Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 53

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 53

.....yes, the taste that they have been hearing since their childhood. Although his face has changed from that face seen in the video. That face with no hair at all, but the sergeant is the only thing that differentiates it from this face now and also there are no smiles, no laughs, no room to joke. Then there is the coin of charisma, perfection, the light of worship, self-control and the collection of the fullness of the virtues of those who try to hold on to greatness. Of course, at this point, she got into a serious confusion on this face and her heart could not make the right decision. Hear the pictures of the video I want to come back. The sound of accusing voices made me want to answer her again..... Her thoughts were interrupted by Mammah's shock. "Nimrah, do you think so?". Mammah said rolling her eyes. The secret of her heart was released, shaking Mammah's head and saying, "Mammah, it's okay". "She is lying wlhy Mammah, she is completely like this now, that's all she has to think about, even if we are alone in the room, she is in front of you." Ruky is the one who is talking to Nimrah. She also took revenge, but she didn't lose anything. Then Daddy Imran said, "I also want

Standalone post1,666 words

53

.........3:21pm

Jerarrun motocin masu baƙin gilashi suka fice daga filin jirgin cikin tsari mai ɗaukar hankali. Babu jiniya ko wani babban motsi da zai saka ace wani babban ƙusar ƙasa ne, amma tsaron dake zagaye da motocin ya isa ya sanar da kowa ba tafiya bace irin ta yau da kullum, sannan koma su waye sunada wani girma da muhimmanci. A motar tsakiya da Daddy Imran ya ƙarɓi tuƙin Dada ne a gefensa. A baya Mammah da ƴan gatanta Ruky da Nimrah sun sakata a tsakkiya. A binda zai baka mamaki kamar basu ba bakin surutun nan ya mutu murus. Dan har Daddy Imran ya kasa haƙuri sai da yay magana.. “Mammah wai yau bakunan kafi autanki sun mutu ne? Na jisu tsitt kamar basa a motar nan”. Murmurshi Mammah tayi da ɗan kallon Nimrah da Ruƙayyan da suka lafe a jikinta. Dan gara ma Ruky wayar Mu'azz ce a hannunta tana kallon hotunan da sukai a airport ɗin. Nimrah kam idanunta a rufe suke da alama tayi zurfi a tunani. Ba kuma tunanin kowa bane face na wannan baƙo nasu da Uncle Ammar ya faɗa musu shine Dadan da suke ji ana faɗa tun tasowarsu. Duk da fuskarsa ta canja daga waccan fuskar data gani a video. Waccan fuskar da babu gashin saje sam, sai dai kuma sajen ne kawai ya bambanta ta da wannan fuskar ta yanzu da itama babu yawan murmushi, babu sakewa, babu filin kai wargi. Sai tsabar kwarjini, kamala, hasken ibada, kamewa da tarin cikar haiba irin ta masu tantsar riƙe girma. Tabbas a wannan gaɓar ta shiga ruɗani mai tsanani akan wannan fuskar da zuciyarta ta kasa yankema hukuncin daya dace. Jitai hotunan bidiyon na son dawowa. Sautin muryoyin da ke zargi na so sake yi mata amsa kuwwa..... Tunaninta ne ya katse saboda girgizatan da Mammah tayi. “Nimrah mi kike tunani haka?”. Mammah ta faɗa tana kafeta da idanu. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki tana girgizama Mammah kai da faɗin, “Mammah ba komai”. “Karya take yi wlhy Mammah, gaba ɗaya yanzu haka ta koma, haka kawai sai kiga ta shiga tunani bare ma idan muna ɗaki mu kaɗai, a gaban ku ne batayi”. Ruky ce mai maganar tana hararar Nimrah. Itama ramawa tayi, sai dai batace komai ba. Sai Daddy Imran ne ya ce, “Nima dai naso lura da haka, duk tayi sanyi babu kuzari. Daughter mike faruwa? Ko baki da lafiya ne?”