Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 63

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 63

.....sakama Afeef's feet and hair kifff on the floor with his cup of tea. Torment caused him to break the shocking volume of data and make everyone jump in the hall. She or the one who invited her to work has already turned her foot and folded her legs, you can't say she did it.... In this way, the leaders of the group are the five and not everyone else. From top to bottom, Jush finished looking at him and analyzing him. Before he started speaking, he was full of documents of the rulers. "Why did you try to deliver this message directly to us after there was Dagger leading you before today? He gave you his orders for any work. Is there anything wrong with him that you disagree with?". Since Mole does not speak Oga Jush language, Black Spider translates for him. Mole bowed his head in reverence and trembled. He can speak the same language as Black Spider. He confirmed that if he wants to catch a group of people, he will follow them step by step, because the bad guy knows how to hide the bad guy in.....

Standalone post1,686 words

63

.........Mu'azz ya shigo a gajiye, dan daga makaranta yake mashin ɗinsa ya samu matsala a hanya sai da Ammar ya biya ya ɗakkosa, dan haka sukai dare. Sun maida hankali a kansu suna musu sannu da jajanta abinda ya faru Dada ya fara sakkowa daga sama. Dan kafin ma ya bayyana ƙamshinsa ya fara isowa hancinan wasun su da takunsa. Tamkar an saita shima Afeef ya fito daga kitchen ɗauke da tea zai sha. Dan su abinci sai sun zaɓa. Nimrah da hankalinta ke kan kwance ma Afrah kai sam bata ji batun sakkowar Dada ba. Sai hankalinta ya koma kan Afeef. Alƙawarin datai ma kanta na yau sai ya kwana da kumburarren baki ta tuna. Ta kalla dole sai Afeef ya bi ta gabanta sannan zai wuce sai ta saki murmurshin da ALLAH ya tabbatar ma Dada ganinsa sakamakon idanunsa da suka sauka a kanta daga stairscase ɗin da yake sakkowa. Har zai kauda kai sai ya fahimci kallon da take ma ƙafafun yaron nan da ko sunansa bai sani ba. Sam bai kawo tunaninsa akan abinda take shirin yi ba, dan kamar ƙyaftawar ido kawai ta sakama Afeef ƙafa sai gashi kifff a ƙasa shi da kofin shayin nasa. Azaba ta saka shi fasa gigitacciyar ƙarar data saka kowa zabura a falon. Ita ko mai gayya da aiki tuni ta maida ƙafarta ta naɗe yanda take baka isa cewa itace ta aikata ba....

###########

Tunda fa yau Malam Buba ya buɗe ido ya gansa a gaban shugabannin kungiyar duhu yaji yana neman susucewa, dan kuwa wannan shine karonsa na farko a tsawon fara aikinsa da su shekara takwas. A haka ma iya shugabannin ƙungiyar ne su biyar ba kowa da kowa ba sauran members. Daga sama har ƙasa oga Jush ya gama ƙare masa kallo da nazartarsa. Kafin ya fara magana cike da gadarar taƙadaran masu mulki. “Miyasa kai ƙoƙarin isar da wannan saƙon kai tsaye garemu bayan akwai Dagger dake jagorantar ka kafin yau?. Duk wani aiki shike baka umarnin sa. Ko akwai wani kuskure ne daka gani a tare da shi da ka ji rashin yarda?”. Kasancewar Mole ba jin yaren Oga Jush yake ba Black Spider ya fassara masa. Mole ya sake risinar da kai cike da tsantsar girmamawa yana kuma girgizawa. Shima da yarensa daya iya yay magana black Spider tafinta. Ya tabbatar idan yana son kama kurwar mutanen nan sai ya bisu mataki-mataki, domin kuwa mugu shi yasan makwantar mugu ai. “Ranka ya daɗe babu wata matsala shakanina da oga Dagger sai alkairi. Shi mutum ne mai amana kuma yasan aikinsa. Kwana biyu ban samesa bane ga kuma abinda na gani na cimin rai. Na kuma tabbatar kuna buƙatar wannan bayanin da gaggawa saboda matuƙar muhimmancin sa.” Koda Black Spider yay ma oga bayani sai oga Jush ya zubama Mole idanu yana sake nazartar sa. Cikin gamsuwa ya ce, “Naji daɗin hakan ƙwarai da gaske. Dan yabon Dagger da kayi ya tabbatar mana kaima mutum ne mai amana. Da kaci amanarsa muma mun san zaka iya cin tamu. Zaka iya bayanin ka yanzu kam”. Sosai Mole yaji daɗin wannan yabo, dama kuma irinsa yake son ji. Cikin ƙara kwantar da kai ya fara bayani dalla-dalla akan dawowar Dada. Babu wanda a cikinsu bai rikice ba kam. Dan oga Jush ma har miƙewa yayi tsaye tsabar firgici. Cikin tsawa-tsawa Viper ya ce, “Kasan abinda kake faɗa kuwa? Kai ya akai kasan shi?”. “Babu tantama ko kokwanto a maganata oga, duk da a yanzu ya canja kamannin fuska ya ajiye gashin saje bazai layance min ba ai. Sannan taya zan manta da wanda gudan jini na take a hannunsa. Sai da na sake tabbatar da dukkan abinda zan kawo muku sannan na yarda nazo nan. Kuma na baku damar bincikawa kuma, dan kullum suna fita da Imran ɗin nan, sai dai ban san ina suke zuwa ba. Da farko nayi tunanin zai gane ni, sai kuma naga shekara takwas da rabi ba kwana takwas bace ba. Oga ku taimakeni yarinyata ta dawo hannuna nima, dan sun mata asiri bata ko tuna tanada uba. Mun bata video ɗin nan da kuka bada amma babu wani motsi daya nuna alamar ma saƙon da muke ƙoƙarin isarwa ya mata tasiri”. Komai babu wanda ya iya sake ce masa a cikinsu. Dan halin da suke ciki a yanzu yafi nashi......

