Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 52

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 52

.....while he was not there, he felt the tears coming down his face. He could hardly restrain himself and began to persuade them. Then Nimrah woke up to the body of the person she was in. A person who has not even figured out who he is is missing. There are two names that she heard, Mammah and Mamy, they only mention him now. (Dada! and Muhammad). The way she was talking, he was also worried about what was happening. God bless him, Mammah is trying to get up, Daddy Imran should sit comfortably. Nimrah was trying to leave his body, but Aunty Ummi held her. Dada, too, just turned his attention to Mimi himself, he extended his hand to them, and they quickly came to him and hugged him, crying. He put his hands on the backs of Biebah and Mu'azz, making a gesture of persuasion, and then rubbed Ruqayya's head as well. Before he slowly said, "It's okay". Together they went to greet each other and wipe away their tears. While they and Bilal could not stop looking at him, the appearance of his face to them became something great and appreciated. He was the same person they knew, but the look on his face that they had never seen before did not change him a bit. He also saw how they focused th

Standalone post1,536 words

KIƊA A RUWA 2

52

........“Mammah are alright?”. Nimrah ta faɗa tana shafa fuskarta ga hawaye na gudu suna ɗiga har kan fuskar Mammah ɗin. Mammah ta buɗe idanu a hankali tana kallonta, sai kuma tai ƙaramin murmushi da kai nata hannun kan fuskar Nimrah ta shafa da jinjina kai. Sake lumshe su tai kafin ta sake buɗewa kai tsaye akan Dada. Shima dai ita yake kallo, cikin wani irin yanayi mai zafi da kamilalliyar fuskarsa ta kasa iya shanyewa. Dan in mai kallonsa bai ƙarya ba ma ƙyallin hawaye idanun nasa keyi. Mammah kam ta kasa jarumtar riƙe nata hawayen tamkar shi, a take ta sake su suka fara kwarara tamkar an buɗe fanfon ruwa. Hannun nata dai data shafa fuskar Nimrah shima takai kan fuskarsa ta sake shafa fuskar a karo na biyu, ɗayan hannun kuma takai kan Imran. “ALLAH yay muku albarka”. Ta faɗa hawaye na sake zubo mata. A tare suka amsa da amin. Imran da a wannan gaɓar zuciyarsa ta matuƙar raunana da tausayin wannan ahali ya haɗiye abinda ya toshe masa maƙoshi da ƙyar, dan baima san kuka yake ba shima sai da yaji saukar ɗumin hawaye akan tashi fuskar. Da ƙyar ya iya dauriyar dai-daita kansa ya fara lallashinsu. Sai lokacin Nimrah ta farga da jikin wanda take. Mutumin da ko gama tantance wanene shi batai ba. Sai suna biyu da taji Mammah da Mamy sun ambace sa da shi kacal a yanzu. (Dada! da Muhammad). Yanda take mutsu-mutsu yasa shi shima farga da abinda ke faruwa. ALLAH ya soshi dai-dai Mammah na ƙoƙarin tashi ne, Daddy Imran ya kamata ya zaunar da ƙyau. Har neman faɗuwa Nimrah take wajen barin jikinsa, sai da Aunty Ummi ta riƙeta. Shima Dada sai ya basar kawai tare da maida hankalinsa kansu Mimi, hannu ya miƙa musu, da sauri kuwa suma suka nufoshi suka rungume sa suna kuka. Hannunsa ya ɗaura a bayan Biebah da Mu'azz yana ɗan bugawa alamar lallashi, sannan ya shafa kan Ruƙayya itama. Kafin a hankali ya furta, “It's okay”. A tare suka shiga jinjina kawuna suna ɗagowa da share hawayensu. Yayinda su Bilal suka kasa daina kallonsa, dan bayyanar fuskar tasa a garesu ta ƙara zama wani abu mai girma da kimantawa. Dadan ne dai da suka sani, sai dai sajen dake kan fuskarsa da basu taɓa gani a baya ba ya canja shi kaɗan. Shima ganin yanda suka zuba masa idanun gaba ɗaya ga falon yayi shiru tamkar an musu tsawa sai ya motsa tausasan laɓɓansa kaɗan ya furta, “Kallon fa?”