Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 26

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 26

.....send her only Uncle Jamilu and Khadijah the Quaggo. Why did she decide to go to her son's name to inform Mammah about her situation and whether she would get any help. Uncle Jamilu also paid for her car. Mammah was not happy to see them. Especially Gwaggo Nanah and the wife of Uncle Jamilu Badiyya who are hundreds of people are praising the Lord's judgment and seeing the house that Mammah is in today and her descendants. Indeed, the world is a fool's girlfriend, the one who said that he is not the one. Mammah had already put them in Kulu and the workers had prepared guest rooms for them. When they arrived there at eleven in the morning, they said that they had left in the morning and they took the car straight away. Mammah, who was happy, said, "First take a bath with hot water and then come to bed. Don't tell me that the children are all in bed yesterday. Gwaggo Khadijah laughed a little and said, "Send the invitation to Maman Ma'aruff by ALLAH. Don't let them sleep, we won't be going back today. There will be a service to celebrate their name later." "As if you don't know what they planned including Fati. Biebah was the only one who was able to follow them to Lailah's house,

Standalone post1,566 words

26

..........KWANA UKU da dawowar Mammah suka karɓi baƙuncin ƴan Bauchi da sukazo sunan Aunty Mommy. Gwaggo Khadijah, Gwaggo Alawiyya, da Gwaggo Nanah. Sai matar Uncle Jamilu da wannan ne karonta na farko da tazo. Dan tun abinda taima su Mammah ɗin a wancan shekarun take jin matsanancin kunyar zuwa inda suke. Sai dai har cikin ranta taji nadama. Musamman da ayanzu su Mammah ɗin ne riƙe da rayuwarsu tunda su Ja'afar ne suka buɗema Uncle Jamilu babban shago kayan sakawa a can Bauchin ƙyauta, da shi suke ci suke sha. Sannan kuma suka ɗauki nauyin karatun yaransu a makaranta mai ƙyau. Gwaggo Nanah kam ta fita zakka a cikin ƴaƴan Inna, tana iya ƙoƙarinta dama tun ma suna cikin wahalar rayuwa kamar yanda Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya keyi. Sai dai tsoron ƴan uwanta su Yaya Babba ke hanata zuwa inda su Mammah suke. Wannan karon kuwa itama sun mata halin nasu, dan mijinta ya gudu ba'a san inda yake ba shekara biyu kenan duk sun ƙi taimaka mata, ga wahala tana ciki ita da yara. Babu mai taimaka mata sai Uncle Jamilu da su Gwaggo Khadijah ɗin. Shiyyasa ta yanke shawarar zuwa sunan nan danta sanar ma Mammah halin da take ciki ko zata samu wani taimako. Kuɗin mota ma Uncle Jamilu ne ya biya mata. Ba ƙaramin daɗi Mammah taji da ganinsu ba. Musamman Gwaggo Nanah da matar Uncle Jamilu Badiyya da suketa ɗari-ɗari suna jinjina hukuncin UBANGIJI da ganin gidan da Mammah ke ciki a yau da zuri'arta. Lallai duniya budurwar wawa, wanda yace shine kuwa ba shi ɗin bane ba. Tuni Mammah ta saka su Kulu masu aiki suka gyaro musu ɗakunan baƙi, dan sunyi isowar wuri lokacin sha ɗaya na safe, sunce tafiyar asuba sukayi dan mota suka ɗakko kai tsaye. Mammah dake ta farin ciki ta ce, “Ku fara yin wanka da ruwa mai zafi sai kuzo ku karya. Bara kiga nasa a kakkaɓo min yaran nan duk suna gado jiya sun raba dare ne suna shargallen su”. Gwaggo Khadijah tai ƴar dariya da faɗin, “Aike da gayyar nan taki Maman Ma'aruff sai ALLAH. Kinga barsu suyi barcinsu, muda ba yau zamu koma ba. Anjima ma wata hidimar ce ta bikin suna a kansu”. “Kamar ko kin san harda fati suka shirya wai. Biebah ce kawai ta iya bin su Lailah gidan maijegon, yanzu babu jimawa suka fice suma dan jiya sai goma suka dawo”. Yanzu kam Gwaggo Alawiyya ce ta ce, “Kai waɗan nan yara ALLAH dai ya saka musu da alkairi. Wlhy samun surukai irinsu sai an tona Addah.” “Ai su Shariffa sun wuce surukai ƴaƴane Alawiyya. Babu abinda zan cigaba da musu sai addu'a da fatan suma ALLAH ya basu masu yi musu”. Gwaggo Nanah dake jinjina kai ta ce, “Wlhy ki musu ki ƙara muma muyi musu, ga gidan Yaya Babba can su Haire su da surukai ba arziƙi. Jiya matar Haƙilu kamar zatai dambe da Haire akan ɗanta, ke bakiji wannan tujara ba abin kaico”. Murmurshi Mammah tayi, saboda a saki zancen ta ce, “ALLAH ya ƙyauta to, ai zamanin ne ya zama abin tsoro sai addu'a kawai. Kunga kuyi wankan kuzo ku karya hirar tafi armashi”. Godiya suka yi ta juya ta fita. Dukan su suna jin ƙaunarta a ransu, Badiyya kam kunyarta take ji sosai shiyyasa tunda suka gaisa tai shiru kanta a ƙasa. Sarai Mammah ta fahimceta, dan haka ta ƙuduri aniyar cire mata abinda ke ranta gaba ɗaya, dan ita babban fatanta ta haɗe kan zuri'ar Abdul-rasheed ba rabuwar kansu ba....

