
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 48
.....reproduce. I have never heard any bad behavior of Dada in the house except his elders". "There is no foreigner Naja, they are hiding the truth because of you. But from him to Imran, they were closed. Later, Imran went in and out because of his wealthy father and was expelled at the age of three. Don't be surprised that they have privileged you, because that is what he planned to do to you to bury this truth that I am telling you today. Zak-Shadow has gone beyond what you think, and no matter how serious the people of this house, even his mother and Imran, will not do anything that is not the order of Zak-Shadow. But I'm telling you to go and research carefully from now on for a month. I know you will look for me again by yourself, even though I know they can change the story for you because they hide the truth about killing your parents. But instead of asking them since you are a schoolgirl, research what happened in Bankaura area in 2013 and you will get all your answers. If you ever need to see this number again, you can ask for it. Here's this, if you can calm down, look at them...” Nimrah barely answered one letter, but her heart was heavy and she said, “Har yan.....
........“Zaki san wacece ke nan gaba kaɗan Naja. Su kuma mutanen nan baki da wata alaƙa da su face riƙo”. “Riƙo!?”. “Tabbas riƙo. Shi sojan nan da kikaga ya kashe mahaifiyarki nan da tsohon nan Kakanki ya kuma bada umarnin a kashe yaran nan a kuma tayar da bomb a cikin gidan shine ya kawoki gidan. Bari na fito miki a mutum. Sunansa Haysam Abdul-rasheed Shehu, soja ne mai muƙamin Lieutenant Colonel a lokacin da waɗan nan abubuwan suka faru shekara takwas kenan.......” Tsaff ya kwashe labarin komai ya bata shekaru takwas da suka wuce. Sai dai labarin ya bata shi ne a yanda suka tsara ba'a yanda yake gaskiya ba. Daga ƙarshe ya ɗora da faɗin, “A dalilin wannan kisan gillar da yay ma nahaifin Ummanki da Ummanki da danginku da mahaifinki ne aka kamashi aka rufe a prison. Shine har yanzu yake can a ɗaure....” Cikin matsanancin ruɗani Nimrah ta furta, “Taya zan yarda da kai. Bayan su sunce su yana ƙasar waje? Mutanen nan fa sunmin komai a rayuwa, fiye da yanda wasu iyayen na kema ƴaƴan da suka haifa. Ban kuma taɓa jin an faɗi wani mugun hali na Dada a gidan ba sai alkairansa”. “Babu wani ƙasar waje Naja, suna ɓoye gaskiya ne saboda ke. Amma daga shi har Imran akan haka aka rufesu. Daga baya shi Imran saboda babansa mai kuɗi ne ya shiga ya fita aka fiddoshi a shekara uku. Kada kuma kiyi mamaki dan sun miki gata ai, saboda abinda ya tsara suyi miki kenan dan a binne miki wannan gaskiyar da nake faɗa miki a yau. Zak-Shadow ya wuce duk yanda kike tunani, kuma komai tsanani mutanen gidan nan har mahaifiyarsa da Imran bazasu yi abinda ba umarnin Zak-Shadow ɗin ba. Amma na baki dama kije kiyi bincike a hankali daga nan har wata ɗaya. Nasan zaki sake nemana da kanki, duk da nasan zasu iya canja miki labarin saboda su ɓoye miki gaskiya akan kashe miki iyaye da yayi. Amma maimakon su ki tambayesu tunda ke ƴar makaranta ce kiyi binciken miya faru a yankin Bankaura a 2013 zaki samu dukkan amsoshin ki. Duk randa kika buƙaci sake gani na number ɗin nan dai zaki nema, koda wani abu ne ya shige miki a bincikenki ki kirani kawai zan baki haske akan ko miye. Ga wannan idan kin samu nutsuwa ki duba su...” Da ƙyar Nimrah data amshi ledar daya batan ga zuciyarta tai nauyi ta furta, “Har yanzu bai zama lallai na yarda da kai ba, amma kuma bazan ƙaryataka ba, dan zuciyata na matuƙar rawa da abinda na gani a videos ɗin can. Amma na barma UBANGIJI komai ya bayyana min gaskiya batare da ya barni da wayona ko dabarata ba. Idan kuma ta tabbata hakan ta faru Daddy Imran.....” ta kasa ƙarasawa saboda hawayen da suka ziraro mata. Sharesu tayi da cigaba da faɗin, “Kai ma ya kamata nasan waye kai?”. “Naja'atu ba yanzu ba. Amma na miki alƙawarin nan gaba kaɗan zaki sani. Amsa ɗaya zan baki dan rage damuwa akai na. Ni ɗaya daga cikin ahalinki ne, wata rana kuma zaki tabbatar da ni dake jini zai zama ɗaya”. Bata wani fahimci kalamansa na ƙarshe ba. Ba kuma ta nema son sani ba dan basu ne masu muhimmanci a gare ta ba. Shima sai bai sake magana ba, dan ya fahimci a yanzu shiru take buƙata. Motar kawai ya tayar ya koma makaranta. Cikin sa'a ya samu an fito break, sauka tayi batare da masa magana ba balle sallama, ya bita da kallo yana murmurshi, sai dai ita ko waiwayensa batai ba ta ƙarasa gaban gate inda securitys suke. Bai san mita gaya musu ba suka barta ta shige.. shima sai ya tada motar yabar wajen ransa cike da nishaɗi yau gashi ga Nimrah har sunyi magana. Ji yake kamar ya warware speakers yay ta rawa a hanya. Amma ko baiyi a yanzu ba zuwa dare dole yay party.....
