Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 49

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 49

.....he will attend for three days. Woke up, rabbi, and the fire increased. The sky is looking for shaking the country as a whole. Especially when the information about Zak-Shadow himself was found, there is a secret back in prison. Government House has refused to say anything more since that announcement until late at night. The last thing is to put a security guard to surprise everyone in their neighborhood Mammah, especially the door of their house. Within an hour, soldiers were brought to the neighborhood and surrounded their house. Even those related to them such as Uncle Nasiru who would enter the house had to be searched and cleared. Even Aunty Mommy who arrived also had to tell them that. This has once again confirmed to everyone what is important, especially the media who have already gone to the corner of radio, television and social media to follow the trend. But when they got the house they had to be patient, and then they started talking about Zak-Shadow because he was not healthy enough, that's why he was taken to the house and security was put in place and his condition was not seen. This issue has raised a new issue. Citizens, politicians, and foreign pirates starte

Standalone post1,687 words

49

.........Ba gidan Mammah kawai ba a wannan safiya ƙasar ce gaba ɗaya data wayi gari da wannan batu ke neman rikicewa. Ya rabbi, kwatanta muku irin yanda ƙasar ta ɗauki al'amari bazatar nan da shugaban ƙasa yay ma kowa ɓata lokaci ne. Domin kuwa ƙura uku ce ta tashi a lokaci guda. Masoya masu farin ciki da godema UBANGIJI. Manyan azzalumai da hankalinsu ya tashi dan Janar ya mamaye su. Yara matasa irin su Nimrah da basu san miya faru ba. Dan haka suka fara neman bayanai akan dalilin rufe wannan gwarzon haziƙin soja da aka tashi a wannan safiya da zancensa tako wace manhajar social media. Dan gaba ɗaya media tamkar zata fashe ne da wannan batu da hotunan Zak-Shadow da aka rasa ma daga ina mutane ke samo su. Kafofin sada zumunta, gidajen rediyo, gidajen tv. Jama'ar gari, zaka rantse fitowar tasa ce kawai abu mafi muhimmanci a wannan satin a ƙasar... Babbar tsiyar da shugaban ƙasa ya tafka musu kuma ana fitar da sanarwar aka kuma sanar da barinsa ƙasar wani babban taro zuwa ƙasar waje da zai halarta na kwana uku. Wayyo ya rabbi, ai sai wutar ta ƙara sama. Saman data nema girgiza ƙasar gaba ɗaya. Musamman da aka samu bayanan shi kansa Zak-Shadow akwai ƙishin-ƙishin ɗin baya cikin prison. Gashi gidan gwamnati sunƙi sake cewa komai daga waccan sanarwar har zuwa yanzu da dare ya ratsa. Abu na ƙarshe zuba wani masifaffen tsaro daya bama kowa mamaki a anguwar su Mammah musamman ƙofar gidansu. Dan ko awa ɗaya ba'ai da sanarwar ba aka kawo sojoji anguwar suka zagaye gidansu. Hatta masu alaƙa da su irin su Uncle Nasiru da zasu shiga gidan sai da aka bincike su tsaf. Ko su Aunty Mommy da suka iso suma sai da akai musu hakan. Hakan ya sake tabbatar ma kowa abin da babbane, musamman ƴan media da tuni suka yoma anguwar tsinke na rediyo dana television harma dana social media dan son bin ƙwaƙwaf. Sai dai yanda suka samu gidan dole suka haƙura, sai kuma suka fara juya maganar akan Zak-Shadow baida isashiyar lafiya ne shiyyasa aka kaishi gida aka zuba tsaro kuma dan kar a ga halin da yake ciki. Wannan batu ya sake tada sabuwar magana. Ƴan ƙasa da ƴan siyasa da masu fashin baƙi suka fara kai-kawo da ka-ce-na-ce. Wasu suna sukar shugaban ƙasa, wasu suna yaba ma abinda yayi. Yan bani na iya na haɗa hotunan karya da videos a social media a zuwan Zak-Shadow ne aka fitar a prison magashiyan cikin raunuka da galabaita. Kai wani fa idan ya tsara maka batun ga abinda ya faru sai ka rantse a gabanshi akai komai ma......

