
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 27
.....La Ruky, full of love for her, said, "Should we drink ice-cream, baby?". She shook her head no. Then he frowned a little, turning his gaze towards Nimrah behind the mirror. "Uncle's children, shall we go and drink ice-cream?". Fedo said, "Yes Uncle". Nimrah was about to speak and Bintu shut her mouth, they knew her and Ruky's mouth the same. Seeing that she was going to get upset, Feedo put her hand on Bintu's hand and together they pressed Nimrah. She had to give them a few hot mints and they let go of each one of them. Badan Nimrah and Ruky wanted to go to drink this ice-cream. That's how it went until everyone chose the flavor she wanted. He added snacks to them. No matter how much they wanted him to take them home, he refused, so he withdrew their opinion and they stayed there. But the lack of innocence made them unable to let go and beat them. It's something they all have, not their upbringing. He or she stops talking to them and takes their picture with his iPhone. Seeing that the Isha prayer had started, Nimrah's mind was raised. If you see them outside at this time, it must be one of their Uncles, Ya Mu'azz or Aunty Biebah, or they were accompanied by Aunty Lailah Angu
27
.........“Sorry Trouble Buddy na. ALLAH ke ɗin ce kin cika wulaƙanci, Uncle Haneef fa ya haɗu ALLAH. Amma kiyita wani shan ƙamshi. Dan ALLAH ko kaɗan ki dinga kulashi mana, ALLAH idan ya ganki zakiga duk bakinsa yaƙi rufuwa”. “Ai shiyyasa bazan kulashin ba. Ni fa bana son susun namiji haba. Mutum babu wani jan aji. Kuma ni an faɗa masa za'a min aure ne yanzu mtsoww!!”. Bintu dake dariya ta ce, “Baby ai kece zaki saita shi yanda kike so. Amma kina wani yayyarfashi, jifa da salla yanda ya mana siyayya”. “Mayya dama ke ai kwaɗayi ne zai kashe ki ke da Ninah”. “Ya kashe mu dai, tunda tare muke”. Cewar Nimrah tana hararta. Ramawa tai itama, sai dai dai-dai nan Haneef ke dawowa dan haka hirar tasu ta tsaya. Fitowa yay da kansa ya buɗema Ruky gaba, zata zille ta shiga baya inda su Nimrah ke shirin shiga suka turata suna ƙumshe dariya. Juyawa Haneef yay ya kallesu da musu jinjina yana murmurshi. Daga haka ya rufe mata ƙofar ya zagaya dan suma har sun rufe. Yana fara tafiya a titi ya ɗan kalla Ruky, cike da son birgeta ya ce, “Muje shan Ice-cream ne Baby?”. Kai ta girgiza masa alamar a'a. Sai ya ɗan marairaice fuska, tare da maida lallonsa kan su Nimrah dake baya ta mirror. “Yaran Uncle muje mu sha ice-cream ne?”. Cike da iyayi Feedo ta ce, “Yes Uncle”. Nimrah zatai magana Bintu ta rufe mata baki, dan sun san bakinta ɗaya da Ruky. Ganin zata fisge itama Feedo ta ɗaura nata hannun akan na Bintu suka haɗu suka danne Nimrah. Sai da ta sakar musu wasu shegun mintsini masu zafi suka saketa kowanne na sosa wajen. Badan Nimrah da Ruky sun so ba akaje wajen shan wannan ice-cream dai. Haka ya jasu har ciki kowacce ta zaɓi flavor ɗin da take so. Ya ƙara musu da snaks. Duk yanda suka so ya maida su gida ƙi yay, haka ya janye ra'ayinsu suka zauna a wajen. Sai dai rashin sabo ya sasu kasa sakin jiki su dukansu. Dan abu ne da su dukansu ba tarbiyyarsu bace. Shi ko yanata tsiyaya musu zance da ɗaukarsu hoto da wayarsa iPhone. Ganin fa an fara sallar isha'i hankalin Nimrah ya tashi. Dan in har ka gansu a waje irin wannan lokacin tabbas da wani a cikin Uncles nasu ne ko Ya Mu'azz ko Aunty Biebah ko kuma sun raka su Aunty Lailah anguwa ko Ammie. Amma basu kaɗai ba balle wannan da saurayi ma wai. “Nimrah ya naga kin miƙe?”