Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 64

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 64

.....ush was the first to move. He straightened up in his chair slowly, as if he was relieving the burden of a serious thought. He didn't look at anyone. Then the table in front of him. "Zak-Shadow..." He said the name in a low voice. Black Spider raised his head a little and looked at him, but he didn't say anything. "I thought it was over." Oga Jush spoke again, this time his voice was full of bitterness and anger that he could not suppress. Viper's thick wind blew. In his bitter state, he said, "Many people like him become stubborn because of their own stubbornness. Their bed is empty and empty and they feel they are not finished. They disappear only by repeating the word and they will come back even if they are full." He made a strong sigh, a sigh that shows the great determination that boils his heart on this side. Then silence passed through the room again, everyone with their own thoughts. Their son even encouraged Jush to get into trouble. Oga Jush interrupted their silence again. "We should ask him now, not just his return." He raised his head and looked at each of them in a row. Before he continued, "The question is... what did he come back to do?" It's as if this word is

Standalone post2,483 words

64

..........Babu wanda ya sake furta komai a ɗakin sai babbar jakar dake gefen oga Jush yay ma Mr Specter nuni da idanu. Mr Specter ya jinjina kai da tura jakar da ƙafa gaban Mole. “Ga wannan kaje da ita zamu nemeka idan buƙatar hakan tashi.” Wani irin daɗi ne mai barazanar fasa zuciya ya daki zuciyar Mole. Duk da yaji damuwa da shirunsu bayan maganarsa ta ƙarshe, dan yaso ace sun tattauna fiye da haka domin su ƙara yarda da shi fiye da yanzu. Amma ko hakan ma ai tafiya tayi riba, dan ya tabbatar maƙudan kuɗi ne irin wanda aka saba bama Dagger yana tsakura musu yanda yaso, shima yau gasu an bashi matsayin nashi. Lokacin gina sabuwar rayuwa yayi, dan yana son sanda Nimrah zata dawo hannunsa tasan shi cikakken uba ne da zai mata gata....

Bayan sun sallami Mole ƙofar ɗakin ta maida kanta ta rufe. ɗakin ya sake komawa wani irin yanayi na shiru. Ba hayaniya. Ba motsi. Sai na ac. Shirun da kan gitta tamkar mutuwa ta ziyarci waje. Shirun da yake sa zuciya ta dinga tambaya kafin harshe. Oga Jush ne na farko da ya motsa. Ya gyara zama a kujerarsa a hankali, kamar wanda ke sauke nauyin wani tunani mai tsanani. Bai dubi kowa ba. Sai teburin dake gabansa. “Zak-Shadow…” Ya faɗa sunan cikin murya ƙasa-ƙasa. Black Spider ya ɗaga kai kaɗan ya kallesa, sai dai bai ce komai ba. “Na zata an gama da shi.” Oga Jush ya ƙara faɗa, wannan karon muryarsa cike da ɗaci da zafin rai daya kasa dannewa. Iska mai kauri Viper ya furzar. Cikin nashi yanayin ɗacin ya furta, “Oga dama mutane irinsa nada taurin rai saboda taurin kansu. Gadararsu ta banza da wofi kansa su dinga jin ba su gama ba. Su kan ɓace ne kawai da maimaita kalmar zasu dawo koda da cika baki ne.” Ƙwafa mai ƙarfi oga yayi, ƙwafar dake nuna babban ƙudirin dake tafasa zuciyarsa a wannan gaɓar. Sai kuma shiru ya sake ratsa ɗakin, kowa da irin tunanin da yake yi. Dan su sun ma fi oga Jush shiga cikin razani. Oga Jush ya sake katse shirun nasu. “Tambaya ya kamata muyi ma kammu yanzu, ba dawowarsa kawai ba.” Ya ɗaga kai ya dubi kowan nen su a jere. Kafin ya cigaba da faɗin, “Tambayar ita ce… me ya dawo domin yi?” Tamkar ya dakesu a zukata ne da wannan kalma, dan babu wanda baiyi motsi irin na mai cizon cinnaka ba. Black Spider da ya jingina da bango, muryar sa na shaƙewa a naƙoshi ya amsa da, “Idan har ya sake kafa gida, to yana nufin yana da abin karewa.” Viper ya ɗan yi murmushi mara daɗi. “Ko kuma ita ribar ƙafar ba, dan ina ji a raina riƙonta a garesa da manufa. Karfa ku manta yana da wayo, yana da target.” Oga Jush ya lumshe ido na daƙiƙa kaɗan. Kafin a hankali ya ce, “Tabbas maganarka gaskiya ce. Musamman idan muka kalla Mole. Tana kusa da shi. Kuma ba ta san komai ba a kansa.” Black Spider ya ɗan jinjina kai da furzar da numfashi mai nauyi. “Wannan ne mafi haɗari. Ku duba, mun bata video ɗin nan, amma babu wani motsi…” Shiru ya sake mamaye ɗakin kamar an kashe iska. Kowa ya nutsu cikin tunani, ba don rashin amsa ba, sai don girman barazanar da ke gabansu. Viper ya gyara zamansa da faɗin, “Idan har yarinya ta iya jure irin wannan barazanar, to tabbas tana da ƙarfin zuciya da dole sai mun sake nazartar ta… ko kuma tana cikin shakka da wasi-wasi. Kuma dole mu gaggauta......” Oga Jush ya ɗaga hannu da alamar yarda da zancen Viper ɗin. “Yarinyar ba matsala bace,” Oga Jush ya furta yana zuƙar sigari, sai da ya fesar da hayaƙin da sake gyara zaman ƙasaitarsa yana kakkaɓe tokar sannan ya cigaba da faɗin, “Matsalar ita ce wanda ke kusa da ita. Ku sani Zak-Shadow bai dawo domin zama ba. Idan har ya sake takun zahiriyya, to lallai ya dawo ne domin ya gama abin da bai kammala ba a baɗini.” “Kenan oga hakan na nufin idan yarinyar bata motsa ba, zamu tilasta mata ta motsa dole?.” “A’a. Ba da gaggawa ba.” Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya saki wani murmushin mugunta mai armashi da ban tsoro. Sai kuma ya haɗe fuska da ƙarasawa da, “Amma daga yau… ta zama hanyar shiga.” A tare suka bubbuga tebirin gabansu alama na amincewa. Babu dariya. Babu tambaya. Babu jayayya. Shirun da ya biyo bayan maganar ya fi kowace hukunci nauyi. Wannan shirun ya fi kowace tsawa firgita.....