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ ★JAMUS★

Yanayi ne mai armashi da ni'ima dake kaɗawa a irin wannan lokacin na yammaci a ko'ina ma kake a duniya. Koda lokaci ya banbanta ƙasashe irin wannan yanin a kowacce ƙasa yana da tasiri sosai saboda yakan zama abin so ga kowa, musamman mutane masu nutsuwa da rashin son hayaniya. Zaune a balcony ɗin ɗakin hotel ɗin nutsatstsen matashin dattijo ne cikin yanayi na ƙasaita da nutsuwa. Yanda ƙafafunsa ke harɗe a zama irin na izza zai tabbatar maka da kasancewarsa cikakken mutum. Sanye yake cikin ƙananan kaya da sukai masa ƙyau sosai kalar ruwan madara marasa nauyi. Hakan ya bayyana cikakken jikinsa dake a buɗe musamman daga sama, sam ba siriri bane, ba kuma yi da ƙiba mai yawa dan har yanzu ainahin jikinsa bai gama dawowa ba. Sai dai ko a haka ƙarfinsa a bayyane yake na ma'abota lafiya da cikar kamala. Gaba ɗaya hankalinsa yana akan littafin hannunsa ne da yake nazari, da ganin littafin kasan mai matuƙar amfani ne. Sosai hasken fatarsa ya sake washewa, ƙasumbar daya tara tun a prison na nan bai kwashe ta duka ba daga fuskarsa, sai dai yanda take kwance luff da style ɗin gyara na musamman zai baka tabbacin yana samun kulawa, dan harda wasu ƴan tsilli-tsillin gashi da sukai fari alamar furfura ta baiwar matsawar shekaru na cikar kamalar girma. Yanda siririn farin gilashin daya sanya ya zauna masa a kan nutsatstsiyar fuskar tasa ko kaine hasidin iza hasada dole ka furta masha ALLAH. Balle ga wani ƙamshinsa mai natsuwa daya cika wajen. Gefensa kaɗan ƙaramin coffee table ne da mug daketa turiri alamar coffee ɗin ne a cikinsa. A hankali yakai hannunsa da ƙumbar ke fes-fes batare da ya ɗauke idonsa daga kan book ɗin ba ya ɗauki kofin. Kan lips ɗinsa dake dai-dai da taswirar fuskarsa ya kaishi yana mai kurɓar coffee ɗin da alamu suka nuna dole zai yi zafi. Dai-dai nan aka buɗe ƙofar glass ɗin wajen data kasance mai bango guda. Duk da yaji an buɗe ɗin bai kalli wajen ba, bai kuma dakatar da kansa daga abinda yake ba har mai buɗe ƙofar ya bayyana. Ba kowa bane face Daddy Imran, shima dai sanye yake cikin ƙananun kayan tamkar Dadan. Hannunsa riƙe da tab... Da shima hankalinsa ke a kanta gaba ɗaya. A haka ya gyara kujerar gefen sa ya zauna yana faɗin, “Hummm wai kasan mike faruwa kuwa yau a gida Zak...?”. A karo na farko Dada ya ɗan ɗaga ido ya kallesa, sai kuma ya maida kan book ɗinsa yana buɗe shafi na gaba. Sai a lokacin ne cikin golden voice ɗinsa dake fita a nutse ya furta, “Miyasa baka son hutar da kanka”. Murmurshi Daddy Imran yayi da faɗin, “Ai ba abinda kake tunani bane. Takardar yi maka afuwa ce ta fita daga fadar shubagaban ƙasa a yau. Daga bakin mai magana da yawunsa a shafinsa na X.” A yanzu kam sosai Dada ke kallonsa. Hakan yasa Imran miƙa masa tab... Ɗin. “Duba ka gani, dan ƙura ta tashi fa. Yanzun nan Faro ma yay kirana ya ƙara min bayani”. Tab... Ɗin Dada ya amsa bayan ya kife book ɗinsa a saman cinyarsa, ya kai hannu ya ɗan gyara gilashin idonsa. Shi ke karatun amma Daddy Imran ke faman murmurshi, zuciyarsa na ƙara cika da jin ƙaunar Janar Yusuf Shu'aibu Tafida. A hankali Dada ya furzar da iska daga bakinsa yana ajiye tab... Ɗin a coffee table ɗin tsakkiyarsu. Sai kuma ya jingina bayansa da kujerar ta lumshe idanunsa yana sake furzar da iskar. Fin sakanni talatin yana a hakan Imran dai bai ce masa komai ba dan yasan akwai abinda yake nazari. Har sai da ya ɗago dan kansa yana mai sauke birkitattun idanunsa a kansa.... “Akwai matsala ne?”. Imran ya katse shirun nasa da kallon da yake masa. Anan ma sai da yaja kamar minti ɗaya kafin ya girgiza kansa, sai kuma ya motsa lips kaɗan ya furta, “Imran, da nasan Janar zai yi hakan da na bashi shawarar kar yayi”. “Mi yasa?”. “Fitar da wannan afuwar tamkar zaburar da su ne a kansa.” “Ni kuma sai nafi tsoron bats tashi zasuyi ba ta kai zasuyi. Dan Faro ya sanar min yanzu haka gidan soji ya ɗauki zafi da ƙananun magana. Suma ƴan siyasa nayin nasu”. “Wannan dole zata faru ai, baka fahimceni bane. Shima Janar ya manta yanzu shi ɗan siyasa ne ba soja mai iya bada umarnin da za'abi ba koda ba'a so kuma dole ai shiru. Amma a siyasa koda a zahiri akwai shiru to a baɗini za'a samu matsin lamba ta cikin gida”. Kai Imran ya shiga jinjinawa, dan ya fahimci abinda Dadan ke hangowa. Cikin sauke ajiyar zuciya ya ce, “Na fahimceka yanzu kam. To yanzu minene mafita? Dan shima ana sanar da afuwar yana barin ƙasar fa”. Karo na farko Dada ya saki ƙaramin murmushi, sai kuma ya taɓe baki kaɗan yana shan coffee ɗinsa da kallon Imran. “Imran dole zamu koma gida a satin nan....” “Amma Janar yana so ka huta da ƙyau, idan son samu ne ma kamar wata biyar”. “Bamu da wannan isasshen lokacin. Idan kuma mukai wannan sakacin za'a mamayemu a gaɓar daya kamata ace mune mukai mamaya. Ka kirashi yanzu....” daga haka ya miƙe. Imran ya bisa da kallo har ya ɓace masa. Kafin ya sauke ajiyar zuciya da furzar da iska mai nauyi yana zaro wayarsa a aljihu. Sai da ya fara nazartar time ɗin ƙasar da shugaban ƙasa yake a yanzu kafin ya rubuta text message ya tura masa. Daga haka ya miƙe shima yana ɗaukar tab... Ɗinsa da kofin coffee ɗin da Dada bai sha ko rabi ba ya koma ciki dan lokacin sallar magrib yayi.....

