Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 55

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 55

.....no one cares about his release from the prison. You should do the right thing before those who are behind it make any move. I'm sure they won't go to sleep these hours." He didn't just listen, the words of the doctor had a great impact on the General's mind. But he smiled with a big smile and said, "If I drink ALLAH, everything will be looked at and the right thing to do. But we can have a problem with the members of the party on the issue of 60-40 positions". "Because of me?". "Because our government belongs to everyone and not the members of the party who think they have a hard time waiting for these results. Even if it is 60-40, let's say that the party also does 30-30 with the rest of the community outside the party. This will increase our evaluation and understand our change from yesterday to today. It is not long before the people of the country have to see the faces of those who have been ruling them since their birth. Only the youth and the nut drinks and politics. One person can become a councillor, become a chairman, become a member of the state assembly, become a governor, become a member of the federal parliament, another party leader, tomorrow a minister, the next

Standalone post1,606 words

55

...........“Baka ganin kayi gaggawa akan fitar da yaron nan kuwa Genaral? Kasan fa ita siyasa shegiyar aba ce a zahirinta da baɗinin ta.” Murmushi shugaban ƙasa yayi mai ƙayatarwa, cike da girmamawa irin wadda ake bama oga, duk da ba wani girmarsa yayi sosai ba, amma a siyasa ubangida zai kira shi. “Ranka ya daɗe a zahiri wasu zasu iya kallon al'amarin a haka. Sai dai idan mukai dubi da gaskiya abinda ya dace ace nayi kenan akan Haysam. Duk wanda yasan shari'ar Haysam a shekara takwas data gabata ya san Shari'a ce ta gaba gaɗi akayi. Dan kuwa an ɓoye muhimman hujjoji da yawa shiyyasa shari'ar ta taƙaita aka rufesa. A yanzu kuma fito da shi zai taka rawar gani mai yawa dana tabbatar kowa zai ji daɗinta.” “Hakane, ni ka cire tani na fahimceka, kuma ina goyon bayanka akan duk abinda zaka yi. Sai dai lokaci yayi da zaka duba ƴan jam'iyya suma. Kayi baɗe-naɗen bada muƙamai a fara gudanar da mulki. Sannan shi Haysam ɗin wane shiri kake da shi a kansa? Dan bayan takardar afuwa baka sake cewa komai ba game da fitarsa a prison ɗin. Ya kamata kayi abinda ya dace kafin masu hannu a rufesa su suyi wani motsi. Dan na tabbatar ba zasu kwanta barci ba awannan gaɓar”. Ba saurare kawai ba, tasiri sosai maganganun ogan keyi a kwakwalwar Janar. Amma sai ya murmusa cike da dattako ya furta, “In sha ALLAHU duka za'a duba ayi kuma abinda ya dace. Sai dai ƴan jam'iyya zamu iya samun matsala da su akan batun 60-40 na muƙamai”. “Saboda mi?”. “Saboda gwamnatin mu ta zama ta kowa da kowa ce ba ƴan jam'iyya da suke ganin sunyi wahala dan jiran waɗan nan sakamakon ba. Idan ma har za'ai 60-40 ya kama ace itama jam'iyya tayi 30-30 ita da sauran al'ummar wajen jam'iyar. Hakan zai ƙara kimantamu a fahimci canjin mu daga na jiya zuwa yau. Bawai akoda yaushe ƴan ƙasa suyita ganin fuskokin da tun haihuwarsu sune ke mulkar su ba. Abar matasa da shaye-shayen ƙwaya kawai da bangar siyasa. Mutum ɗaya kaga yayi kansila, yayi Chairman, yayi Dan majalisar jiha, yayi gwamna, ya koma ɗan majalisar tarayya, wani shugaban jam'iyya, gobe minister, jibi takarar shugaban ƙasa why? A ƙasar mu kawai ake wannan kwamacalar, ai ko a gidanka kullum ake maka abinci kala ɗaya zaka gaji, kuma duk yanda za'aso canja kalar miyyar zakaji ɗanɗanon ɗaya ne dai tunda hannu ɗaya ya girka. Oga mu kalla komai da idon basira mana”. Sosai oga ke jinjina kai da yima kalaman Janar fashin baƙi dalla-dalla, lallai gaskiyar Oga Jush janar Yusuf da shirinsa ya shigo. Ya kwantar musu da kai ne kawai dan samun nasarar kai da kai. Hakan kuma na nufin dole ya ɗanɗana kuɗarsa. A zahiri kam murmurshi yayi mai ƙayatarwa. Cike da makirci ya furta, “Tabbas zancenka nakan gaskiya. Kuma na gamsu kwarai da gaske. Sai dai kuma ta ina ya kamata mu fara? Menene shirin ka kai a yanzu? Musamman ma akan Haysam da kake gani zai iya taka mana wata rawa a mulkin nan?”. Shirye-shirye kam nada yawa oga, bani kuma da hurumin zartar da su sai an zauna tebirin shawara. Akan Haysam kam bani da wani shiri bayan fitar da shi gaskiya. Hasalima bana jin Haysam zai yarda ya koma gidan soja, dan likitoci sun tabbatar bashi da isashiyar lafiya, yana buƙatar dogon hutu a gida ko asibiti. Kaga kuwa bai kamata mu tunkare shi da wani batun aikin gwamnati ba yanzu tukunna. Sai in har ya buƙaci hakan ne da kansa”. Harga ALLAH a wannan gaɓar sai da Oga yaji ajiyar zuciya mai ƙarfi na neman kufce masa. Ya dai danne da ƙyar......

