sai godiya tsakanina da ku. Dan kuwa kwanakin da nai kawai na shaida alkairin mutanen wannan gida.” “To Alhamdullahi ALLAH yasa mu dace. Bari naje na huta munsha zaman jirgi zuwa anjima ka shigo mu ƙara gaisawa?”. “To to shike nan Hajiya, ALLAH ya huta gajiya nagode sosai.” Fuskar Mammah da murmushi ta amsa da amin Kafin su Shariffa su kamata har zuwa ciki. Shi dai Uncle Tasi'u na biye da su sum-sum kamar munafuki, sai dai harga ALLAH yayi matuƙar girgiza da ganin irin wannan katafaren gida mai kama da wani ƙaramin estate wai duk mallakin Adda A'isha ne da zuri'arta. Addarsa fa dake wujiga-wijiga akan marayun ƴaƴanta dana gayyar soɗi na kishiya data kama ta riƙe ita mai son miji. Addar nan tasa dai daya damfara gida ya gudu ya batta da sanin bata ga tsuntsu bata ga tarko a lokacin, amma a yanzu sai gasu a wannan ƙosashen gidan a babban birnin tarayyar ƙasa da dukkan alamu suka nuna nasu ne, kai shifa tun a motar dasu Ja'afar ɗin suka ɗakkosu dama zuciyarsa ke bugawa, yanzu kuma da suka shigo gidan ma sai yaga motocin da sukafi wadda suke ciki, sannan ba ɗaya ba a ƙalla motoci sun kai bakwai a gidan harda wadda suka dawo ta takwas. Bai ji zuciyarsa na tsitstsinkewa ba sai da suka shiga cikin katafaren sashen Mammah ita ɗaya, dan dama sashenta dana Dada sunfi kowanne girma a gidan. Kafin kace mi kuma ƴan aiki har uku sun zagayeta suma da tasu gaisuwar girma. Ga waɗan nan tsala-tsalan matan daya fahimci matan su Ja'afar ne sai rawar jiki suke akanta kamar wata uwarsu mahaifiya...

.....★DUBAI★.....

“Inaga a wannan gaɓar zan saka a kashe mijin nata, dan hakan ne kawai zai saka ta yarda ta saduda ta mallaka min kanta”. A wani irin firgice Hajiya Hasiba ta ɗago tana kallon Adeel mai maganar. Mamawo kuwa abincin da suke ci ne ya nema ƙwareta. Sai da ta ɗauki ruwa tasha da sauri. Shi ko ko'a jikinsa, dan tamkar ma bai ga halin da suke ciki ba ya cigaba da maganarsa. “A karo na farko ina son sanin wanene shi mijin nata? Miya taka a ƙasar taku? Ɗan wace zuri'a ce? Miye ƙarfin ikon sa?”. Su duka biyun rasa mai bashi amsa akayi, dan dama daga su sai shi ne a dining room ɗin. Su Ismat sunbi Nabeeha sun fice a gidan tun da sukaji zancen zuwansa. Ɗan dukan table ɗin yayi ta yanda suka dawo hayyacinsu firgigit. Da ƴar tsawa da raini da wulaƙanci ya ce, “Ko kuma kuna bin bayan wulaƙanta ni da take ne....?” “A'a wlhy bama bin bayanta. Da muna da iko da zuciyarta ma da tuni kun jima da zama ma'aurata maybe ma kun haihu. Mijinta ba kowa bane, ba ɗan kowa ba, baya da komai, baya taƙama da komai. Kawai soja ne a ƙasar mu, kamar yanda muka sanar maka tun farko kuma yana prison yanzu haka, shekaru ashirin da biyar kuma aka yanke masa a can”. “What! Shine kuma take tunanin zaman jiransa?”. “Shirmenta ne kawai Prince, amma tun kan ya shiga prison ma ita ta bar masa gidan sakamakon auren yarinya ƴar shekara 7 da yayi saboda ya ɗakota a wajen yaƙi. Daga ƙarshe ma mukaji ashe shine ya kashe mata iyaye dan ya aureta, da alama wani laƙanin asirin aka bashi dan dama yanda yake juya sojojin da wani gadararsa har manyan suna tsoronsa kai ka san ba haka kawai bane, dole akwai aikin asiri a ciki”. “Woow naji daɗin wannan labarin ƙwari da gaske. Yanzu ita yarinyar tana ina ne?”. “Tana a gidansu tare da ahalinsa. Sai dai a yanzu takai kusan 15years da wasu watanni”. Komai bai sake cewa ba ya miƙe kawai, da kallo suka bishi yana tafiya cike da ƙasaita da gadara, sai da yaje gab da fita a dinning room ɗin sannan ya juyo yana kallonsu. “Zamuje ƙasarku tare da ɗaya a cikinku”. Daga haka ya fice abinsa batare da jiran amsarsu ba.........✍️ KIƊA A RUWA 2