. Cikin yanayin ɗage gira kaɗan akan su Ma'aruff. Tamkar waɗanda ya farkar a barci duk sai su Ja'afar suka fara sakin murmushi, kafin su Ammar su sake rungumesa kamar wanda suka ji kunya. Ya ɗan murmusa kaɗan shima a karo na farko, yana shafa bayansu. Cikin golden voice ɗin nan tasa data iya shanye abubuwa da yawa ya sake furta, “Shi dai wannan kukan bazai ƙare ba halan. Imran kama ƙannenka magana su daina min kuka”. Murmurshi Imran yayi yana kallonsu, yayinda su Bilal da suka ɗago a jikinsa ke goge hawayen suna murmushi. Cike da lallashi Daddy Imran ya ce, “Gaskiya Haysam ya faɗa, yanzu ba lokacin kuka bane lokacin farin ciki ne. UBANGIJI ya nuna mana wannan ranar batare da mun biyasa ko sisi ba, hasalima ba muyi zato ko tsammani ba. Dan haka a maimakon kuka sai muyita jera masa godiya da kirari zaifi mana alkairi da ƙarin farin ciki a zukata”. Cikin gamsuwa suka shiga jinjina masa kai suna ƙara share hawayensu. Dai-dai nan cikin kasa haƙuri Ruky ta rage murya da faɗin, “Mammah dan ALLAH waye?..” Mammah da idanunta ke jajur na kukan da tasha ta ɗaga tana kallon Dada dake zaune a kujerar kusa da ita hannunsa riƙe da nata, murmushi tayi mai cike da abubuwa da yawa, kafin ta janye ta maida kansu dan Nimrah da Rukyn na zaune ne ɗayan gefenta, sai dai daga ƙasan carpet ganin haka su Biebah sukayi, duk sun ƙagu ta basu amsa... Zatai magana caraf Uncle Bilal ya ce, “Mammah karki faɗa dan ALLAH, sai sun bada goron albishir sannan”. Murmurshi Mammah ta sake saki mai faɗi tana share hawayen da suka sake silalo mata. Yayinda shima Bilal ɗin hawaye yake sharewa tamkar su Biebah da nasu suka gagara tsayawa. Sanyi jikin su Nimrah ya sake yi, tamkar zasu saki kuka suma suka sake maida kallonsu ga Daddy Imran. Hannu ya ɗaga musu alamar shima babu ruwansa, dan haka akai ƴar dariya mai zuwa batare da an shirya mata ba. Dan shi kansa Dadan sai da ya ɗan yi gajeren murmushi yana kallonsu su duka biyun ƙasa-ƙasa. Sai kuma karo na farko ya miƙa musu hannu alamar su zo garesa... Ruƙayya dai babu musu ta rarrafa inda yake, Nimrah kam ɗan shiru tayi kamar mai tunani, sai da Mammah ta kamo hannunta tare da mata nunin taje da ido sannan. Itama matsawar tai, amma sai ta zauna kusa da Ruky idannunta a ƙasa dan gaba ɗaya jinta take kamar a cikin matsa-tsi, ba kamar sanda suka shigo ba da take sakayau. Ba ta san dalilin rawar jikinta ba. Ba ta san dalilin bugun zuciyarta ba. Ta san sunan Dada kawai, sunan da take ji a bakin kowa na gidan, suna mai nauyi da daraja a cikin gidansu, sunan da ake furtawa da girmamawa da bege. A karo na farko hoton bidiyon nan ya ratsa cikin tunaninta. Sunansa na ainahi yay mata amsa kuwwa acan ƙasan ƙirji matsayin wanda akace ya kashe mata Ummanta, (Aka ce ko kika gani da idon ki) wani sashe na zuciyarta ya tuna mata, samun kanta tai da matse yatsun