Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 8

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 8

.....before his speech, but his eyes kept looking at Hajiya Hasiba's phone screen until he woke up. Hajiya Hasiba noticed Adeel's look at her phone, but she didn't think of anything until they passed. It happened only at night when Firt lady called that Adeel wants to talk to her, if she is not worried and wants them to meet. Hajiya Hasiba was taken by surprise, she asked if he was okay? The First Lady did not answer saying that it was on a picture that he saw on her phone when they were in a meeting. Hajiya Hasiba rolled her eyes and pursed her lips, before she said, "What about your daughter, Nabeeha? You know she's married, but you don't know who her husband is and what he's trying to do." Showing no concern, the First Lady answered him and said, "Oh God, I repent, what about Hajiya Hasiba, how many marriages are there in this day and age? You're just doing business. Her husband is not arrogant, do you know who Adeel is? Hmmm, I'm waiting for thirty minutes from now to investigate and make a decision. I just sent a message that he will send a car to take you to where he is." Then she hung up her phone. Hajiya Hasiba was silent for a long time, nothing came to her mind and brain

Standalone post703 words

.......Adeel ibn Ubaidullah Qureshy. Cikakken balarabe ne ɗan asali gaba da baya. Jinin sarauta dan kuwa daula babba suke da ita a yankin larabawa. Sannan zuri'arsu zuri'a ce mai ɗunbin dukiya da kaso huɗu na arziƙin Dubai yana da alaƙa da shi. Adeel irin gagararrun yaran nan ne da giyar mulki data kuɗi ke ɗawainiya da su. Dan kuwa iya shegen da yake zubawa a cikin Dubai ba'a magana. Harkar business ce ta haɗashi da Hajiya Hasiba, a dalilin First Lady da suke aminta. Sunyi wani zaman meeting Hajiya Hasiba ta kasance kujerarta kusa data Adeel a meeting room ɗin, irin ta ajiye wayarta a table sai aka irin kirata ɗin nan, bata ɗaga ba kasancewar suna a halin meeting har kiran ya tsinke, dai-dai screen ɗin wayar na komawa yanda yake ƙyaƙyƙyawan hoton Nabeeha dake a fuskar wayar Hajiya Hasiba ya bayyana. Sai ko karaf a idon sa. Cak ya tsaya da bayanin da yake ya zubama wayar ido, abokan meeting ɗin nasa sukaji shiru duk sai suka ɗago suna kallonsa, cike da basarwa ya ɗauke idanunsa ya cigaba da jawabinsa, amma bini-bini idonsa nakan screen ɗin wayar Hajiya Hasiba har aka tashi. Hajiya Hasiba ta lura da kallon da Adeel kema wayarta, amma sai bata kawo komai a ranta ba har suka wuce. Mizai faru da daddare kawai sai ga Firt lady ta kirata wai Adeel nason magana da ita, idan ba damuwa kuma so yake su haɗu. Mamaki ya kama Hajiya Hasiba, ta tambayi ko lafiya? First Lady ta bata amsa da cewar wai akan wani hoto ne da ya gani a fuskar wayarta sanda suke meeting. Sosai Hajiya Hasiba ta zaro idanu tana dafe baki, kafin ta ce, “Kai ranki ya daɗe ɗiyarki ce fa Nabeeha, kin san dai tana da aure kin kuma san waye mijinta da fitinarsa”. Cikin nuna rashin damuwa First Lady tai murmurshi da faɗin, “Yo ALLAH na tuba sai me Hajiya Hasiba, aure nawa ne a wannan zamanin da shi gara babu. Ke dai kawai ai sha'ani. Mijinta kuwa girman kansa na banza ba ko sisi, kin san waye kuwa Adeel? Hummm na baki dama daga nan zuwa minti talatin ki bincika sai ki yanke hukunci. Ni dai na isar da saƙo yace zai turo mota a ɗaukeki a kaiki inda yake ”. Daga haka ta yanke wayarta. Shiru Hajiya Hasiba tai na tsawon lokaci, dan babu abinda ke zuwa mata a zuciya da brain sai fuskar Zak-Shadow. Amma dai ta daure ta fara binciken waye Adeel kamar yanda First Lady ta bata shawara. Tun a ambaton farko kanta ya nema bugawa, jin nasabar gidansu kawai, jin ɗan waye daga zuri'ar daya fito. Data bincika arziƙin zuri'ar tashi kawai bama shi wadda ya mallaka ba bata san ta rikito a kujera ba tsabar rawar jiki. Har lokacin da za'a ɗauketa yayi bata iya ta dawo a hayyacinta ba saboda matsanancin mamaki. Ai babu ɓata lokaci ta shirya a gurguje tabi ɗan aiken. Ai ko kanta da zuciyarta sun nema fashewa saboda inda aka kaita matsayin wajen hutawarsa. Wani mahaukacin azababben garden ne da in ka kirashi da suna aljannar duniya bakai ƙarya ba. Ga masu hidima zagaye da wajen da wasu mugayen masu tsaro ya subahanallah. Ita dai haka aka kaita har inda yake jiki na ɓari. Kallo ɗaya yay mata ya maida kansa ga laptop ɗin gabansa, a haka cike da isa ya nuna mata wajen zama. Sai ta dinga jin kamar ba Adeel ɗin juya bane da sukai zaman meeting, koda yake ko'a jiyan dama yanda yake magana da isa da ƙasaita kasan akwai girma da izza. Amma a yau ɗin ba'a magana. Ya share fin mintuna goma sannan ya gyara zamansa, babu wani tauna harshe ko girmamawa kai tsaye yana kallonta ya furta, “Yarinyar dana gani kan wayarki nake buƙata, ina fatan ba hotonki bane dan naga kuna kama sosai, tsufa kawai zaki nuna mata”. Kan Hajiya Hasiba a ƙasa tana murmurshi ta ce, “A'a bani bace. First born ɗina ce, sunanta Nabeeha”. “Nice...” Ya faɗa cike da iskanci yana ajiye kofin hannunsa. Sai da ya ƙara busar iska ya cigaba da faɗin, “Za'a iya kawo min ita a yau? Zan bada ko nawa ake buƙata, daga biliyan 1 zuwa sama”.