. Haneef ya faɗa yana kallonta. “Uncle Haneef kayi haƙuri ka maidamu gida. Wlhy idan Mammah taji zatai mana faɗa, balle Daddy ko su Uncle's”. “Haba-haba ai in sun san nine babu wani faɗa da zasuyi”. Miƙewa itama Ruky tayi, hakan yasa suma su Feedo duk suka miƙe. Kafin ma Nimrah ta bashi amsa Feedo ta ce, “Wlhy Uncle koni Abbana ya sani ubana zai ci. Muje ɗin kawai ma ƙarasa a gida”. Babu yanda ya iya dole ya miƙe, ya tayasu tattare kayan suka fito. Kamar ɗazu yanzu ma dole Ruky gaba ta shiga. Cikin ƙankanin lokaci ya iso gidan Aunty Mimi da su. Yay horn maigadi ya buɗe masa gate ya shige. Suna fitowa a motar maigadi ya iso inda suke. Kai tsaye gaban Nimrah ya isa yana miƙa mata ledar hannunsa da faɗin, “Hajiya gashi wani yace a baki. Yata jiran dawowar ku amma yaji shiru yanzu babu jimawa yabar wajen nan.” Ba ita ba hatta su Ruƙayya da mamaki suke kallonsa. Cikin kasa daurewa Nimrah tace, “Kuma ni Nimrah yace a bamawa?”. “Tabbas ke yace, yace sunansa Kamal malaminku na islamiyya”. Ruky ce ta amshi ledar tana faɗin, “Wato shima Sayyadi Kamal ɗin nan ɗan naci ne fa na lura”. Daga haka tabar wajen fuuu. Tsaff su Nimrah sun fahimci fushin Haneef tai amfani da shi akan Kamal. Dan haka suka wayance da masa godiya suka shige cikin gida. Sun sami sauran dangin mijin Aunty Mimi da basu kai ga wucewa ba. Suka gaishe su suka wuce ɗakin da suke sauka in har sunzo gidan. Dama can suka kai kayansu da daddare. Ƙaton gado ne da zai iya isarsu koda su shida ne a ɗakin, sai wadrobe da mirror, sai ƙofar bayi. Kayan hannunsu duk suka ajiye suna zubewa a gadon kowa na faɗin wash, dai-dai nan Ruky data rigasu shigowa ta fito daga bayin alamar har tayi alwysSuma duk miƙewa sukai, dan rashin yin sallar akan lokaci na tsaye a ran kowannensu. Bintu ce kawai ke period dan haka taja ledar snaks ɗinsu ta fara ci tana faɗin, “Bari muga mi Sayyadin ya aiko mana da shi shi kuma”. Tsaki Nimrah tayi a karo na farko tana shigewa bayi abinta. Fiddo ta sanya dariya dan Ruky ma harta kabbara salla. Dariyar su Bintu data cika ɗakin ya saka Nimrah fitowa da sauri, itama Ruky dai-dai tana idar da sallar ta juyo tana kallonsu. Litattafai ne a ledar saƙon Sayyidi Kamal suka nuna musu. Feedo ta ce, “Wannan fa shine auren ustaz ɗin, kaga wata lukutar jaraba wai saƙon littafai. Ninah kina cikin yanayi gaskiya”. Nan ma dariya suka sanya harda Ruky yanzu kam. Dan haka Nimrah ta watsa musu harara ta kabbar sallarta itama. Koda ta idar sun gama mata shaƙiyancin nasu, dan haka bata sake tada zancen ba ta haye gadon ta kwanta wai kanta ke ciwo. Da ƙyar suka lallaɓata ta zauna suka ƙarasa shan Ice-cream ɗinsu da snaks ɗin bayan Feedo ta idar da salla itama. Dan haka koda Aunty Mimi tai kiransu suzo su ɗeba abinci sukace mata sun ƙoshi. Bata takurasu ba dan taga abinda suka shigo da shi, ta kuma san aikin Haneef ne......