🤣🤣Na lura da Janar ya fara zama makiri hwa shima🤭🏃.

>>>>>>>★<<<<<<<<

Jin ƙamshin daba na Mammah ba bai sa Nimrah ta fahimci inda ta kawo kanta ba. Dan turaren, turare ne da bata san kowa da shi a gidan ba, sannan ba irin shi Dadan yake ba a ɗazun. A maimakon ma fahimta ko tunanin wani abu kasala irin ta mai son yin barci ta risketa. Cike da shagwaɓa muryarta a ɗan ɗashe irin na wadda ta tashi a ciwo da muryar raɗa ta furta, “My Mammah goodnight, ki min addu'a idan kin tashi salla”. Daga haka ta rufe idannunta tana sake naɗe jikinta a jikin da zuciyarta ke bata na Mammah ne saboda rashin man kai... Tun daga buɗe ƙofar ɗakin, shigowarta zuwa hawowa gadon duk a cikin kunensa. Amma da yake mazan maza ne koda ta shige masa a jiki bai motsa ba, baima da niyyar yin hakan face mamakinta daya cika masa zuciya. Idan banda rashin man kai da wautar yarinyar nan taya zata kasa bambance jikin Mammah da nasa. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya daga cikin ƙirjinsa, shi ba abin ya motsa ba ko sanar mata ba Mammah da take tunani bace girma yay tangal-tangal. To mima ya kaishi wannan gangancin, ai gara ya barta kawai yanda ƙafarta ta kawota ta fitar da ita, ko shi zuwa anjima idan tayi barci ya sulale yabar mata ɗakin. Dan da yasan ma suna shigowa kwana irin haka da bai kawo kansa ba shi kam... Tunaninsa ya tsaya cak, saboda yanda ta juyo gaba ɗayanta yana fuskantar sa. Yanda ta sake ƙanƙamesa dole ya lumshe idanunsa dake cike da son yin barci yana ɗan cizar lips. Sai da ta gama mutsu-mutsunta dan kanta ta nutsu tana sake mamuƙeshi sannan ya saki numfashin daya riƙe a cikin ƙirjinsa. A haka ya fara jin saukar ɗumin numfashinta a hankali cikin jikinsa. Tun yana saurarenta har shima barcin yay awon gaba da shi batare da ya farga ba, dan ya gaji matuƙa, ga magunguna da yake sha na saka shi barci dama. Ga hayaniyar daya sha yau tasu da yawan magana da aka saka shi..... Ƙarfe uku dai-dai ya farka, sabo da tashi sallar dare yasa komai nauyin barcin da yake ciki idan lokacin yayi sai ya farka. Idanunsa ya buɗe a hankali, tare da karanto addu'ar tashi barci a saman lips ɗinsa. Ya motsa hannunsa da nufin kunna lamp yaji ya masa nauyi, ya ɗan laluba da ɗayan sai yaji mutum. Abinda ya faru a farkon dare ne ya faɗo masa. Ya ɗan cije lips ɗinsa kaɗan yana kai hannun ƙasan pillow, ALLAH ya taimake sa ya samo wayarsa. Dannata yay screen ɗin ya kawo haske, kai tsaye hasken ya faɗa kan kyakkyawar black beauty face ɗinta. Cikakkiyar girar ido da eyelashes da suka dace da girman idanunta, hancinta dake zaune ɗaram a fuskar tata da madaidaicin bakin tsiwa mai pink da baƙi. Cike da kame kai irin na manyan jarumai da nutsuwa ya janye idanun kai kace baiga komai ba ma. Sai ma zameta ya shiga yi a hankali daga jikinsa data kanainaye dan gaba ɗayanta a rabin jikin nasa take, yanda har ya gyara mata kwanciya ya ja bargon ya rufa mata bata ko motsa ba sai ma filon daya saka mata a madadinsa ta sake kanainayewa ya sashi fahimtar tana da nauyin barci, sannan ta saba da wannan rungume filon shiyyasa shima ta masa ɗaurin goro batare data fahimci shi ba filon nata bane ba. Bedroom slippers ɗinsa ya saka ya fice a ɗakin dan gwara salin alin ya bar mata ɗakin ya koma inda ya baro ya ƙarasa daren kada a tafka abin kunya. Ko'a mafarki bazai so ta buɗe ido ta ganshi ba balle tasan abinda ya faru.....

