Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 51

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 51

..... they whispered, O Mu'azz, who was near them, gave them a picture. He didn't even care about them and he started taking them, and finally he went back to watching everyone's video until Mammah scolded him. Laughing, he said, "Mamma, be patient, GOD is there to meet. If we don't take a picture, he won't worry. Is there a vip room like this in the waiting hall of the airport?" Everyone is surprised by Mu'azz's speech. Uncle Ja'afar answered him, "There must be such a Mu'azz even among the leaders." Satisfied, Mu'azz said, "It's the same, Uncle. Since everything is different in our country, there is a difference between the son of the poor and the son of the rulers." It won't even be ten minutes before the plane will land. However, since they were in the same part of the waiting people, they did not know the cakes that were being baked until the travelers who came out of the plane started to come out. They were eager to see the face of someone they know enter the vip lounge until they got impatient. They had to sit for more than thirty minutes until water and lemon were brought to them, after about three minutes the security at the outer door opened it. All the people at the door

Standalone post1,543 words

KIƊA A RUWA 2

51

.........★AIRPORT★

Ba ƙaramin mamaki su Mammah sukai da ganin inda aka kawosu ba. Airport fa, sukam wa garesu da zai dawo daga wata ƙasa. Imran ne kawai yay tafiya, basa jin kuma dan zai dawo zai musu irin wannan tattarowar iya su kaɗai. Kowa da magana a bakinsa sai dai sunyi dauriyar dannewa. Ba a kai su Mammah da iyalanta cikin waiting hall na jama’a ba. Sai ma wani mamakin da aka sake basu, dan kuwa Jami’an tsaro masu bakaken kaya suka sake tarbarsu anan ɗin sannan suka jagorance su zuwa wani ɓangare na musamman a airport ɗin da zasu iya rantsuwar basu taɓa sanin akwai shi ba. (VIP lounge) wurine da ya sha bamban da hayaniyar waiting hall. Ga tsaro ko’ina. Iska mai sanyi ga ƙamshi mai saka nutsuwa. Ga kujeru masu taushi da ƙawa kai kace wani shiryayyen falon hutawar shugaban ƙasa ne. Koda yake ko ba'a faɗa ba kai kasan wannan wajen sai dai tanadin zaman shugaban ƙasar. Sai da Mammah ta zauna sannan kowa ya zauna ana kallon kallo. Su Nimrah kam kasa haƙuri sukai cikin raɗa-raɗa sukace Ya Mu'azz dake kusa da su yay musu hoto. Bai ko yi musu ba ya fara ɗaukarsu, daga ƙarshe ya koma yima kowa video sai da Mammah ta masa daƙuwa. Cikin dariya ya ce, “Mammah yi haƙuri, ALLAH wajen ne ya haɗu. Idan bamuyi hoto ba ai ansha damu. Wai dama a waiting hall na airport akwai vip room irin wannan?”