Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 62

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 62

...and then he went to bed on his own. Nabeeha's body trembled as she held him. Hajiya Hasiba's heart was pounding and she was pointing at both of them with her finger. "You are not enough, wlhy, I did not give birth to a son who would defy me. Even Jeddah, which you think I have allowed, is a waste until the time when I look back. And you will know that you are ashamed of the little halak. Even if it was your father who sent me these words, I am right with him. I will go and find him to his house, wlhy". After that, she left and closed the door and turned the key again... >>>>>>>%<<<<<<< All in all, Mr. Buba wanted to see the night. He got a message from the president saying that they want to see him tonight. He or she is the husband of this blessed day. It's time for them to rub shoulders with Dagger, it's time for them to be soaked with money called money, not the shopping money that Dagger gets them. He was so deep in his thoughts that Daddy Imran yelled at the caretaker and got up and opened the gate after looking to see who it was. When the manager finished closing the gate, he came back and sat down and touched him and he was shocked, then his eyes fell on Nimra.....

Standalone post1,499 words

62

.........“Ai ku ke da haƙuri masu uba. Yanzu ku ku ɗin nan dana gama ƙare rayuwa a wahalar yi muku gata har kuke shirya yanda zaku barni kamar Jiddah. Koda yake ke Ismat ma ai kin barni ɗin, to halan da kika koma gidan uban naku gwal aka maidaki? Har waye Nasiru? Mi yake da shi? Wane gata ya baku a rayuwa matsayin uba da zaku bijire min ku zaɓe shi sama dani?”. “Momy kiyi haƙuri ku duka kuna da muhimmanci a garemu kuma darajar ku ɗaya ce. Dan tare kuka haife mu har duniya ke iya kallon mu da daraja irin ta ƴaƴa masu iyaye guda biyu da aka haifa da aure. Momy ba damuwar mu dukiyar da kuka tara ko gatan da kuke mana ba. Abinda ke tsakanin ki da Daddy daban haka muma, ke matsayin mata kike kuma ƴar uwar sa, muko sunan mahaifi yake amsawa, albarkar ku da addu'ar ku kawai muke buƙata a cikin rayuwar mu, sai mu zauna lafiya. Sannan koda bakwa tare zaman mu a tare da shi zaifi bamu daraja musamman ga masu iya zuwa neman auren m.....” Tauuuu!!! Kake jin saukar mari mai ƙara a fuskar Ismat da sai da kanta ya bigi gado. Jikin Nabeeha na rawa ta riƙota. Zuciyar Hajiya Hasiba na tafarfasa da hanƙoro a cikin ƙirji ta miƙe tana nuna su su duka biyun da yatsa. “Ku baku isa ba wlhy, ban haifi ɗan dazai bijire min ba. Ko Jiddah da kuke ganin na ƙyaleta na barta ne zuwa lokacin dazan waiwayeta. Kuma zaku san kunyi da ƴar halak. Idan ma uban baku ne ya aikoki ki faɗa min waɗan nan zantukan ina dai-dai da shi. Zan je kuma na sameshi har gidan nashi wlhy”. Daga haka ta fice fuuuu tare da rufe ƙofar bummm ta sake murza mata key......