★ Sai sha biyu su Nimrah suka tashi da ƙyar, shima sai da Mammah tazo da kanta ta tashesu. Dan suna yin sallar asuba suka koma gado. Aiko sai shagwaɓa suke mata wai ta barsu sai ƙarfe ɗaya sannan. “Shike nan kun fasa zuwa gidan sunan kenan? Ai da nasan haka ne sai na tadaku kun wuce Tahafiz. Ga ƴan Bauchi can tun sha ɗaya suka iso ku kuna nan kuna barci”. Tuni duk suka watsakke, cike da farin cikin jin zuwan ƴan Bauchi. Zasu nufi ƙofa a guje Mammah ta dakatar da su. “Kai kuji min ƙazaman banza. Haka zakuje musu da kayan barci? Ba brush kamar wasu ƙazamai. Maza ku koma ku gyara jikinku, wata taje ɗakin Biebah yanda zakuyi sauri”. Cike da farin ciki sukace to. Mammah ta fito tana murmurshi. Koda ta dawo falon wajen su Gwaggo Alawiyya ta samu su Ma'aruff sun iso gidan. Dan tun ɗazun ta sanar musu sukace zasu zo yanzu. Sai ko gasu da ledoji niƙi-niƙi na kayan ciye-ciye. Fuskokinsu washe da murmushin ganin gwagwgwannin nasu. Badiyya na sinƙe-sinƙen kai ganin yanda suma basu nuna mata komai ba kamar Mammah sai ta ware aka fara gaisuwa da tambayar yara. Yaya Ja'afar ya ce, “Haba Gwaggo, kwa taho ku kaɗai duk babu yara? Bayan kun san ba ganin juna ake ba tsahon lokaci sai irin haka ta faru”. “Makaranta tasa haka Ja'afar, amma in sha ALLAHU idan anyi hutu sai su zo. Tunda kudai kun tattaramu kun watsar, yaushe rabonku da Bauchi balle Maiduguri?”. “Dama idan sunje Bauchin ba ganinsu muke ba Adda Khadijah, iyakarsu gidan Yaya Jamilu da Adda Alawiyya. Dan nidai sau biyu suka taɓa zuwa min lokacin rasuwar Inno surukata, da ciwon Ahmadi”. “Munyi laifi Gwaggo Nanah, amma kiyi haƙuri zamu gyara in sha ALLAHU. Wani lokacin abubuwan ne ke yawa. Mafi yawan lokuta kuma zuwa Bauchin kasuwa ke kaimu. Ki tambayi Aunty Badiyya sau da yawa shima Uncle Jamilu a kasuwa muke samunsa ba gida muke zuwa ba. Itama Gwaggo Alawiyya takan jima bata gammu ba. Maiduguri ne dai kam ma zamuce muna shiga dan ziyara kai tsaye”. “To na gamsu, amma dan ALLAH a gyara, mun san mu masu kuskurene a gareku, amma kuyi mana afuwa kunji, Yaya Abdul-rasheed mutum ne mai son zumunci da Adda A'isha da Adda Yakura, na tabbatar kuma akwai wanan jinin alkairin nasu a tare daku, kar ku biyema aikin son zuciyar wasunmu ku watsar damu gaba ɗaya. Suma lokaci zai yi da zasu yi nadamar abinda suka shuka. Dan har ma wasu sun fara, Yaya Babba a tsakanin nan babu abinda yake sai tafka asarori kala-kala, ga yara cike da gida, mata har huɗu. Yaya Haruna ne ma za'ace da ɗan sauran damshi-damshi. Shi ko Yaya Garzali ma yaje ya tare saudia aikatau ƙiri-ƙiri ko takan matan baya bi sai ya gadama.” Sosai zancen ya girgiza su. Sai dai basu ce komai ba face ALLAH ya ƙyauta. A haka Ammar ya shigo shima da Mu'azz. Nan fa falon ya sake lacamewa da farin ciki. Sai kuma gasu Nimrah na fitowa cikin kwalliya tsaff suna baza ƙamshin turaren da suka satarma Aunty Biebah na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Cike da farin ciki suka rungume Gwaggo Alawiyya da Gwaggo Khadijah dan su suka sani sukam. Abin birgewa bazaka taɓa cewa ba jininsu bane su. Sun gaida su Gwaggo Nanah suma. Suka amsa musu da kulawa duk da basu san alaƙarsu da gidan ba. Garama Fiddo ƴar Aunty Mommy data kwana a gidan itama, tunda sun jajje Bauchin ita. Gwaggo Khadijah ta ce, “Oh ni Dije Maman Ma'aruff ƴan matan nawa duk sun miƙe. Kaga yara kamar wasa sun ƙosa. A wannan sai aure”. Caraf Mu'azz ya ce, “Tab ɗin wazai kwasa Granny? Wannan gayyar ciwon kan da basu iya komai ba sai dambe da neman masifa da ƴaƴan mutane”. Baki duk suka tura gaba. Gwaggo Khadijah ta ce, “Kunga ƙyaleshi ƴan uku Ko nace ƴan huɗu dan banbu Bintu ne. Ai ana yin auren duk zaku daina ko. Kuma dai ai kowa da ƙuruciyarsa, shima idan za'a faɗi abinda yayi ai sai kowa ya gudu”. Dariya suka shiga yima Mu'azz suna masa gwalo, shiko yana hararsu da musu alamar zai kama su. Su Yaya Ma'aruff dai na murmurshi ne, Yaya Ammar kam dining ya nufa yana faɗin shifa yunwa yake ji, mi aka dafa ne?. Miƙewa su Nimrah sukai suma suna faɗin yunwar suke ji. Daga haka suka koma kan dinning ɗin harda su Mu'azz aka bar su Yaya Ja'afar suna hira da su Gwaggo Khadijah.....

