
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 66
.....the room, a heavy silence, the kind that tests courage and respect. The President continued to say, "I waited for a week. Not because I was not in a hurry... but because I made sure you are safe. Then rest, and meet with Mammah and relatives and families as appropriate." Dada bowed his head a little, before he said, "Thank you for your patience. I don't want to hurry. I prefer certainty." The President bowed his head. "That's why you came back." Dada was not surprised. But he smiled a little, then he attacked Imran a little. Imran and General laughed together. The general said again, "It's not Imran. I knew it before you stepped on this land. And I know that your return does not mean rest. That's good for us, I believe again that this country is still in the heart of Zak-Shadow, and it is the future in his big dreams of life." Dada leaned on the chair and exhaled heavy air, then he put his sharp eyes into the General's. No joke, but no joke. Full of confidence in his position as a soldier who is not afraid of facing problems, he said, "If that's the case... why did you call me here?". The president was silent for a while, averting his eyes, and then said in a thick voice: "Bec
66
.........Shiru falon ya ɗan ɗauka na mintuna. Shiru irin na manya kowa na nazartar ɗan uwansa. Kafin Shugaban ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida ya katse yanayin. Bada murmushi mai yawa ba, amma da girmamawa ta gaskiya kuma ta musamman da amana ya furta, “Zak-Shadow”. Kai daga jin yanda sunan ya fito daga bakinsa kamar sirri da aka daɗe ana ɓoyewa kasan yana cikin farin ciki mara misali ne. Dada ya wani ɗan lumshe idanun sannan ya buɗe su. A nutsensa ya amsa da. “Ranka ya daɗe, Your Excellency.” Shugaban ƙasa ya ɗan yi murmushi. Hakama Imran dake kai coffee bakinsa sai da ya murmusa. “Anan… babu ‘Your Excellency’. A yau, ni da kai ne da Imran kawai. Ba matsayin shugaban ƙasa ba, matsayin abokin aiki a gidan soja kawai. Idan kun so zaku iya ƙarawa da wani abinda kuke ganin ya dace ku ambace ni. Amma ba bigiren siyasa ko shugabancin ƙasa ba”. Yanzu kam ba Daddy Imran kawai ba, har Dadan sai da ya saki wani guntun murmushin gefen baki yana sake gyara zamansa na ƙasaita. Shiru ne ya sake ratsa ɗakin, shiru mai nauyi, irin wanda ke gwada ƙarfin zuciya da girmamawa. Shugaban ƙasa ya cigaba da faɗin, “Na jira sati guda. Ba don rashin gaggawa ba… sai don na tabbatar kana lafiya. Sannan ka huta, ka gana da Mammah da ƴan uwa da iyalai yanda ya dace.” Dada ya ɗan jinjina kai, kafin ya furta, “Na gode ranka ya daɗe. Dama ni ba na son gaggawa. Nafi son tabbaci.” Shugaban ƙasa ya jinjina kai. “Wannan dalilin ne yasa ka dawo.” Dada bai yi mamaki ba. Sai dai ya ɗan murmusa, sai kuma ya ɗan harari Imran. Ƙaramar dariya Imran da Janar sukayi a tare. Janar ya sake faɗin, “Ba Imran bane ai. Na sani tun kafin ka taka ƙasar nan. Kuma na sani cewa dawowar ka ba ta nufin hutu. Hakan ya mun daɗi, dan na sake gaskata har yanzu wannan ƙasar tana cikin zuciyar Zak-Shadow, kuma itace gaba a cikin manyan burukan sa na rayuwa.” Dada ya ɗan jingina da kujerar yana furzar da iska mai nauyi, sai kuma ya zuba kaifafan idanunsa cikin na Janar. Ba wargi, amma ba wasa. Cike da dakiyar sa matsayin soja da bai san tsoron tunkarar matsala ba ya ce, “Idan haka ne… me yasa kuka kira ni nan?”