
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 25
.....she said with a smile, "How does my head hurt". "Ayya Auta, it's stress. Go back, take medicine, go to bed before the housekeepers come back and stop you." She saluted him. Uncle Nasiru also greeted her. When she answered, she went to send Mammah... Not long after, she came back and said that he is coming soon. She didn't sit down and continue eating, she took the plate and went to the kitchen. Even she returned with water in her hand trying to pass to the room. Just then, Uncle Tasi'u entered the hall with a salute. They all answered and looked at him. But Uncle Nasiru stood up and looked at him. He or Imran did not know him in fact, it was only news that the incident happened, so there were no signs of surprise or concern with him. He was waiting for him to come. But he couldn't answer and his mind was completely focused on Uncle Nasiru. "Tasi'u!". Uncle Nasiru was shocked and surprised. For the first time Tasi'u was down on his head, his eyes were full of balls. About five seconds before he got up again and stepped where Uncle Nasiru was, his feet seemed to be dancing. He was going to Uncle Nasirun's presence and he fell on his knees. Imran opened his eyes wide and straight
25
..........★A falo kam daga Imran har Uncle Nasiru sunji matuƙar daɗin ganin yanda jikin Mammah ya ƙara ƙyau. Da alama ta samu maganin da yafi wanda take samu anan gida. Dan wannan ne karon farko da suka fita Egypt ɗin dama. Kasancewar su Nimrah duk sun wuce islamiyya da ƙyar gidan shiru, dan ca sukai bazasu ba yau suna murnar dawowar Mammah. Sai da Yaya Ma'aruff ya fatattakesu sannan kowa ya wuce baki a sama. Sai Biebah kawai itama bata jima da dawowa daga school ba. Mu'azz yabi Imam gida. Mammah ta kalla Biebah dake laƙai-laƙai ɗin cin abinci saboda bata jin daɗi yau da ciwon kai ta dawo makaranta ganin Mammah ɗin ne ma ya ɗan watsakkar da ita. Sai dai ganin baƙon dake gidan ya tsaya mata a zuciya kamar sauran ƴan uwanta. Dan yanzu haka ma Aunty Momy da Aunty Ummi da Ammar na ɗakinta suna sake tattaunawa. “Biebah tashi kira Uncle ɗin ku”. Idanu Biebah ta ɗago tana kallon Mammah, sai kuma ta amsa da to cikin sanyi tana tashi. “Kina lafiya kuwa Biebah?”. Cewar Imran. Idanunta na cika da ƙwalla ta ce, “Yaya kaina ke ciwo”. “Ayya Auta stress ne sannu. Jeki dawo kizo kisha magani kije ki ɗan kwanta kafin akkunayen gidan su dawo su hanaki”. Kai ta jinjina masa. Shima Uncle Nasiru yay mata sannu. Nan ma amsawa tai ta wuce aikar Mammah...
Babu jimawa ta dawo tace yace gashi nan zuwa. Bata zauna cigaba da cin abincin ba ta ɗauka plate ɗin takai kitchen. Koda ta dawo da ruwa a hannunta ƙoƙarin wucewa tai ɗaki. Dai-dai nan Uncle Tasi'u ya shigo falon da sallama. Duk amsawa sukai suna kallonsa. Sai dai zaram Uncle Nasiru ya miƙe yana kallonsa. Shi ko Imran bai san shi ba a zahiri sai labari a sanda wancan abin ya faru, dan haka babu wani alamun mamaki ko damuwa a tare da shi. Sai ma sannu da zuwa da yake jera masa. Sai dai ya gagara amsawa dan hankalinsa shima gaba ɗaya yana kan Uncle Nasiru ɗin ne. “Tasi'u!”. Uncle Nasiru ya faɗa cikin matsanancin mamaki da al'ajabi. Karo na farko Tasi'u yay ƙasa da kansa, idanunsa na cika da ƙwalla. Fin sakan biyar kafin ya sake ɗagowa tare da takowa inda Uncle Nasiru yake ƙafafunsa nayi kamar suna rawa. Yana zuwa gaban Uncle Nasirun kawai sai ya zube akan gwiyawunsa. Imran ya zaro idanu waje sosai yana miƙewa, dan zuwa yanzu kam ya fahimci lallai akwai matsala, sannan baƙon yana tare da wani babban al'amari, yo dukda ba yaro bane babba da shi ya durƙusama Uncle Nasiru. Mammah ya kalla, ya ga ta duƙar da ƙai itama kamar mai kuka. Sai shima ya girgiza kansa. Muryarsa a raunane ya ce, “Mammah waye shi dan ALLAH? Naga kuna kama ba ɗan uwa bane ba shin?”