★+++++++++++++++★ Ƙarar da Afeef ya fasa ta daki falon gaba ɗaya. Kowa ya zabura kamar an harba bindiga. Kofin shayin ya watse, ruwan ya zuba a kafet ɗin tsakkiyar falon, shi kuma yana mirgina a ƙasa yana riƙe ƙafarsa yana nishi. “Wayyo ALLAHA! Wayyo kaina, ƙafata”. “Subhanallah!” “Innalillahi!” Muryoyin su Aunty Shariffa suka gauraye falon. Mammah ta miƙe da sauri tana nufarsa, Aunty Lailah ma ta biyo bayanta. Hakama Biebah da Ruky da har zata nufi kitchen ta dawo. Hanoon da Dayyan sun miƙe tsaye suma a firgice, hakama Mu’azz da sauran yaran su Aheel na tsaye kowa na kallon abin kamar fim. Dada ma ya tsaya cak, sai dai baiyi magana ba. Sai idanuwansa da suka sauka a wajen. Kallon farko ya tsaya ne kan Afeef dake kwance yana nishi. Kafin ya maida kan kafar daya riƙe da hannu biyu yana magowa alamar tana masa raɗaɗi. Slowly ya maida kan Nimrah ƙasa-ƙasa ta yanda babu wanda zai ce ita yake kallon. Tsaye take. Hannunta biyu riƙe da ƙugu. Fuskarta a haɗe, kamar bata fahimci me ya faru ba, ta wani zuba masa idanu kamar kowa. Idanun kuma darr babu alamar na mai laifi data firgita sakamakon ganin abinda ta aikata. Dada ya ɗan lumshe ido, ya sake buɗe su a hankali, ya maida kallonsa kan Afeef. Sai dai yanzun ma bai da alamar cewa komai. “Subahanallahi kaji ciwo ko ruwan zafin ne ya ƙona ka?” Mammah ta faɗa tana durƙusawa kusa da shi da kamo sa jikinta. “Zafi nake ji!. Kafa ta…” Afeef ya faɗa hawaye na ziraro masa a fuska. Biebah ta kalli shayin da ya zube. Cikin nuna mamaki ta ce, “Wai yaya ma haka ta faru? Naga babu komai a hanyar nan dai amma kamar wanda yaci tuntuɓe irin wannan muguwar faɗuwa haka”. Afeef ya ɗaga kai, idanunsa na sauka kan Nimrah kai tsaye ya ce, “Ita ce. Ita ta saka min ƙafa.” Falon ya ɗauke shiru na daƙiƙa ɗaya. Kafin Nimrah data zazzaro masa idanu ta ce, “Ni?!” ta faɗa cikin kamar ma mai mamaki irin na karya. Sai kuma ta shiga tafa hannaye “Kai! Amma kai mugun maƙaryaci ne. Ta ina zan iya kada ƙaton nan kamar ka to?!”. Hanoon da ranta ya ɓaci sosai ta watsa mata harara, sai dai batace komai bata. Ruky data gama sanin wacece Trouble Queen ɗinta ta haɗiye dariyar dake son bayyana a fuskarta saboda Dada. Mu'azz ya taɓe baki yana ƙoƙarin danne dariya shima, dan tsaff ya gane aikin Ninah ɗin ne, haba shekara nawa ana haɗakar tsiyataku a tare. Aunty Lailah da Shariffa kam kallon su biyun kawai suke kamar ba su san dawa zasu yarda ba. “Nimrah… Mi ya faru?”