. Shugaban ƙasa ya ɗan yi shiru yana kauda idanunsa, sannan ya ce cikin murya mai kauri: “Domin wasan ya sake farawa Haysam. Dan a yanda na ilimantu cikin siyasar ƙasar nan babban yaƙi ne a gabanmu ba murƙushe ƙunya kawai ba”. Idanuwan Dada suka yi kaifi akan Janar. Cikin wani yanayi ya furta, “Kana tsoron Ƙungiyar duhu bazata iya mutuwa bane cikin sauƙi?”. “Ba haka nake nufi ba Haysam, ai tunda kafiran baya masu taurin kai da izgili irin su Abu Lahabi suka ƙare a doron ƙasa, daular musulunci ta kafu a cikin idanunsu, a cikin ƙasar da suke alfahari da ita, a hannun marayan nan da suke iƙirarin an haifa a gabansu, sadauki uban sadaukai, masoyin ALLAH ɗan gatansa, mai faɗa da cikawa kyakkyawan balarabe ɗan dangi. To waɗan nan dauɗar duniyar ba komai bane ba. Idan ma mu mun shuɗe a cikin yaƙin, wasu da zasu ƙarasa mana ZASU TASO NE. Kawai ina son ka fahimta, a yanzu ƙungiyar duhu ta ɓoye. Ta canja fuska. Ta sake yin mamaya ta mutane da dukiya. Amma tana nan kuma tana motsi da motsin ƙarfin ikon ƙasa da masu shugabancin ƴan ƙasar. Amma bana son hakan yasa kaji tsoro, dan tsoro shine matakin farko na rauni da tarwatsewar ƙarfin iko, sannan shi ke bama marasa ƙarfi ƙarfi akan masu rinjaye. Shike bama masu taka baza da bazar ƙarfin masu ƙarfi gadara da ɗauka sune a sama dole a bisu. Shi ke sawa suji kamar zasu iya juya duniyar bayan talakawan ƙasar da suke amsa suna ƙasar tasu” Murmurshin da Dada ya saki a yanzu har sai da ya bayyana fararen haƙwaransa a cikin idanun shugaban ƙasa da Imran. Sai kuma ya ɗan taɓe baki. “Na riga na ji motsinta tun ina sakaye. Sai dai ranka ya daɗe ka sani bazamu ce mu bama jin tsoro ba, saboda mutane ne tamkar kowa. Muna da rauni, muna da ruhin mutuwa tamkar kowa. Muna son rayuwa, dan wannan ɗan adam taka ce irin na kowane rai. Sai dai hakan bazai hana mu sadaukarwa ba, saboda addininmu addinin jarumta ne. Mun san kammu, mun san makomar mu da darajar rahamar da mahalicci mu yayi mana. Yanda sahabban MANZON ALLAH suka ƙare rayuwarsu wajen bama MASOYINMU kariya da kafa daular da har a yanzu muke ci daga arziƙinta, muma na baya da bamu ganshi ba, amma soyayyarsa bata da iyaka a jininmu bazamu bari wasu munafukan cikinmu da azzalumai suka mamaye da ƙyale-ƙyalen duniya ba su saida mu a hannaye marasa daraja. Zamuyi da basirar mu, da ƙarfin mu, da lokacin da UBANGIJI ya bamu, randa umarninsa na gushewarmu ya tabbata sai mu kwanta mu barma na baya sauran aikin, dama mun san duniya kasuwa ce, sanda wani ke kammala cin tashi sannan wani ma ke shirin shigowa tashi sayayyar. Dan haka ba ruwana da ƙarfinsu, dukiyarsu, mamayarsu, dan koda da Imran da su Ma'aruff suka mamaya zamu haɗa duka mu zubar da su da ƙarfin ikon ALLAH”. Shugaban ƙasa ya ɗan yi murmushi yana jinjina ƙudirar UBANGIJI mai bada ƙarfin iko ga wasu zukata. Sannan ya gina tsokokin jikinsu da ƙarfi mai bayyana a idanu. Ya rage naka ka zama irin Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi wajen nuna godiyarka ka gina kyakkyawan aiki, ko ka zaɓi butulce masa wajen lalata wannan baiwar a neman duniya da burge mutanen ciki dan kawai a kiraka wane a riga ko dukiya ko suna. Imran da yasan duk abinda zai fito daga bakin Zakin sa tun daga ƙarƙashin zuciya ne bawai cika baki ko gadara irin ta wawayen mutane ba, sai ya lumshe idanu yana ɗan sakin