. Idanun Nimrah suka ɗan ciki da hawaye, muryarta na ɗan shigewa ciki ta ce, “ALLAH ba komai Daddy sharri take mun. Kuma lafiyata ƙalau” sai ga hawaye sharr. Mammah da taji hankalinta ya tashi ta kamota jikinta, dan ita kanta a tsakanin nan tana lura da Nimrah ta ɗan rage kauɗi, sai take tunanin ko exam ɗin da suka fara ce a makaranta. Itama dai Ruky idonta har ya tara ƙwalla. Ta riƙo hannun Nimrah cikin nata tana faɗin, “Dan nace haka kike kuka, to kiyi haƙuri bazan ƙara ba”. Cikin ɗan tura baki Nimrah dake kwance jikin Mammah ta ce, “Nifa ba dan kinyi magana bane ba, kawai kaina ke ciwo”. Sannu Mammah da Ruky suka shiga jera mata. Daddy Imran kam ya saki murmushi da faɗin, “Mammah kina fama.” Duk abinda suke Dada na jinsu. Amma ko motsawa daga yanda yake zaune bayansa kwance jikin kujera ya lumshe idanunsa baiyi ba. Zama ka rantse barci yake a hakan... Dai-dai nan jerarrun motocin dake tafe da tawagar jami'an tsaro suka iso cikin anguwar. Tsakiyar KOBI STREET. Dai-dai gate ɗin gidan zuri'ar Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi da yasa mutane fara farga da abinda ke faruwa. Dan kuwa duk da akwai jami'an tsaro a tare da su hakan bai hana wasu biyosu ba tun daga airport dan samun labari duk da su ɗin ba ƴan jarida bane, amma ganin Imran da yaso fargar da masu wayo yasa suka tsargu shiyyasa suka biyo su dan tabbatarwa, da alama kuma zasu samu abinda suke so ɗin musamman ganin inda motocin suke ƙoƙarin shiga. Maigadi kansa ya girgiza da abinda ya gani, balle su Malam Buba dan su Mammah basu fita da driver ko ɗaya ba daga gida duk su Ammar ne suka ja motocin sanda zasu fita. Yanzu kam wasu motocin ma sai sojojin nan ne suka dawo da su dan har suka iso gida hawaye wasun su sun kasa tsayawa. Sai da gaba ɗaya motocin suka gama shigowa kafin kowa ya fara ƙoƙarin fita. Su maigadi dai sunyi tsuru-tsuru suna kallon ikon ALLAH. Kusan motar su Mammah ce ƙarshen buɗewa, Nimrah da Ruky suka fara fita, kafin itama Mammah ta fito hankalinta duk akan Nimrah datai mata wani kalar tausayi. Riƙota tai tana kai hannu a goshinta, “Ciwon kan ne?”. Nimrah ta ɗan girgiza kai tana Kama hannun Ruky da itama ta zagayo inda suke cike da damuwar yanayin twiny ɗinta. Dai-dai nan aka buɗe ƙofor ɓangaren da Dada yake, a nutse ya fara sauke ƙafafunsa dake sanye cikin baƙin takalmi Boot mai ɗan tsaho. Kafin bayyanar baƙin wandonsa zuwa shafaffen cikinsa dake kwance cikin bakar t-shirt ɗin jikinsa kasancewar yayi zanzaro ne. Daga maigadi har Driver suka ɗan zuba masa ido daga can inda suke tsaye tamkar an basu aikin yin hakan ne. Har sai da ya kammala tsayawa cak akan ƙafafunsa sannan suka ɗaga idanun nasu a hankali zuwa kan fuskarsa dake sakaye cikin norse mask da p-cap. Shi kam da bai san sunayi ba, sai ma a bazata juyayyun idanunsa suka sauka akan Nimrah da Mammah kema magana ƙasa-ƙasa tana tattaɓa mata kai, anyi sa'a itama ta ɗago nata zata harari Mu'azz daya ƙaraso wajen yana tsokanarta wai tana ma Mammah shagwaɓa, ai ko sai idanun Dada cikin natan. cikin sauri ta janye dan har tsakkiyar ƙwalwa taji kaifinsu da tasirinsu ya riski tsakiyar zuciyarta. Shi kam baima nuna yasan mi akai ba ya maida idanun nasa ga kallon gidan cike da mazewa.......

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

★Gaba ɗaya tambayoyin zuciya sun gagara ƙarewa a zukatan su Maigadi dama jami'an sojan da aka bari gidan, dan suma dai har yanzu basu san wanene ba balle abinda ke faruwa. Sai dai duk sun sha jinin jikinsu. Amma a ɓangaren mutane biyu da suka san Dada tun a baya sun shaida tabbas shi ne ba saƙo ba ba kuma mafarki ba duk da yaƙi buɗe fuska. Dan haka suka kasance a firgice fiye da sauran. Saboda ɗimuwa ce ta gaske ta samesu da ruɗani na bazata. Tambayar kawunansu kawai suke ta yaya hakan zata kasance? Dan tabbas wanda akace an fitar a prison kwanaki biyar kacal da suka shuɗe ba zaiyi kama da hakan ba sam a idanun mai kallo. Yafi kama da jarumin dake rayuwa a ni'imtaccen muhalli da kwanciyar hankali da nutsuwar rayuwa. Da alama ana raina musu hankali ne ko wani abu daban gaskiya......

