
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 4
.....it's a joke. It is politics. Right and politics are not separated from blood." Imran's head shook. Wanting to reassure himself, he said, "I understand, that's why they locked you up because they were scared." They are afraid of you. They were scared of the truth. They are afraid of what you know." "I know." Dada said slowly as he recovered a little. Silence filled the room again with his thoughts, and after ten seconds he turned his gaze directly on Imran, a gaze that gathered three deep years: bravery, longing, wisdom, and the pain that surrounded the heart of a person from person to person like a stone. Imran broke the silence by saying, "My mistakes brought you here Haysam, I will sacrifice my life to see you get out again" and wiped away the tears that fell on him again. Dada's eyes slowly blinked, not paying attention to Imran's first conversation, he said, "God bless him, I know they won't leave him without all those who support us. Imran... get back to me when you have time. We have a long talk. And don't worry again. You are the only one I never blame.” Yes.....
4
........Dada dake kallonsa kallo mai cike da ƙauna daga UBANGIJI ya ɗan ɗaga hannunsa yana masa Alamar ka tsaya ka nutsu. Sai kuma ya sake motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta “You’re a soldier Imran… but seeing you like this is giving me a headache. What’s happening to you?why are you acting like a woman?”. Shima ya ɗan kawar da kansa gefe saboda idanunsa na son suyi wani abu saboda hawayen da suka sakko a fuskar Imran sharrrr. Kuka ko ɓacin rai ne shi kansa bai ma san wannene yake ji da ganin hawayen Imran ɗin ba. Cikin dakewarsa, idanunsa na kallon gefe ya sake furta, “Bazan tambayeka yaya kowa yake ba? Dan hakan shine mafi girman abinda zai sosa min ZUCIYA. Na ganka, shi ne abinda yafi komai muhimmanci Imran.” Da ƙyar Imran ya tsaida hawayensa. Fuskarsa da murmurshin ƙarfin hali ya ɗan matsa gaba, hannayensa duk biyu ya ɗaura kan teburin. “Munyi ƙoƙari.. Munyi komai… amma suka zaɓi yimana wannan zaluncin Haysam…” Dada ya katse shi da murya mai sanyi amma mai ƙarfi da nutsuwa, “Ba zalunci bane. Siyasa ce. Dama kuma ita siyasa ai ba ta rabuwa da jini.” Kai Imran ya girgiza. Cikin son ƙarfafa kai ya ce, “Na fahimta, kenan sun kulle ka saboda sun tsorata. Sun tsorata da kai. Sun tsorata da gaskiya. Sun tsorata da abin da ka sani”. “Na sani.” Dada ya furta a hankali yana ɗan murmurshi. Shiru ya sake mamaye ɗakin kowa da abinda yake tunani, fin sakan goma ya maida kallonsa kan Imran kai tsaye, kallon da ya tattara shekara uku masu zurfi: jarunta, kewa, hikima, da raɗaɗin da ya gama zagaye zuciyar mutum daga mutum ta zama tamkar dutse. Imran ya katse shirun da faɗin, “Kurakuraina suka kawo ka nan Haysam, zan sadaukar da rayuwata domin ganin ka fita kuma” ya share hawayen da suka sake silalo masa, batare daya bari yayi magana ba ya cigaba da faɗin, “Bayan rufe mu sun sauke COAS shima, sai dai bai daina gwagwarmaya ba, dan yanzu haka da tsayawarsa nazo nan.” Idanu Dada ya lumshe a hankali, batare da kula zancen Imran na farko ba ya furta, “ALLAH ya saka masa da alkairi, dama nasan ba zasu barshi ba shi da duk masu goya mana baya. Imran… ka dawo min nan idan ka samu lokaci. Muna da magana mai tsawo. Kuma kada ka sake jin damuwa. Kai kaɗai ne wanda ban taɓa zargi ba.” Idanun Imran suka sake zubo hawaye saboda wannan kalmomi