>>>>>>>%<<<<<<<

Gaba ɗaya a ƙage Malam Buba yake da son ganin dare yayi, dan yau jinsa yake tamkar an masa albishir da mukullin shiga aljanna. Saƙo fa ya samu daga shugaban nin su cewar yau suna son ganinsa da daddare. Shi ko mizai ce da wannan ranar albarka. Lokaci yayi da zasu goga kafaɗa da Dagger, lokaci yayi da shima zai jiƙe da kuɗi masu suna kuɗi ba kuɗin cefane da Dagger ke sammusu ba. Yayi zurfi a wannan tunanin nasa har Daddy Imran yay horn maigadi ya tashi ya buɗe gate bayan ya leƙa yaga wanene. Sai da maigadi ya gama maida gate ɗin ya rufe ya dawo ya zauna ya taɓashi sannan yay firgigit, sai kuma akai sa'a idanunsa suka sauka akan su Nimrah dake fitowa daga motar. Agogon hannunsa na ƙarfe da ya gama cin duniyar sa a tsufa ya kalla, dan yana aiki lafiya lau, ko ya samu matsala badawa take a gyara masa saboda yana son agogon sosai. Ganin lokacin tashin su da saura mamakinsa ya kasa ɓoyuwa, sai kuma maigadi ma ya riga shi da faɗin, “Da alama yau masu gidan sun ɗakko maganar da suka saba a makaranta. Dan in ka gansu a gida ba lokacin tashi ba akwai wata a ƙasa. Kai waɗan nan yara ban taɓa ganin ibilisai irinsu ba. Anya basu da aljanun faɗa kuwa?.” “To waya sani ko su gare su”. Cewar Malam Buba da duk hankalinsa ke kansu. Dan ji yake tamkar ya zama ƙuda yaje ya tambayi Nimrah miye damuwarta. A kwanakin nan ji yake ƙaunarta na sake mamaye masa zuciya da ɓargon jiki. Idan ya ɗau wani lokaci bai ganta ba ji yake kamar yay tsuntsuwa ya shiga gidan. Sai yata dannewa da ƙyar yake samun kansa. Maigadi bai lura da halin da Malam Buba ke ciki ba dan fitowar Sanda da tunda ya buɗe gate yay wuff ya shige ɗakinsu ta sashi maida hankali a kansa. Harararsa Sanda ɗin yayi tun kan yace komai, dole ya haɗiye abinda yaso faɗar kuwa koda tunawa da malam Buba a wajen.....

★A ciki kuwa tunda su Nimrah suka shigo falon Mammah dake zaune tana cin apple su Shariffa na mata hira, sai Dayyan dake kallon Film, Hanoon na daga gefensa tana latse-latsen waya da bata gajiya tasan akwai matsala. Dan Dada ne ya fara shiga, hakan yasa su Lailah sukai tsitt daga hirar da suke yi suka sake nutsuwa saboda girmamawa suna masa sannu. Dayyan ma da sauri ya gyara zamansa dan har cikin rai yake jin tsoron Dadan nan dako harkarsu baya shiga a gidan, kai ko kallo basu ishe shi ba. Ɗan zungurin Hanoon dake murmushi idonta a waya yayi, ta ɗago zata watsa masa harara a bazata taga Dada. Ai da sauri itama ta gyara yanayin ta, sai dai ita bana tsoro bane kawai harda na soyayya. Mammah kawai ya gaisar, yana amsa gaisuwar su Shariffa ya nufi hanyar upstairs. Dan haka Mammah ta maida idanunta kan Imran cike da neman amsar tambayarta akan su Ruky. Zama yay ya gaida Mammah, shima su Lailah suka gaishe shi. Su Dayyan dama gaisuwarsu sai sun so, amma da yake shima Imran ɗin shakkarsa suke ji kasancewar ba wasa ya taɓa yi da su ba sai suka gaishe shi. Amsa musu yay suma da maida hankalinsa akan Mammah data kasa haƙuri ta jefa ma su Nimrah tambaya. “Yanzu ina farin cikin kwana biyu kun nutsu ashe lumbu-lumbu kuka min. Yau kuma mi kuka aikata?”. “Hummm! Ɗan tsohon shugaban ƙasa suka sumar Mammah”. Ba Mammah ba hatta su Dayyan sai da suka ƙwalalo idanu waje. Lailah da Shariffa kam na haɗa baki wajen faɗin, “Ɗan tsohon shugaban ƙasa fa Yaya!”. “To waɗan nan yaran kuma ai inaga shi kansa shugaban ƙasar dake kan kujerar mulki idan tsayawa zai yi bazar da shi zasuyi. Ina ga aikin soja kawai zan kaisu dan al'amarin nasu zaifi armashi a can”. “Oh ni A'ishatu ALLAH kana gani, to miyay musu da zafi har takai da sumarwa? Sannan ma wai yaro ne kamar su ko yaya?”. “Mammah ina fa sa'ansu, ajin ƙarshe fa yake a makarantar tasu. Kinga ko ai kusan sa'an Mu'azz kenan ake batu”. Salati Mammah ta sake sakawa tana zabga tagumi, yayinda su kuma suke cika baki da iska suna hararar Dayyan da Hanoon dake dariya, dan su abin dariya ya basu harga ALLAH. Yara kamar jinin Chaines jama'a. “Kun bar wajen ko sai na tashi kan ku”. Daddy Imran ya faɗa yana harararsu gani abinda suke ma su Dayyan. Ɗaki suka nufa sunama su Dayyan ɗin alamar zasu haɗe. Imran ya girgiza kai kawai yana danne dariyarsa, shi wlhy bai san yaya zai yi da yaran nan ba. Jifa ba'a gama kashe wani case ɗin ba suna ma wasu gargaɗi a cikin gida, dole ne a wannan gaɓar itama Ruƙayya a mata aure kawai zai fi samun nutsuwa. Sai da suka gama shigewa ya zayyanema Mammah komai da bayanin da sukayi har Dada yace akai zancen court, sai dai shima bai san dalilinsa na yin hakan ba. Amma yafi ƙyautata zaton kawai yayi hakan ne dan barazana tunda abinda su yaran suka faɗa dole su iyayen yaron zasu so case ɗin ya tsaya iya inda yake a yanzu. Mammah ta gamsu, tare da jera musu addu'ar shiriya. Daga haka shima Imran ya miƙa yay musu sallama dan yace zaije gida ne anjima zai dawo.....