. Kowa murmurshi yake da zancen Mu'azz. Uncle Ja'afar ya bashi amsa da, “Ai dole ne ya zama akwai irin wannan ɗin Mu'azz kodan shugabanni ko”. Cikin gamsuwa Mu'azz ya ce, “Haka ne kuma Uncle. Tunda dama kasarmu komai yana da banbanci dana talaka dana masu mulkin”. Basuyi ko zama mintun goma ba jirgin da ake tsumayen zai sauka ya sauka ɗin. Sai dai da yake a ɓangaren ɗaya suke na masu jira basu san wainar da ake toyawa ba har matafiyan da suka fito a jirgin suka fara fitowa. Tun suna tsumayen ganin fuskar wanda suka sani ya shigo vip lounge ɗin har suka haƙura. Dan kusan sai da sukai zaman fin mintuna talatin zuwa lokacin har ruwa an kawo musu da lemo, bayan nan kusan wasu mintina uku security ɗin dake ƙofar ta waje ya buɗeta. Duk ƙofar kuwa suka zubama idanu dan a ƙage suke su kam. A bazata Daddy Imran dake gaba ya bayyana a idanunsu. Kusan a tare duk suka miƙe, idan ka cire Mammah da bata motsa ba ta dai zuba masa idannunta na girma kawai. Yayinda zuciyarta ke wani irin bugawa da bugu mai girman gaske a cikin ƙirjinta. Hakama Nimrah dake kwance a jikinta tana game da wayarta, kasancewar hankalinta na kan game ɗin bata san mike faruwa ba ita kam. “Oh kona koma ne?”. Daddy Imran ya faɗa yana ɗan wara idanunsa akan su Ammar dake tsaye kawai sun zuba masa idanu abubuwa na musu yawo a zuciya da ƙwaƙwalwa. Murmurshi suka saki a tare, kafin su ɗaga ƙafafunsu da sukai musu nauyi na rashin dalili su nufesa a jere, zaratan mazajen Mammah kenan guda huɗu, masu kamanni ɗaya, dan su duka huɗu da mahaifinsu suke kama, Dada ne kawai ya ɗakko hasken fatarta amma shima kamaninsa irin nasu ne. Dai-dai lokacin itama Nimrah ta ɗago saboda zaburar Ruky da uhununta na ambaton Daddy!... Sai dai ta yunƙura zata tashi itama ta tsaya cak, kamar yanda suma Uncle's nasu suka tsaya ɗin. Dan takunsu bai gaza biyar ba suka iso inda Imran ya ke, sai dai kamar jira yake su iso ɗin suna ajiye ƙafafunsu a takun ƙarshe shi kuma ya matsa gefe tamkar mai shirin basu hanyar wucewa, hannunsa ɗaya riƙe dana Ruƙayya, ɗaya kuma ya nuna musu ƙofa. Dai-dai nan ƙofar wajen da suka zubama idanu su duka ta shiga buɗewa, buɗewar data kasance tamkar tare da zukatansu dake rufe ne tsawon shekaru takwas da wata shida.... Ɗasss! Ɗassss! Ɗasss!! Sautin takunsa ya fara bayyana a cikin shirun su mai nauyin gaske, dan a wannan gaɓar ko numfashi mai ƙarfi babu mai yi idan ka cire Imran da fuskarsa ke cike da wani irin murmushi mai nauyi da armashin gaske. Kafin bayyanarsa cikin kwarjini da kamalar masu natsuwa ta wanzu cikin idanunsu. Shi ɗin ne dai, shi ɗin da suke zaman jira tsahon shekaru da hawaye da bugawar zukata a kowace daƙiƙa ta kwanakin da suka shuɗe da abubuwan da bazasu lissafu ba.