>>>>>>>%<<<<<<<

Fitowarsa ya saya Imran dake tsaye jikin mota yana duba wayarsa kamar wanda ke jiran lokaci ɗagowa yana kallonsa. Shima kallon nasa yake, koda suka haɗa ido sai ya ɗauke nasa, kai kace baiga Imran ɗin ba ma. Dan kai tsaye gaban motar ya buɗe ta gefen mai zaman banza ya shiga abinsa. Imran dake binsa da kallo yay murmushi yana ɗan taɓe baki, kafin shima ya zagaya gefen driver ya shiga ya zauna.. Sai da ya tada motar ya ɗan kallesa da faɗin, “Ni harna fara tunanin binka ciki ma, jin shiru bayan kace gaka nan fitowa”. Dada bai amsa ba. Ya daidaita zamansa ne kawai, ya jingina da kujerar, yana mai lumshe idanunsa. Sai da suka fice gaba ɗaya a gidan sannan Dada ya ɗan saki numfashi, tare da motsa lips kaɗan, cikin murya ƙasa-ƙasa ya furta, “Hmm.. yaranka basa ji.” Imran ya ɗan juya kai ya kallesa, sai kuma ya saki murmushi da maida hankalinsa a titi sosai. “Oh, su ne suka tsaidaka kenan? Mi ya faru?” A nan ma shiru yay kamar bazaiyi magana ba. Irin shirun nan na manya, wanda baya nufin babu abin cewa, sai dai ana tattara abin faɗar ne saboda ɗabi'ar rashin son magana. Imran yasan halin kayansa, dan in kaji doguwar magana a bakin Zak... Ɗinsa ɗayan biyu ne. Kodai akan aiki, ko yana tare da Mammah ko da shi randa yaso hirar. Sun riga sun fice daga unguwar, har sun shiga babban titi, Imran na kallon hanya cike da natsuwa. “Wai bazaka gaya min ba, sai na sauke ka a hanyar nan?”. Idanu Dada ya ɗan buɗe yana harararsa, Sai ya kauda kai gefe, kamar yana kallon wani abu a waje, ya ɗan taɓe baki, murmushi yana ƙoƙarin kufce masa amma ya haɗiye kayansa. “Kana son bani ciwon kai ne kawai kai da su Imran. Tsabar mugunta yaron nan kawai ta sama ƙafa ya kife a ƙasa shi da kofin tea. Ta kuma fiske abinta baka isa cewa ita ta aikata ba, harda kiransa mai ƙafar talo-talo”. “ALLAH ya shirya min Ninah” Imran ya faɗa yana ƴar dariya. Dada ya juyo ya watsa masa harara. “Oh abin ma sugar yay maka kenan? Idan taji masa ciwo kuma fa?”. “In banyi dariya ba kuka kake son nayi. Indai su Nimrah ne kaɗan daga aikin su ka gani.” Shiru ya sake ratsa motar. Amma wannan karon shiru ne mai ɗauke da dariya a ciki. Dan Dada gintsewa kawai yake, amma yanda ta saka ƙafar yaron ya kife kifff kawai ke dawo masa cikin rai. Yana buɗe file ɗin daya ɗauka a gaban motar ya sake furta, “Na shaida hakan yau kam, dan ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta bata kariya bayan yaron ya tabbatar ita ce ta kada shi, Mammah kuma ko faɗa bata musu ba fa.” Imran ya saki dariya sosai har yana ɗan dukan sitiyari. Sai da yay mai isarsa, Dada da ya kallesa ya girgiza kai kawai. “To wai wanene aka kada? Nasan dai ba zasu ma Mu'azz ba”. Dada ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Cikin yaran mutum nan ne. Dama na fahimci ƴar tsama suke da su”. “Kaji fitina, yaron da a tsaye ya fisu sau biyu!” Imran ya furta yana dariya. “Ba ku kuke ɗaure musu ƙugu ba, ba Mammah ɗin ba, ba kai ba balle Uncle's da Auntys ɗin nasu. Abinda suka aikato a school yau banji wani yace musu dan mi ba, ƙarshe ma Mammah na gayama su Ma'aruff dariya na jiyo sunayi Bilal harda musu kirari”. Imran ya sake kallonsa, wannan karon da nishaɗi sosai. “Ba wani ɗaure musu ƙugu da muke. Dole akwai abinda ya aikata musu shima, dan duk ƙiriniyarsu basa faɗan rashin gaskiya. Ɗazu ma lawyer ɗin nasu ya kirani yana min bayani wai yaron ya farfaɗo, amma iyayen sun kawo lawyer suma, da farko da sun dage sai an sake maido su station ƴan sandan suka nuna masa basu cika 18years ba, basu da hurumin riƙesu anan.” “A’a. Ba da gaggawa ba.” Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya saki wani murmushin mugunta mai armashi da ban tsoro. Sai kuma ya haɗe fuska da ƙarasawa da, “Amma daga yau… ta zama hanyar shiga.” A tare suka bubbuga tebirin gabansu alama na amincewa. Babu dariya. Babu tambaya. Babu jayayya. Shirun da ya biyo bayan maganar ya fi kowace hukunci nauyi. Wannan shirun ya fi kowace tsawa firgita.....