★★★★

Tsoron haɗuwa da Dada ya hana su Nimrah fitowa. Sai da yunwa ta ishesu Nimrah tai ƙundun balar zuwa ga ɗiba musu abinci ta koma. Da yake yau babu islamiyya haka suka cigaba da maƙalewa a ɗakin har akai magriba. Sai bayan sallar isha'i sannan suka fito bayan sun gama leƙowa sun tabbatar da Dada ya wuce sama baya falon, dan idan ya dawo sallar isha'i wani lokacin babu mai sake ganinsa. Su aunty Lailah ma suna sashensu basu kai da zuwa hirar dare ba. Hanoon ce kawai da Afeef yanzu zaune. Mammah ma tunda tai salla bata fito ba. Nimrah na rungume da magenta da in tana gida haka take manne da ita kamar ɗa, ta zube a kujera Ruky kuma ta nufi kitchen ɗiba musu abinci. Afeef da yafi tsanarsu saboda abinda suke musu dan shima fitinanne ne irinsu yaja tsaki yana miƙawa yabar falon. Sarai Nimrah ta jisa, dan haka ta bishi da kallo cikin rai kuwa tana ayyana (shege mai suffar tsaka. Ka rubuta ka ajiye yau da kumburarren baki zaka kwana a gidan kuwa) a fili kam sai tayi ƙwafar data saka Hanoon kallonta, harara ta wurga mata tana zazzare mata manyan idanunta sai kace Hanoon ɗin bata girmesu ba. Dole Hanoon ɗin ta ɗauke kai dan ita tana da tsoro Ba kamar Afeef ba. Dai-dai nan Biebah ta shigo falon. Daga gidan Aunty Mimi take tun safe. Da gudu Nimrah taje ta rungumeta. Hakama Ruky data fito plate ɗin abincin ta ajiye tazo ta rungumeta. Har cikin ransu suke ƙaunar Biebah, dan itama tana son su matuƙa. Dai-dai nan Mammah itama ke fitowa a ɗaki. Kamar an saita sai gasu Aunty Lailah da yara duka. Nan fa falon ya kacame aka zagaye Small Mom Biebah dake raba musu tsarabar chocolate da tayo musu.......... ✍️