Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 54

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 54

.....Lai is the lion of the house, and the shield that takes the role of a father... ✨✨✨✨✨✨✨ Since he entered the room and made sure that everything in it was new, he stood quietly and looked at everything in detail. Everything was prepared more than he needed. To the fragrance of a young heart, I wake up. He slowly sat down on the sofa in the living room, in his humble and dignified posture, he rested his head and closed his eyes, showing extreme fatigue. For the first time, the thought he was repressing came back into his head. He saw everyone from his descendants including the one who was born here but there was no Nabeeha. Where is she going? Since it is the praise of the house and she is not here? Even if she left, no one knows when she will return. Instead of getting these answers to the new picture of his face, it was none other than Nimrah. The girl he left behind was seven years old... now she is a woman, clean, calm, and in a strange way. The worry that he had read about her came to him in the middle of his thoughts, then he was talking to Imran Bilal and he brought in someone else. He didn't speak at that time and Imran got up and praised Bilal, he was there and Imran ca

Standalone post1,898 words

54

.......Afalo kam su Kulu ne ke faman tsaftacesa, dan harsu Ja'afar Mammah ta kora sashensu. Tace kowa yaje ya huta a barma gobe kuma idan ALLAH ya kaimu. Kodan su Lailah dake fama da kansu, musamman ma Shariffa data tsufa da yawa. Badan sun so ba suka wuce, dan Dadan ma tuni yana ɗakinsa dan ya samu ya huta da wannan hayaniyar. Tamkar ba dare ba su Kulu suka gama gyaran ko'ina suka saka ƙamshi. Sai falon ya ƙara zama cikin nutsuwa. Shayin Mammah na ƙa'ida Kulu ta ɗauka takai mata ɗaki, ta sameta zaune tana karatun Alkur'ani, dan haka ta ajiye sannan tai mata sallama dan zasu wuce suma su kwanta yau sun sha aiki, dan ma su Aunty Mimi basu barsu su kaɗai ba sun tayasu. Kai kawai Mammah ta ɗaga mata, ta cigaba da karatunta. Itama sai ta fice tana jin ƙaunar wannan baiwa har ƙasan zuciyarta. Duk da basu san miya faru da Dada ba, yanda ƴan gidan basa gajiya da hirarsa sun san yau suna cikin matsanancin farin ciki da dawowar tasa. Dan ko su yau da ganinsu na farko da shi sun tabbatar lallai shine zakin gidan, sannan garkuwa mai ɗaukar matsayin uba...

✨✨✨✨✨✨✨

Tunda ya shigo ɗakin da komai na cikinsa ya tabbatar sabo ne ya tsaya shiru yana kallon komai daki-daki. An shirya komai fiye da yanda yake buƙata. Ga ƙamshi mai ƙarama zuciya butsuwa na tashi. A hankali ya kai zaune cikin sofar ɗakin, cikin yanayin zamansa na ƙasaita da girma ya kwantar da kansa tare da lumshe idanunsa dake nuna matuƙar gajiya. A karo na farko tunanin da yaketa dannewa ya shiga dawo masa cikin kai. Yaga kowa daga zuri'arsa harma da wanda aka haifa baya nan amma babu Nabeeha. Ina ta shiga? Tunda yabar gidan ne itama bata nan? Ko tayi tafiya ne tunda babu wanda yasan da dawowar sa. Maimakon samun waɗan nan amsoshin sabuwar hoton fuska ya gitta masa a brain, ba kowa bace sai Nimrah. Yarinyar da ya bari tana shekara bakwai… yanzu ta zama mace, cikin tsabta, nutsuwa, da wani yanayi mai ban mamaki. Damuwar da ya karanta a tattare da ita tazo masa a tsakkiyar tunani, sai kuma sanda yake magana da Imran Bilal ya shigo da wani, wanin da yaji sun kira doctor wai zai dubata bata da lafiya. Baiyi magana ba a lokacin sai Imran ma ya tashi yabi Bilal ɗin, yana gurin kuma har Imran ɗin ya dawo, shi kuma bai tambayi abinda ya faru ba, Imran ɗin kuma yaƙi faɗa masa komai suka cigaba da maganarsu. Ji yake acan wani sashe na zuciyarsa kamar ya kamata yasan mike damunta. Koba komai ita ɗin AMANARSA ce ai... Idanunsa ya buɗe tare da ture tunane-tunanen ya miƙe. Kai tsaye ƙofar da yake tsammanin ta bathroom ce ya nufa, dan gwara yaje yay wanka ko zai samu nutsuwa daga waɗan nan shirmen tunanin nasa...

Ƙarfe goma dai-dai ya kammala kimtsawa cikin kaya marasa nauyi daga akwatin kayan da sukazo da shi daga Germany. Ya saka turare kaɗan. Maimakon kwanciya sai ya nufi hanyar fita, dan yaji hira da Mammah kawai yake buƙatar yi. Bai san suwaye da waye a upstairs ɗin ba. Bai kuma yi tunanin leƙa kowane ɗaki ba ya sauka ƙasa. Tunkan ya gama sauka a stairscase ɗin ya fahimci babu kowa a falon. Dan hatta fitilu sa ma an kashe. Ƙaramin murmushi iya lips ya kufce masa, dan yasan aikin Mammah ne wannan, in ba haka ba yaran nan zasu iya kwana suna hira basu gaji ba balle tunawa da gidajen auren su.

