Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 65

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 65

....that's it. If they are going to go home to Lagos then he will buy them a ticket. Caraf Afeef said he didn't agree, he liked Nan more, the son of wlhy won't go and take revenge. After that, Hanoon's phone was disconnected and she continued to talk, and she told Nimrah to be careful in this house. He or Dayan has a different determination in his soul. Ever since he came home, he has been doing the same for these two children. Their rudeness made him swallow his greed. They were in the room for a while before they left to leave Afeef, the son of his roommate Mu'azz did not come in. That night, Afeef did not sleep for a long time and was plotting what he would do to Nimrah. During the night, he sat up on the bed, his legs were shaking, his face was as if he had eaten a lemon. He thought the phone was tight, but his thoughts were on his knees. (By Allah, I will not let go) He remembered the smile that Nimrah gave him after Dada was taken out. As soon as they looked at each other, Ruky and the hypocrite Mu'azz made a gesture with their fingers and laughed. Ruqayyan also saw the way she was looking at him as she looked at him. Including showing him how the leader of the gangsters put

Standalone post844 words

65

........A gidan Mammah kam bayan komai ya lafa, aka taimaka wa Afeef aka kai shi sama, ƴan uwansa Hanoon da Dayyan na tare da shi. Dan wata irin tsanar Nimrah da Ruƙayya suke ji na ƙara tasiri a zukatansu. Hatta ƴan gidan kowa ya basu haushi yau, yanda ko sau ɗaya ba'ama Nimrah faɗa ba balle cigaba da tuhumar gaskiya. Dan koda su Ma'aruff suka shigo kasancewar basa gidan su duka huɗun sunje duba wani makwafcinsu ne da baida lafiya da aka basu labari ko nuna zargin ma Nimrah basuyi ba su. Ƙarshe ma hira suka koma abinsu kamar komai bai faru ba. Hanoon ta kira Abbansu ta sanar masa komai, baya ƙasar dan tunda ya kawo su gidan yay tafiya. Shima ransa ya ɓaci har yana faɗin sai yayi maganin Nimrah idan ya dawo. Tunda yaga tsoronta suke ji a gidan. Shi yama rasa dangantakar su Adda A'isha da yaran duk da dai adadin jikokinta kawai ta sanar masa batai masa bayani ba bayan hakan. Shiyyasa yake tunanin jikokinta ne. Wayar yace a bama Afeef, ya lallasheshi da tabbatar masa zai dawo a cikin satin nan. Idan kuma zasu koma gida Lagos ne to ya saya musu ticket. Caraf Afeef yace shi bai yarda ba, yafi son Nan ɗin, dan wlhy bazai tafi ba sai ya rama.. Sallama yay musu da faɗin sai ya zo to. Daga haka aka yanke wayar Hanoon na cigaba da faɗin, sai ta koyama su Nimrah hankali a gidan nan. Shi ko Dayyan ƙudirinsa daban a cikin rai. Dan tunda yazo gidan hakanlinsa akan yaran nan biyu yake. Rashin mutuncin su ya saka shi haɗiye kwaɗayinsa. Sun jima a ɗakin kafin su fice su bar Afeef, dan abokin kwanan nashi Mu'azz bai shigo ba. A daren Afeef ya jima bai yi bacci ba yana ƙulla abinda zai ma Nimrah. Dan can cikin dare ma zaune ya tashi a kan gado kafarsa na masa masifar zogi, fuska a haɗe kamar ya ci lemon tsami. Waya ya ɗauka yana danne-danne, amma tunaninsa na kan ƙulle-ƙullensa. (Wallahi ba zan bari ba) Ya tuna murmurshin da Nimrah ta masa da gwalo bayan fitar Dada. Da yanda suka kalla juna da Ruky da munafukin nan Mu'azz sukai wani salo da yatsu suna gimtse dariya. Itama Ruƙayyan yana ganin yanda take kallonsa tana murmurshi. Harda gwada masa yanda shugaban ƴan iska ta saka masa ƙafa. Hakan na nufin itama ta gani amma da yake mufuka ce bakinsu ɗaya ne ta musanta harda bata kariya. “Yar iska… zanyi maganinki ta yanda ko takuna kika ji sai kin firgita ” ya faɗa ƙasa-ƙasa. Sai kuma yay ƙwafa da sake faɗin, “Ba kince kina da wayo ba.” Ya saki murmushi yana cizar lips da ƙara faɗin, “Zan tabbatar muku na fiku zama tantiri. Zaku san ni cikakken rainon yahudawa ne. Idan ba yau ba, gobe. Idan ba a falon ba, a wani wuri.” Ya saki wata shegiyar dariyar data farkar da Mu'azz a barci. A fili ya sake faɗin, “Sai kin gane baku kaɗai bane jiƙaƙƙun tantiran ƴan iska a gidan nan”. Sarai Mu'azz yaji furucin Afeef na ƙarshe. Sai dai bai ce komai ba, baima nuna masa ya farka ba. Amma ya fahimci akwai abinda yake shiryawa kuma akan Nimrah. Ji yay tausayin Afeef ɗin ma ya kama shi, dan wlhy ya tabbatar yace zai cigaba da shiga sabgar Ninah da Ruky a gidan nan to da wahala ba'a fita da shi a ambulance zuwa asibiti ba wataran. Dan yafi kowa sanin yaran nan, zaman lafiyarka da su kawai kada ka shiga sabgarsu. Anan kam zaka ga biyya, amma saɓanin hakan ALLAH ne kawai mai ƙwatarka saboda hanyoyin mugunta iri-iri sun santa kamar goyon iblis. Bari ya barsu da shi jikinsa zai gaya masa....

★A ɓangaren Nimrah tuni tama manta da wani batun Afeef. Dan koda suka shiga ɗakin su tsara yanda zasuyi yawo a weekend ɗin nan suke yi, suna fatan ALLAH ya ɗorasu akan Mammah kada ta hana su duk da suna hutun tahfiz ne. Sun jima kafin su kwanta sanin gobe akwai makaranta, duk da dai basu san ya zata kaya ba tunda sun bazar da ɗan shugaban ƙasa mai sauka a ƙasa. Nimrah ta kwanta amma bacci ya ƙi zuwa. Ruky ko tuni ta yi bacci tana sauke numfashi a hankali. Ita kam… ido biyu a rufe amma zuciya a buɗe. Haka kawai abinda ya faru ɗazu a falo kuma ya shiga dawo mata a rai. Ba kuma akan kowa ba sai kallon Dada ne yake dawowa mata a kai. Ba tsawa. Ba magana. Sai shiru da kallonsa mai kaɗa hanjin ciki.. Dai-dai lokacin dogarinsa ya kammala zuba coffee a kofuna masu shegen ƙyau na zallar farin gilashi mai garai-garai daga haɗaɗɗen coffee maker dake saman Centre table ɗin. Gaban kowa ya kai ya ajiye. Kafin cikin girmamawa ya nema izinin tafiya. Kai Janar ya jinjina masa alamar bashi dama. Sai ya sake risinawa sannan ya fice ya maida ƙofar ya rufe musu, bayan ya ƙara rage hasken falon ya bar blue ɗin wuta mara ƙarfi kamar waɗanda ke cikin club.........✍️