na ƙarshe. Cikin jinjina kai ya ce, “Zak… har abada damuwa bazata barni ba in har kana a wannan wajen. Dan haka bazan taɓa barin ka a nan ba har abada”. Dada ya yi murmushi. Ba mai annuri ko farin ciki ba. Murmushi ne kawai irin na jarumta da taurin zuciya. Shi yasan fitarsa a wannan wajen sai wani ikon ALLAH, amma ba abune mai sauƙi ba. “Karka damu Imran. Ina a nan ne. Amma ba zan tsaya nan ɗin ba kamar yanda ƙaramin tunaninsu ke basu”. Sai ya jingina da kujera yana ɗan lumshe ido. “Kamar yanda na gaya maka kai ƙoƙari ka dawo. Idan ba haka ba ka fara zargina da guduwa, dan babu gudu babu ja da baya sai na ƙarasa wannan aikin”. Tabbas Imran ya tabbatar da alwashinsa cikin idanunsa da suka sake rikicewa, ya kuma san wanene Zak-Shadow ɗinsa, kaɗan daga aikinsa ya aikata dukkan abinda ya ƙudurta. Zama ya gyara cikin sassauta murya dan baya son akai ga matakin da Haysam ke harin saboda komai zai sake jagulewa ne. “Dan ALLAH kar akai ga haka MAZAN FAMA. Ina sha ALLAHU zan dawo. Zan dawo duk rintsi, zan......” Motsin buɗe ƙofar da ake yi ya katse Imran. Sojojin ɗazun ne suka dawo, hakan ya sasu fahimtar lokaci ya cika. Dan haka kafin ma suyi magana Dada ya miƙe abinsa, sai kuma ya ɗan zubama Imran ido na sakan ɗaya, kafin cikin dakakkiyar muryarsa ya furta, “Imran…” Imran ya ɗago kai yana kallonsa fuskarsa cike da damuwa da kewa.. Ƙaramin murmushi yay masa, tare da furta, “Ka tsare min kanka. Daga yanzu ka saka a ranka sabuwar ƙaddara ta fara motsi.” Daga haka ya juya abinsa yay gaba, ya bar Imran cikin shiru mai nauyin da bin bayansu da kallo, idanunsa cike da hawaye, dan a wannan ƙadamin yama manta da kansa a matsayin soja.......
<<>><<>><<>><<>> Imran ya ɗan sake murmusawa yana shafa kai, cike da girmamawa ya ce, “Sir zan sha ruwan dai, abinci kuwa amin afuwa kada madam tayi fushi nabar nata”. Ƙaramar dariya Genaral yayi duk da kuwa shima ba mutum ne mai yawan fara'a ba. Cike da dattako ya ce, “Gaskiya bazan so ɗiyata kam tai fushi ba. Amma duk da haka sai kaci, dan na saka an shirya maka ne na musamman”. Babu yanda Imran ya iya dole ya haƙura suka hau teburin cin abincin da aka cika da kayan daɗi. Sai da suka fara cin abincin cikin nutsuwa falon shiru janar ya katse shirun da faɗin, “Ina fatan babu wata damuwa tare da Haysam? Yana cikin ƙoshin kafiya?”. Sai da Imran ya haɗiye abincin bakinsa sannan ya jinjina kansa, sai dai fuskarsa ta janza zuwa damuwa. “Alhamdullih Sir. Babu wata bayananniyar damuwa ta zahiri. Dama kuma mun san bayan killacewa babu abinda zai yarda ya ɗauka ga wani na ƙasƙanci in dai Haysam ne. Dan har yanzu JININ MAZA na'a kan FARCE”. Sosai Janar yay murmurshi mai faɗi. Ya ɗauki ruwa yana tsiyayawa a kofin gilashi. “Wato Imran da ƙasar nan tasan asarar da tayi na killace Haysam na kwana ɗaya kawai data jima da yima kanta da kanta ALLAH ya isa. Balle ma ace na tsawon shekaru uku da wasu watanni. Irinsu Haysam a ƙasa tamkar hasken diamond ne a tsakiyar sahara. Amma ban san miyasa ba, maimakon aga haskensu anfi kallon wahalar ɗakkosu da gujewa zafin saharar ne da yawanta..” “Sir bazasu fahimta ba, irinku ƙalilanne ke fahimta saboda zukata masu ƙyau da ALLAH ya baku. Amma wlhy a tsayin rayuwata ban taɓa cin karo da mutum mai tsananin kishin ƙasa da son cigabanta ba irin Haysam. Mutum ne shi mara tsoro, mai tsayawa akan gaskiyarsa koda kuwa ace zata ƙona shi. Sannan yana so da sauri, shiyyasa yake komai da sauri. Amma na rasa miya tare musu?”........✍️