<<%>><<%>><<%>>

Gab da magriba Daddy Imran ya bar gidan. Su Aunty Ummi kam har akai isha'i suna nan abinsu suna hidima da Dada. Dan abubuwan da aka shirya masa harma ya rasa mizai ci a ciki. Abin zai baka mamaki yanda gidan ya nutsu babu hayaniya duk da yaran dake cike da shi. Amma kowa ya nutsu waje guda alamar wargi ma waje yake samu. Duk da kuwa baƙon idon daya saka su nutsuwar ko harara baima kowa ba. Hasalima cike da so da ƙauna ya dinga rungumesu lokacin da ake gabatar masa da kowa da sunayensu. Dan Mammah bata rage kowa ba hatta ƴaƴan Uncle Tasi'u ya masa bayanin su a taƙaice, sai dai komai baice akan su ba. Ga shi macen ta mugu-mugun jin mutuwa akansa. Dan a cewarta bata taɓa ganin namijin daya daki zuciyarta a kallon farko irin Dadan ba, wanda ita kanta ta tabbatar ko cikakken kallo ɗaya bai mata ba. Lokacin da akai masa rakiya ɗakinsa da aka zubama kaya jiya jitai tamkar tayi tsuntsuwa ta bishi, sai dai babu dama...

Duk wannan bidirin da ake babu Nimrah a falon, dan tunda suka shigo tai wucewarta ɗakinsu. Kayan jikinta da gaba ɗaya ƙamshin turaren Dada ya gauraye ta cire, jin ƙamshin yaƙi barin har jikinta dole tai wanka kafin al'awalar la'adar. Koda ta fito tai sallar sai ta haye gado ta kwanta dan wani ma ɗan zazzaɓi take ji. Lokacin da za'aci abinci bayan dawowar mazan sallar la'asar Mammah taga babu ita ta fara jajenta. Dan haka ta aika a duba mata ita. Nusaiba da tazo kiranta ta sameta kwance, sai tai tunanin barci take, dan haka ta koma tace tana barci. Mammah datai tunanin ko ciwon kan ne tace a barta tayi barcin... Nimrah da sarai tana jin sanda Nusaiba ta shigo tun tana juye-jiye da tunane-tunane har barcin gaskiya ya ɗauketa, daga nan kuma zazzaɓin na gaske ya rufeta. Gab da magriba Mammah ta shigo ɗakin da kanta, anan taji jikin nata da zafi. Babu ɓata lokaci ta saka Biebah ta haɗo mata abinci da magani, tashinta Mammah tayi, da ƙyar kuwa ta yarda taci abincin kaɗan tasha maganin, sai ga amai. Aman ne ya sata galabaita dole aka kira doctor ya dubata. Tunda ya dubata yay mata allura ta sake komawa barci shine bata farka ba sai kusan tara saura. Lokacin su Aunty Mommy da Mammah ta kora gida akan dole duk suka shigo suka sake dubata suka wuce. Sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, dan Mammah ta tabbatar weekend ɗin nan kaf a gidan zasu yi shi. Yo sukai yawo mara dalili ma balle wannan mai dalili ya samu. Ruky na ɗakin Nimrah ta farka, cike da farin ciki tai kanta, dan tun da Nimrah tai amai aka kira doctor itama ta koma kalar tausayi, abokiyar rayuwa ba lafiya ba nutsuwa. Ita ta shiga hidima da ita sai kuma ga Biebah ta samesu, dan ta baro ɗakinta ne tana mitar takura mata da zaman Hanoon yayi, yarinyar ta cika iyayi da feleƙe, ko jiya dauriya kawai tayi da ƴar kunyar baƙunta ga Hanoon ɗin, amma harga ALLAH yau ji take bazata iya ba. Itama ganin Nimrah ta farka sai ta sakin batun Hanoon ta nufesu da farin ciki tana mata sannu..........✍️