<<<<<<(✷‿✷)>>>>> ★CAMPAIGN★
Kwanaki 100 na campaign suna gab da cika, dan kuwa ana satin ƙarshe na kammala taron kowane kamfen. Dan haka amsa kuwwar cikar kwanakin tamburan siyasa na gab da cika, tako ina ƙasa ta kara hargitsewa dan kowa burinsa satin ƙarshen nan ya tumfayesa da zuciyar yan kasar. Baka iya jin komai sai sautinkan waƙoƙin da aka rairana ƴan siyasa. Yayinda hankalin matasa kacokan ya koma can. Wasu ma sun ajiye harkokinsu da sana'o'in su ne kacokam. Kamar dai yanda aka saba alƙawuran nasu guda huɗu ne ga al'ummar ƙasa a lokacin da suke kan munbarin campaign. Zamu gyara muku harkar karatun, zamu inganta wutar lantarki, zamu wadata ku da ruwa, zamu gyara asibitoci. Cikin rashin lissafi da auna abubuwa a yanda ya dace, da taro da kwabon da ake raba mana mu talakawan ƙasa da ɗan sabulai da zannuwan ɗaurawa mai hoton ƴan siyasar a jiki sai kaji mun sallama muna bada kai bori ya hau. Babu ruwanmu da tantance wane shugaban ya dace damu? Mi muke so a ƙasar da kawunanmu bayan waɗan can lissafin huɗu da ko a karatu sukazo ya kamata ace mun haddace su tsaff zuwa yanzu daga daɗin bakinsu mu nemo cigabansu. Amma ina babu batun tantancewa, a wasu wajajan ma siyasar ta haɗa rigima ne tsakanin ƴan uwan juna saboda ni ina son wannan wane ɗan uwana yana son wancan ba jam'iyyar mu ɗaya ba. Wasu har gaba zakaga ta ƙullu mai girma a tsakaninsu. Yayinda su ƴan siyasar da sukeyi domin su suna can tare suke shan shayi, tare suke ƙulla mai fishshesu musamman akan abinda zasu ribantu da shi game da kuɗaɗen da suka kashe wajen jawo ra'ayinku idan sun haye. Wanda ma bai haye ba akwai hanyoyin da za'a bi dan maida masa wahalarsa ta bayan fage kune a ruwa...
Alhamdullahi duk da irin tasu tafiyar bata banbanta data Janar Yusuf ba a yau kasancewar a ƙarƙashin damarsu ya ke shima a siyasar kamar saura abinda shekarun baya suka zo da shi wajen campaign shima dai shine a yau yake zuwa da shi. Kuma Alhamdullah zamu ce akwai nasara a al'amarin dan yana da magoya baya sosai a cikin jam'iyya da al'ummar gari. Abinka da soja, a kwanakin kai-kawon duk da wahala da jigatar rashin barci dana hutu zuciyar maza a tsaye take da ƙyaƙyƙyawan fata. Tun ana farkon satin nan da sukai zama da Imran ya kuma gana da Uncle Nasiru basu sake haɗuwa ba. Dan a zahiri Imran baida alaƙa da siyasar Janar. Gara-gara ma Uncle Nasiru har campaign ya rakashi sau biyu. Duk wani abinda ya dace su tattauna sun kammala sun ajiye kundin shirinsu gefe har sai ta ALLAH ta kasance. Wato aci zaɓe ko a faɗi... Tsahon kwanaki sun cika cir, awanni 48 ya rage a fara jefa kuri'a, dan haka batun campaign komai ya lafa a koma jiran ranar jefa kuri'a da gwamnati ta riga ta fitar kuma kwanaki 2 ne kacal, dan yau alhamis....
★_______★ ★RANA BATA ƘARYA Yau safiyar asabar. Safiyar zaɓen shugaban ƙasa. Duk wani masoyi na yan takara a kowane ɓangare jikinsa na'a farce ne. Ba yan takara kaɗai ba da zuri'ar su yan kasa kansu kowa hankalinsa nakan fata ga wanda yake so. Dan haka kasar ta wayi gari a yanayin sai addu'a kawai. Wasu cike da fata, wasu cike da tsoro duk da tako ina jami'an tsaro na aikinsu ne. A ka'ida daga shekara sha takwas ne za'a iya saɓe zuwa sama. Dan haka su Nimrah basa cikin masu jefa ƙuri'a. Amma ganin su Mu'azz zasu suka maƙale zasu je. Mammah kam Daddy Imran da kansa yazo ya ɗauketa ita da Hajjo ya kaisu suka jefa kuri'arsu da wuri sosai tare da Janar Yusuf Shu'aibu Tafida da iyalansa. Duk da dai ba kai tsaye Daddy Imran ya fito a tawagar janar din ba saboda bada ƙafa. Amma janar na jefawa da iyalansa suna a rukuni na biyu da suka jefa suma. Daga can Mammah tabi Hajjo suka wuce can gidan dan suma su Gwaggo Khadijah zasuje gaida Abba, amma su basuje jefa kuri'a ba daga gida za'a kaisu can tunda Mammah ce ta riƙesu tace sai an gama zaɓe zasu koma gida, kuma acan suke da mazaɓa.........✍️KIƊA A RUWA 2