Duk da basa ganin ainahin fuskarsa, sannan ba wasu kaya bane na alfarma a jikinsa. Hasalima sanye yake da ƙananun kaya da suka kasance baƙaƙe daga sama har ƙasa. Baƙin wando da riga t-shirt mai gajeren hannu data bayyana murɗaɗen damtsen hannunsa duk da kuwa jikinsa bai gama dawowa ba kamar da, sai dai ya ciko fiye da sanda ya fita a prison. Fuskarsa da norse mask daya ɓoye bakinsa da hanci, sai ƙwayoyin birkitattun idanunsa da ko yana a cikin kwanciyar hankali basa zama tas-tas, daga sama da hula p-cap itama baƙa. Hannunsa ɗaya a aljihu, ɗaya rataye da jacket ɗinsa da itama ta kasance baƙa. Sassanyan ƙamshin turarensa da duk suka sanshi da shi kuwa ya cika wajen... Kamar yanda suka tsaya cak suna kallonsa haka shima ya tsaya cak yana musu kallo mai matuƙar nauyi da tsawa a zuciya. Dan kuwa Imran ya matuƙar yi masa bazata. Sam bai sanar masa da zuwansu tarbarshi ba, kasancewar dama saukar tasu sauka ce ta sirri kamar yanda ya buƙata. Da wani irin slow motion ya janye idanunsa daga kallonsu ya maida su kan Mammah dake zaune a inda take, sai dai kamar wadda ta suma dan babu inda ke motsi a jikinta sai idanunta dake tsaye a kansa cak... Nimrah kwance a kafaɗarta itama dai ta zuba masa ido ne kamar yanda kowa ke kallon nasa. A bazata idanunsa daya janye slowly daga kan Mammah suka shige cikin nata. Shigewar data saka mummunar faɗuwar gaba riskarta. Dan ji tai tamkar an matse zuciyarta da hannu ne har sai da ta kumburo kamar zata fashe sannan aka saki. Kasa jurewa tayi, a hankali ta fara lumshe idanun nata dake cika da hawaye na rashin dalili. Hakan kuma yay dai-dai da cigaba da takowar Dada inda suke kai tsaye dan burinsa kawai ya iso gaban Mammah... Karo na biya ya fara motsawa a hankali, yanda ɗakin yay musu shiru tamkar an tsaida duk wani motsi na ƙasar da mutanen cikinta yasa sautin takalmin nasa cigaba da bada sauti kamar ɗazun. Sautin daya cigaba da bugawa da bugun zukatansu har ya ƙarasa inda Mammah da Nimrah suke ya tsaya cak. Kafin a hankali ya tura ƙafarsa ɗaya baya, ya sauke gwiwar ɗayar ƙafar itama a ƙasa tamkar mai shirin bama budurwa zoben baiko. Hannunsa ya kai ya zare p-cap ɗin ya ajiye a ƙasa, ya sake maidawa ya zare norse mask ɗin shima. Duk dai Mammah na kallonsa tamkar sumammiya, dan idannunta ne kawai dake yawo a kansa ke motsawa... A ɓangaren su Ja'afar da su Aunty Ummi, Lailah, Mimi, Mommy, Shariffa da Biebah kam idan akace maka suma sun suma ɗin ne tamkar Mammah kada ka musa. Dan yanda duk suka kasance a tsaye ƙyam babu motsi babu ƙyafta ido ya isa shaida ga mai kallonsu. Dai-dai yana gama sauke norse mask ɗin cikin tamkar fisgar numfashi Mimi ta furta kalma mai nauyi da girgiza zuciya a karo na farko, kalmar data zama tamkar ta yayyafa musu ruwan sanyi ne daya farkar da su a suman nasu... “D..a...da!!”. Sai kawai ta tafi luuuu zata zube ƙasa saboda yanda jikinta ya ɗauki rawa. Da sauri suka zabura kanta dan taro ta, sai dai kuma hankalinsu ya rabu biyu. Dan a dai-dai wannan lokacin itama Mammah da sunan Dadan ya daketa sakamakon fitarsa a bakin Mimi jikinta ya hau rawar, duk da ƙoƙarin da take na riƙe kanta hakan ya gagara. Hannunta ta motsa a hankali tare da kai shi kan fuskar da ta shafa kumatunsa dake ɗauke da kwantaccen gashin saje mai adon farin gashi tsilli-tsilli. Da wani irin gudu hawayen da take riƙewa suka zubo a saman fuskarta, lips ɗinta dake rawa suka motsa a hankali ta furta, “Muhammad!”. Sai kawai ta tafi itama luuuuu ɗin kamar Mimi, sai dai ita da alama suna ma tayi. Ƙarar firgita Nimrah ta fasa tana cukuykuye Mammah jikinta na rawa, hakan yasa shi kuma Dada tarosu su biyun duka a jikinsa ya rungume.... Ƙarar Nimrah ce ta kasance tamkar zaburarwa garesu duka. A tare sukai kansu suma. Wata irin runguma Ammar daya fara isowa yay ma Dada tare da fashewa da kuka mai matuƙar dukan zuciya, dan a wannan gaɓar wlhy ya manta da kansa a matsayin namiji. Tamkar yanda Ammar yayi suma su Ma'aruff rungumesan kawai sukai suna hawaye.. A hankali Dada ya lumshe idanunsa da suka juye lokaci guda, cikin wani kalar sanyin jiki da tsinkewar jini ya shiga ƙoƙarin shanye hawayen da yake jin tamkar suna neman ciko masa idanu shima. Da ƙyar Imran daya ƙaraso inda suke da ruwa a hannu ya shiga ɗagasu ɗaya bayan ɗaya. Nimrah dake jikin Dada male-male batare data fahimta ba ya fara kallo, janyewa yay kawai yana murmurshi a zuciyarsa da ƙoƙarin shafama Mammah dake jikinsu su biyun ruwa. Cikin sa'a kuwa ta kawo nannauyan numfashi.......✍️