. Mammah ta kira sunanta a hankali, sai dai ta kafeta da idanu. Shagwaɓe fuska Nimrah tayi, kafin ya ce, “Ni Mammah sharri kawai yake mun. Kowa ai yana ganin tsifa nake ma Afrah. Yanzu nida ke can, yana nan ƙafar barewa ce da ni balle na iya zunguro shi?. Ƙilama ƙafafun nasa ne basu da kwari, dan gasu nan tsulai-tsulai kamar na talo-talo wlhy”. Kafin kowa yace komai Afeef ya harare ta. “Wallahi ke kika saka min ƙafa!”. Caraf Ruky ta ce, “Karya kake! Dan ina tsaye ta kusa da ku ni ban gani ba” A hasale Hanoon dake hararar Ruky ta karɓe da, “K dama ai bazaki faɗi gaskiya ba bakin ku ɗaya munafuka fitinannun yara! Kawai”. “Ke ma fitinanniya! Dan ni da Buddy na albarka kullum Mammah ke saka mana da iyayenmu”. Nimrah ta faɗa tana murguɗa ma Hanoon baki da nuna su Shariffa. Hanoon zata sake magana Mammah ta dakatar da su. “Ya isa haka. Mu'azz bani first aid kit” Mammah ta faɗa tana kama ƙafar Afeef da cigaba da faɗin. “Bari mu fara ganin kafar yafi wannan gardamar taku.” Sai lokacin ta juya ta kalli Dada da tamkar baya ma a falon kamar tana neman taimako. Amma sai gani tayi hankalinsa ma akan wayarsa yake gaba ɗaya. Dole ta haƙura ta maida idanuwan nata ga Afeef. Abinda Mammah bata sani ba sarai Dada na lure da kallon datai masan, amma ya fiske. Sai ma mamaki da jinjina ƙarfin halin yarinyar nan da yake a ransa. Dan tsaff ta koma inda ta tashi abinta hankali kwance ta cigaba da ma Afrah tsifarta babu alamar tausayin yaron ko ɗigo. Murmurshi ne yay kamar zai kufce masa amma ya matse. Sai ma ya nufi ƙofa abinsa yana faɗin, “Mammah sai na dawo”. Maganarsa ta saka hankalin su Shariffa dawowa kansa. Sai lokacin suka tuna ko gaishe shi basuyi ba. Aiko cikin sauri suka fara gaishe shin, dole ya dakata yana amsawa. Nimrah dake jin idanu masu kaifi a kanta tun ɗazun sai dai ta rasa wake kallon nata ta ɗan motsa kaɗan, zuciyarta na bugawa, amma fuska a tsuke kamar ba ruwanta. Nata idanun ta ɗan ɗago a karo na farko ta saci kallon Dada da kowa ke gaidawa. Cikin sa'a kuwa sai idanun nata suka faɗa cikin nasan. Cikin sauri ta janyesu ta sauke kanta ƙasa ƙirjinta na sake bugawa.. Dada da shima ya janye nasa cike da basarwa yana sake ɗaure fuska ya ɗan ja numfashi a hankali. Sannan ba tare da ya ɗaga murya ba ya furta “Sai na dawo”. Muryar sa ba tai ƙarfi ba. Amma amonta da tasirinta ya ratsa kowa dake falon, musamman Nimrah. Dan kallon da ya sake yi mata kafin ya juya, ya sa zuciyarta ta buga sau biyu. Domin ta fahimci abu ɗaya. Dada ya gani. Kawai bai faɗa ba ne. Sannan bai nuna alamun yama san abinda akai ba. Bai ce Nimrah ba. Bai ce Afeef ba. Bai yi hukunci ba. Sai dai taji tasirin kallonsa na ƙarshe ɗin nan da idonta ya gani, dan bazata iya tantance na baya da bata san wanene ke mata shi ba.........✍️