
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 5
..... their attention is on him. In the language they were talking about, he said, "We should do what we need to do, we don't have enough time." "Of course it is Black Spider. Now who is at our table?". Sitting up Black Spider, he calmly picked up the remote and clicked. The image of Zak-Shadow appeared on the body of a giant missile that took up almost half of the wall, a solid soldier, and the picture below is indeed a male hero, and he is in his work uniform, and the signs confirm that he is at work. But the way they all took a breath at the same time will give you proof of that. Black Spider began to speak like this, "This man has destroyed our plans in the east and the west in an incalculable amount. We allowed him to be more powerful than us, and he gave him a chance to play before we changed his style of music. It's time for us on this side. Although our Target Zak-Shadow continued to be an obstacle to our plans. Many of our strategies failed in front of him. But now, when we wait for it to arrive.....
5
.......Falo ne babban gaske, sai dai gaba ɗaya an kashe fitulun cikinsa sai wasu candles da basufi uku ba kacal aka bari suna ci, suma a cikin kwalba suke dan haka haskensu baida tasiri mai yawa sosai. Yanayin duhun wajen ya ɓoye ainahin fuskokin mutanen dake zaune a cikin falon harma da sirrin tsarinsa, koda yake fuskokinsun ma a rufe suke da facemask ta yanda koda ace akwai hasken wutar baka isa tantance su wanene ba. Cikin wani ɓoyayyen harshe suke magana, harshen da babu makamncinsa a ƙasarmu. Sai ɗan ƙarar kofuna alamar akwai abinda ake sha, sai ko room hitter dake basu ɗumi saboda yanayin sanyi da ake ciki. (Waɗan nan sune manyan munafukan shaiɗanci, kowannen su nada laƙabin suna, dan babu mai amfani da sunansa na yanka balle kasan ainahinsa a addini ko yanki balle harshen yare. Hasalima gamayyace daga ɓangarori ta waje da cikin gida). Ɗaya daga cikinsu ne ya ajiye kofin shayin hannunsa, tare da yin gyaran murya. Lokaci ɗaya abokan zaman nashi duk suka nutsu, tare da maida dukkan hankalinsu garesa. Cikin harshen da suke maganar ya furta, “Ya kamata muyi abinda ya tara mu, dan bamu da lokaci isashshe”. “Tabbas haka ne Black Spider. Yanzu minene a teburin mu?”. Zama Black Spider ya gyara, tare da nutsuwa sosai ya ɗauki remote yana dannawa. Hoton Zak-Shadow ne ya bayyana a jikin ƙaton majigin daya cinye kusan rabin bango, tsayayyen jarumin soja, da ko'a hoton kasan eh da gaske Gwarzan maza ne, dan kuwa a cikin uniform ɗin aiki yake, alamu kuma sun tabbatar yana kan aiki akai masa hoton batare daya sani ba, hakan kuma bai hanashi fita da ƙyau ba kuma tartar har kwarjininsa na dukan zukatan maƙiya koda basu bayyana a fili ba. Amma yanda duk suka ja numfashi a lokaci guda zai baka tabbacin hakan. Black Spider ya fara jawabi kamar haka, “Wannan mutumin ya lalata shirye-shiryemu a gabashi da yammaci da yawan gaske da bazasu ƙididdigu ba koda a kintace. Mun ƙyaleshi badan yafi ƙarfinmu ba, sai dan bashi dama ya gama taka irin tashi rawar kafin mu canja masa salon kiɗa. Lokacin mu ya yi a wannan gaɓar. Duk da a baya Target ɗinmu Zak-Shadow ya ci gaba da zama cikas a shirye-shiryenmu. Dabarun mu da yawa sun durƙushe a gabansa. Amma yanzu, lokacin da muke jira ya iso garemu, wato dama ta dawo hannunmu.” Cikin wata ƴar iskar dariya Viper ya amshe zancen da murya mai taushi amma cike da shaiɗanci irin ta shaiɗanun azzalumai, “Kamar yanda Black Spider ya faɗa a yanzun nan babu jimawa mun tabbatar da bayanin sirri ta hanyar yaran Dagger. Zak-Shadow ya bar sansaninsa na tsaro domin wata tafiya ta sirri a jejin, sai dai bamu san inda ya nufa ba, amma hakan mu ba damuwarmu bace kai tsaye, duk da dolene mu sani dan aikinmu ya tafi yanda ya dace akansa. Wannan shi ne gibin da ba zai taɓa tsammani ya bari ba a gaɓar da zai fuskanci illarmu mai muni, dan zamu zuba masa dafinmu mai ƙarfi da har abada babu makarin warkewarsa a zuciyarsa”. Dariya suka kece da ita a tare, sai kuma suka koma tsitt kowa ya nutsu. Dagger da sam bai dara ba sanda ake dariyar, sai ma danna hannunsa da yake a kan tebur da ƙarfi cike da fusata, dan shi kaɗai yasan adadi tsanar da yayma Zak-Shadow a duniyar nan, saboda shine ya kashe masa ƙaninsa a wani hari na bayanan sirri da basu san yaya akai Zak-Shadow ɗin ya bankaɗo ba a kansu. Cikin kaushin harshe ya fara faɗin, “Sirs! Nayi muku alƙawari gamu mayaƙanku ba za mu bari wannan dama ta sulale ba! Dole mu kafa tarkon da zai karya ƙarfinsa gaba ɗaya. Zan jagoranci ɓangarena da ƙyau kuma da tabbatar cikar buri fiye da baya! Dan ina son da hannuna na gurfanar da shi a ƙasan ƙafafu na cike da ƙasƙanci da wulaƙantarwa. Dolene ya ɗanɗani fiye da abinda na ɗanɗana a wancan karon, da ace zaku bani dama bashi ba kaf ahalinsa sai na shafe babinsu a doron wannan ƙasar, na kuma........” Mr Specter ya katse shi cikin jan girma, dan kuwa dukansu Dagger matsayin yaronsu yake, matsayinsa kawai shine shugaban mayaƙansu, hakan na nufin amfani ake da shi domin cimma manufa, kawai dai ita tunkunyar sharri ba'a banbance farfesun kayan ciki a cikinta, haɗawa ake har kashin dabbar da ruwan
*_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._