>>>>>>>%<<<<<<<

Fitowarsa ya saya Imran dake tsaye jikin mota yana duba wayarsa kamar wanda ke jiran lokaci ɗagowa yana kallonsa. Shima kallon nasa yake, koda suka haɗa ido sai ya ɗauke nasa, kai kace baiga Imran ɗin ba ma. Dan kai tsaye gaban motar ya buɗe ta gefen mai zaman banza ya shiga abinsa. Imran dake binsa da kallo yay murmushi yana ɗan taɓe baki, kafin shima ya zagaya gefen driver ya shiga ya zauna.. Sai da ya tada motar ya ɗan kallesa da faɗin, “Ni harna fara tunanin binka ciki ma, jin shiru bayan kace gaka nan fitowa”. Dada bai amsa ba. Ya daidaita zamansa ne kawai, ya jingina da kujerar, yana mai lumshe idanunsa. Sai da suka fice gaba ɗaya a gidan sannan Dada ya ɗan saki numfashi, tare da motsa lips kaɗan, cikin murya ƙasa-ƙasa ya furta, “Hmm.. yaranka basa ji.” Imran ya ɗan juya kai ya kallesa, sai kuma ya saki murmushi da maida hankalinsa a titi sosai. “Oh, su ne suka tsaidaka kenan? Mi ya faru?” A nan ma shiru yay kamar bazaiyi magana ba. Irin shirun nan na manya, wanda baya nufin babu abin cewa, sai dai ana tattara abin faɗar ne saboda ɗabi'ar rashin son magana. Imran yasan halin kayansa, dan in kaji doguwar magana a bakin Zak... Ɗinsa ɗayan biyu ne. Kodai akan aiki, ko yana tare da Mammah ko da shi randa yaso hirar. Sun riga sun fice daga unguwar, har sun shiga babban titi, Imran na kallon hanya cike da natsuwa. “Wai bazaka gaya min ba, sai na sauke ka a hanyar nan?”. Idanu Dada ya ɗan buɗe yana harararsa, Sai ya kauda kai gefe, kamar yana kallon wani abu a waje, ya ɗan taɓe baki, murmushi yana ƙoƙarin kufce masa amma ya haɗiye kayansa. “Kana son bani ciwon kai ne kawai kai da su Imran. Tsabar mugunta yaron nan kawai ta sama ƙafa ya kife a ƙasa shi da kofin tea. Ta kuma fiske abinta baka isa cewa ita ta aikata ba, harda kiransa mai ƙafar talo-talo”. “ALLAH ya shirya min Ninah” Imran ya faɗa yana ƴar dariya. Dada ya juyo ya watsa masa harara. “Oh abin ma sugar yay maka kenan? Idan taji masa ciwo kuma fa?”. “In banyi dariya ba kuka kake son nayi. Indai su Nimrah ne kaɗan daga aikin su ka gani.” Shiru ya sake ratsa motar. Amma wannan karon shiru ne mai ɗauke da dariya a ciki. Dan Dada gintsewa kawai yake, amma yanda ta saka ƙafar yaron ya kife kifff kawai ke dawo masa cikin rai. Yana buɗe file ɗin daya ɗauka a gaban motar ya sake furta, “Na shaida hakan yau kam, dan ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta bata kariya bayan yaron ya tabbatar ita ce ta kada shi, Mammah kuma ko faɗa bata musu ba fa.” Imran ya saki dariya sosai har yana ɗan dukan sitiyari. Sai da yay mai isarsa, Dada da ya kallesa ya girgiza kai kawai. “To wai wanene aka kada? Nasan dai ba zasu ma Mu'azz ba”. Dada ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Cikin yaran mutum nan ne. Dama na fahimci ƴar tsama suke da su”. “Kaji fitina, yaron da a tsaye ya fisu sau biyu!” Imran ya furta yana dariya. “Ba ku kuke ɗaure musu ƙugu ba, ba Mammah ɗin ba, ba kai ba balle Uncle's da Auntys ɗin nasu. Abinda suka aikato a school yau banji wani yace musu dan mi ba, ƙarshe ma Mammah na gayama su Ma'aruff dariya na jiyo sunayi Bilal harda musu kirari”. Imran ya sake kallonsa, wannan karon da nishaɗi sosai. “Ba wani ɗaure musu ƙugu da muke. Dole akwai abinda ya aikata musu shima, dan duk ƙiriniyarsu basa faɗan rashin gaskiya. Ɗazu ma lawyer ɗin nasu ya kirani yana min bayani wai yaron ya farfaɗo, amma iyayen sun kawo lawyer suma, da farko da sun dage sai an sake maido su station ƴan sandan suka nuna masa basu cika 18years ba, basu da hurumin riƙesu anan.” Dada ya ɗan yi ƙwafa kaɗan, murmushi na neman kufce masa. Ya dai juyo gefe yana ƙoƙarin ɓoye abinsa. Kamar baya so ya furta, “Yara ne. Amma ba ƙanana bane tunda har suna da wayon banbance abubuwa. Dan itama Ruƙayya aure zan mata” Cike da neman magana Daddy Imran ya ce cikin raha, “Hmm… yanzu ka fara ganewa kenan?” Dada ya kallesa. “Gane mi?” Imran ya ɗaga masa gira cike da tsokana da son ganin ya ƙure shi. “Cewa ɗiyata Nimrah ta girma.” Nan ne Dada ya kasa danne kansa. Ya saki ɗan murmushi mai nauyi, ya kauda kai gaba ɗaya yana girgiza kai a hankali. “Kar ka fara”. Ya faɗa cikin gimtsewa. Dariya Daddy Imran ya saki. “Wlhy dole in fara. Saboda kallon da ka mata yau a station… ai na san wannan kallo.” Dada ya ɗaga kai yana harararsa da sake ɗaure fuska, sai dai murmushin dake makale a fuskarsa ya neman fallasa shi. “Imran!” Ya faɗa da gargaɗi. “Yi haƙuri Babban Yaya, wannan idanun bana son suna hararata.” Sake hararar tasa kuwa Dadan yayi yana ɗauke kai. Imran ya murmusa da cigaba da faɗin, “Amma kai ka fi kowa sanin damuwar ka. Ka ƙi kace komai akan dawowar Nabeeha. Zak.. shekara takwas fa ba wata takwas bane. Lemon tsami, kanwa, azumin nan duk basa hana komai, kwantarwa ne kawai na lokaci. Ya kamata kayi abinda ya dace, bance Nimrah ba, dan tabbas tayi ƙanƙanta a shekaru, amma da wayonta. Sannan Nabeeha ba sakinta kai ba balle kace. Komai ya dai-daita, sai dai ka sani aiki bazai samu dukkan ƙarfinka ba, sai kaima ka Dai-daita. Wannan danne damuwar ta tsiya-tsiya bazata haifar da ɗa mai ido ba”. Dada da ya ce, “Hummm” kawai ya yi shiru. Sai dai wannan shiru ba na ɓacin rai bane. Na tunani ne… da ɗan murmushi a zuciya. Dai-dai nan suka iso inda suka nufo. Ɓoyayyen guesthouse dan haɗuwar ta sirri ce da shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida...........✍️