Ƙofofi huɗu na corridor ɗin daya tabbatar bedroom ɗin Mammah na cikinsu ya zubama ido, bai san wanne ne ɗakin ba, amma yana ƙyautata zaton na farko ne. Duk da haka sai da yay kusan sakan biyu kafin yay knocking ƙofar. Daga ciki Mammah dake ƙoƙarin rufe Alkur'ani ta juya tana kallon ƙofar, sai kuma ta furta, “Waye? Shigo”. “Uhhmm”. Ya faɗa cikin maƙoshi tare da murza handle ɗin ƙofar. Cikin takunsa na nutsuwa da ƙasaita ya tura ƙofar ya shiga da sallama mai cike da girmamawa.. A jiyar zuciya mai nauyi Mammah ta sauke da jin muryarsa, kafin fuskarta ta washe da murmushi mai sanyi tana mai zuba masa raunanan idannunta. Sai da ya kai zaune kusa da ita, sannan ya furta, “My Sweet Mammah”. Murmurshi Mammah ya ƙara ƙawatuwa, jin komai take tamkar a mafarkin data saba. Cike da jin nutsuwar zuciya na tuna zahiri ne ba mafarki ba ta furta, “Na zata yanzu kamayi nisa a barci Muhammad”. “Mammah na kasa barcin ne, shiyyasa na taho kawai muyi hirarmu mu more, hira ta zahiri ba wadda nake gani a mafarkina ba. Ina yaran naki? Naji gidan shiru tun 10”. “Duk na kora kowa makwanci, su kuma iyayen dabar gida, dan in aka biye musu nan zasuce zasu kwana ma”. Ya ɗan murmusa. “Har yanzu basu canja hali ba kenan?”. “Cabjawar tasu ɗin nan ai babu rana, ƙila to in kun fara aurar da ƴaƴa.” Yanzun ma murmushin ya sake yi. Itama Mammah shayin data zuba masa ta ajiye gabansa tana nata murmushin. Daga haka suka cigaba da hira cike da shauƙi da kewa. Gaba ɗaya hirar ta ta'allaƙa ne akan abubuwan da suka faru a lokacin da baya nan. Musamman gyaran gidan nan, albarkar kasuwancin su daya sake haɓaka, auren su Ma'aruff da akasha kicimmili, da yanzu su Bilal da suka dage akan sai randa ya dawo zasuyi nasu. Ganin bai tambayi ina Nabeeha ba ita ta ɗakko masa batunta akan zuwa da safe zata kira Hajiya Hasiba ta sanar musu tunda basu san da dawowar tasa ba. Shiru yay kamar bazai ce komai ba akan batun, sai zuwa can har ma ta ɗakko wani sai kuma ya furta, “Ba gidan take zaune ba kenan?”. Mammah ta ɗanyi murmushi da girgiza kai. “Yanzu dai ya kamata ta dawo ɗin, tunda gaka sai ka bata haƙuri akan laifin da take gani ka mata, in sha ALLAHU a satin nan za'a zuba kaya a sashen naku.” Yanzu ma maimakon amsa batun zai bada haƙurin ko zuba kaya a sashen nasu sai kawai cayay, “Zan huta anan sashen dai tukunna Mammah. Yaran can uku kuma kukace yaran Uncle waye?...” Mammah tasan sarai ya fahimci wa ake nufi tun a ɗazun, kawai yana son sake ji ne a bakinta. Murmurshi tayi da jinjina halin Muhammad ɗinta da bazai canja ba. Kai tsaye ta maimaita masa sunan Uncle Tasi'u ɗin, ta kuma ɗora da labarin duk yanda suka haɗu a Egypt har kicimillin da aka sha da ƙannensa a watannin baya da yasa Uncle Tasi'un haƙura ya koma kan aikinsa sai jiya kuma yazo da yaran. Ta lissafa masa sunansu. “Babban shine Dayyan, sunan mahaifinku ya saka masa, sai macen Hanoon, ƙaramin Afeef. Nasan halinka Muhammad, sannan nasan halin ƙannenka, in har baka amshi tuban Tasi'u ba suma zasu sake birkicewa ne. Nasan shi mai laifi ne a garemu, amma sanda ya aikata yaransa basu sani ba ma. Sannan shima daya aikata ɗin bai ragemu da komai ba da UBANGIJI ya ƙaddara zamu samu, sai ma ɗaukaka da sanadin hakan ya jawo mana. Tunda gamu a yau cikin rufin asirin ALLAH da yalwarsa da har shima yazo ya raɓemu da zuriarsa zai ci. Dan ALLAH da kaina ina roƙon komai ya wuce kaji”. Dada daya zubama Mammah idanu ya ɗan murmusa. Sosai yake jin wannan baiwar ALLAH a zuciyarsa, yana mata wata irin ƙaun mara misali, kyawawan halayyar nan tata ita ke sakashi yin sanyi a wasu lokutan koda ya ɗauki zafi damuwa ta mamayesa. Tabbas wanda ya samu mahaifiya irin Mmamansa ya more, dan uwa ɗaya ce tamkar da dubu. Flaks ɗin shayinta ya ɗauka ya ƙara kawai, batare daya sake cewa komai akan zancen ba. Itama bata sake cewar ba, sai ma ta ɗakko wani batun. Sun cigaba da hirarsu har sha ɗaya da wani abu, agogo ta kalla da faɗin ya kamata yaje ya kwanta. Sai ya kalla gadonta dake gyare tsaff yana murmurshi. “Anya Mammah ba gadonki zaki bani na kwana ba, maybe hakan yasa na sake yarda ba mafarki nake ba fa ina tare dake a yau ɗina.” Cikin ƴar dariya Mammah dake kallon gadon itama ta ce, “In dai gado ne gashi nan Muhammad kayi kwanciyarka akai”. “To Mammah ke fa?”. “Ga ɗaki nan ba kowa, dama ɗazu su Mimi sun saka a gyara musu shi na kora su.” “A'a Mammah kiyi kwanciyarki a ɗakin ki, zan koma sama na kwanta”. “Ai ni nace ka kwanta abinka ko. Bari ma kaga na duba Nimrah ko zazzaɓin nata ya sauka. Dan duk ciwon da kaga ya kwantar da Nimrah da Ruƙayya ba ƙarami bane ba.” A karo na farko kan al'amarinta ya furta, “Kina shagwaɓa su ne da yawa Mammah shiyyasa.” “Toba dole ba Muhammad, ku yanzu duk kun girma, idan nace wayyo kafin naga wani a cikinku na gansu su huɗun nan. Ga Biebah kam tunda ka dawo gida na tabbatar ta fara mana bankwana kuma.” “Ai gara ta tafi nata ɗakin itama haka nan Mammah. Yanzu fa kusan 26 take nema. Damma bata da girman jiki tunda har su Ruƙƙayya na neman taddota naga”. “Ruƙayya da Nimrah kam tubarkalla, dan nan da wata shekarar tsaff zasu danne uwar tasu kam. A hakama wai tattalin jiki suke basa son suyi ƙiba.” Guntun murmushi Dada yayi da ɗan taɓe baki. Itama Mammah data kammala haɗa duk abinda take buƙata tai masa sallama ta fice. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali. Sai kuma ya miƙe ya hau gadon da bismilah, wani irin sanyi na ratsa masa zuciya da ɓargon jiki. Shifa yanda yake jin kewar Mammah bai ƙi ace ma ya kwanta a kusa da ita ba ko zai samu sassauci....