. Ɗagowa Mammah tayi ta kalla Imran tana ƙoƙarin maida hawayen da suka cika mata idanunta. Fuskarta da ɗan murmushi. Babu wani ko ɗar ta amsama Imran tambayarsa. Dan har cikin ranta kallon Imran take dai-dai da su Haysam. Jinsa take tamkar ɗan data ɗauki cikinsa ta haifa. “Imran Tasi'u ƙanina ne uwa ɗaya uba ɗaya. Baka san shi bane saboda wasu abubuwa da suka faru a baya. Amma sun riga sun wuce na yafe masa. Mun haɗu da shi a asibiti nd kwana huɗu kenan.” Gaba ɗaya Imran sai yaji kamar ma yayi mutuwar tsaye. Ga kukan Uncle Tasi'u daya cika falon. Dan kuwa ya riƙe ƙafafun Uncle Nasiru ne yana raira kuka da kalmomin ban haƙuri kamar wani yaro. Yayin da shi Uncle Nasirun ya gagara sake iya cewa komai yana tsaye kawai shima idanun nasa sun kaɗe jazur. Kukan Uncle Tasi'u ne ya sakko da su Aunty Ummi. Ko muce Biebah taje ta kirasu dan komai dake faruwa tana kallo daga inda take laɓe. Ammar daya gama kaiwa wuya cikin fushi ya ce, “Ni wlhy wannan drama ɗin ta isheni haka nan.” Duk juyawa su Mammah sukai suna kallonsu, dan basu san da sakkowar tasu ba. Sai dai kan wani yay magana Aunty Ummi ta ce, “Ba kai kaɗai drama ɗin nan ta isa ba Ammar harda mu ma. Shiyyasa ma su Yaya Ja'afar suka bar gidan, dama kuma jiran zuwan Uncle Nasiru kawai mukeyi muma. Idan Mammah nada zuciyar kawaici da haƙuri mu bamu san wannan ba, babu yanda za'ai maciji ya saremu a bakin rami mu sake maida ƙafarmu da tunanin bazai sake na biyu ba. Ai ko hausawa sunce sanin hali yafi sanin kama. Dan haka Uncle! Yaya kodai ku bashi shawarar ya koma inda ya fito, ko kuma ya nema masauki a wajen wannan gidan magana ta gaskiya”. Tana gama faɗar haka ta juya zata bar falon tana hawaye. Take mata baya su Ammar sukai suma. Mammah zata dakatar da su Uncle Nasiru ya girgiza mata kai alamar ta barsu.... Dole Mammah tai shiru, shi kuma ya miƙe yana sake faɗin, “Tasi'u tashi muje can gidana, mu basu lokaci nan da kwana biyu.” Daga shi har Mammah ɗin babu wanda yay jayayya, dan Uncle Nasiru yaya suke kallonsa uwa ɗaya uba ɗaya. Bayan wucewarsu shima Imran bai jima ba ya wuce gida abubuwa da yawa na masa kai-kawo a rai da zuciya......
(((★)))(((★)))(((★))) ★PRISON★
Yana komawa ɗakinsa ya zauna a gefen gadon sa yana kallon sojojin dake ƙoƙarin ɗaura tvn da suka kammala haɗawa a jikin bangon ɗakin. Baiyi musu magana ba, dan ko gaisuwar da sukai masa bai amsa ba a sanda ya shigo hannu kawai ya ɗaga musu. Suna kammalawa suka fice daga ɗakin tare da maida ƙofar suka rufe masa. Shima sai ya rufe idanu kamar yana barci amma ƙwaƙwalwarsa ce ta shiga aikin aunawa da lissafin abinda ya faru. “Facemask Analysis. Camara jikin agogo”. Ya furta a saman lips yana wani ɗan gajeren murmushi har lokacin idanunsa a rufe. A zuciya ya cigaba da ayyana suffar mutumin dalla-dalla da irin ƙwaƙwalwar ma'aikacin daya san aikinsa. (Fuskar bogi, agogo, tsayayyun idanu na masu busashiyyar zuciya da shekarun girma na tantance gwagwarmayar rayuwa na tsawon lokaci. Yanayin motsin ƙwayoyin cikinsu na ƙwararren operatives. Hakan na nufin wani daga cikin manyansu ne. Ba sabon shiga ba. Barazanar da ya faɗa. Sun ce suna sarrafa shugabanni… hakan na nufin akwai infiltration a cikin gwamnati. Wannan na iya zama sashin da ke kai rahoton Board of Inquiry. Ya ambaci makusanta. Hakan na nufin da damar su Imran ya