<<<<<<•>>>>>>> Duk wani masoyi na gaskiya yau Mammah ta amsa wayarsa. Har sai da takai ta ma fara gajiya da amsa wayoyin su Aunty Ummi suka koma tayata. Wasu ma ko gane su basayi. Kai da ka ga mutanen gidan a yau kasan farin cikinsu ya canja matuƙa, canji kuma mai girman gaske. Dan bakin kowa yaƙi rufuwa. Mammah kam ta yini ne da tasbihi a baki na nuna godiya ga UBANGIJI, duk da hakan sabone a rayuwarta mace ce mai yawan ibada. Tuni Ja'afar da Ma'aruff sun fita gidajen abinci sunata saya suce a rabawa mutane. Sun kuma turama Uncle Jamilu kuɗi masu yawa sukace acan ma ayi dan mabuƙata sunfi tacan. Duk inda sukaje a fitarsu tare da sojoji ne, dan yau kowaye a cikinsu ya fita a gidan nan sai ya kasance da rakkiyar sojoji. Hatta su Nimrah da zasu tahfiz duk da ma sai da Uncle Nasiru ya korasu dan da sunce bazasu je ba suma dai sojoji suka musu rakiya, hasalima cikin sojojin ɗaya yay driving. Tsabar kuma yanda zaka fahimci shirin fa bana wasan yara bane har a ƙofar ajinsu sai da soja biyu suka tsaya, hakama ajin su Abees da su Afry. A wannan gaɓar Nimrah fa tana a cikin ruɗani ne. Amma tayi jarumtar shanyewa da danne komai a ƙasan zuciyarta ta barma isowar mutumin da duk ake wannan kai-kawo a kansa zuwa gida. Dan har yanzu dai basu ji komai akan batun zai zo gidan ba. Ba Nimrah ce kawai a ruɗani ba a wannan lokacin harda su Malam Buba driver, da Nabeeha dake can gidansu cikin matsanancin farin ciki, dan al'amarin yazo musu a matuƙar bazata kamar yanda yazo ma shugabanninsu. Gashi sai samun kira Malam Buba yake daga su Dagger, suna son jin ko Dada ya iso gida ne.........✍️