★
“Ke kuwa daga ina kike haka?”. Ruky ta faɗa tana kallon Nimrah cike da tuhuma. “Ina baya ne zaune kawai”. Itama Nimrah ɗin ta bata amsa batare data kalleta ba. Gaba ɗaya sai Ruky taji wani abu mai nauyi ya tsaya mata a maƙoshi. Sai kawai ta ɗauke kanta bata sake mata magana ba. Sai ma kular abincinsu data tura mata. “Kinci ne?”. “Uhmm”. Ruky ta bata amsa a daƙile tana tashi tabar wajen. Sai kuma duk Nimrah taji babu daɗi. Riƙo hannun Ruky ɗin tai kawai da sauri ta rungumeta. Ruky zata kwace Nimrah tai saurin faɗin, “I am sorry my luv.” “Wace luv ɗin. Kima daina yaudarar kanki Nimrah. Amma zan baki shawara ɗaya, koma mi kike ɓoyewa a kwanakin nan ki tabbatar ba abinda zai ƙona ki ko ruguza rayuwarki bane. Komi zakiyi ki dinga tunawa da UBANGIJI mai jinki mai ganinki. Bana zarginki da aikata komai mara ƙyau kona rashin ɗa'a, amma zuciyata na rawa da hangen-hangen abubuwa masu yawa.” “Nagode da kikai min kyakkyawan zato, kuma ki cigaba da min, dan in sha ALLAHU har abada bazan taɓa aikata wani abu na saɓama UBANGIJI ba. Abinda kuma kike tunanin ina ɓoyewar ma nan gaba kaɗan zaki sani ba mummuna bane. Amma Please ki bar fushi dani. Fushi da juna na nufin sheɗan yaci galaba a kanmu, mun kuma yima kammu alƙawarin babu shaiɗan a tsakkiyarmu har abada duk tsanani”. Sai da Ruky ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan ta ce, “Haka ne ki yafe min” daga haka ta rungume Nimrah, itama rungumeta tai suka shirya.......
>>>>>>>>✷‿✷<<<<<<<<< ★BAYAN WATA BIYU★
7:00am
“Mammah!!” “Mammah!!!”. Muryar Bilal ya karaɗe gidan cikin sauti mai tada hankali yana sakkowa daga upstairs da steps bibbiyu. Ba Mammah kaɗai ba hatta su Ruky da gudu suka fito daga ɗakinsu, dan Nimrah ma daga bayi ta fito wanka, ALLAH ma ya sota bathrobe ce ba towel ba. Biebah ma wandon kayan barci ne kawai a jikinta sai best, sai dai ta yayimo hijjabin salla a hannu batare data saka ba. ALLAH sarki Mammah ita kam tana cikin ruturarta, dan har tayi wanka kasancewar ta mai wankan wuri. Dan tana idar da sallar asuba tai azkar wanka take fara yi kafin ta fito. A yanzu ma kammala shirinta kenan tana son fitowa tama su Nimrah magana su shirya su rakata gaishe da Baffa wannan kiran na Bilal yay mata amsa kuwwa. Jikinta har rawa yake wajen ƙoƙarin fitowa a ɗakin saboda tsabar jin tashin hankali. A ƙofa sukai karo da Bilal ɗin da waya a hannu. Rungumeta kawai ya fashe da kuka yana faɗin, “Mammah Dada! Dada Mammah shugaban ƙasa....” ya kasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙesa. Dai-dai nan kuma Ja'afar da Ma'aruff ma suka shigo suma a kiɗime. Sai ga Ammar da Mu'azz suma daga sama. Kuma kowa da waya a hannu Mammah kawai suke ƙwalama kira. Rikicewa Biebah da su Nimrah sukai, sai kawai Biebah ta koma ɗaki da ɗan gudu ta ɗakko wayarta. Yayinda Nimrah da Ruƙayya suka nufi Mu'azz suna tambayar abinda ke faruwa. Dan su Uncle Ma'aruff gaba ɗayansu sun rungume Mammah ne suma suna kuka. Hawaye Mu'azz ya share yana miƙa musu wayarsa, a tare suka amsa, rubutu kawai suka gani a X, kafin ma su sake tambaya cikin kuka Mu'azz ya ce, “Ku karanta”.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida (RTD) ya fitar da sanarwa a shafinsa na X kamar haka.
★★Bayan cikakken nazari da sake duba shari’ar da ta shafi Haysam Abdul-Rasheed Shehu, wanda aka fi sani da Zak-Shadow, Gwamnatin Tarayya ta fahimci cewa an samu kura-kuran shari’a da suka shafi yadda aka gudanar da bincike da hukunci a wancan lokaci. Bisa ga ikon da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar ƙasa ya bai wa Shugaban Ƙasa, tare da shawarwarin hukumomin shari’a da na tsaro, Shugaban Ƙasa ya amince da ba da cikakkiyar afuwa ga Haysam Abdul-Rasheed Shehu. Wannan mataki ba wai hujja ba ce ta cewa an warware dukkan tambayoyi da ke tattare da shari’ar, sai dai wani yunƙuri ne na tabbatar da adalci, kwanciyar hankali, da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam★★. A ƙarshe Gwamnatin Tarayya na kira ga al’ummar ƙasa da su zauna lafiya, su guji yaɗa jita-jita ko ɗaukar doka a hannu, yayin da hukumomi ke ci gaba da aikin su bisa doka da ƙa’ida. Wannan ƙasa ce mai doka da zaman lafiya, kuma babu wanda yafi ƙarfin doka.