ajiyar zuciya. Shugaban ƙasa ya sake katse shirun da faɗin, “UBANGIJI yayi ma rayuwa albarka, ya ƙara mana ƙarfin zukata da jajircewa. Ya ɗora nasararmu akan masu zalunci. Duk mai son kaimu ƙasa ya Rabbi ka kaishi a lokacin da muke barci batare dama mun sanshi ba. Haysam ka godema ALLAH kaji, dan ya baka abubuwa da yawa da bai baima da yawan mutane ba. Irin ku kai da Imran kaɗanne a cikin wannan haɗamammiyar al'ummar tamu da basu da burin komai sai na son tara dukiya da suna cikin haɗama da babakere. Burin kowa ace shi ɗin shi ne dai, yana mantawa da ranar tafiya babu ko zoben ƙarfe a ɗan yatsa, sai farin ƙyalle da a kwana uku zai fara ruɓewa ma, sai wannan halayen dai da in ka gagara ginawa akan gaskiya, amana, imani, tsoron ALLAH. Kowa gani yake kawai daya mutu ya huta. Bai hango kwanciyar shekaru da za'ai a cikin kabari balle ranar rarrabe ayyuka, kowa dai sai yace aljanna ta mai rabo ce. To aljannar an faɗa maka layin rabon kunu ce balle kace idan kaga idon sani a wajen zai ƙara maka kofi ɗaya akan kasonka naka ya ƙara yawa. Iya nauyin sikelinka, iya matakin da zaka taka daga falala ko uƙuba. Ya rabbi kasa mu cika da imani”. “Amin ya rabbi”. Dada da Imran suka amsa a tare. Karan farko Imran ya saka baki a tattaunawar tasu. “Ranka ya daɗe nima ƙarfinsu bashi yafi damuna ba ko nake kallo a barazanar wannan yaƙin. Zak.. ka san abin da ya fi haɗari?” Dada ya girgiza kai. “Ba kai bane”. Imran ya cigaba da faɗa. “Ban gane ba”. Cewar Dada yana tsare Imran da idanu. Sai dai maimakon Imran ɗin ya bashi amsa sai shugaban ƙasa ya amsa masa da. “Gaskiya Imran ya faɗa, ba kai ne haɗarin ba a yanzu. Abin da ke kusa da kai ne. Shiyyasa dole a fara wannan aikin a rufe, dan zuwa yanzu koda sun sami labarin dawowarka zasu fara maida hankali a binciken tabbatarwa ne kafin shiri”. Shiru ya ratsa falon kamar hukunci. Dada bai tambaya ba. Bai kuma ƙaryata ba, sai ma nazartar maganganun yake dalla-dalla a ƙasan zuciya.. Fin minti biyu kafin ya kallesu su duka. Kai tsaye ya furta, “Minene shirin yanzu?”. Shugaban ƙasa ya ɗaga gira kaɗan. “Ajiye aikin soja a zahiri. Sannan sabon muƙami a ɓoye. Ba muƙami na takarda ba. Ba wanda zai gani. Ba wanda zai sani. Ba wanda zai ji, sai mu ukun nan kacal”. Shiru kawai Dada yayi yana kallonsu. Sai Imran ne cikin dunƙule hannu ya furta, “Yes ranka ya daɗe. Wannan itace power ta gaskiya, power ta ruɗani. Power ta mamaya, sannan ta ƙarfin iko”. Ƙaramar dariya shugaban ƙasa yayi, dan yanda Imran ɗin yayi dole kai dariya. Shi kansa uban gayyar duk da ya fuske sai da ya murmusa a zuciyarsa. Janar ya buɗe drawer jikin center table ɗin ya zaro wata takarda, Imran ya miƙawa yana faɗin, “Ba takardar aiki ba. Umurni ne. Jagorancin sashen tsaro na musamman”. Ya maida idanunsa kan Dada. “Kai kaɗai zaka ba da rahoto kai tsaye gare ni. Kana da damar haɗa ɓoyayyar rundunar aiki, a cikin kowanne jami'an tsaro na ƙasar nan ko farar hula. Sai dai ka sani zan saka ɓoyayyen tsaro a bayanka, dan kai ma tsaron lafiyarka zai koma ƙarƙashin ikona ne daga yau a gida da waje. ALLAH ya bamu fiye da nasarar da muke fata da buƙa”. “Amin ya rabbi ranka ya daɗe”. Cewar Imran cike da farin ciki. Dada ma ya ɗan yi murmushi kaɗan. Sai kuma cikin ɗan taɓe lips ya furta. “Sir! A ɓoye baiyi ƙarfi ba? Karfa ka manta akwai soji biyu tare da ni.” ya ƙare maganar da kallon Imran...........✍️