Koda Mammah ta fita sai da ta share guntayen hawaye tana murmurshi, kayan nata takai ɗakin kusa da natan sannan ya nufi ɗakin su Nimrah. Har sun kashe fitila alamar sun kwanta, dan haka ta haska da fitilar wayarta tana ƙarasawa. Ganin Biebah a ɗakin ya bata mamaki, sai dai batace komai ba ta tattaɓa jikin Nimrah dake barci, jin zazzaɓin ya sauka yasa ta sauke ajiyar zuciya. Addu'a ta sake musu su duka sannan ta fice. Koda ta koma ɗakin ba kwanciya tayi ba, alwala ma ta ɗauro ta kabbara salla....

Kusan 12:30 Nimrah ta farka. Bayi ta shiga tayi fitsari, koda ta fito ta koma gadon sai ta kasa barci. Tunane-tunane marasa daɗi suka cika ƙwaƙwalwata. Tun tana turesu da fatan barci ya sake ɗaukarta harta fahimci bafa ɗaukar tata zaiyi ba. Ga kanta har ya fara mata ciwo. Bargon ta yaye tare da sakkowa a gadon ta saka bedroom slippers ɗinta ta fito a ɗakin gaba ɗaya. Gara ta koma ɗakin Mammah ƙila gurɓataccen tunanin nan nata ya barta karma zazzaɓin daya sauka mata ya sake dawowa. A hankali ta murɗa ƙofar ta shiga dan tasan Mammah ta kwanta yanzu, dan tana barcin wuri saboda tashi sallar dare da bata wuceta. Bata damu da ganin ɗakin da duhu ba, dan Mammah bata son kwana da haske koda na lamp ne, shiyyasa suma suka koya. Da lalube ta isa gadon, hankali kwance ta haye, jin mutum data san Mammah ce yasa ta matsa sosai ta shige jikinta tare da gyara bargo da ƙyau........✍️

Yau fa akeyinta, ke madam Ninah ya da haka?🤣. Gaskiya Dada kana cikin alheri yau ɗin nan🤭, ga tsuntsu daga sama gasashe😂 koya kukace mutane na🥱😜.