hannunta cikin juna, ta sake sunkuyar da kai, dan ji take tunaninta na neman hargitsewa da rabuwa kashi-kashi a kwakwalwar ta. A lokacin suma su Shariffa suka ƙaraso. Cike da matuƙar girmamawa suka shiga gaisheshi. Idanunsa dake karantar yanayin Nimrah da babu wanda zai iya fahimta ya ɗauke. Kallo ɗaya yay musu suma ya janye idanunsa, su ɗin ƙanne suke a garesa koba auren ƴan uwansa a kansu, sai kuma ga alaƙar auren ya ƙarama matsayin ƙarfi. Cikin kamewarsa da cikar kamala ta uba kuma babban wa ya shiga amsa musu, tare da musu fatan alkairi a cikin aurensu. Sosai suka sake shiga cikin yanayin kunya, girmansa ya sake mamaye musu waje ko kallonsa sun gagara yi, dan koba shekaru shi ne uba ga mazajensu, sannan shi ne garkuwa, shi ne ginshiƙi. Babu wacce ta iya amsawa a cikinsu sai ma sake sunkiyar da kawuna da sukayi. Sai su Mammah ne suka amsa addu'ar tasa da amin. Sai da suka miƙe suka koma wajen zamansu sannan Ruky da Nimrah suka fara gaishe shi. Suma ya amsa musu da tambayarsu karatu. Suka amsa da Alhamdullah har yanzu kan Nimrah a ƙasa tana cuɗa yatsunta cikin juna. Yatsun nata ya ɗan sake zubama idanu a fakaice tare da janyewa duk a lokaci ɗaya dan cikin sakanni harya gama karantar akwai abinda ke damunta bayan kasancewarsa baƙon ido a cikin waɗanda ta sani, sai dai babu wanda zai ce kallon nata yake, sai ma maida hankalinsa da yay kan Mammah can ƙasan ransa kam mamakin girmansu yake ita da Ruky da Mu'azz fiye da kowa. Ƙasa-ƙasa yay maganar da babu wanda zaice ya ji abinda ya faɗa mata. Sai murmushin ta kawai da kowa ya gani a bayyane.... Shigowar Daddy Imran daya fita ta katse Mammah daga maganar datai niyyar yi, ya dubi su Ma'aruff yana faɗin Su tashi suje gida kafin mutane su farga da abinda ke faruwa. Dan tabbas ana gama sanin Zak-Shadow ne a airport ɗin ba ƴan media da jama'ar gari ba hatta munafukai bazasu barshi ba, dan dama ce mai sauƙi a garesu duk da zagaye suke da jami'an tsaro da suka fara fargar da mutane akwai wani babba dake airport ɗin, saboda a fitar nan tashi ya fahimci hakan ta hanyar ƙananun maganar da ya fara jin na tashi, da ƙyar su Ma'aruff suka miƙe, dan sun san gaskiya Yaya Imran ɗin ya faɗa. Dada ne ƙarshen miƙewa riƙe da Mammah da har yanzu hawaye sun gagara barinta. Ya kuma maida facemask ɗinsa. A yanda suka fito cikin tsari da nutsuwa duk da kuwa ta hanyar sirri ce yaja hankalin tsirarun mutane dake ta wajen kansu. Dan tamkar ƙyaftawar ido sojojin da suka zo da su da jami'an tsaron da suka tarar na farin kaya a airport ɗin suka zagaye su, suma an ajiye su ne a sirrance batare da sanin su Imran ɗin ba. Wannan kuma duk aikin shugaban ƙasa ne. Mutane da son ɗauke-ɗauke a waya kam har sun fara batare da sun farga da sanin su wanene ba. Sai dai yanda jami'an tsaro sukama mutanen zobe yasa kowa fahimtar koma su waye su lallai masu muhimmanci ne a ƙasar. A haka suka shiga motoci babu ɓata lokaci aka bar wajen. Sai dai mi, kafin ma su isa gida guntayen videos ɗin da wasu suka ɗauka da ƙananun magana da ake a airport ɗin har ya fara yawo a media, sai dai anata canki-in-canka ne na rashin sanin wanene. Mike faruwa?. Yayinda ƴan bin ƙwaf nacan sun fara bibiyar al'amarin dan sunyi ma kansu alƙawarin kafin dare sai sun gano su wanene ɗin.........✍️