<<%>><<%>><<%>>

Da yamma shagalin suna aka sha sosai a gidan Aunty Mimi, duk da kuwa haihuwa ce ta huɗu tayi. Babu ƙarya su Nimrah sun cashe da rawa iya iyawarsu. Kasancewar hall aka kama iyakar kuma mata ne kawai a wajen dan ko su Mu'azz basu shiga ba sai abin ya ƙayatar. Ƙarfe shida aka tashi saboda sallar magriba. Nan fa motoci suka fara ɗibar mutane zuwa gidajensu. Su Nimrah dai yau a gidan Aunty Mimi zasu kwana. Dan haka sukabi ƙanin mijinta da yazo kwasar yaranta dana family ɗin mijinta. Duk da dai da farko ca sukai su bazasu shiga cikin yaran ba, sai da Aunty Shariffa ta fara musu faɗa da tabbatar musu zako ta kaɗa kansu zuwa gida sannan suka nutsu saboda suna son zuwa can ɗin su ƙarasa weekend ɗin su. Ga Bintu kuma ta ƙaru sun zama su huɗu yanzu. Haneef dake matuƙar son Ruƙayya na sharewa yana faman murmushi yace su jira shi ya kai yaran ya dawo to. Feedo ce ta amsa masa da “To Uncle”. Su Ruky kam aka wani ɗauke kai gefe. Murmurshin shaƙiyanci Nimrah tayi, tare da ɗagama Bintu gira ɗaya cike da gulma. Aiko suka kwashe da dariya. Ruky da tasan da ita suke ta balla musu harara da jan tsaki zata bar wajen Nimrah ta riƙota........✍️ KIƊA A RUWA 2