★Itama saboda da tashi sallar asuba ya saka ta farkawa a kiran sallar farko. Duk da suma Mammah ta horesu da tashi sallar dare tun basu kai hakan ba. Yau ma dan alluran da doctor yay mata ne sukai tasiri wajen ƙara nauyin barcinta yasa har bata farka ba a lokacin da sukan tashin. Cikin lalube take kiran sunan Mammah, sai dai jin shiru da jin gadon empty sai ita kadai yasa ta buɗe idon. Dama tasan da wuya Mammah takai yanzu a gado bata sauka ba, dan ita in har ta tashi sallar ta ta dare bata sake komawa gado kuma sai in barcin rana. Nimrah na buɗe ido ta maida ta rufe saboda ganin duhu. “Mammah baki kunna fitila ba? Wayyo duhu ba ƙyau”. Tayi maganar ne da mirginawa gefen gadon cikin lalube ta taɓa makunnar lamp. A take kuwa ɗakin ya gauraye da haske, sannan ta buɗe idanun. Ɗaki dai shiru babu alamar Mammah a ciki, dan haka ta shiga waige-waige, sai kuma ta zubama inda alamun kwanciyar mutum ta nuna idanu. Ta ɗauke ta maida toilet, sai dai tsin babu alamar motsin ruwa a nan ma, dan haka ta sauka a gadon gaba ɗaya. Kamar yanda suka saba gyara gado da sun farka yasa ta janye blanket ɗin da filos tahau ƙoƙarin gyarawa. Ta kammala tana maida filoluwan idannunta suka sauka akan baƙin agogon dake a side drawer, mai ƙyau da tsada da tambarin sunan mawaad Company. Daga gani kasan an saye shi da kuɗi masu nauyi. Bata kawo komai a ranta ba ta ɗauke idanun nata ta ƙarasa aikinta. Tunanin Mammah na bayin yasa ta fice abinta zuwa ɗakinsu. Ta samu suma su Biebah duk sun tashi, dan daga ita har Ruƙayya akan sallaya ma suke. Ruky na Sallah Biebah na karatun Alkur'ani. Sai ita ma ta wuce bayi abinta. Da yake sheɗan sheɗan ne sai da ta kabbara salla ya tuna mata a hannun data ga agogon nan da rana. Sai ko da ƙirjinta ya buga, da ƙyar ta iya ture tunanin a ranta ta cigaba da sallarta. Suna idarwa kuma suka hau tilawar Alkur'ani dan yau akwai tahfiz akwai kuma amsar hadda. Wannan ya sake mantar da ita batun agogo na wucin gadi.........✍️