zo wurina shekaru biyar da suka wuce. Yanzu kuma sune suka saka aka dakatar da shi. In dai haka ne to akwai idanu dake zagaye da Imran cikin rundunar soji ko wajenta, lallai Imran zai iya shiga haɗari akoda yaushe dan ko zai mutu bazai bisu fuska da fuska ba. Ya furzar da iska mai nauyi yana runtse idanu, dan Imran wani sashe ne na jikinsa da taɓashi tamkar ruguza jarumtarsa ne. Abu na uku tambayar su (Me yasa suka barni da rai har yanzu? Nima wannan tambayar ta jima a raina. Tabbas da nine a matsayinsu, zan kashe wanda nake tsoro musamman in haɗarinsa zai zama babbar barazana ga ƙasata bawai a karan kaina ba. Amma su suna bukata na a raye. Me yasa?) yay shiru na tsawon lokaci, sai kuma ya tashi zaune da ƙyau ya ɗauki pen da takarda ya rubuta wannan tambayar. _“They need me?. For what? To watch me? To use me? Or to fear me?”_ Pen ɗin ya kai saman lips ɗinsa da suka ɗan bushe dan yau yana azumi. Abu na huɗu (Wasan da suke cewa ya fara… hakan yana nufin wani babban shiri da suke da shi a wannan tsakanin kenan? Wani sabon hari ne?. Ko wata rawar juyin siyasa?. To amma ai basa buƙatar mutum kamar ni wajen gane kosu su waye?, ko ina matsalar?. Wannan kuskurensu ne ko ni ne ban fahimta dai-dai ba?) ya sake yin shiru alamar dogon nazari. Tsohon lokaci yana kai kawo da tunaninsa, sai kuma ya kai dubansa kan television ɗin da aka saka a ɗakin. Karo na farko ya miƙe yana ajiye littafin hannunsa da pen ɗin, gaban tvn ya isa, sai da ya gama duba ko ina na jikinta ya tabbatar babu camara sannan ya ɗauka remote ya fara searching channels, tashoshin dake cikin decoder ɗin da aka haɗata da ita duk zaɓaɓɓune. Domin guda uku ne kacal ba'a komai a cikinsu kuma sai abinda ya shafi labarai. Labaran ma ba kowane labari ba. Dan a yanzu dai kusan harkokin siyasa ne da campaign da aka fara kusan wata uku kenan. Idanun ya janye a hankali cikin salon yin luuu da su ya maida gefe da sakin murmurshin nan nasa na ƙeta. Sai kuma ya maida remote ɗin ya ajiye inda ya ɗauka ya koma bakin gadon ta sake zama.. Gaɓar da tafi tsaya masa ce ta sake maimaita kanta a brain ɗinsa. (Sun ce suna sarrafa zuciyar manyan. Idan haka ne, bayanan da Imran ya kawo min game da janar mai ritaya… dole sai na sake nazari. Domin kuwa wani daga ciki yana iya zama mai sarrafa Janar a gefe, da wannan damar kuma kaɗai za'a iya cimma Imran. Dan tabbas tunda har suka faɗa ya fahimci cewa ziyara ta farko da ta biyu na Imran sun haifar da damuwa a ɓangaren kungiyar shaiɗanun nan, shiyyasa ma suka hana shi cigaba da zuwa. Ya ɗan murmusa kaɗan, dan ya fahimci abu mafi mahimmanci har yanzu suna tsoronsa. Shiyyasa suka hana a ziyarcesa, suka hana yay communication da kowa, suka saka aka killaceshi inda baya ganin kowa sai masu tsaronsa dake kawo abinci dama duk abinda yake buƙata. Ya jima da gane a jikin masu tsaronsa akwai camara dake isar da saƙon shigarsu da fitarsu wajensa. Zuwan baƙon nan ma ba saƙon da yazo faɗa bane kawai maƙasudin zuwansa nan, suna son suga ko ya raunata a zuciya zuwa yanzu. Suna son su gane ko ya ragargaje da raunin kaɗaici. Suna son su tabbatar ko har yanzu yana da ƙarfi daga irin ƙarfin da suke tsoro. Gaba ɗaya ma sai yaji ya sake raina wayonsu. Dan da da gaske, suna da ƙarfin ikon da suke faɗa, ba zasu zo su gaya min ba. Babu mai saƙon barazana da ikon cikakke sai wanda yake jin tsoron wanda aka aika wa saƙo. Yay ƙwafa, saboda wannan tunanin ya ƙara masa ƙarfin gwiwa, da fushi, da nunin ya sake tashi tsaye da shirye-shiryesa. Dole kuma ya aikama Imran saƙo batare da jinkiri ba...........✍️KIƊA A RUWA 2